Showing 72001 words to 75000 words out of 82877 words

Chapter 25 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2731

ta zauna ita kaWai duk dama ba wani da wuri suka fita ba sai bayan la'asar.


A haka har ta je wurin ajiye butoci ta Wau butar ta nufi hanyar bayi.


"Assalamu Alaikum!!!"


Wani bugawa gaban Zahra yayi da mugun ?arfi, jin muryar da ta daki dodon kunnenta

Mashkur kwa jin ba a amsa ba yasa ya ?ara yin sallamar a karo na biyu, Zahra bata san lokacin da ta saki butar hannunta ba tsabar yanayin da ta tsinci kanta a ciki wanda ta kasa gane farinciki ne ko akasin haka.

Mashkur kwa jin ba a amsa masa sallama ba dama daga cikin zauren ?ofar gdn yake hakan yasa ya ?ara sallama a karo na uku a niyyarsa idan ba a amsa ba zai koma ne ya sake dawowa duk da ya san cewa akwai mutane a gdn tun da gdn a buWe yake.


"Wa alaikumus salam"Zahra ta tattaro gabaWaya ?arfin gwiwarta ta amsa masa sallamar cikin sanyin muryarta.

"Ya salam"Mashkur ya ambata a cikin zuciyarsa jin muryarta cikin dodon kunnensa hakan ya sa ya fara tunanin ko dai a mafarki ne tazo masa kamar yadda ta sake zuwa masa a mafarki.Hannu yasa ya murje idanunsa jin idanunsa biyu ba a mafarki bane hakan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.


A hankali ya fara takowa cikin gidan a ransa yana ayyana cewa yau sai dai Ammi ta kauda idonta domin ba zai nuna kara ko kawaici ba akan Zahra yadda yake ji a cikin zuciyarsa yayi kewarta wacce bata da kwatankwaci ko misali, kewace da zai iya cewa bai taSa yin irinta ba a tsawon rayuwarsa bai taSa kewar wani abi ba sama da Zahrarsa.


Yana shigowa da ita ya fara tozali a hanyar bayi tana tsaye ri?e da sanda a hannunta sai buta dake yashe a ?asa wacce har murfin ya buWe ruwan ya zube da alama ma butar daga hannunta ta suSuce.

Sanye take da doguwar rigar ash clour sai hula a kanta jelar gashinta har gadon bayanta, kallonta yake cikin wani yanayi da yake jin tamkar ya fashe da kuka saboda tsananin farinciki lallai ya yarda cewa Zahra itace komai nasa Zahra itace abincin ruhinsa, Zahra itace rayuwarsa ma baki Waya.Duk da cewa bai yi arba da fuskarta bane a yadda take tsaye ta bashi baya ne amma yana ji a jikinsa cewa fushi take dashi yana ji a ransa cewa tayi fushi dashi ne hakan ya hanata juyowa ta fuskanci inda yake bare ya ga kyakkyawar fuskar nan tata mai cike da annuri da haiba.

Yana takowa har sai da ya zo inda take, hankali da tunaninsa bai kawo masa cewa ina su Ammi suke ba shi dai burinsa da karkatuwar tunaninsa bai wuce da ya kalli Zahra ba ya lallasheta shine kawai.

Zahra kwa jin takun tafiyarsa hakan ya tabbatar mata da ya ?araso wurinta, tana jin sai da ya kusa zagayowa zai fuskanci gabanta tayi sauri ta ?ara juya masa baya ba tare da ya kalli fuskarta ba.Dakatawa yayi ya tsaya tare da ri?e tsantsa da hannu biyu yana jin fushin nata na taSa masa zuciya duk da kasancewarta mai ha?uri da juriya to tabbas abin da zai sanyata fushi ba ?aramin abu bane.Duk da ya san zancen gizo bai wuce na ?o?i ma'ana rashon zuwansa amma da ta bashi dama ya bayyana mata dalilinsa hakan zai sa ta karSi uzurinsa!



