Showing 30001 words to 33000 words out of 80635 words

Chapter 11 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

yi sallama. Irin addu'ar da Umma take yi wa Baffanmu yayin da zai fita kasuwa irin sa na yi masa. Sosai ya ji daɗi ya sumbaci goshina sannan muka yi sallama.


Na zauna a falon ina ƙarewa Kayan cikinsa kallo kaya ne na alfarma wanda kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da hakan. Launin ruwan toka da kuma dogayen labulaye ruwan ƙasa, haka kawai na ji raina a dagule ba rasa me ke yi mini daɗi, duk kyawun kayan sai na ji ba su wani burge ni ba balle ƙyalƙyalin su ya ɗaɗa ni da ƙasa.
Ban motsa daga wajen ba sai na ji sallamar 'yan uwana kafin na miƙe har sun shigo. Da sauri na isa gare su tare da rungume Adda Azima tsam a jikina.


Dangin su Baffa ne da na Umma da kuma na Dada. Sai Adda Azima da kuma Abasiyya. Na gaishe su cike da girmamawa duk suka amsa mini fuskokinsu a washe.


"Ikon sai illahi ke kuwa Aisha ina kika samo waɗanda kujeru masu laushin tsiya?. Kana zama yana lotsewa da kai".


Furucin Goggo Azumi kenan da take matsayin uwa ga Umma domin ita ta riƙe ta har ta aurar da ita bayan rasuwar iyayenta. Na kasa cewa da ita komai illa ƙasa da na yi da kaina ina murza yatsun hannuna da aka feshe shi da ƙunshi.
Adda Azima ta taɓo kafaɗata tare da faɗin"ina kayan ki suke?".


"Su na wancan sashin".


"Kamar ya suna wancan sashin?".


Goggo Azumi ta yi saurin katse ta da faɗin"me ye haka Azima?. Ai ke abin ki taya ta murna ne ma da farin ciki Allah ya yi mata ilhama ta tsinci dami a kale, a wannan zamanin wani na mijin ne zai yi wannan ɗawainiyar ga matar. Ya sauya nata komai lokaci guda, ke dai 'yar nan wallahi sai don barka Allah ya rufa miki asiri ya rage naki ki yi wa kanki karatun ta nutsu, ki yi masa biyayya dai-dai iyawarki".


Har yanzun ban ɗago kaina ba na ce amsa cikin faɗin"in sha Allah ". Suka tashi suka shi shiga ɗaki, banɗaki da kuma kitchen duk suka gani suna ta yaba ƙoƙarin Abdul-hameed da gwaɗa tsaruwar kayan da aka zuba.


Adda Azima ta ja ni ɗaki tare da titsiye ni da tambayar"ki faɗa min gaskiya Aisha ke kika buƙaci wannan kayan daga gare shi, ko kuma kin raina ƙoƙarin su Baffa ne wajen ganin gazawan su game da kayan da suka yi miki?". Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi da kuma sauti kana na sama zarafin faɗin"wallahi Adda ko ɗaya ni ban roƙe shi abinda kike zargi na dashi ba, mahaifiyarsa ce ta ce kayan basu yi wai zata ji kunya a wajen ƙawayenta inda suka ga kayan shi ne ta ce a cire su a sanya waɗanda".


"Ke Aishatu ki ji tsoron Allah mahaifiyarta san ce ta ce haka?". Na ɗaga mata kaina cike da son tabbatar mata da gaskiyar zancen ina mai ɗaurawa da"haka ta ce, da farko ta ce a mayar da kayan gida shi ne ya bata haƙuri aka bar saka su a wancan sashin". Ina iya jiyo bayyananniyar ajiyar zuciyar da ta sauƙe kana ta riƙo hannuna ta riƙe game cikin nata"kar ki gayawa kowa wannan maganar ko da kuwa Umma ko Dada ne suka buƙacin jin inda kayan ki yake ki shauda musu canza miki wasu ya yi, naki an adana miki su. Kar ki faɗawa kowa cewar mahaifiyarsa ce ta ce a cire kayan kin ji?". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau na ce"to in sha Allah zan yi yanda kika je".


