Showing 48001 words to 51000 words out of 82877 words

Chapter 17 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2731

bata ?i ace ta jita jikin Mubarak ba yanzu.



Runtse idanunta ta da ?arfi hakan ya yi dai dai da shigowar kiran Neesa, da sauri ta buWe idonta tare da mi?ewa zaune da sauri ta Wakko wayar duk a tunaninta Mubarak Win ne.Ganin sunan Neesa yasa ta yi jifa da wayar akan gado tare da komawa ta kwanta, tana jin wayar na ?ara amma ta share ba ta Wauka ba.

Kiran ne ya cigaba da shigowa, a fusace ta tashi ganin abun ba na ?are bane ta danna ok tare da kara wayar a kunne ckn bambamin masifa ta ce.



"Wai Neesa wane irin abu ne wannan? Kin ringa kiran mutum kmr dai kin bani ajiyar wani abun d...



"Ke yanzu ba lokacin jaraba bane, labari ne marar daWin sauraro ya sameni yanzu nan" Neesa ta katse ta.



"Labarin uban me?"Tace ckn zafin rai



"Wallahi dai an Waurawa Mubarak aure da shegiyar yarinyar nan Zahr...

Dummm haka kunnen Zee-zee ya Wauke ta daina jin komai, kokawa su ka fara ita da numfashinta, ckn ?arfin hali ta saki wayar tare da bin jikin bango ta kamo hanya tana tafiya idonta na lunshewa numfashinta nabkai komo da sauri.A haka ta kamo ?arfen jikin step Win ta tarki sakkowa, ta zo tsakiyar step Win kawai sai zamewa ta yi ji ka ke girrrrrrr tana gangarowa, sai da ta zo har ?arshe sai ji ka yi dimmmm ta faWo ?asa kanta ya bugu...





MAMAN AFRAH >?p?>?p?>?p?=?
?



SANADIN KISHIYA NE

>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE 2?? 1??



Aunty da ke cikin falon tana zaune ta na shan fruit ba ta lura da fatowar Zee-zee ba domin ta ba ta baya ne hnkalinta kuma akan tv da ke kuma falon da girmansa, jin ?aran bugawar abu hakan ne ya sa ta jiyo da sauri.Aikuwa idonta ya sauka akan Zee-zee da ta faWo kwance kmr ma babu rai a tare da ita, sakin plate Win fruit Win a kiWime ta tafi wurin Zee-zee ta shiga jijjigata ckn kuka tana kiran sunanta.


Amma Zee-zee ko motsi ba ta yi ba, ga jini na zuba daga goshinta inda ta bugu, Auntyn ce ta shiga kiran mai aikinsu tana zuwa ta sa ta kama mata ita suka fita da ita, tare da kiran direba ya nufi asibiti da su.Likitoci sun du?ufa akanta a inda su ka samu damar saita numfashinta dama dai suma ne ta yi, numfashinta ga dawo amma har lokacin idanunta a rufe su ke amma ba wai bacci ta ke ba ba dai ta ckn hayyacinta dan sai wasu surutai ta ke yi tana ta ambaton sunan Mubarak da kuma Zahra.Hakan ne ya sa Auntyn ta fahimci akwai wani abu da ya faru da a tunaninta Zee-zee sanadin damuwar da ta ke ciki ne hakan ya faru amma jin wasu maganganu mararsa kai da ?afa ya sa ta fahimci akwai wata a ?asa! Dan haka ta yi al?awari a cikin satin nan za a yi aikin da komai zai zo ?arshe da ma malamin da ta ke jiran dawowarsa wanda zai musu aikin ne ya tafi Lagos hakan ne ma ya dakatar da abun amma da tuni an wuce wurin.Amma yanzu ana sa ransa nan da kwana huWu ko biyar zai bayyana a garin na Zariya.