"Fatima!!!" Ya kira sunan cikin wata siga mai tattare da lan?asa harshensa, tabbas yana ji a ransa kamar babu wani suna a sunayen mutane da yake jin daWin furtawa akan harshensa sama da sunan masoyiyarsa Zahra.

Rabon da taji an kira sunanta cikin siga mai daWi haka tun sanda suna tare da Mashkur Win lallai so ba ?arya bane ha?i?a ka kanji komai na masoyinka yafi daWi.

Rasa ma ya zai yi yayi, kama tsantsa yayi da hannu biyu yana nazarin ta yadda zai Sullowa al'amarin.

Takawa yayi ya sake juyowa inda ta sanya gabanta, itama kuma sai ta samu kanta da kasa sake juya masa baya.Idanunsa ya sauke akan fuskarta mai cike da ?uraje a hankali ya cigaba da kallon hannunta mai ri?e da sandar shi ma dai hannun kurajen ne a jiki idanunsa suka sauka akan yatsanta mai Wauke da zoben azurfar da ya bata wata ?wallar tausayinsu ce ta cika masa idanu, hatta ?afarta dake sanye cikin silifas sai da yaga gabaWaya ?urajen sun baibayeta.?ago da fuskarsa yayi ya maida kan tata fuskar idanunta dake rufe ruf sai ruwan hawayenta da ya gangaro kan kumatun ta ya zubawa idanu a take ya runtse idanunsa sai hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa shima.



A hankali ya mi?a hannunsa ya kamo sandarta ta, yana jin wani abu na taSa masa zuciya wai yau Zahransa ce ta zama makauniya gashi a gabanta amma bata ganinsa da idanunta sai dai idon zuci, wai yau sandar da zai yiwa Zahra jagora ce a hannunsa.



MMN AFRAH>?p?=??=?
?

SANADIN KISHIYA NE




NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



*Wannan page Win sadaukarwa ne ga Waya daga cikin ?ungiyarmu ta FIRST CLASS WRITER'S ASSO.. MARYAM ABDUL'AZIZ (MAI ?OSAI) da Allah ya nufa da yin AURE muna miki murna tare da fatan alkairi Allah bada zaman lafiya da zuri'a Wayyi ba.* =?O?=?O?>??



PAGE 3?? 6??


Sandar da ya ri?e ya ja a hankali yana jin wani abu na taSa masa tsakiyar zuciyarsa, ita ma bin sa take cikin raunin zuciyarta dan ba kowane namiji bane zai yiwa mace so irin wanda Mashkur ya mata ba.Sannan ba kowane namiji bane zai kai mace matsayin da Mashkur ya kaita a zuciyarsa, matsayine da samun makamancinsa sai an tona so ne da ?auna wanda bashi da kwatankwaci.



Bai tsaya a ko ina ba sai a zauren ?ofar gida inda suke yin hira a wancan lokacin, sai da ya kaita wurin dutse yace mata ta zauna zaunawar ta yi ita ma tana jin wani shau?i na ?auna a ranta ashe ita ma har yanzu tana da wannan matsayin?Matsayin da namiji zai baiwa mace sanadin soyayya da ?auna abin da ta gama fitar da rai da samunsa, abu Waya ta sani shine tana samun irin kulawar nan ne daga Amminta da kuma ?anwarta Hauwa'u.



Amma yau gashi Mashkur Winta ya dawo mata da wannan matsayin, a baya tana samun tarin masoya maza wanda a har kullum suna zuwa ?ofar gidansu domin su samu soyayyarta amma tun da ?addara ta sameta hatta mata ma gudunta suke babu wani wanda ke son kusantar ta sai dai tana jinjinawa ?awarta Hannatu da ke zirga-zirga wajen ganin ta zo inda take tana kwantar mata da hankali.


"Fatima na"Ya kirata yana daga jingine a jikin bango dan yau baya jin ko zama zai iya kawai so yake ya jure duk wata wahala ta tsayuwa ko da kuwa wuni ne ko kwana zai iya yi a tsaye domin Zahransa.



