Showing 6001 words to 9000 words out of 82877 words

Chapter 3 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2747

kamar yadda ya saba kullum yana komawa gida da rana idan ya ci abinci aka yi la,asar sai ya koma wajen hayar sai kuma dare.Da ya ta shi ma ta layin gidan na su Zahra ya biyo ta ?ofar gidan ya wuce wai ko Allah zai sa ya hangota ko da daga nesa ne hakan zai sa ya ji sanyi a cikin zuciyarsa.Amma haka ya zo ya wuce ta ?ofar gidan na su ko mai kama da Zahra ma bai gani ba.


Duk da hakan ma ya dai ji daWi a ransa ganin ya yi tozali da gidan da Zahrarsa ke ciki >?? amma fa in ji shi.


***************

Ammi ta yi farinciki sosai da abinda yaron kirki ya mata tunda ba ta san ko da sunanshi ba,amma?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kuma ga shi ya yi sanadin fitar su daga cikin ?unci da tashin hankalin da su ka samu kan su a ciki.Sai godewa Allah ta ke yi a ranta ta na kuma sanyawa yaron da ya taimake su albarka tunda shi ne sila.

Kallon 1k Win da ya ba su ta yi tana nazari da tunanin abin da za ayi da kuWin yadda har za a siyi abinda za a juya daga ?wandala su koma naira biyar.KuWin wajen Zahra ta Wakko cinikin doyar da ta yi jiya 350 da su ta haWa aka siyo flour da barkono da maggi sai mai wainar flour ta yi aka daka yaji me Wankaran daWi wanda ya sha maggi da kayan ?amshi.

Tun da Zahra ta fita tallar ko awa Waya ba ta yi ba sai gata da bokitin wainar ta ?are har ana nema.Wannan dalilin ne ya sa Ammi yanzu sau biyu ta ke yin wainar a rana dan wani lokacin ma kafin a fita da ita ta ke ?arewa a gida.Allah y sanya albarka a sana,ar su ci su sha har su yi sauran bu?atu.Yanzu ba su da wata damuwa dan har uniform Win Zahra da ya yage sanadin hakan ta daina zuwa scul,yanzu an Winka mata tana zuwa makaranta abinta dama day take yi tana aji biyar na secondry.Dama yanzu wainar ma ko tallar ba a fiya fita da ita ba a gida ta ke ?arewa dan haka makaranta ta ke tafiya,ita ma Hauwa,u a primary 2 ta ke.



*Bayan sati biyu*


MASHKUR da so ya yiwa mugun kamu ne ya rasa inda zai tsoma ransa kullum cikin tunani ya ke da kuma son ya sa Zahra a idanunsa.Zuwa wannan lokaci son wacce ba ta ma san yana yi ba ya gama masa katutu ya kuma masa dabaibayi da Waurin goro.wanda ya ke ganin duk duniya babu mai warware masa ?ullin da so ya masa face wacce son nata ya kamashi.


Da la,asar sakaliya ne ya shirya tsaf cikin dogayen kaya sun yi matu?ar karSarsa tare da fito da kyawunsa.Bai sanya hula ba hkn sai ya ?ara fito da kyansa saboda bayyanar kwantaccen gashin kansan ba?i mai she?i,bai Wauki machine Win ba sai ya taka da ?afarsa zuwa gidan su Zahra.


Tafiya ya ke amma gabansa sai dukan tara tara ya ke yana kusantar gidan faWuwar gaban nasa na ?ara tsananta.Sai da ya je ?ofat gidan ya ja tunga ya tsaya sai sannan ya fara tunanin idan ya shiga gidan me zai ce ya kawoshi?? shin ko zai ce saboda ya zubarwa Zahra awara ne shine ya zo ya sake ba su ha?uri? haka ya yi ta tunane tunane amma ya kasa samun takamaiman abinda zai faWa amma a zuciyarsa yana jin ?aunar Zahra na ?ara azalzalarsa yadda ba ya jin zai iya tafiya ba tare da ya yi tozali da ita hakan ba ?aramar cutar da zuciyarsa zai yi ba tabbas so akwai radaWi da zafi a zuciya ta yadda idan har baka samu ka ambatawa wanda zuciyar taka ke muradi ba cutuwar sai da zuciyar masoyin zata tsinci kan ta a ciki sai ya fi ciwo.

