Showing 78001 words to 81000 words out of 82877 words

Chapter 27 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2731

suka shiga direct part Win Zee-zee suka nufa dan acan Mummy za ta lallasheta daga marin da Mubarak Win ya mata, ?ofar part Win a buWe,sallama Mummy ta yi yafi a ?irga amma babu amsa, hakan yasa Mubarak ya ce ta shigo ta zauna a falo zai dubo ko bayi ta shiga.


Bedroom biyu ya duba bai ganta ba haka duka bayin da suke Wakunan ya duba bata ciki, hakan yasa ya tafi Waya Wakin tun da ya tunkaro yake jin magana ?asa-?asa, yana shigowa idanunsa ya sauka akan su,kan sa ya dafe tare da sakin wani ?ara mai ?arfi, hakan ya maido da su hayyacinsu da suka yi nisa cikin yanayin da ba su san da shigowar Mubarak Win ba.


Mummy jin ?aran da ya fasa yasa ta tashi a firgice ta bi inda ta ji ?aran na fitowa, tana zuwa ita ma ta yi tozali da abin da ya gani, sai jan bedsheet suke suna ?o?arin rufe jikinsu.Yanke jiki Mummy ta yi ta faWi tsabar ruWewa.MUSTY mi?ewa ya yi tsirara ya taho zai fice amma abin mamaki sai gani ya yi Mubrak ko alamar taSashi bai yi ba hakan yasa ya fito a guje, ya zo babban falon ya ga ba?ar doguwar riga ta mata da alama ta Zee-zee ce a hannu ya Wauka sai da ya zo get Win sannan ya zura rigar dan bayaso ya fita tsirara ace a kamoshi a kaishi dawanau ayi zaton mahaukaci ne.Haka yasa rigar ya fice yana godewa Allah dan ya san da ace mijin Zee-zee ya dam?eshi da ba lallai ya barshi da rai ba, hakan yasa ya Wau al?awari daga yau ya daina yin zina barw har ya kaiwa wata matar aure ziyara gidanta dan ya san yau dai Allah ne ya kuSutar dashi.


_MUBARAK_



Ganin Mummy kwance sume yasa ya juya ya Wakko wata ?atuwar sanda dan baya so Mummy ta farka da dakatar dashi daga abin da ya yi niyya hakan ne ma yasa bai tsaya dukan kwarton ba dan ya san Sata lokaci zai yi sannan ma kwarton bashi da laifi tun da kawoshi aka yi, kuma Mummy za ta iya cewa kar ya taSa Zee-zee.Tun da ya Wakko sandar nan yake jibgar Zee-zee wani duka da ya kai mata a baki gabaWaya ha?oran suka yi bankwana da bakinta, babu ha?orin da yayi saura a bakin kamar bakin tsohuwa idan ta buWe ta rafka ihu sai ya ?ara doka mata sandar, sai da ya mata jina-jina sannan ya nuna ta da yatsa yace.


"Watsatstsiya mazinaciya mai kawo ?ato har gadon aurenta, ki je na sake ki saki uku! Kuma wallahi kafin minti uku ki bar gidan nan in ba haka ba sai dai azo a Wauki gawarki!"


Dur?ushewa ta yi tana faman kururuwa jikinta kaWai abin kallo ne yadda buraWan sanda suka mata, wani hijabi mai maSallai da ake yayi wanda ya kai mata har ?asa ta sanya dama ta siya ne dan take basaja in zata je wani wuri amma ba wai dan tana sanya hijabi ba.Tana sanya hijabin ta fara takawa tana Wingisawa har wani botsarawa take irin na guragu dan ?afarta in ba sa'a ba ya gotar mata da ?ashi, haka ta fito dan tana zuwa get Win ma da ta kasa tafiya da rarrafe ta fito ?ofar gidan a nan ta samu napep mai napep Win ne ma ya taimaka ya sanyata a ciki dan ba za ta iya hawa ba.



