Showing 15001 words to 18000 words out of 80635 words

Chapter 6 - BOYAYYAR MANUFA Book Complete Document by Maimuna Tijjani Iyam .txt

ni dai roƙo na mu bi komai a hankali, mu yiwa yarinyar nan adalci mana kar mu tauye mata haƙƙinta don kawai zuciyoyinmu su yi fari. Yaron nan shi ya ce ta je ta yi da istikara to menene laifinta bayan gudanar da hakan ta ji cewar ba ta son shi. Bamu ilmi fa mu Yaya duk yanda muka kai ga son haɗa yaran nan aure babu wanda muka iya matuƙar Allah bai tsara su zamo ma'aurata ba. Ko yanzun mun cika burin mu tunda mun haɗa zuri'armu aure, ga Abubakar da Azima sannan in sha Allah ga Adnan shima da Abida shin ko hakan kaɗai bai isa ya sanya mu godewa Allah ba?".


Furucin Baba Alhaji kenan da ya tursasa mini sakin nauyayyen ajiyar zuciya ina sulalawa ƙasa na zauna dirshan. Na kifa kaina akan gwiwata ina sakin wani kuka marar sauti. Na fahimci tunanin Baffa shi ne daman can bana son Hamma Ahmad tabbas haka ne amma bayan da na yi istikata haƙiƙa na ji ya ƙara cirewa daga raina.
Har na ji motsin su Baffa su na ficewa ban ji Umma ta ce ko kanzil ba, na yi tunanin fitar su zai sanya ta shigowa ta ji daga gare ni sai na ga saɓanin hashashena. Abasiyya ma ficewa ta yi ba tare da ta ce da ni komai ba, hakan ya sanya ni ƙara sakin wani kukan mai ƙarfin gaske.


Ban san tsawon lokacin da na ɗauka zaune a wajen ina kuka ba, har sai da na ji ana ƙiran sallan zurh sannan na tashi ina jin wani jiri yana ƙoƙarin mai da ni ƙasa. A daddafe na fito na yi alwalan na koma ciki na yi salla ina jin wani zazzaɓi mai zafi na ƙoƙarin rufe ni.


Jin motsin Umma ta ta tsakar gida ya tilasta mini fitowa, tana zaune tana tsintar yakuwa na iske ta na zauna ina yi mata sannu ba ta tanka mini ba. Ban ƙara tsintar kaina cikin tafkin mamaki ba sai da na kai hannu zan ɗauki yakuwan domin tsintar da dakatar da ni"ajiye min kayana ban nema ki yi min ba, ki je ki yi kwanciyarki kawai".


Kamar yanda maƙeri yake dukan ƙarfe haka na ji tamkar ana sanya guduma ana dukan ƙirjina. Idanuna cike da hawaye na ɗago ido na kalle ta sam ba ni take kallo ba ta mayar da hankali ga abinda yake gabanta.
"Umma don Allah ku yi haƙuri wallahi ba laifi na ba ne, ba n...". Tun kafin na dire zancen ta katse ni" bana buƙatar jin komai daga gare ki 'yar nan". Hawayen da suka ciko mini kurmi idanu zubowa. Na kai hannu zan riƙo nata ta janye ban san lokacin da ya cilla wani uban ihu ba ina faɗin"na shiga uku ni kam na shiga uku".


Na tashi a zabure na faɗa ɗaki na ɗauko jikan da na kasa sanya shi a jikina, na lulluɓa shi a kafaɗata. Kamar zautacciya haka na fita ina tafe ina kuka na ɗaura hannayena a kaina. Na faɗa cikin gidan tamkar wacce aka jefo Dada da Adda Abida suka tashi a tare su na tambayata lafiya. Na isa ga Dada ina kwantar da kaina a kafaɗata.


"Me ya faru?".


Ban amsa ba ta har muka zauna na zamar da kaina izuwa kan cinyarta, a hankali take bubbuga bayana tana mai cigaba da cewa"me ya faru ne? Ko Umman naku ce ba lafiya?". Sai a sa'ilin na ɗago fuskata muryata har ta dishashe"Umma ta daina Kula ni yaya zan yi Dada?". Na ƙare zancen ina ƙara fashewa da wani kuka tare da mayar da kaina kan cinyarta.