Tunanin hakan ya sa ya tattaro gaba Waya jaruntarsa da kuma karfin hali ya tunkari zauren gidan na su Zahra a cewarsa ko da a cikin gidan ne ya ?ir?iri dalilin zuwansa da dai a koma bai ganta ba.

"Assalamu Alaikum"Ya ke sallama daga cikin zauren gidan.sai da ya yi sau biyu sannan ya ji muryar Hauwa,u ta amsa daga cikin gidan.

"Wa alaikumus salam waye ? Indai waina ce ta daWe da ?arewa Ta amsa sallamar tare da jefo tambayar da amsa a lokacin da ta nufo zauren.

"Mashkur ne"Ya masa mata.

"Lah Yaya mai kuWi kai ne a gidan na mu?Wallahi rannan nake tambayarka wurin Yayata na ce mata ina wannan mutumin da ya bani kyautar dubu guda amma sai cewa ta yi bata sani ba kuma kar na ?ara tambayarta" Ta kai ?arshen maganar tana washe baki kamar gonar auduga.

Dariya ce ta suSuce masa sai da ya tsagaita ya kalleta ya ce

"Ai bn san kina nemana ba da tuni na zo kin ganni"

"Eh wlh dama fa sunanka zan tambaya sai kuma yanzu na ji ka faWa ashe sunanka Yaya Mashkur"



"Eh ina Mama?"

"Lah ba Mama sunanta ba Ammi sunanta kuma tana bayi"

"Oh ai ban sani ba amma yanzu na sani "
"Ni na Wauka ma masu siyan waina ne kasan yanzu Ammi ta daina siyar da doya,wainar fulawa ta ke yi Yaya Zahra ta daka yaji me...


"To uwar ?an surutu kamar wacce ta ?one akai, faWi ba a tambayeki ba" Zahra da dawowarta kenan daga makaranta sanye da uniform ta faWa tana aika mata wani hararar ki ka ?ara magana ni da ke ne.


Wani daWi ne ya ziyarci zuciyar Mashkur lokaci Waya ya ji duk wani nauyi da ya danne masa zuciya ya gushe,jin daddaWan amon muryarta mai ratsa zuciyar masoyi, a take ya sauke wata sassanyar ajiyar.Yana jin muryarta fa ya ji wannan yanayin to ina ga ,in ya yi tozali da kyakykyar fuskarta kuma, dan ya bata baya ne muryarta kawai ya ji bai riga da ya ganta ba.SaSanin Hauwa,u da ta ke fuskantar inda Zahrar ta ke tahowa.


A hankali ya juyo juyo zuwa inda ta ke akan fuskarta idanuna suka sauka ,Zahra kwa na ganin shi ne ta yi saurin sunkuyar da kanta ita ta Wauka ma su siyan waina ne amma sai ta ga mutumin da ba ta yi tsammani ba,mutumin da har abada ba za ta taSa manta karamcinsa gare su ba mutumin da ya taimaka musu a lokacin da su ke ?ololuwar neman taiakon shi sa yana juyowa ta ji nauyinsa.Shi kwa gani ya yi kamar an ?ara mata kyau ne gani ya yi ta canja masa gani ya yi ta wuce yadda ya ke ta tunano fuskarta da ya gani a waccen ranar.


"Ina wuni" Muryarta ta katse masa tunanin tsabar kyan da ta ke da shi duk da kyan nata ba shi ne abin da ya Warsa masa son ta ba a cikin ransa ba, a,a tarbiyarta da kawaicinta girmama na gaba sannan uwa uba ha?uri wanda ya fuskanci hakan a ranar da ya Sarar mata da doya da ta kasa ce masa ko da uffan ne.