"Ina fatan babu wani matsala ko?". Sai da na yi dogon tunani sosai kafin na ce da babu komai. Ta jinjina kanta tana sakar mini hannuna dake saƙale cikin nata.


"To mu zamu tafi, don Baffa ya yi gargaɗin cewar kar a daɗe a gidanki saboda tare kuke da 'yan uwan mijinki kar suka kamar wani abu ne ya kawo mu". Na yi saurin riƙe hannunta da hakan ya sanya ta komawa ta zauna daga yunƙurin miƙewar da ta soma yi.


"Don Allah ku zauna a nan zuwa bayan zurh akwai mutanen da zasu zo, ta ce na zama cikin shiri. Ban san yanda zan yi ba ni kam".


"Ki kwantar da hankalinki za ki iya in sha Allah. Wasu kalan baƙin ne?".
"Ƙawayen ta da wasu daga cikin dangin su".


Ta ɗan yi jim kana ta ce"shikenan bari na yi magana a Goggo Azumi ko ni sai na zauna nan su kuma sai su wuce gidan Abida. Don itama ba a koma mata ba tun daren jiya".


"To".


Muka fito tare da ita izuwa falon sanda muke shigowa ya yi dai-dai da lokacin da Asabe da wasu mata biyu suke shigowa da kulolin abinci da lemukan gora masu sanyi. Suka gaisa da dangina sannan suka fice.
Sun ci sun sha sannan suka fara haramar tafiyan bayan sun yi sallan zurh, a lokacin Adda Azima ta ce na yi wanka.
Ta sanar da Goggo Azumi abinda ke gudana ita ma ta yi na'am akan ta zauna ɗin tare dani. Wata doguwar rigar atamfa kalar ja da aka ɗinka mini daga gida, shi ta fidda mini ta ce na sanya. Ta ɗaura mini kallabi sannan ta zaɓo mini wani laffaya ruwan madara daga cikin kayan lefena ta naɗa mini, ta gyara mini fuskana tsaf tare da feshe ni da turare ba fito na yi cas da ni. Na ƙara fito a matsayin amarya daga sama har ƙasa.


Na kalli kaina a madubi ina jinjina kaina, na juyo ina kallon ta ina cewa"ki cire kayan da za a rabawa dangi da kuma naku daga cikin kayan lefen". Ta waro idanu"ke rufa min asiri, ko safiyar yau sai da Baffa ya yi gargaɗin cewar bai yarda an taɓa komai daga cikin wannan kayan ba. Don haka ki bar kayanki".


Take na ji ni a wani irin yanayi na daban na zauna a bakin ƙaton gadon ina cewa"Baffa fushi yake yi da ni har yanzu, wallahi ko wani irin farin ciki nake yi inna tuna hakan sai na ji gabaɗaya na nema walwalata ba rasa".
Ta tausasa amon muryarta"ba ya fushi dake kuma a sannu a hankali komai zai wuce kamar babu wani abun da ya taɓa faruwa in sha Allah".


Sallamar da aka yi a ƙofar ɗakin ya dakatar da ni daga maganar da na yunƙura da nufin furtawa, Adda Azima ta amsa Asabe ta shigo ta durƙusa har ƙasa "Hajiya ce ta ce azo a sanar dake in kin shirya ki fito baƙinta sun iso".


"To za ku tafi tare ko kuma za ta biyo bayan ki ne?".


"A'a zata iya biyo bayana kawai na zo sanar da ita ne".


"To ga ta nan fitowa".




Adda Azima ta amsa mata, har ta fice daga ɗakin ban ɗauke idona daga gare ta. Adda Azima ta ƙara gyara mini laffayan tare da jawo shi ya ɗan rufe mini rabin fuskata. Ta riƙo hannuna muka fito bayan ta gama jaddada mini cewar na nutsu kuma kafin na yi komai na yi tunani na kuma san yanda zan na amsa musu magana. Muna jiyo tashin maganar mutane a falon ƙasa ƙasa.


Cike falon yake da jama'a muka shigo muka zauna wata mata ta rangaɗa guɗa, muka gaishe su a ladabce duk suka amsa mana.
"Wacece amaryan a cikinku?".