LangaSar da kansa yayi gefe Waya yana kallonta cike da soyayyarta da yake jin tana huda kowane lungu da sa?o na jijiyoyi zuciya da kuma gaSoSin jikinsa kowace gaSa tana amsar nata sa?on, duk da cewa a wani Sangaren tausayinta ya cika masa zuciya dan har yanzu ma akwai hawayen tattare a cikin kurmin idonsa, amma hakan kuma bai hana farincikin ganinta bayyana a cikin ?ahon zuciyarsa, tabbas da ace addinin islama ya halatta cewa namiji yana iya rungumar mace ko da ba matarsa bace to da yau babu abin da zai hana shi ya rungume Zahra ko ya Wan ji sau?in azalzalar da son ta da ?aunarta ke masa.


Ita dai Zahra fuskarta na fuskantar waje Waya ne saitin hanyar shiga cikin gida inda dutsen ya fuskanta, duk da ba gani take ba amma dai wuri Waya ne fuskar ke kalla.


"Zahra!!!" Ya kira sunanta a karo na biyu jin bata amsa na farkon ba, kallonta yake har baya son idanunsa su ?ifta dan sai yake gani kamar idan ya ?ifta zai ga babu Zahra a wajen, wani tausayin nata ne ya daWa mamaye ransa domin gashi shi yana ganinta amma ita bata ganinsa, Allah sarki rayuwa kenan idan baka mutu ba tabbas ba a gama halittarka ba.


"Zuciyata cike take da muradin jin bugun zuciyarki a har kullum, amma sanin wani ne mallakin taki yasa na sanyawa tawa zuciyar ha?uri juriya da ganin na tilasta mata ta cireki amma hakan ya faskara domin Allah shi ke sanya so da ?auna a zukatan bayinsa haka kuma shi yake fitarwa.Idanu na kullum muradin su ganinki ko da kuwa a mafarki ne, ?afafuna burinsu su taka zuwa inda kike sannan uwa uba kunnuwana son jin sautin da amon muryarki, amma sai gashi na zo gareki Zahra kina min rowar muryarki kn san yadda nake cike da son inji muryarki ko yayane? Kai ko da kuwa ace kalaman da lafuzan da za su fito daga bakin naki ba masu daWi bane dan Allah ki ce wani abu Zahra ko na samu sassauci a cikin zuciyata" Ya kai ?arshen zancen yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da ita ma Zahra sai da ta ji ?aran saukar ajiyar zuciyarsa.


Shiru dai ba ta yi magana ba


"Ki shiga gida bari na je gida nima akwai wani abu da zanyi"Yace cikin sanyin murya tare da fara yin taku kamar tafiya zai yi.


"Dawo!" Ya tsinci muryarta cikin taushi da sanyayawa.


Murmushi ne ya mamaye kyakkyawar fuskarsa dan ya san dama a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dan ya san ita ma tana cike da murna da shau?in ganinsa kawai dai tana son yin rigima ne ta hanashi jin muryarta.


"Ashe dai ana so na har yanzu"Ya faWa cikin zolaya.

Tafin hannu Zahra tasa ta rufe fuskarta dan wata kunya ce ta lulluSeta.

"Meye na kunyar kuma uhm?"Ya tambaya yana ran?wafowa ya kama sandar hannunta,suka ri?e a tare.

"Ba kai bane..."Ta faWa tana turo baki gaba.

"Ni ne me?"

"Ka ?i zuwa"

"Amma ai gashi na zo yau ko?"

"Ka makara ai"

"To gani a min hukunci, ko dan hana ni jin muryarki da kika yi kaWai ya isheni hukunci"


"Ai mai hukunci ne ke faWar hukunci ba wanda za a yiwa ba"


"Kaina bisa wuyana a mini hukuncin"


"Frog jump nake son ka min"


"Hahaha babu komai bari in yi tun da kina son in wahalar miki da kaina"Yace yana dariya.