Sai da Zee-zee ta kwana biyu a asibitin sannan su ka samu kanta, bayan ta dawo hayyacinta ma sai ba ta da aiki sai kuka kmr matar marigayi, duk da Neesa da Aunty na ba ta baki amma ita hakan bai mata ba ita kaWai ta san halin da ta ke ciki.Itace kuma a ganinta ya dace ta auri Mubarak ba wata ba domin itace ta ke masa so na ha?i?a, saboda shi ta watsar da karatunta ta ke biye masa saboda shi ta baro wajen iyayenta ta dawo garin Zariya da zama amma shi ne zai watsa mata ?asa a ido ya manta da ita ya auri wata tabbas sai ta ga abinda ya turewa buzu naWi!=?E?
@&?


Bayan an sallamota daga asibitin ma so ta ke ta fita ta je gidan su Zahra ta koya mata hankali ta ga in za a kai ta gidam Mubarak Win dan ba za ta taSa barinta ta shiga gidan Mubarak ba ko ta yaya ne kai ko kasheta ne za ta iya akan ta buWi ido ta ga Mubarak Winta na rayuwar aure da wata ba ita ba.Dan sai dai akai gawar Zahra gidan amma dai ba wai a raye ba=?1?=?D?



Aunty ce ta lallaSata akan ta yi ha?uri komai ya kusa zuwa ?arshe, dan itama tana da irin burikan Zee-zee a ranta amma kuma ba ta hanyar da kowa zai san su suka mata abinda za su mata Win ba.Haka dai ta ha?ura dan ta ji daWin irin yadda Aunty ta zauna ta faWa mata zallar raahin imani da tsoron Allah na malamin da zai musu aikin wanda yanzu kawai dawowarsa za a jira.

Malamin da ake sa tsammanin zuwansa a kwanaki sai gashi ya kwashe sati guda da kwana uku. Lokacin da ya dira a garin na Zariya, ba ya yiwa ko waye aiki kuma ko nawa za ka biyashi ba zai maka aiki ba matu?ar ya dawo daga tafiya sai ya Wan huta na kwanaki.


A haka mutane ke daurewa da ?a,idojinsa domin sun san aikinsa sha yanzu ne magani yanzu.Dan haka ma su Aunty an ji labarin dawowarsa amma ana jiran ranar da zai fara ganin mutane.


A wannan lokacin da malamin ya dira garin Zariya a lokacin ne kuma aka kai kayan lefen Zahra daga gidan su Mubarak, wannan kuduri ne na Mummy dan dama sai da ta shirya takanas ta je su ka gaisa da Ammi ta ga Zahra sosai ta yi farinciki da ganin Zahra matsayin matar Wanta, haka ma Ammi sai ta ji hankalinta ya Wan kwanta ganin mahaifiyar Mubarak Win mace mai kima da sanin ya kamata ga kuma sanin darajar Wan adam da karrama mutane.


Akwatuna dozin biyu aka kawo ma?ute da kayan masu tsada na gani na faWa, ga manyan gwala gwalai da azurfofi masu matu?ar tsada.Tun kafin ?an kawo kayan su taho tun da Baffa ya zo ya sanar mata ana gobe za a kawo kayan ta farfaWa har da Umman Mashkur aka karSi kayan ita kuma Zahra tun safe Ammin ta ce ta tafi gidan su Hannatu ?awarta idan anyi magariba sai ta dawo sannan ?an kai kaya da masu ganin kayan sun tafi.


Tun da garin ranar ya waye jikinta ya ?ara yin sanyi, sosai ta ke jin ranta babu daWi dk da tana ta ?o?arin ta ga ta danne abun a zuciyarta, amma da ta je gidan su Hannatu sai da ta yi kuka sannan ta samu salama dan sosai kewar Mashkur ke matu?ar damunta, dan ko wayarta har yau a kashe ta ke Mubarak ma sai da ya kawo mata iphone 7 sabuwa dal a laderta wai su ke magana itakwa ko ta kan wayar ba ta bi ba Ammi ta baiwa ta ajiye mata dan ita ba ta jin ta san wasu kalamai da za ta ke faWa masa idan ya kirata dan ko zuwa ya yi wurinta nauyi ta ke ji sosai a zuciyarta ta masa hira kmr yadda su ke yi da Mashkur dan sau tari ma idan au na zaune a zauren da Mubarak Win sai ta dinga ganin Mubarka na rikiWewa yana koma mata Mashkur sosai take ganin yana mata gizo.