Adda Azima ta yi musu nuni da ni, matar da tayi zancen ta yamutse fuska"yanzu Hajiya duk kyau, nasaba, dukiya da ilmin Abdul-hameed ya rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar. Wannan raino zai yi ko meye?". Duk suka saka dariya kafin Amma ta furta"kin san ance so gamon jini shi kuma wacce ta yi masa kenan".


"Haka ne kam".


Ta kuma faɗa a daƙile, raina ya soso sosai amma na danne zuciyata. Nasiha suka yi mini a taƙaice sannan suka fara cin abincin da Asabe ta jere su a nan cikin falon sashina. Har suka kammala ba su ce da mu mu tashi mu tafi ba. Haka nan muma ba mu gosa ba sai da suka tashi tafiya suka buƙaci lambar asusun ajiyata na ce dasu bani dashi.


Sosai suka ta yin mamaki kwatankwacin irin mamakin da wanda ya ga wani da bai iya wani aikin ibada kuma baya neman sani akan sa. Suka ajiye mini wasu kuɗaɗe suka tafi bayan na yi musu godiya da fatan sauƙa lafiya.


Su na gama fita na janye laffayan daga kaina zan yi magana Adda Azima ta yi saurin taran numfashina"ki yi haƙuri shine kawai abinda zan iya faɗa miki, domin ki kaɗai za ki riƙe ki ci riba a rayuwarki".


Wasu hawaye suka gangaro mini"ki kai kuɗin a su Umma babu abinda zan yi dasu.


"A'a ki ajiye a wajen ki, ki fara nunawa mijinki tukunna. Alabashi sai ki yi duk abinda kike da niyya ki yi dasu".


Lallashina ta yi ta yi da ba ni haƙuri, na sha jin ana yiwa amarya huɗubar haƙuri a mafi yawan lokuta sai dai ban yi tsammanin cewar tun daga wayewar ranar da aka kai ni gidan mijin zan ci karo da hakan ba.


"Ya jikin Hamma Ahmad?".


"Uhmm da sauƙi yau dai ya ɗan ɗaga har ya fito waje". Na dafe ƙirjina"na shiga uku daman sosai ne rashin lafiyan".


Sai da ta gyara zaman ta kana ta ce"da sauƙi dai kawai za a ce". Na yi shuru ban ƙara cewa komai halin da yake ciki ya yi mini tsayiwar ƙayar fiki a raina.
Sai da ta yi sallan Asr sannan Abdul-hameed da wani abokinsa ɗaya suka shigo suka gaisa sosai da Adda Azima.


Ya sanya aka mayar da ita har gida bayan ba yi sallan isha'i na zauna akan sallayan na zuba tagumi. Ya zo ya zauna a gabana tare da naɗe dukkan ƙafafunsa waje guda tamkar mai zaman tahiya. Ya ɗage mini gira" wannan tagumin fa na menene?".


Na sauƙe numfashi tare da yin ƙasa da kaina"babu".


"Ban rabo ki da iyaye da 'yan uwanki don na dunga saki tagumi ba, ina so na ganki kullum cikin walwala sannan bana son ki na ɓoye mi duk wani abunda yake damun ki don Allah kin ji?". Na gyaɗa masa kaina alamar na ji, ya yi ɗan murmushi kana ya ce"kin amsa na ji".


"To in sha Allah".


"Yauwa don kin ga bayan amanar ki da iyayenki suka ba ni, ranar ɗauri aure da safe Hamma Ahmad ya roƙe ni da na kula dake sosai na kuma zamo bango a gare ki da za ki jingina dashi a duk lokacin da kika shiga wani matsala. Na kuma yi masa alƙawarin ƙawata rayuwarki da farin ciki marar yankewa".
Ji na yi tamkar an sanya igiyar kirtani an dai daure ni dashi. Na gaza cewa dashi komai cikin raina ina ƙara jinjina matsayin Hamma Ahmad a gare ni.


"Baƙin Amma sun zo ina fatan komai ya tafi dai dai, ba zan iya tambayanta ba shiyasa na tambaye ki".


Zancen sa ya katse mini hanzari, a hankali na furta"babu wani abu komai lafiya har kuɗi ma suka ba ni masu yawa".


