Showing 63001 words to 66000 words out of 82877 words

Chapter 22 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2740

Daddy idan na tsaya zan iya suma kasan dai can dama tun ina yaro ina da tsoro abu ?an?ani yana firgitani bare kuma wannan kana ganinta kasan mutum idan yana kallonta kaWai zai iya yin mafarki"Yace yana langaSar da kai gefe.


Wani tausayin Mubarak ne ya kama Daddy, sosai yaji tausayin Wan nasa na shigarsa a take yaji yafi tausayin Wansa akan Zahra dan Allah kaWai ya san me ta yiwa Allah ya jarabceta da hakan.Amma Wansa bai jiba bai gani ba azo ana bashi tsoro tabbas da sake.


Fara takawa yayi a hankali ya ?arasa gaban Mubarak Win tare da janyoshi jikinsa ya rungumeshi yana jin ?aunar Wan nasa na ratsa dukkan sassan jikinsa.


"Ka kwantar da hankalinka babu mai takuraka kaje inda take, dan babu yadda za ayi na zaSi wata a kanka amma dai za a nema mata magani a matsayinta na matarka"


"Godiya nake Daddy"

"Ka fi ?arfin komai, jeka ka shiga wankan kaji"


"To Daddy" Yace tare da janyewa daga jikin Daddy yana Wan murmushin samun nasara.

Yana shiga bayi Daddy ya fito daga part Win, ya koma part Win Zahra, ganin suna kuka ita da su Hannatu ya dakatar da su tare da cewa su shirya za su tafi asibiti.Ita dai Mummy da to kawai ta bishi dan ita ta ma rasa a ma'aunin da za ta saka abin da ya samu Zahra.

Sun shirya tafiya Mummy tace Hannatu ta zauna ta yi girki su je su dawo.Haka kwa akayi sai da suka fito Mummy tace Hauwa'u taje ta kirawo Mubarak su tafi, amma Daddy yace wai zazzaSi ya rufeshi ba sai an je dashi ba, ita dai Mummy mamaki ya hanata magana kuma bata so ta cika Daddy da tambaya a gaban su Zahra dan hakan zai iya kawo raini dan ta san maganar ba haka take ba.


Daddy ne je jan motar dan dama ruWewar tunanin halin da Mubarak yake yasa ko direba basu taho dashi ba, Mummy a gaba sai su Zahra a baya. A wani katafaren private hospital Daddy yayi parking.Asibiti ne da ya amsa sunansa domin akwai ?wararrun likitoci wanda suka san aikinsu da ?warewa, hakan yasa asibitin ya zama mai matu?ar tsada sai dai akwai biyan bu?ata domin komai ana yinsa ne cikin ?warewa.


Office Win babban dector Win wanda asibitin yake mallakinsa ne suka nufa, su Mummy sun samu wurin sun zauna shi kuma Daddy yayi nocking ?ofar office Win, izinin shiga aka bashi bayan sun gaisa da Doc Win dama sunsan juna anan Daddy ya shiga faWa masa abin da ke tafe dashi bai yi mamaki ba dan sun saba da irin waWan nan dan indai abin da ya shafi fata ne suna da skin Doc wanda gabaWaya yayi karatunsa ne akan fata dan haka , shi ma kuma mai asibitin ya san abin da ya shafi Sangaren fata dan shi ma karatu ya yi na Sangarori da dama sai dai akwai inda yafi ?warewa.


A nan aka tafi da Zahra wani Wakin gwaje -gwaje domin duba menene ainihin mafarin ciwon nata, da kuma yadda za a magancesa.Abin mamaki duk na'urar da aka gwada domin gane cutar Zahra babu abin da na'urar ke nunawa, abin ya baiwa likitocin mamaki dan dama tun lokacin da suka yi tozali da jikin Zahra suka yi mamaki tare da jinjina irin ?urajen nata.