Har get Win gidan su mai napep Win ya kai ta, mai gadin gidan Aunty na buWe get Win ya ga Zee-zee bai ma ganeta ba, sai da ta kira sunansa a hankali da ya ?wara mata idanu ya shaidata, tuntsurewa ya yi da dariya, dan tun da yake bai taSa ganinta a napep ba kuma ganin yanayinta ya tabbatar masa da cewa itama dubunta ta cika kamar yadda dubun Auntyn nata ta cika yanzu.


"Za ki iya shigowa ne ko kuma jiranta za ki yi a napep Win ya wuce da ku tashar kano dan nasan itama gata nan fitowa"Mai gadin yace yana dariyar ?eta.

Wannan furucin nasa ya tabbatarwa Zee-zee cewa akwai matsala dan tun daga yadda yake mata dariya ta san yai dubunsu ta cika ita da Aunty tun da babu wani da ya isa ya rainta bare har ya mata dariya.


"Fice min daga gida, babu ni babu ke har abada dama yara ke haWawa ko bayan rabuwa to ke kwa juya ce banda WanWana mini azaba babu abin da kika yi to yanzu dai Allah ya tona asirinki na daWe da dawowa hayyacina daga asirin da kika mini kawai bin diddiginki nake in ga iya gudun ruwanki"Mijin Auntyn Zee-zee da ya koro Auntyn har bakin get yake faWa, yana hankaWota bakin get Win yasa mai gadi ya rufe get Win.


Ido biyu suka yi da Zee-zee da ke cikin napep da?er ta shaida Zee-zee, kuka suka fashe da shi tare da rungume junansu da Auntyn ta shiga nepep Win, haka mai napep Win ya kai su tasha suka ahiga motar Kano Autyn ce ta sallameshi da yake da ?aramar jakarta a hannunta, tun da mijin nata ya kamata da jinin al'adarta yai za ta sanya masa a zoSo ya dan?ara mata saki uku, dan dama ya daWe da sanin tana bin malamai dan wani abun ma ba a hayyacinsa yake ba dan ma yana addu'a shi yasa asirinta ya tonu.



Bai fi tafiyar minti ashirin ba su ?arasa Kano motar su ta yi accident dama sharon ce mota wacce mutane ke cewa delete all aikuwa ta yi deleting Win dan kowa ya ji a jikinsa, wasu sun mutu wasu sun samu mugayen raunuka, ciki har da Zee-zee da ta samu karaya biyu a cinya da karaya a ?afa,hannun kwa fit a cire daga jikinta sai buguwa da ta yi a kan ta, Aunty kwa kafaWar ce ta goce ga kuma ga kuma karaya a ?afa.






>?s?>?s?>?s?>?s?>?s?>?s?>?s?>?s?>?#?

MAMAN AFRAH>?p?>?p?=??


SANADIN KISHIYA NE




NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



PAGE3?? 9??


=??=??=??=??=??=??=??=??



Aunty ta bayar da number Baban Zee-zee aka zo asibitin da aka kai su bayann na yi accident Win, halin da suka tarar da su
yasa Maman Zee-zee kuka kamar me, haka aka shiga ba su taimakon gaggawa, sannan aka maida su gida aka musu Wori Zee-zee ba komai ne damuwarta ba sai ganin babu hannunta gabaWaya ji ta ke gabaWaya komai ya tsaya mata cak, ga sakin da Mabarak ya mata ga kuma wannan abin da ya faru wai yau ita ce babu hannu sannan ba za ta iya tafiya ko nn da can ba saboda Worikan da aka mata a cinyarta da ?afarta ga rashin ha?ora sosai ta ke jin da na sani akan komai da ta aikata a rayuwarta.Allah ya isa kwa ta jawa Auntyn ta ta fi cikin carbi domin gabaWaya halin da take ciki ita ce silar sanyata a ciki, ita ma Autyn da na sani take domin kuwa gashi ita ma sanadin son zuciya ta zo tana da na sani akan abubuwan da ta aikata!.