"To Alhamdulillah ina can ina tunanin abinda zai faru". Ya yi ɗan jim kafin na ji hannayen sa akan nawa, na ɗago idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na kasa ɗauke nawa kamar yanda shi ma ya kafe ni da nashi.


"Danginki ba su ce ina kayanki ba da suka zo?".


Na yi nasarar yanje nawa ido gefe guda"basu ce komai da suka tambaya na ce dasu yana ɗayan sashin".


"Kin zaɓin ki ɓoye musu gaskiya kenan?". Na furzar da iska daga bakina"in dai ina sonka ai dole na zama mai kare ta a ko yaushe a kuma gaban ko waye".
Ban yi aune ba na ji ya jawo ni jikinsa yana ga furta mini kalaman godiya. A nan sashin muka ci abincin daren, washe gari da safe bayan mun shirya muka je gaishe da Amma a nata sashin.


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


______________________________


Page 1️⃣7️⃣


Na ga saƙonni ku na addu'o'in da kuka yi mini bisa rashin lafiyan da na yi, na gode sosai da kulawan ku a gare ni. Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.


*********************
Tana zaune akan lallausan kafet ɗin da yake malale a cikin falon tana karatun wani ƙaramin littafin addini a hannunta, da siririn farin gilashi akan karan hancinta. Ta ɗago ido ta yi mana kallo ɗaya tare da mayar da kanta ƙasa. Muka ƙariso muka zaune tare da yi mata sannu.


Sai da ta ja lokacin kafin ta rufe littafin ta ajiye gefe gudu kana ta amsa gaisuwar tamun.


"Sai yanzu ka sama fitowa?". Ya yi ƙasa da kansa yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ke faɗin"Amma wallahi mun makara bamu tashi da wuri ba".


Ta jinjina kanta"ko sallan asuba baka fita ba lafiya?".


"Sanda na tashi har an shiga sai kawai na yi a gida".


Ta yi shuru na wasu daƙiƙu kana ta furta"ba laifi hakan ma ya yi". Tana rufe bakinta Asabe ta yi sallama tare da dire kulolin abincin da ta riƙo a hannunta, ta kuma komawa ta ɗauko plate.


Na yunƙura da nufin taimaka mata muryar Amma ta dakatar da ni.
"Koma ki zauna ba aikin ki bane". Jikina ya yi sanyi ƙalau na koma mazaunina na zauna tare da yin ƙasa da kaina, sai da Anty Alawiyya ta shigo na ɗago na gaishe ta ta amsa mini tana yatsina fuska.


Sai da muka gama cin abincin Asabe ta dawo ta tattare kwanukan tare da gyara wajen tsaf. Na bi ta da kallo sa'ilin da take ficewa daga cikin falon babbar macece sosai don a ƙalla za ta iya yin sa'ar su Umma.


"Ka yi magana da Aminu ne?".


"E na yi kuma ya shaida min cewar har yanzu yana son matarsa, ba zai kuma sake ba akan wannan dalilin. Ni a gani ne ta yi haƙuri kawai ta koma kan 'ya'yanta".


Na shuru ina sauraron su domin na ƙasa fahimtar zancen. Amma ta yi gyaran murya kana ta ɗaura da faɗin"Alawiyya ba zata koma gidansa ba matuƙar wannan matar tana ciki sai dai ya zaɓa ko 'yata ko kuma matarsa".


Sai a lokacin na soma gane kan zancen duk dai akan Anty Alawiyya ce da tun ɗazun ta yi shuru tamkar ruwa ya cinye ta.
Ina iya jiyo ajiyar numfashin da ya sauƙe ya ce"shikenan zan sanar dashi hakan".


Haka suka cigaba da tattaunawar su har ya miƙe yana musu sallamar zai fita. A daƙile ta ce dashi ya dawo lafiya haka nan ma Anty Alawiyya. Al'amin kam daman bamu yi karin kumallon dashi ba.


"Tashi ki raka mijinki".


Na tsinkayi muryar Amma a sama, na miƙe a hankali na bi bayansa har ya isa wajen motarsa yana tsaye alamar shi ma ni yake jira.