"Ki yi haƙuri a hankali zasu fahimta cewar ba laifinki bane, dole yanzu da suke cikin ɓacin rai sai kin yi haƙuri da su".


Ban tanka mata illa sausauta kukan da nake yi da yi, haka ta cigaba da kwantar mini da hankali tare da nuna mini cewar komai zai daidaita da iznin Allah. Zancen da Adda Abida ta furta ya sanya ni ɗago kaina babu shiri tare da zube rinannun idanuna akan fuskarta da take yatsina shi yayin maganan.


"Ai daman duk tsuntsun da ya ja wallahi shi ruwa yake duka. Ta yaya daman za ki yi tsammanin cigaba da samun yanda kike so bayan kema ba ki yi musu abinda suke so. Ki yi ɗamara domin wannan shi ne wasa farin girki".


Tsawa Dada ta doka mata da ya tilasta ta haɗiye raguwar zancen ba tare da ta furzo mini su ba.
"Ba ki da hankali ashe Abida? Ko kin manta wacece kike gayawa wannan kalaman?. Kema ashe duk taron tsintsiya ne babu shara, ke dole aka yi miki da Adnan? In ce dai sai da kika furta kina son sa sannan, to me yasa ita ma ba za a bata damar zaɓan wanda take so ba, laifi ne don ta faɗa abinda ke zuciyata? Kar ki kuskura na ƙara yin kin maimaita irin haka don ranki zai yi mummunan ɓaci, tashi ki ba ni waje shashasha kawai".


Ba tare da ta ko kalle gefen da nake ba ta tashi ta shige ɗaki, na riƙo hannun Dada gam na riƙe"kin gani kin gani ko Dada. Kowa wani kallo daban yake yi mini yaya zan yi da raina, ina zan sanya kaina na ji sanyi don Allah Dada ki faɗa mini". Lallashina ta cigaba da nusar da ni cewar duk abinda ya yi farko tabbas ƙarshensa yana nan zuwa.


A jikinta na wuni ko nan da can bata motsa ba saboda zazzaɓin da ya rufe. Ko abinci na kasa ci ruwa ina sha nake dawo dashi. Tunda na zo Abasiyya bata kula ni ba balle tazo inda nake har ta yi mini sannu ko taya ni jimanin halin da nake ciki.
Sai da aka yi sallan Asr, magrib ta fara kawo kai Dada ta ce na je ni gida bai kamata duk abinda Umma ta yi mini na guje ta na ƙi komawa ita ma in aka yi salla zata shigo su yi magana. Na ɗan dakata ko Abasiyya za ta ce zata raka ni amma na ga babu alamar za ta motsa daga inda take, dole na ja ƙafafuna na yi gida.


Ko sannun da na yi mata yanzu ma bata amsa ba, na ji wasu hawaye suna rige-rigen fitowa daga idona. Zan yi magana ta ɗaga mini hannu dole na haɗiye zancen a cikina na tashi duk da bana jin daɗin jikina na ɗauki tsintsiya na fara share tsakar gidan. Ina gamawa ana ƙiran sallan magrib.


Na yi sauri sawa Umma ruwa a buta na ajiye mata sannan nima na zubo wata butar na fara. Ina shafar kai na ji an yi kutubal da butar gabana na ɗauro da sauri don ganin waye.
Na miƙe a sanyaye ganin Abasiyya tsaye a gabana tana kuka. Kafin na kai ga tambayar ta me ke faru, ta riga ni fara magana.


"Hankalinki yanzu sai ya kwanta za ki kashe shi ki huta, wallahi kin ba ni mamaki da kika saka yin Wannan sadaukarwa ga Hamma Ahmad kin san tsananin farin cikin da ya shiga kuwa sanda na sanar dashi cewar kin amince masa. Amma duk da haka sai da kika karya masa zuciya ga shi can ya yanke jiki ya faɗi a kasuwa a dawo shi bai san inda kansa yake ba, wallahi idan kika yi sanadin da ya mutu ko ya kamu da wani ciwon ba zan taɓa yafe miki ba".