"Lafiya ?alaw ?an makaranta an dawo" Cewar Mashkur cikin zumuWi.

"Eh "ta masa masa har lokacin kan nata a sunkuye.

"Am ki duba min ko Ammi ta fito mu gaisa "Ya ce har lokacin idanunsa a kan ta.


"Na ji ?aran buWe ?ofar bayin bari na faWa mata"Hauwa,u ta ce tana juyawa cikin gidan.

"Zan wuce" Ta ce a hankali, da ya ke Mashur a setin hanya ya ke kuma zauren ba wani girma ne da shi ba.

"To to Bismillah" Mashkur ya faWa yana matsawa gefe yana kuma ji a ransa cewa ina ma kar ta daina magana,ina ma dai ta dinga zance kar tai shiru dan ya dinga sauraren muryarta yana jin daWi da wani shau?i a zuciyarsa.Ai kuwa haka ta zo ta giftashi ta wuce shi kuma yana binta da ido kamar dai an ce wannan ne gani na ?arshe da zai mata a duniya.Haka ya koma ya jingina da jikin katanga yana mai lunshe idanunsa tare da huro iska mai dan zafi daga cikin bakinsa, yana a haka ya ?ara jiyo muryrta a dodon kunnensa.

"Ammi ta ce ka shigo daga ciki"

Idanun ya buWe da sauri dan tunaninsa gizo ne ta ke masa ,amma ganin ya sauke idanun akan ta hakan ya tabbatar masa da zahiri ne.

"To "Cewar Mashkur yana bin bayanta zuwa cikin gidan.


Da sallama ya shigo gidan ,Ammi da Hauwa,u su ka haWa baki wurin amsa masa akan tabarmar da Ammi ta nuna masa ya zauna ita kuma Ammin tana kan kujerar tsugunno ta mata.Gaishe da Ammi ya yi ta amsa masa cikin jin daWi da nuna farinciki.Iyayensa ta tambaya ya amsa mata da duk suna lafiya.

Bayan gaisawar shiru ne ya Wan biyo baya kafin daga bisani Ammi ta masa godiyar kuWin da ya baiwa Hauwa,u ranar nan nuna mata ya yi babu komai.Sosai ta yaba da hankali da tunanin yaron.



"Da ma wucewa na zo yi shi ne na biyo mu gaisa" Ya ce yana sunkuyar da kansa ?asa dan sai da ya shigo cikin gidan ma ya ji gaba Waya nauyi da kunyar Ammi sun kamashi.


"Allah sarki amma na ji daWi ?warai da gaske da wannan karramawa "Ammi ta faWa cikin farinciki.


"Ba komai" Cewar Mashkur a hankali.


"Ga ruwa Yaya Mashkur mai kuWi" Hauwa,u ta faWa tana ajiye masa jug da kofi a gabansa.

"Nagode"Ya ce yana Wan murmushi dan yarinyar ba dai surutu b kuma bada dariya.Ita dai Ammi da ido ta bi ta dan Hauwa,u sai dai addu,a.



Bayan ya Wan jima ya yiwa Ammi sallama ya tafi ransa fari ?al duk da bai sake ganin mutuniyar ta shi ba dan tun sanda ta shiga Waki bata ?ara fitowa ba...





*NEXT PAGE*



*MAMAN AFRAH***>?p?=?
?=??

* *KISHIYA* *NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



*Na*

*Mmn Afrah*



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE 6??



----------- Tun daga wannan rana zuciyar Mashkur ta rasa sukuni kullum cikin za?uwar san yin tozali da Zahra ya ke hakan ya sanya daga ya Wauki kwanaki kamar sati biyu haka sai ya ?ir?iri zuwa gidan Ammi dan kawai ya ga Zahra.Ita kuwa Zahra ba maganar da je haWasu sai gaisuwa wataran ma idan ya zo ba ya ganinta ta tafi talla wataran makaranta Ammi ce ta fara fahimtar inda ya dosa domin idan ya zo in Zahra ba ta nan sai ya yi ta Wan kalle-kalle kamar dai akwai wani abun da ya ke nema.Ko in Zahra na nan ya yi ta satar kallonta wannan dalilin ya sa Ammi fahimtar abinda ke tattare da Mashkur Win.