Ya kafe ni da ido da hakan ya sanya ni yin ƙasa da nawa ina wasa da yatsun hannuna. Ya yi murmushi tare da faɗin"haka aka ce miki ki zo ki sani a gaba ki yi shuru ki kasa cewa dani komai?".


"Amma ce ta ce na raka ka".


Ya ɗan matso kusa da ni ya sunkuyo da kansa kaɗan ta yanda tsayin mu ya daidaita dashi ya ce"to shikenan sallame ni na tafi". Na watsa masa idanuna ya ɗage mini gira yana ƙara faɗin"ina ji fa".


"Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya. Allah ya tsare ka da dukkan abin ƙi ya haɗa ka da dukkanin alkhairin dake cikin wannan rana. Ya azurta ka da halal ya kuma nisanta da haram komai ƙanƙantarsa".


Ya kasa cewa da ni komai illa tsura mini idon da ya yi babu ko ƙiftawa, sai da na yarfa hannuna a fuskarsa sannan ya dawo dai-dai yana sakin wani ƙayataccen murmushin da ya ƙara fito da ainihin kyawun zubin tsukakkiyar fuskantar da sajensa ya kwanta ya yi luf.


"Na gode da wannan tarin addu'o'in nakin gare ni, idan Allah ya dawo da ni lafiya sai na ba ki wani babbar tsaraba".


Ya ƙare zancen yana lakace mini kunci, har ya shiga cikin motar ina tsaye a wajen. Ya zuge gilashin motar yan kallona ya ce"ki matsa kar na ƙara fancakala miki ruwa". Sosai furucin nasan ya sanya ni sakin dariya, na matsa gefe ya ja motar ya fice daga cikin gidan.


Na sauƙe nauyayyen ajiyar zuciya kana na koma sashina na kwanta, raina cike da kewar yan uwana.


Ban san sanda bacci ya ɗauke ni sai jin sallamar Asabe a ƙofar ɗakin ne ya farkar dani, na yi miƙa ina sakin salati sannan na zo na duɓe ƙofar.


"Hajiya ce ta ce a zo a sanar dake an kammala girkin rana, idan kina buƙata a shigo miki dashi". Na ƙirƙiro murmushi na dasa a fuskata"sannu da ƙoƙari Baaba, amma a bari zuwa anjima kafin shi ɗin ya dawo sai a shigo dashi".


Ta ɗan kallo ni ta ce"ai baya dawowa cin abincin rana ban sa ni ba dai ko yanzu zai fara".
Na yi saurin wayincewa na ce"to shikenan a shigo dashi a iya na mutum ɗaya".


"To"


Ta amsa dashi tana ɗaukar hanyar ficewa, na mayar da ƙofar na rufe ina furzar da iska daga bakina. Jin ana ƙwala ƙiran salla ya sanya ni ɗauro alwala na gabatar da sallan zurh sannan na ɗan calcakale abincin da Asabe ta shigo dashi. Gabaɗaya sai nake ji na wani irin domin a gida sam ban saba cin abinci ni ɗaya ba.




Wanka na yi na saka wani doguwar rigar yadin material na nufi sashin Amma. Tana kan sallaya tana lazimi na tarar da ita na zauna har ta gama muka shafa addu'ar tare.


Tana tashin na yi saurin miƙewa na naɗe sallayan na ajiye, sai da ta zauna sannan na zauna ina yi mata sannu da huta, ta amsa mini.


"Lafiya?".


Tambayar da ta watsa mini ya cikina kaɗawa. "Daman na zo ne ko kuma buƙatar ayi miki wani abun sai na yi miki".


Sai da ta yi ɗan jim tana ɗauka makunnin na'urar sanyaya ɗaki dake cikin falon ta kunna shi, kana ta furta "ba na buƙatar komai sai dai ina so na yi miki wasu tambayoyi".


"Na yi alƙawarin sanar dake dukkan gaskiyata akan dukkan tambayar da za ki yi mini".


Ta jinjina kanta"yaushe kuka haɗu da Abdul?".


"Mun haɗu dashi a lokacin bikin Hammana a hanya ya fancakala mini ruwan kwata a jikina, tun daga lokacin yake bibiyata har ya zo gidan mu ban sani ba".


Shuru ya biyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login