ƁOYAYYAR MANUFA


©️ Maimuna Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 0️⃣9️⃣


Kafin na yi magana Umma ta riga ni furta"me ya same shi?".


"Yana can an dawo dashi daga kasuwa ya faɗi ko motsi ba ya yi".
Ko hijabin Umma ba ta gama sawa a kanta ba ta kamo hannun Abasiyya za su fice, na zabura zan bi su har mun isa zaure Umma ta juyo ta yi mini wani kallo tare da tsawan da ya sanya ni saurin sunkuyar da kaina ƙasa jikina yana rawa tamkar mazari.


"Ina za ki je? Ko so ki ke ki je ki baƙin cikinki ya ƙarisa shi? Idan kika leƙa ko ƙofar gida ba da yawuna ba".


"Don Allah ki bar ni na je".


Na faɗa ina ƙoƙarin isa gare ta zan kama hijabinta ta yi saurin buge hannuna suka fice, a wajen na durƙushe akan ƙafafuna ina sakin wani kukan mai tsuma zuciya. Na sha kuka a wajen har sai da kaina ya fara sarawa, da ƙyar na ja ƙafafuna na tashi na koma ciki ina tafe ina haɗa hanya tamkar bugaggiya.


Na faɗa ɗakin kwananmu ina mai cigaba da sakin wani kukan, ina jin kaina yana sarawa da matuƙar ƙarfi, a gigice na sauƙe wahalallen ajiyar zuciyar da ya tafiyar da kukan da nake yi.


"Ya Rabbi".


Na furta haƙwarana suna datse harshena, wani hali Hamma Ahmad yake ciki shi ne babban abinda nake buƙatar sani a halin yanzu fiye da komai. Sai na yi yunƙurin tashi domin na je na dubo shi sai na tuna gargaɗin Umma a gare ni dole na koma na zauna. Ganin zaman ba zai fishshe ni ba ya sanya ni tashi na je na fita na yo alwala nazo na fara gudanar da sallan magrib sannan na ɗaura da nafila.


Na daɗe ina yin sallan da ban san adadin yawan raka'o'in da na yi ba, sai da aka yin ƙiran sallan isha'i sannan na tsagaita. Na yi sallan isha'i sannan na kwanta akan sallayan ina maida numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceto rai. Na kasa motsa lwa daga wajen haka nan izuwa yanzu na kasa yin hawayen da nake yi ina jin daɗi a cikin ƙalbina.


Har karfe tara ya buga babu wanda ya shigo hakan ya sanya ni komawa zaure na zauna ina jiran dawowansu.


"Me kike yi a nan wajen?, tashi ki shiga gida".


Na yi Muryar Hamma Adnan tamkar a mafarki, na yi figigi na buɗe idona ina ƙoƙarin miƙewa ya komar da ni na zaune.
"Ina yake ina Hamma Ahmad ɗin?".


Na faɗa cikin dushashewar muryar da yake nuna cewar mai shi ya ci kuka ya ƙoshi, sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya furta"jikinsa da sauƙi sosai, ko awa biyu ma bamu yi a asibitin ba aka sallame shi. Ƙarin ruwa kawai aka yi masa sai kuma magangunan da aka ba shi".


A bayyane na sauƙe ajiyar zuciya"Alhamdulillah ina so na je na duba shi, amma Umma ta hana ni".
"Ki kwantar da hankalinki ai jikin ma da sauƙi, su Umman ma yanzu zasu dawo tashi ki shiga gida".
Ciki muka koma yana tambayata na ci abinci na ce masa a'a da kansa ya zubo mini abincin ya ajiye mini tare da umartata akan na soma ci. Sai da ya yi mini jan ido kafin na kai lomar farko cikin bakina.