Ta yi farinciki sosai saboda ta yi matu?ar yabawa da hankali da tunanin yaron ga kuma uwa uba tarbiya, sai dai tana son Zahranta ta yi zurfi a karatu duk da ba wani hai garesu ba amma tasan Allah yana tare da su.


*BAYAN SHEKARA ?AYA*


Zahra sun kammala secondry school ta ci exam sosai dama Zahra akwai ?azo sosai ta ke da maida hankali a karatun ta.Yanzu sosai ta ?ara cika komai na ta ya ?ara bayyana kyaunta ya ?ara fitowa idan ka mata kallo Waya ba za ka so ka Wauke ido akanta ba.Sosai ta ke da kyan fata she?i da kyalli idan ka ganta sai ka Wauka ?ar gidan wani hamsha?in me kuWi ce yadda alamun hutu suka zauna a jikinta.

Maza ne suka yo mata caaa abin har tsoro ya ke baiwa Ammi kullum cikin zuwa sallama da Zahra ake hakan ya so ya Wagawa Ammi hankali duk da ta san irin tarbiyar da ta baiwa ?arta amma duk lokacin da ?a mace ta ke a wannan mataki dole sai uwa ta yi takatsan tsan ,sannan ta maida hankali da sanya ido sosai akan ?arta.Domin kuwa mataki ne da ya ke sanya budurwa ta ji itama eh macece tunda za ta fara kula samari idan ba ,a barta ta ri?e waya to lokaci ne ta kai matsayin da za ta fara ri?ewa waya kuma ita ce matakin komai.


Bare yanzu zamani ya Saci dole sai iyaye sun ?ara sanya ido sosai akan tarbiyar ?a?ansu sannan sun ?ara sanin da wane abokai ko ?awaye ?a?ansu ke ma,amala da su domin idan kana so kasan waye mutum ko kuma waye Wanka ko ?arka to ka bincika waye abokinsa ko wacecec ?awarta to duk halin da ka samun abokin Wanka ko ?awar ?arka da shi to shi ne halayen da naka Wan yake da su=?L? Allah haWa kowa da aboki na gari.

Loakacin ne Mashkur shi ma ya fara tunanin sanar da Zahra sirrin da ke cikin zuciyarsa ko Allah zai sa ta amince da shi gudun kar wani ya masa wuff da ita.Dan ya lura yanzu samari na dandazon zuwa neman a kira musu ita dan ma dai wani lokaci in ya je gidansu Zahra ya kan ji an zo kiranta sai ya ji Ammi ta ce bata nan ta fita duk kuwa da Zahra tana nan ba kuma komai ke sai ta yi hakan ba sai lura da cewa yanzu masoyi na gaskiya ya yi wahala wa su kawai dan su yi soyayya kawai ba dan aure ba wa su kuma dan su lalata maka rayuwa=?-?.


Bayan ya je gidan ya shiga ya gaishe da Ammi ,kansa ya sunkuyar da kai ?asa hakan yasa Ammi tambayarsa ko akwai wani abu ne sai da ya Wan nisa kafin cikin jin nauyinta ya faWa mata yana son ganin Zahra.Murmushi ne irin na manya ya kuSuce mata dan dama ta daWe da gane inda ya dosa.Amsa masa ta yi da to ya mata sallama ya fita zauren gidan domin jiran zuwan Zahra ,ita kwa Ammi da kallo ya bishi tana ayyana babu abinda zai hana ta bashi Zahra duk da har yau ba ta san su waye iyayensa ba, sai dai in Zahra ce ba ta son shi domin ta yi al?awari ba za ta taSa mata auren dole ba.