Dan ko ranar da Hauwa'u ta sanar mata cewa Mashkur ya bar gari ya koma Kano kwana ta yi tana kuka ba tare da kowa ya san hakan ba.



Bayan ?an kawo kaya da ?an ganin kaya sun watse Zahra Hannatu ta rakota gida da ya ke babu nisa da gidan nasu da gidan su Hannatu.Ammi ce ta ce Hannatu ta zauna ta ga kayan ita kwa Zahra ko kallon inda kayan ma su ke ba ta yi ba, Hannatun ma tana jin babu daWi a haka ta WaWWaga kayan sama-sama shi ma dan kar Ammin tave ba ta Waga ta gani ba.Amman da ace auren soyayya ne aka yi ko kuma Mashkur Zahra ta aura ai ganin kayan lefe sai sun yiwa kayan Wai-Wai saboda farinciki.


Yanzu kwa ga dai kaya iya kaya amman basa murna da kayan sai dai fatan alkairi kawai.


Bayan Hannatun ta tafi an fito daga sallar isha,i sai ga Baffa Abdullahi da wani uban ?aton buhu irin wanda ake saka hatsi kwano arba,in a ciki, bayan sun gaisa da Ammin ya ce kaya ya zo ya gani, Ammin ta masa iso Wakin da su Zahra in da su ke ajiye kayansu a ciki tunda har yanzu ba sa yarda su kwana sai a Wakin Ammi.Ganin uban akwatuna rututu kamar dai ba a san ciwon kuWin ba haka ya shiga jijjiga kai kmr ?adangare, ai mamakinsa bai ?aru ba sai da ya shiga bubbuWe akwatunan sai ya ga duk yanda Mairamu ke bashi labarin yawan kayan, da ya ke da ita aka karSi kayan, dama saboda kallon ?wa?waf amma sai ya ga yawansu ya zarta hakan.




"Kai masha Allah ?ata ta yi goshi"Yace yana buWe akwatin da ta ke sha?e da manyan shaddodi masu mugun tsada, ?amshinsu sai tashi ya ke.

Ammi dai ba ta ce masa komai ba tana dai zaune tana binsa da kallo, Hauwa'u ce ma da ta ya kirata Wakin ta ke zizzige masa zip Win akwatunan, ta faki idon Ammi ta galla masa harara ta gefen ido shi ma kwa bai gani ba hankalinsa akan abin duniya sai washe baki ya ke kmr an masa bushara da gdn aljanna.


Buhun nasa ya buWe ya shiga kwasar shaddodin nan yana zurawa a ciki, daga Ammi har Hauwa'u kallonsa kawai su ke babu wanda yace kanzil=?L? sai da ya Wauki goma sha biyar sannan ya ja murfin akwatun ya rufe y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a cewa Hauwa'u


"Haulatuna zige zip wannan akwatin na sa albarka na gama da ita" Yace yana tashi tsaye ya nannaga buhun.



"To"Kawai Hauwa'un ta ce tare da zigewa a rufe.


"Maidata gefe ki janyo min akwatun atamffin wanda su ka fi kowanne tsada, kmr dai wannan shaddodi"


Shiru Hauwa'u ta yi ba ta ce komai ba sai dai ta yi abinda ya ce.Ana buWe akwatin atamfofi, kawai sai ji su ka yi ya fashe da kuka yace.



"Allah ji?anka Yaya, yanzu duk wannan ganimar baka raye, kaico sai dai ni in gani Allah sarki Wan uwa me daWi, daWin abun ma ni ina raye da sai dai ake ta jimamin ina za a samu wani naka Wan uwanka na jini wanda zai sanyawa kayan albarka kmr dai yadda na ke sanyawa yanzu"Yace yana goge idanunsa da ko Wigon hawaye babu, ya ja hanci tare da Waga atamfofin.Ya dinga jida yana sawa a buhu sai da yasa turmi goma a ciki ya ga buhun ya cika taf sannan yace.