Ina cikin ci Umma ta shigo duk muka yi mata sannu da zuwa, ba ta amsa mana da kalamai ba illa ɗaga mana kai da ta yi tana shigewa ɗaki. Da ƙyar nake haɗiye abincin ta maƙoshina da nake jin tamkar ina haɗiyar ciyawa mai cike da ƙarangiya.
Hamma Adnan shi ya yi ta kwantar mini da hankali ta hanyar furta mini cewar jikin da sauƙi, ko da na yi shirin kwanciya sam bacci ya gagari idanuna sai faman juyi nake yi idanuna ƙas tamkar na soyayyan kifi. Furucin da Abasiyya ta guntso ta fesa mini suna amsa-kuwwa a nau'rar naɗar sautina.


Tabbas a 'yan tsakanin nan Hamma Ahmad ya nuni mini kulawa tsantsa sai dai a ba a yi wa zuciya dole musamman wajen tusa soyayya. Yanda na ga rana haka na ga dare ƙiran sallan assalatu farko kuwa a kunnuwana ya fara sauƙa na tashi jikina sam babu ƙwari na je na yi alwala. Na zo na fara sallan ina iddarwa na kifa kaina a bisa gwiwana raina cike da tarin damuwar da na kasa warware shi.


Sai da gari ya fara yin haske na fito na fara yin sharan filin tsakar gidan, babu wasu kwanukan wanke-wanke domin daren jiya ni ɗaya jal na cakali girkin da Umma ta yi, don haka kwano ɗaya na wanke. Na zauna a dakalin ƙofar ɗakin kwananmu na zabga tagumi da hannuwa bibbiyu.
A haka Baffa ya fito ya iske Umma ta na biye dashi a baya suka fito, na zube a gabansu tamkar baiwa ina gaishe su fuskokin su babu yabo babu fallasa suka amsa mini ba tare da sun ƙara cewa da ni komai ba. Hakan ya sanya ni tashi na koma mazaunina na zuba musu ido suna zantawa akan jinyar Hamma Ahmad ɗin.


"Allah dai ya kiyaye gaba amma tabbas an auna sa'a. An kuma tsallake rijiya da baya domin yanda mai babban suna ya yanke jiki ya faɗi a rumfarsu babu wanda ya yi tsammanin abin zai zo da sauƙi haka. Haka aka kawo mana shi ranga-ranga tamkar matacce".


Umma ta jinjina kai cike da damuwar da ta bayyana ƙarara akan fuskarta"Amin kam Allah kuma ya bashi lafiya ya sauya masa da mafi zama alkhairi a gare sa".


"Amin zan fita kasuwa amma da wuri zan dawo". Addu'ar Allah ya kiyaye ta yi masa kamar kullum har zai fice na yi saurin katse shi da faɗin"Baffa idan ka ba ni izni ina so na je na duba jikin nasan, tun jiya na so zuwa Umma ta ce na dakata".


Sai da ya yi jim kafin ya amsa mini a gajarce da hakan ya bani tabbacin cewar har yanzu yana fushi da ni kamar yanda Umma ma take fushi dani.
"Za ki iya zuwa".


Na zame daga zaunen da nake na zuba gwiwoyina a ƙasa ina godiya. Hamma Adnan ya fito suka fita tare. Sai da na ɗauko hijabina zan fita na je zan yi sanarwa Umma. Na tsuguna a gabanta"na shirya zan je".


"Ki saka kunne ki saurare ni da kunnen basira saura idan kika je ki ƙara furta masa wani zancen da zai ƙara haddasa masa wani jinyar. Wallahi akan Ahmad za ki ga tsananin ɓacin raina da ba ki taɓa ganina tunda kika zo duniya".


"To in sha Allah za a kiyaye".


Na tashi na fita ina tafe ina hawaye har ba isa gidan, Abasiyya ce kawai a tsakar gidan tana jan ruwa a rijiyar da sai babu ruwa a famfo ake buɗe ta. Fuskata da maɗaukakiyar mamaki na kafe da kallo don a kalla na yi sallama ya fi baki uku amma ko a jikinta wai a muntsine kakkaura bata amsa mini ba.


"Abasiyya kina ji ina sallama kika share ni?".


Sai a lokacin ta ɗago ido ta yi mini kallon da na kasa gano manufarsa, ta zara gugar cikin rijiyar tana jawo ruwar ta ce"ai ba dole sai na amsa a fili kin ji ba, tunda ina da damar amsawa a cikin zuciyata".