Ganin dai babu wata na'ura data nuna cutar jikin Zahra kowacce aka Wora sai ta nuna babu komai alalmar babu wata cutar amma kuma a zahiri ga shi nan ana gani.Jin bayanin da Doc ya yiwa Daddy sai hankalinsu duka ya tashi musamman ma Mummy da Hauwa'u ita kwa Zahra sunkuyar da kanta a ?asa sunayen Allah kawai take ambato.Dan Doc yace babu yadda za su yi, su san abin da za su yi wurin Worata akan magunguna har sai sun san cutarta kuma gashi na'ura ta?i nuna cutar.Dan haka sai dai su yi ha?uri su koma gida idan an Wan shafi kwanaki sannan cutar ta Wauki kwanaki a jikinta, tunda ance yau ne abin ya fito mata, sai su dawo a gwada ko na'urar zata nuna cutar.Haka suka baro asibitin.


Bayan wannan asibitin sai da suka je asibiti ulu amma gabaWaya sakamakon guda Waya ne wato babu wani abu da ke jikinta bayan gashi nan ?urajen a jikinta babu masakar tsinke.Haka suka dawo gida sun zo suka iske Ammi a gidan dan Hannatu ta kirata a waya ta faWa mata shine suka taho da Ummar Mashkur dan gabaWaya hankulansu a tashe suke.


Dawowar su Zahra shi ya ?ara tayar musu da hankali ganin yadda jikinta ya koma ga kuma ?urajen da mugun tauri da zafi ga suna saka mata zafin jiki, haka suka sha kukan tausayin Zahran babu mai lallashin wani.Babban tashin hankalin ma guda Waya shine da akace babu abin da aka gani a asibiti.Mummy ta jajanta musu daga ?arshe suka musu sallama suka tafi gida ita da Daddy sun ce shi Mubarak bai da lafiya.


Su Ammin sun jinjina musu tare da musu godiya ganin irin Wawainiyar kaita asibiti da suka yi ko neman Ammin ba su yi ba, amma Mummy ta nuna musu babu godiya tsakanin su ai itama ?arta ce kuma jinya tana kan kowa.Su Ammi dama basu sa ran ganin Mubarak ba dan ba kowane namiji bane zai iya zuwa kusa da matarsa idan tana cikin wannan halin ba.


Ammi ce ta samu ruwa ta karanta addu'o in tsari tare da na waraka a ciki tace Zahra taje ta yi wanka da ruwan dan gabaWaya sun tsorata da yanayin duk da sun fawwalawa Allah komai kuma sun yarda Allah ne ya Wora mata amma kana ganin yanayin abin kasan akwai sihiri.




*Mubarak*

Wajen ?arfe biyar ya ?ara fesa wankansa ya sha kwalliya abinsa sai ?amshi yake, key Win mota ya Wauka da wayarsa, yana ganin missed call Win Nazeer amma ya?i kiransa saboda ba ya so ya katse masa hanzari.Ko inda part Win Zahra yake bai kalla ba ya wuce abinsa ya shiga motarsa mai gadi ya wangale masa get ya kama hanyar Hotel Win da su kayi za su haWu shi da Zee-zee



SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS ERITER'S ASSO...


PAGE 3?? 2??


A harabar Hotel Win ya samu Zee-zee na jiran zuwansa, sanye take da wasu kaya da suka kama jikinta, tun da ta ga Mubarak duk ta saki jiki tana wani narke masa Shima sai zumuWin ganinta yake an jima ba a haWu ba.?aki ya kama musu inda suka shiga she?e ayarsu wa'iyazu billah, ba su suka tashi baro Hotel Win ba sai ?arfe tara na dare, ta shiga motarta ta tafi shima ya shiga tashi motar ya nufi gida ban dan ransu ya so ba suka rabu dan in san samu ne su kwana tare.