"A'a ka bari na fasa"


"Ni sai nayi"

"Za mu Sata to"

"Afwan Zahraty ni da ke babu Satawa"

A tare suke saki dariya su duka, dariya suke suna jin kan su babu ya su dariya suke cikin farinciki da annashuwa, kai da ka gan su ka san sun dace da junansu ka san sun cancanci kasancewa a tare tabbas kowane masoyi mace ko namiji idan ya gan su zai ji inama shi ma ya samu abokin rayuwa irin Waya daga cikinsu, domin soyayya ce ta ha?i?a!


"Amma ban san dalilin da ya hanaka zuwa ka dubani ba duk da irin halin da na tsinci kaina a ciki, tun da baka kasance mutum na farko ba wurin zuwa dubani ba saboda auren wani a kaina to amma me yasa lokacin da babu auren wanin a kaina ka kasa zuwa ka dubani? Har na fidda rai da zuwanka kullum ina cikin ?unci da tunanin na Wauka kai ma jin halin da nake ciki ya sa ka ?yamaceni"Ta ?arasa cikin raunin zuciyarta.


"Allah sarki Zahra babu ta yadda za ayi na gujeki ko na ?yamaceki a rayuwa, ba wai wannan ?urajen da makantar da kika samu ba, ko da ace har ?afafu kika rasa ma'ana kika zama gurguwa kika zama kurma sannan kika zama bebiya to wallahi!Wallahi!! Wallahi!!! Ba zan taSa guje miki ba, ba zaki taSa ganin sauyi daga gareni ba hakan kuma ba zai taSa, shafar ?aunar da nake miki ba, sannan hakan ba zai sa na zage duk wata kulawa da zan baki ba! Zahra al?awari na Waukawa kaina cewa duk rintsi duk wuya ina tare da ke a duk halin da kika kasance ko zaki kasance na RAYUWA"

Jin kalamansa take suna shigarta ta ko ina, ji take tamkar ta yi ta kuka dan murna da farinciki tabbas a halin da ake ciki yanzu ba kowane namiji bane zai iya maka haka har ya ri?e maka al?awari.


"To me ya hanaka zuwa?"

"Nauyin ubangiji nake so ki gama saukewa"

"Ban gane ba ?"

"Idda nake so ki gama Zahra, tun ranar da Umma ta sanar da ni mutuwar aurenki nake Woki da murna in zo in ganki, ga kuma larurar da ta sanar min ta sameki sai na ji kamar in zama tsuntsu in ganni a Zariya, amma daga bisani sai na yi tunanin bai kamata na zo gurinki ba kina idda kamata ya yi in bari ki kammala idda a lokacin ne zan ji daWin kasancewa da ke domin kin gama sauke nauyin ubangiji shi yasa na fara lissafi a jiya ne kika gama iddar ki shi ne ni kuma na zo yau domin na san ko a yau za a iya Waura miki aure!"

Ikon Allah Zahra ta ce a cikin zuciyarta lallai Mashkur da ban ne, tabbas halayyarsa da zurfin tinaninsa ya Wara duk inda mutum zai yi tunani.

"Allah sarki lallai ka cika mai dogon nazari da hangen nesa, dama ina ta shakku da tantama akan cewa za ka gujeni "

"Allah sarki Zahra ai babu wani abu da zai sa na gujeki"

"Nagode ?warai da gaske, ina alfahri da kai a matsayin masoyi"

"Ni na fiki alfahri da kasancewarki abar ?aunata"

Shiru ne ya Wan biyo baya yayin da ya karSi sandar ya ri?e a hannunsa ya zuba mata kyawawan idanunsa tamkar yau ya fara ganinta.

"Kallona ka ke ko? Duk da cewa a makance nake kuma fata ta babu ?yan gani amma a haka kake kallona, ai da idanun nawa a buWe suke suna ?iftawa ma amma bana gani daga baya ne suka rufe ruf"


Tun da ta fara bayanin yake kallonta cike da tausayawa.