Wasu hawaye suka kwaranyo mini" Hamma Ahmad fa?".
Ta buga mini tsaki"yau kuma baƙuwa kika zama a cikin gidan?. Ina ce da in kin zo kai tsaye kike shiga duk inda kike so".


"Allah ya ba ki haƙuri, Abasiyya ki yi haƙuri".


Ta buɗe baki za ta fara zance cikin tsiwa, na ji ƙarar sauƙar mari da ya bada sautin tas. Ihun da ta saka suka sanya ni saurin ɗago idona don ganin wanda ya ɗauke ta da wannan marin.
Anwar ne tsaye yana huci ya nuna ta da 'yar manuniyar yatsarsa"ke kina da hankali kuwa? Wannan ba ta fi ki ba ne?. Ko hauka kika yi?. Ki nutsu ki koma cikin hankalinki domin komai ya faru gaba take dake".


Ta yi jifa da gugar hannunta ya faɗa cikin rijiyar tana a sakin kuka tare da shigewa ɗaki. Ya tako ya iso gabana"ki yi haƙuri in ji?". Kaina kawai na ɗaga masa"daman na zo duba jikin Hamma Ahmad ne".


"Ki shiga yana ɗakin zaure".


Kaina na kuma jinjina masa, na juya na nufi zauren kamar kullum sai da na yi sallama ya bani iznin shiga sannan na shigo na zauna a inda na saba zama a duk sanda na zo ɗakin.
Kafin na yi magana ya riga ni"na yi fushi tunda sai yanzu ma za ki zo duba ni".


Na ƙara yin ƙasa da kaina"tun jiya na so zuwa sai kuma su Umma suka zo, babu wanda za a bari a gidan shiyasa amma yaya jikin?.".
Ina jin taƙaitaccen murmushin da ya saka da ya fi kama da na dole kana ya ce" ba komai kar ki damu, jiki da sauƙi alhamdulillah".


Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya cikin karayar zuciya na furta"ka yi haƙuri Hamma Ahmad wallahi ni ma ba yin kaina ba n...". Ban ƙarisa ba ya katse ni"ba komai Aishatu na yarda cewar Allah ne bai yi za mu zama ma'aurata ba kuma na fahimce ki. Kawai kin san zuciya bata da ƙash,i na kasa ɗaurewa ne a lokacin har hakan ya afku".


Ya tsagaita kana ya sauƙe numfashi ya ɗaura da"ko wani gaskiya tana da ɗaci sai dai tabbas tana kwantar da hankali. Ni na roƙe ki akan kar ki ɓoye min komai ki ke ji a ranki game ni, to bai kamata na ga laifinki bayan ki sanar da ni abinda ni da kaina na roƙa ba. Ina miki fatan alkhairi da kuma addu'ar Allah ya ba ki miji na gari wanda zai so ki so na gaskiya koda rabin irin son da nake yi miki ne".


Hawaye suka zubo daga idona ina musgutawa na ce"ka yi haƙuri ba zan taɓa daina baka haƙuri ba Hamma Ahmad, har ƙarshen numfashina".
Sai da na cire rai da samun amsa daga gare shi sannan na ji ya soma faɗin"ban riƙe ki a zuciyata ba Allah ne shaida, sai dai dole zan shiga cikin yanayi amma duk abinda aka sanya haƙuri, dangana da miƙa wuya ga Allah komai zai wuce har ya zama tahiri. Zan tsaya tsayin daka a matsayina na ɗan uwanki wajen ganin kin auri duk wanda kika kawo kina son shi matuƙar da ya cike dukkan sharruɗan da ake nema yayin ɗaura aure".


"Na gode kai ma Allah ya ba da wacce ta fi ni".


Dariya ya yi sosai mai sauti"ba na jin akwai wacce zan iya ƙara so a rayuwata balle har soyayyar ta kai mu ga yin aure. Zan zauna haka na yi ta bautawa ubangijina har na iske wa'adina".


Jikina ya yi sanyi ainun da ina da dama da na sharewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login