Horn yayi mai gadi ya buWe masa get ya shigo yayi parking, door bell ya shiga dannawa yana jiran azo a buWe masa,Zahra tana jin ?aran door bell Win ta san shine saboda taji sanda ya tashi motarsa kuma ko lokacin da mai gadi ya mi?o sa?o a ajiyewa Mubarak Win mai gadin ya tabbatar mata tun yamma ya fita.Wani ?ululun Sacin rai ne ya tsaya mata a ma?oshi ta san dai ba wani wurin abin arzi?i ya tafi ba kawai saboda ta tsinci kan ta cikin ?addara hakan ya nuna bata da wani amfani a wurinsa ita ba ma wannan ne damuwarta ba damuwarta ace shine mijinta kuma wataran zai zama uban ?a?anta amma kwata-kwata cikin halayensa babu na Wauka.


Ajiyar zuciya ta sauke ta juya ta kalli Hauwa'u da ke linke kaya tace mata taje ta buWe masa ?ofar, dan su Ammi da zasu tafi tace Hauwa'u ta zauna tun da sunyi hutun makaranta sai take Wan taimaka mata, kuma Mummy Mubarak Win ma ta dawo da magriba ta duba jikinta nata duk da yanayin jikin nata da sau?i dan tun da tayi wanka da ruwan addu,ar da Ammi ta mata sai taji sau?in raWaWin da ?urajen ke mata sannan zafin jikin nata ma ya Wan ragu sai dan abin da ke zuba daga jikinta ne dai bai daina zuba ba kuma bai ragu ba.


Hauwa'u sai da ta tura baki gaba sannan ta tafi buWe masa ?ofar dan bala,'in haushin sa take ji yadda yayi biris ya nuna halin ko in kula da yayarta, dan ko lokacin da Mummynsa ta zo tana tambayrsa saboda ta ga part Winsa a rufe cewa Hauwa'un tayi ya fita masallaci ita kwa Zahra shiru tayi dan bata son ?aryata ?ar uwarta tun da bata san dalilinta na yin hakan ba.


Tana buWe masa ?ofar ya shigo yake binta da kallo Hauwa'u kwa ta haWe rai suke kallon -kallo, taSe baki yayi ya raSa ta gefenta ya wuce, rufe ?ofar tayi itama ta taSe nata bakin tana ?ara jin haushin sa dan ita ko magana bata masa ba bare ta gaishe da shi tana kallonsa ko inda part Win yayarta yake bai kalla ba ya wuce part Winsa ?wafa tayi ta koma part Win Zahra cike da takaicinsa.



Mubarak kwa jinsa yake a sama sai wani annashuwa yake yana jin ba ya shi, a'uzubillahi mutumin da yayi zina amma yake jin farinciki a ransa babu jin ba?inciki da takaici da kuma nadama da ya aikata saSon Allah.Zaunawa yayi akan kujera ya jingina bayansa tare da rufe idanunsa yana jin daWi sosai a cikin ransa babban abin da ke sashi nishaWi yadda ya ?ara samun kansa a matsayin namiji dan da har ya yanke cewar matu?ar suka haWu da Zee-zee bai taSuka komai ba a matsayinsa na namiji to dole zai sanar da Mummy halin da ya tsinci kansa ayi saurin Waukan mataki.Amma abin mamaki sai gashi bai tsinci kansa a halin da ya tsinci kansa ba da suka kasance da Zahra hakan ya tabbatar masa da cewa Zahra ce tayi wani abin dan kar ya kusanceta saboda bata son sa.



Wani haushinta yaji a ransa ya doka wani uban tsaki, kafin ya tashi domin yin wanka.?aure da towel ya shiga bayin sai kuma ya shiga she?awa kansa ruwa kamar yadda ya saba yin wankan tsarkinsa idan ya dawo daga yawon she?e ayarsa.Sai bayan ya gama jagwalgwalawa sai kuma tunanin Mummyn sa ya faWo masa da ta koya masa wankan tsarkin dama can takan zauna ta tarki koya masa ita a tunaninta matsayinsa na musulmi baligi dole ya iya wankan tsarki ko dan mafarki ma dn ita bata kawo cewa yana neman mata, amma baya saurarenta saboda sangarta.