"Kema Mairamu uwar Wiya uwar amarya da ango kya Winka atamfofin ki sawa ?ar taki albarka, dan waWannan kayan sun fi wanda suka kai mana rnr Waurin aure kyau"Yace yana rufe bakin buhun ya Waure da wani zate, hannu yasa a aljihu ya Wakko ledar viva a kwashi turaruka sai da ya cika ledar sannan yace.



"To Fa'iza ga kaya nan kamar jamfa a Jos sai a bi a hankali wajen rabawa mutane, ki Wauki atamfa Waya tunda tana da tsada ki siyar sai a siyo miki atamfofi masu jikin leda, ki rabawa abokan arzi?i su sa albarka kar a bayar da kayan nan kema ki ji tsoron Allah ki Wauki ko turmi biyu ne kya Winka, sauran kuma in an kaita Wakinta sai a kai mata su idan wataran na ji matsuwar rashin kuWi sai in je in karSo wasu daga ciki, in siyar.Tunda dai nj nayi hanyar auren kuma idan ma an siyar gidan arzi?i ne wasu za su siya mata"



"To hakan za ayi"



"Yawwa ni zan koma, sai kuma na dawo zancen shagalin bikin dan ba wani abu za a tsaya ba tunda an kawo lefe sun ce nan da kwana uku ma za ayi komai a kaita Wakinta"

"Allah sa muna raye"Cewar Ammi ckn takaici dan ta matsa ya fita ya tafi.


"Yawwa ga wannan" yasa hannunsa a aljihu ya fiddo wani kwWon datse Waki da mukullansa, ?ato ne kwaWon dan tun da ya shigo gefen aljihun da kwaWon ke ciki ya ke rinjayarsa, saboda girman kwaWon, Ammi ya mi?awa.

kallon kwaWon ta ke da mamaki.


"Na menene wannan?"

"Wannan Wakin za kike rufewa saboda Sarayi, da masu ganin kayan Sa sai kinsa musu ido saboda za a ke Waukan kayan nn kinsan mutane da son banza sai su ga kayan kmr abin bamza su ke musu Wauki Wai Wai"


"To hakan ma ya yi"Cewar Ammi tana kallon kwaWon dan da alama ma ba zai shiga jikin ?ofar ba saboda ya Sata girma.Hauwa'u kwa baki ta rufe tana danne dariyarta ganin son abin duniyar Baffanta ya wuce tunaninsu.



?ofar gida ya fita sai gashi da wasu samari biyu, Waya ya Wauka masa jakar ledar turaruka, Waya yakinkimi buhun kayan domin ba zai iya Wauka ba.Sallama ya musu ya bi bayan samarin nan a bayan napep Win aka danna buhun kayan da?er ya samu wurin da yazauna a Wosane sbd buhun ya cika wurin, ga kuma ledar turarukan ri?e a hannunsa.Samarin Waya ya zauna a mazaunin direba Waya ya zauna a gefensa, Baffa ya snar dasu inda za su kaishi.



"Kai arzi?i gashin hanci, kana zaune sai Allah ya kawo maka wata hanya da zaka ke samu a jikin masu hannu da shuni, musamman ace mutum y samu ?arsa ta auri attajiri ko Wan attajiri to ai daga lokacin kakar mutum ta yanke sa?a"Yace yana gyaWa kai, su dai samarin babu wanda ya tanka masa kuma dai ba su wani fahimci inda labarin ?anzon kuregen nasa ya dosa ba.