_Baffa Abdullahi_


Sannu a hankali Allah ya haWa shi da wani irin ciwon ?afa kansa ce ta shiga cikin ?afar, gabaWaya ?afar tashi ta kumbura, haka take wari gashi naman ?afar sai zabgewa yake, duk abin duniya ya ishe shi gashi kuma an ce sai an yanke masa ?afar dan haka yanzu kuWin aikin ma yake so ya haWa saboda yanzu ko nan da can ba ya iya zuwa bare ya je maula ya samo duk abin da yake da shi ya ?are a neman magani.Dan haka yanzu ganin ?afar tana wari wani irin ruwa na zuba hakan yasa ya sanya gidan da suke ciki a kasuwa domin ya biya kuWin da za a yanke masa ?afar.


Tun da Inna Mairamu ta ji batun siyar da gida ta ringa masa rashin arzi?i tana sai ya saketa domin ba za ta zauna da shi ba dan yanzu in aka siyar da gidan ko gidan kan sa bashi da shi bare ayi zancen wani abin duniya bashi da komai dan dama ya daWe da siyar da gidansa na asali ganin ya mllaki wani gidan.Baffa Abdullahi kwa ya ce ba zai saketa ba dole ta zauna ta yi jinyarsa aure kuma mutu?araba takalmin kaza, dan dama tun da ya fara ciwon ?afar Inna Mairamu ta canja dan dama tana jin haushin sa yana neman auren wata bazawara ciwon ?afar ne kawai ya hana auren ita ma kwa yanzu ta ce ba za ta zauna da shi ba, haka dai ake zaman ba daWi ya kasa gane kan ta.



An sayi gidan ya biya kuWin aikin ?afar sauran kuWin kuma ya biya musu kuWin hayar wani gidan ?asa mai Waki Waya zagaye da langa-langa, haka aka yanke masa ?afar nan ya koma mai ?afa Waya sai dai yana dogarawa da sanda, amma a hakan yake fita ya nemo musu Wan abin da za su ci amma Inna Mairamu ba ta gode masa kullum cikin wu?anta shi take, har sai yake jin duniyar ta fice masa a rai akan abubuwan da Mairamun ke masa duk da ya san cewa alhakin su Ammi ne da ya Wauka yake tambayarsa.




_Mummy_


Tun da Mubarak ya yayyafa mata ruwa ta farfaWo ya sanar da ita ya saki Zee-zee ta ji ba daWi a ranta duk da cewa Zee-zee Win ta yi abin da dole sakin ne maslaha tun da gaba ba a san me za ta yi ba, amma Mummy sai ta ji gabaWaya ma tsoron rayuwar take, kuma ta san dama tun da Mubarak ya rasa Zahra to da wuya ya maida gurbinta!. Daddy jin abin da sirikar tasa ta yi yasa ya shiga ruWani hakan yasa ya tuna halaccin da aka musu akan Zahra da kuma rashin adalcin da ya musu na sanya wa a saketa duk da sun gano daga baya bata da laifi tuggun Zee-zee ne.


_Mubarak_



Tun da Zee-zee ta masa wannan abin ya ji duk ya tsani rayuwar bariki, ya ji baya son ko sha'awar ?ara aikata zina, domin ya san cewa abin da yake yi ne aka masa duk da cewa bai taSa neman matar aure ba bare har ya je gidan aurenta amma ya san zinar da yake aikatawa ce tasa ya auri mazinaciya sannan zinar da yake aikata wa ce Allah ya raba aurensa da Zahra domin faWin Allah maWaukaki (Mazinaci ba ya aure sai mazinaciya, ko mushrika, mazinaciya bata aure sai dai ta auri mazinaci ko mushriki, an haramta wannan ga muminai) Tabbas Zahra ba mazinaciya ba ce babu shi sa Allah ya kawo ?arshen zamansa da ita tun kafin ya yi tarayyar auratayya da ita, lallai zina ba ?aramin ?azanta ba ce, innba ?azanta ba ace baka san halal Winka ba kowa sai ka haWa jiki da shi ai ko dan lafiyarka ka guji kuma ka ?auracewa zina!