Alwala ya sake ?ar Wai-Wai wato maimakon alwalar sallah da ake wanke gaSoSi sau uku-uku na wanka kuma sau Wai -Wai haka yayi kamar yadda Mummyn ta koya masa.Ruwan ya Wako ya shiga wanke kansa zuwa fuskarsa har sai da yayi hakan sau uku, sannan ya wanke Sarin jikinsa na dama sau Waya sannan sai ya wanke na hagu shima sau Waya sai kuma ya haWe jikinsa gabaWaya da ruwan yana mai cuccuWa ko ina.


Da har zai fita yayi sallan a hakan kamar yadda Mummyn tace masa idan mutum yayi wankan tsarki yana iya yin sallah a haka indai a lokacin ne ba tare da ya sake alwala ba alwalar da mutum yayi a farkon wankan ta wadatar.Amma kawai sai yaji a ransa gwara dai yayi alwalarsa hakan yayi alwalar ya fito ya shirya ya gabatar da sallah.Dama sun ci abincinsu shi da Zee-zee acan Hotel Win dan haka baya bu?atar wani abinci, dan dama so yake zuwa gobe a kawo masa kuku daga gidansu domin yake masa abinci, dan baya jin ko da abinci daga part Win Zahra ya fito, ba ita ta girka ba zai iya ci ba saboda ?yan?yaminta da yake ji.


Zahra haka suka kwana basu rintsa ba saboda cikin dare sai ?urajen suka shiga mata zugi da sukarta, addu'a suka shiga yi ita da Hauwa'u dan tsabar tausayin Zahra da Hauwa'u hawayen tausayin ?ar uwarta ne kawai ke kwaranyar mata sai Zahran ce ta shiga lallashinta tare da nuna mata cewa ba komai bane jarabawa ce ita ko fatan ta Allah bata ikon cin jarabawarta ta.Hakan yasa ita ma Hauwa'u daurewa suka dinga addu'a har asuba haka suka kwana basu rintsa ba.


_BAYAN SATI GUDA_


Mubarak da Zee-zee sosai sai abubuwan da suka yi gaba dan yanzu burinsu bai wuce su mallaki kansu ba a matsayin ma'aurata dan gabaWaya Mubarak Win haukacewa yayi akanta.Baya ma batun Zahra dan tun washe garin kawota har yau bai ?ara sanyata a idanunaa ba, dan bai ?ara kallon ko da hanyar part Winta ba bare kuma har yayi sha'awar shigar.Ko Mummy idan ta zo dubata in ta tambaya yana shigowa sukan ce mata eh dan Ammi ta gargaWesu akan su guji faWawa mahaifiyrsa cewa ga abin da yake mata dan bata so su shiga tsakanin uwa da Wa.



Zahra kwa bata damu da halin ko in kula da yake nuna mata ba, idan ya fice yawonsa sai lokacin da ya ga dama yake dawowa.Bare yanzu an kawo kuku da ke yin girki da kuma mata guda biyu matashiyar budurwa da kuma wata dattijuwa saboda aikin gida.


A ranar alhamis ne misalin takwas da rabi na dare Mubarak ya shirya tsaf domin zuwa gidansu domin gabatarwa da Daddynsa maganar son ?arin aurensa shi da Zee-zee saboda ta nuna masa Sacin ranta da kuma cewa matsawar ba zai gabatar da maganar aurensu ba a gaban iyayensa.Shima dama yana son hakan dan ko da ya tuntuSi abokinsa Nazeer shima cewa yayi ya ma fi son ya auri Zee-zee wayayya kuma ta san komai yadda za ta tafikar da shi, kuma su ma har sa ke zuwa gidansa a matsayinsu na abokansa amma wannan yarinyar da aka kawo ga ance ta zama aljana shi yasa basa son zuwa gidansa.


A part Wi Daddy ya same su har Mummy bayan ya gaishe su suka shiga tambayarsa jikin matar tasa, ya amsa musu da sau?i sosai.Bayan sun Wan taSa hira sai kuma ya shiga gabatar da abin da ke tafe dashi.Mamaki ne ya hana Mummy magana yaron da sati guda kenan da tarewarsa da matarsa amma yanzu zai zo da batun ?arin aure.