"Yaran nan ina kaiku amma kun ?yaleni, ina baku labari ?ar wa na ce ta samu Wan masu kuWi ya aureta, to dama Yayan nawa ya rasu nine auwalinta, shine yau aka kawo akwati guda ashirin harda huWu sha?e da kaya masu tsada, wannan buhun nan da kuke gani kayan dubu Waruruwa ne a ciki, shaddodine masu tsada har goma sha biyar da atamfofi goma ga kuma turaruka masu tsada dk sune ckn ledar nan kmr zan buWe shago, nima rabo nane naje na Wakko"



Kallon kallo samarin suka shiga yi jin abinda mutumin ke faWa.?aya ne ya yiwa Wayan wani zaurencen zance da ido sai Wayanma ya gyaWa kai.


"Gaskiya ne Babanmu Allah sanya alkairi gskiya ka cika uban ?warai, tunda har ka aurar da ita ga wanda ya dace"Suka haWa baki wurin faWa.Wani daWi ne ya ratsa zuciyar Baffa Abdullahi jin an yabeshi.



Dan Allah Baba ka yi mana ha?uri za mu karSawa Babarmu sa?on magani a wani gida maganin gargajiya ne na ciwon zuciya idan muka karSa mata sai mu kaika gidanka sai muje mu kai mata maganin"Mai tu?a napep Win yace ckn sanyin murya da neman izini.


"Haba yaran nan kmr wani wanda mu ke tafiya a ?asa mu da ke ckn adedeta sahu, ai babu damuwa mu je nima har naga gari, bare kuma kuna da hankali naji daWin addu,ar da kuka min, sannan kun birgeni da zaku samowa mahaifiyarku magani a wannan zamanin yara masu tunanu da hankalinku basu da yawa"



Murmushin nasara suka yiwa junansu sai suka ce




"
Mun gode Baba Allah ?ara girma"




"Amin Wiyan albarka"


Sakin hanyar da su ke ka suka yi wacve za ta kaisu gidan Baffan su ka yi wata kwana suka Wauki wani Wan siririn lungu sai ga su sun Sulla wata unguwa mai duhu dk ba wuta, mutane ma sai jefi jefi ke wucewa, hangawa su kayi basu ga kowa basai Waya ya ce.


"Baba fito ka wuce"
"In wuce ina ko dai Waya ya shiga ya karSo maganin"


"Bari ka ji tsoho babu wani batun magani eh ka gane fito kasan inda dare yamaka tun kan jiki ya yi tsami"

"Ku daina faWin haka man bana son wasa fa"


"Babu maganar wasa ka ajiye ledar wannan ka fito ka tafi kawai"Suka ce lokacin da suka fito daga napep Win suka zagaye inda yake zaune.


Ganin da gske su ke ya fara raba idanu, yace
"Wallahi babu inda zanje ?afata ?afar kayana ?an iska Sarayi wlh ihu Sarawo zan yi


Kafin ya rufe bakinsa sula wartosa daga ckn napep Win su ka shiga jibgarsa, ihu zaiyi suka rufe masa bakin, sai da suka masa lilis suka nannaushe bakin har ha?ora su ka fita, kafin su shiga napep Win su ja da mugun gudu su bar layin gudin kar asirinsu ya tonu.



Baffa anan aka barshi yashe a wurin rai a hannun Allah, ko motsi ba ya yi.

Wayyo uban amarya uban
an ango
=??=??=??=??=??=??=??=??=??=??=??=??=??



>??>??>??>??>??Tashi Baffa>?t?>?t?>?t?>?t?
.

MMN AFRAH>?p?=??=?
?

SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?


NA



MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE2?? 3??


Tunda Daddy ya je gidan Baffa ya kai masa akullan gidan da ya bashi, gaba Waya sai ciwon jikinsa a warke, murna ya ke kmr ya yiwa Daddy sujada dan farinciki dan haka kan jin daWi sai cewa ya yi nan da jibi Zahra za ta tare.

Bayan Daddy ya masa bayanin cewa dama su sun gama tsara komai, ya sanar masa cewa zai aiko direba ya zo ya kai su har gidan da ya mallaka masa, sosai ya ji daWi.Dan haka Daddy na tafiya ya Wauki hanyar gdn su Zahra domin sanar da Ammi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login