Wannan dalilin yasa Mubarak ya nutsu ya gane banbancin zare da abawa, hakan yasa ya fara zuwa wani masallaci da ake karatu tsakanin magriba da isha'i yake Waukan karatun Qur'ani sannan yana zuwa wajen wa'azi yana Waukan darussa na gyaran rayuwar yau da kullum da ma gyaran lahirarsa.


Mummy ta fi kowa farincikin faruwar hakan, domin tana so Wan nata ya shiryu ya kasance abin kwatance ko dan wata rana ?a?ansa su yi alfahri da shi a matsayin mahaifi.


DaWin yadda rayuwarsa ta gyara ne ya sa ya je ya sami Daddy lokacin suna zaune a falonsa na ?asa shi da Mummy, dan shi ma yanzu Mubarak Win ya dawo gidan da zama ya baro can gidansa.Bayan an Wan taSa hira da shi ne ya tashi ya je ya tsugunna a gaban Daddy ya fara magana kamar haka.


"Daddy ha?i?a sai yanzu nake jin daWin rayuwata, sai yanzu nake jin nima mutum ne kamili kamar kowa, tabbas ka nuna min gata da kulawa sai dai gatan bai zama na hanya mai Sullewa ba, saboda gata ne da ya sanya na sangarce na ?i karatun boko bare na arabiya amma duk da haka ka kasa tsawatar mini saboda soyayya ka goya min baya, ka ringa ganin ba?in Mummy nah idan za ta faWa min gaskiya, kuWaWen da take hanawa ka bani su ne nake neman mata da su nake shan kayan maye da su domin kuWin ma har rasa me zan yi da shi nake.Ko da ace ni ne silar lalacewar rayuwata to tabbas kai ma kana da alhakin yin haka, kamata ya yi iyaye su kauda kan su daga kallon soyayyar ?a?ansu su koma kallon su waye su me za su zama anan gaba ya rayuwarsu za ta kasance, bayar da nagartacciyar tarbiya ga yara ita ce kyakkyawar abu mai kyau da iyaye za su barwa ?a?an ko da bayan ran su ne domin ba a musu al?awarin rayuwa da su har abada ba, dole akwai tsufa akwai kuma mutuwa dan haka ingantacciyar tarbiya ita ce abin da iyaye za su barwa ?a?ansu, su ma ?a?an su baiwa na su ?a?an irin tarbiyar da aka ba su.Sai da na cigaba da zuwa Waukan karatu da zuwa wajen wa'azuzuka na gane ina cikin matu?ar duhu na jahilci dan Allah Daddy ina fatan iyaye masu hali irin naka za su canja domin rabauta su da ?a?an nasu duniya da lahira!"


Mubarak Win kan sa da ke maganar hawaye yake, haka Daddy da ya rasa me yake masa daWi nauyin yaron yake ji da har ya gane bai kyauta masa ba ya barshi cikin duhun jahilci ya nuna masa soyayyar da gashi ?arshe bata masa rana ba.



"Mubarak! Ina neman afuwarka akan ka yafe mini na san na gurSata maka rayuwa na barka babu ilimi amma ban yi hakan dan na cutar da kai ba na yi ne dan na inganta rayuwarka a nawa ganin kenan, ina ganin ana neman ilimi ne dan a samu aikin gobnati shi yasa nake ganin tun da ina da kuWi ba sai ka Sata lokacinka wajen yin wani abu karatu ba,wanan ya sa nake baka kuWi dan ka fantama ashe ba gata na maka ba rayuwarka na lalata, amma ina so ka yafe mini ina kuma fatan masu hali irin nawa za su gyara su san cewa tarbiya ita ce ginshi?in da kuma jin daWin rayuwa ita ce za ta sanya ka yi alfahri da ?a?anka haka ma mutane su yi alfahri da su"Daddy ya kai ?arshen maganar yana sanya hannu ya share hawaye.