"Duk matan duniya babu macen da zan iya kallo sai ke sannan ban damu wai baka gani ba ni kawai abar ?aunata nasani ke nake so duk yadda ki ke"

Kai ta sunkuyar tana ji a ranta bata da kalaman da za ta yi amfani da su wajen gode masa.Ganin ba ta ce komai ba ya ce


"Ina su Ammi suka je?"


"Sai yanzu ka lura basa nan?"


"Ke ma kina gwada halin ?an ?asarmu ko, a maimakon in an yi tambaya a baiwa mutum amsa amma sai a ?ara masa tambaya"


Dariya ta Wan yi har ha?waranta wanda suke jere tamkar masara suka bayyana suna walwali.


"To kai Win ne da baka tambayi su Ammin ba sai yanzu,sun je gidan suna su dawo"

"Ai kin san hankalina gabaWaya a kan ki, kuma dai na lura ma basa gidan da ace suna nan da na gan su, Allah dawo da su lafiya"


"Hakane kuma, amin ya rabb" Ta ce tana murmushi

Haka su ka cigaba da hirar su cikin farinciki da kwanciyar hankali da kalamai masu taushi da daWin sauraro ga masoya tabbas su kan su sun san sun yi kewar junan su.A haka har aka fara kiran sallar magriba, yana shirin tafiya su Ammin su ka dawo sun gaisa sosai da tambayar bayan saduwa, sannan ya tafi daga nan ma amsalllaci ya wuce domin gabatar da sallar magriba.



_Zee-zee_



Rayuwa gabaWaya ta juya mata baya kullum tana cikin damuwa da fargabar zamantakewarta da mijin nata Mubarak, domin gabaWaya ya birkice mata ban da wula?anta ta babu abin da ya yake haWa su na arzi?i dan gabaWaya ynzu ji yake kaf duniya babu wacce ya tsana sama da Zee-zee.


A wurin iyayensa ne ma take samun Wan salama to su ma tun da suka fahimci cewa babu wani ciki da take dashi dama sharri ta yiwa Zahra sakamakon jin ta da Mummyn Mubarak ta yi tana waya tana sanar da cewa duk abin da ya faru har aka saki Zahra ba kowa bane silar yin hakan sai ita, sai da Mummyn ta gama jin komai wannan yasa gabaWaya suka dawo daga rakiyarta.Dan Mummy har gida ta je ta ?ara baiwa su Ammi ha?uri.



Da kaWan-kaWan Mubarak ya dawo hayyacinsa daga dogon suman da su Zee-zee su ka jefa rayuwarsa na kawar masa da hankalinsa.Tun da ya fahimci abubuwan da ya yiwa Zahra tun daga washe garin tarewarta a gidansa daga bakin Mumuynsa wannan yasa ya ji duk duniyar ta fita a ransa, sannan ya yi matu?ar yin da na sani akan abubuwan da ya yiwa Zahra duk da ya fahimci ba a hayyacinsa ya yi komai ba amma dai tabbas ya yi ba?inciki musamman da ya ji labarin babu wani aure tsakaninsa da Zahra har sai idan ta auri wani mijin.


Ya matu?ar tausayawa Zahra hakan ya sa ya ke jin kunya da nauyin tunkarar gidan su domin zuwa ya basu ha?uri da duk abubuwan da ya mata.


Zee-zee ba su daddara ba ita da Auntyn ta wajen bin wasu malaman dan suna ganin wanda ke musu aikin kamar ya gaza amma duk yawon da su ke a bamza dan al'amuran Mubarak Win kullum gaba su ke basa baya, hakan yasa su ka dawo suka zubawa sarautar Allah ido domin ko da wasa ya hana Zee-zee ta ji daWin rayuwarta.



SANADIN KISHIYA NE


NA



MAMAN AFRAH

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



PAGE3?? 7??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login