?aki ta shiga ta samu Zahra zaune tana duba littattafanta na islamiya ,Hauwa,u na yin home work, sanar mata ta yi akan ta je ta samu Mashkur yana zaure,hijabi ta Wauka ta kama fita gabanta na dukan uku-uku dan ita ba ta iya sakewa ko gidansu ya zo bare kuma ace za su keSe to wai da me ma zai ce mata? ta ga dama ya fiya kallo wannan dalilin yasa ba ta zama a tsakar gida in yana gidan.


Da sallama ta shiga zauren Mashkur da ke jingine da katanga ya amsa shi ma gaban nasa na faWuwa ,dan yana tsoro kar ta ?i amincewa da shi idan kwa haka ta kasance bai san imda zai sa ransa ba tsawon shekara gida da wani abu yana dakon sonta a zuciyarsa.


"Barka da fitowa malama Fatima" Ya ce cikin murya mai sanyi dan ratsa zuciyar masoyiyarsa,yana so ya yi amfani da kalaman masu zafi da jan hankali wajen sanar da ita halin da ya tsinci kan sa akan son ta ,amma ba kalaman yaudara ba kalamai na soyayya wanda za su sa ta ji ita ma ta kamu da son sa.

"Yaya Mashkur Ammi ta ce kana kirana " Ta faWa tana daga can Wan nesa da shi saboda ko da wasa Ammi tana gargaWinsau akan kusantar da kansu ga kowane Wa namiji ta kan faWa musu duk runtsi duk wuya kar su yarda ko amince da kowane namiji wajen tsayuwa ko zama kai ko da kuwa wajen mi?awa mutum abu ne kar su yarda hannunsu ya taSa hannunsu.

Shi ma hakan da ta yi na tsayawa a Wan nesa da ta yi sai ta burgeshi duk dama ya san irin tarbiyar su.


"Fatima!" Ya kira sunanta ba tare da ya Wora da wata maganar ba.Zahra kwa a yadda ya ambaci sunanta har sai da ta ji wani abu ya daki zuciyarta.


"Na,am" Ta amsa masa tana mai Wago kanta aikuwa ta sauke su cikin nasa idanun da yake akwai nepa lokacin kuma da fitilar a zauren.

"Dama wani sa?o nake tafe da shi ,wanda na ke so na sanar da ke ina fatan za ki kalli sa?on nawa da idon basira kamar yadda na sanki da nazari da sanin abinda ya kamata.Kuma inaso kar ki dubi waye ni sannan kar kiji nauyi ko kunyar bayyana min gaskiya"Cewar Mashkur yana binta da kallo ganin tana kallon ?asa a ransa yana ?iyasta tabbas in ya aureta sai ya yi da gaske wurin cire mata kunyar nan sannan zai samu damar morar soyayyarta dan in har da kunyar nan to ba zai samu yadda ya ke so ba kunyar za ta rage masa jin daWi.


"Ina sauraronka ka faWa min wane sa?o ne" Zahra da bata kawo komai a ranta ba game da sa?on nashi ba duk da dai ta ga wasu sauye -sauye da gyara kalamai da yana magana amma dai ba ta kawo zancen soyayya ne sa?on ba.Tana gani kamar ya wuce ajinta.


"Fatima ! Wallahi tun dana sanya idanu na akan ki zuciyata ta kamu da matsannancin son ki, tsawon shekara guda da wani abu ina dakon soyayyarki a zuciyata ina jiran lokacin da za ki fara kula samari domin nima na kawo tayin tawa soyayyar ko Allah zai sa ki karSi ?o?on barata ki zuba min sadaka!" Ya faWa yana zubar da gwiwoyinsa a ?asa tare da haWe hannayensa wuri Waya alamar ro?o.


Zahra da ido kawai ta ke binsa ,ganinsa dur?ushe gabanta wai dan kawai yana neman soyayyarta, a take ta ji wani tausayinsa ya tsarga mata har cikin ?o?on zuciyarta.Shin ma wacece ita da har zai dur?usa dan kawai ta karSi soyayyarsa, haba duk macen da kyakkyawan matashi mai nagarta ilimin addini da na zamani mai sanin girma da sanin darajar Wan adam da girmama na gaba har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login