"Kar ka damu Daddy ai komai ya wuce, dama na faWa maka ne dan in sanar da kai cewa soyayya wacce ba ta bari ya nunawa Wa kurensa ba komai take sanyawa ba sai gurSata rayuwa da tarbiya, dan gashi nan ni dai na gani hakan kuma ya zama darasi"Mubarak ya ce shi ma yana share nasa hawayen.


"Mummyn Mubarak, inaso dan Allah ke ma ki yi ha?uri ki yafe min irin abubuwan da na miki akan kina faWa min gaskiya game da tarbiyar Mubarak, amma soyayyarsa ta rufe min ido ban gane komai sai yanzu na fahimci cewa ke ce mai gaskiya"



"Haba Daddyn Mubarak ai babu neman yafiya ko alfarma a tsakani na da kai, ni dama ban taSa ri?e ka a rai na ba, kullum addu'a da fatana shi ne Allah sa ka gane gaskiya, gaskiya ce kuma AlhSadulillahi ka gane Win sai dai fatan Allah tsare gaba"


"Amin" Daddy da Mubarak suka haWa baki wajen faWa





_Mashkur_


Bayan Zahra ta samu lafiya da kwana uku ya koma Kano saboda kasuwa, dan dama ya baro yaransa ne kuma Zahra ta samu lafiya kamar ma ba ta taSa yin rashin lafiya ba, ya bata sabuwar waya da layika ya ce kar ta yi amfani da tsofaffin layikanta.Sosai ta yi murna da farinciki duk da bata ji daWin tafiyarsa ba, dan ma dai ga waya sai su sha soyayyar su kamar ba gobe kullum suna manne a waya suna soyewa hakan ba ?aramin sha?uwa mai yawa ta ?ara shiga tsakaninsu.



Ammi da Umma murna da farinciki ba a magana yanzu ba su da wani sauran buri da ya wuce a sanya rana ayi bikin, wannan shi ne babban burinsu.


Ammi ta sanya su Zahra suka shirya suka je gidan Baffa Abdullahi suka duba jikinsa, sun sameshi zaune a ?ofar gida a maina ya yi tagumi duk abin duniya y ishe shi dan yanzu hatta Mairamun ma ba ya jin daWin zama da ita gashi ko gidan ya shiga sai take harararsa tana yatsina fuska kullum cikin neman takardar saki take wau ba za ta zauna da mai ?afa Waya ba.



Sallama uku suka yi amma bai san suna yi ba, dama can gidan da ya siyar suka je dubashi da yake ba su san ya siyar sa gidan ba dan ?afar ma ba su san an yanke ba sun dai san yana ciwon ?afa Sai da suka je gidan aka kwatanto musu inda suka koma da yake ba wani nisa tsakanin shine suka ?araso.


"Baffa!" Zahra ta ce tana Wan tafa hannunta kusan fuskarsa, sai kallon mamaki da tausayi suke binsa da shi, dan ganin babu ?afar an yanke kuma ga sanda a kusa dashi duk ya yi ba?i ya rame, amma banda Hauwa'u da dariyar ke neman kuSuce mata dan ta san ba komai bane illa alhakinsu, sai da Ammi ta doka mata harara sannan ta danne dariyarta ta.



A Wan firgice ya Wago yana kallonsu, dan kwata-kwata bai san da zuwansu ba gashi ba dan ya san su farin sani ba da ba zai gane su ba aun canja sosai ga sutura mai kyau a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login