"Ita yarinyar ?ar gidan waye?"Mummg ta tsinci muryar Daddy na tambayar Mubarak dama ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.

Kallonsu kawai take Mubarak Win na yiwa Daddy bayanin shi kuma Daddy na gyaWa kai alamar gamsuwa.


"Insha Allah jibi zan je nema maka aurenta"Daddy ya faWa cikin farinciki.




"Wai lafiyarka kwa Daddyn Mubarak!?Ya za ayi ace yaron da sati guda kenan da tarewarsa ace za a nema masa wani auren"




"Dakata! Shin me kikeso in yi ne?Yaron ya zo min da maganar airen sunna kina maganar satinsa da tarewa, shin so kike ya faWa a halaka bakya ganin yadda ita matar tasa ta gidan ke Wauke da larura a hakan da take ma yake zaune da ita inaga ai yayi jihadi"Cewar Daddy yana kafe Mummy da ido kamar zai kai mata duka.




"Ni bance ba kuma ba haka nake nufi ba amma mutane zasu zagemu ake ganin dan yarinya ta haWu da larura an mata kishiya kuma iyayenta ma ba za su ji...



"Ya isheki, ke kike lissafin mutane ni babi ruwana da mutane zan yiwa Wana duk abin da yake so bare aure sunnar ma'aiki S.A.W kuma ma tun da dai sakinta akayi ba sunna ce kawai za a Wabba?a"Daddy ya katse mata hanzari.


"Shikenan"Mummy tace tare da tashi ta bar falon.

Haka suka shiga tattaunawa kafin daga bisani Mubarak Win ya yiwa Daddy sallama ya bar gidan.Yana dawowa ya kira Zee-zee ya faWa mata abin da Daddy yace.Tayi murna sosai akan labarin nan mai daWi da Mubarak ya sanar mata na batun zuwa neman aurenta ranar sun sha murna ita da Aunty sosai suna ganin aikin Malam yayi daga ?arshe ta kira Neesa ta bata labari sosai tasha mata kirari wai matar Mubarak.



Bayan kwana biyu su Daddy suka je neman auren Zee-zee aka yanke rana sati Waya domin angon yace yana son komai a kusa ne.Babu wanda ya sanar da Zahra halin da ake ciki dama Mummy ita kwa nauyinsu take ji daga ita har Ammin ta yaya za ta tunkareta da maganar wannan bayan tana ganin halin da yarinyar take ciki.Kuma ita ma Ammin kanaganinta kasan tana cikin damuwa dan duk bayan kwana biyu sai ta zo gidan ta duba jikin Zahran wani lokaci kuma su zo ita da Ummar Mashkur, shi dama Baffa Abdullahi ba a maganarsa dan zuwansa Waya shi da matarsa suna can sun tare a sabon gida suna cin duniyarsu da tsinke arzi?i gashin hanci


MAMAN AFRAH


>?p?=??=?
?


SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS ERITER'S ASSO...


PAGE 3?? 3??




An sha shagalin biki sosai aka kashe kuWi iya kuWi, kuWi da ya amsa suna kuWi ba muna kuWi ba, sati guda aka kwashe ana bidirin bikin Zee-zee da Mubarak.Zahra kwa ko da Ammi da Ummar Mashkur suka sameta da maganar ?arin auren Mubarak Win ba ta wani damu ba duk da sun mata nasiha tare da nuna mata cewa, ta yarda da hakan rubutacciyar ?addararta ce.Itama Ammin Mummy ce taje takanas har gida ta sanar da ita dan bata son su samu labarin a gari gwara dai koma menene ace an faWa musu domin hakan kulawa ce.




Ammin ta nunawa Mummy babu komai kuma zata samu Zahra da maganar ita da take ta kanta babu wani abu, haka Ammi ta yiwa bikin ftn alkairi tare da addu'ar samun zaman lafiya mai Worewa.Sosai Mummy taji daWin yadda Ammin ta nuna mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login