Showing 30001 words to 33000 words out of 82877 words

Chapter 11 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2752

wani abu ba.Kyauta tana shiga tsakanin masoya ne idan soyayya ta yi nisa,,, sannan ta fahimceka ka fahimceta"

"Shikenan Mummy"Yace ckn sanyin jiki ya buWe motar ya fito da ledar ya mi?a mata,,, amma dai ya so ya kaiwa masoyiyarsa wannan kayayyakin dan faranta ranta amma dai tunda Mummyn ta masa bayani tabbas ya yarda kuma ya san ba za ta taSa Worashi turba marar kyau ba ko hanya marar Sullewa.

Motar ya shiga dan ya ?agu ya ganshi gaban Zahra yana mata magiya ta so shi ko yaya ne,,, ko ya samu natsuwa a zuciyarsa,,, ya kuma samu sau?in tunaninta da kullum ke masa kai koma a ckn ransa.Hannu ya Wagawa Mummy itama ta Waga masa,,, a ranta tana masa fatan nasara,,, dan dama shi Daddy baya nan,,, shi kuma Nazeer ya tafi wurin Neesa za su yi magana.Dan shima Zee-zee ta masa fushi.


Sakin gilasan motar ya yi ya kunna ac,,, tare da maida hankali ga tu?in da ya ke,,, zuciyarsa sai buga masa ta ke lokaci zuwa lokaci da zarar ya tuno wurin Zahra ya nufa,,, kuma bai san ya za ta kaya ba a tsakaninsu.


Ya ?araso unguwar ckn aminci,,, dai - dai inda suka tsaya ranar da suka biyo bayan Zahra anan ya tsaida motarsa.Idanunsa kafe a gidan su Zahra inda ya ga da aka sauketa a napep ta shiga.


Yana fata da addu,a Allah ya sa nan ne gidan na su Zahra dan idan ba gidan bane bai san inda zai sa ransa ba yau,,, dan ya gama sawa a ransa a yau sai ya yi tozali da ita.Kofar ya buWe ya sa?o ?afarsa guda Waya,,, amma maimakon ya fito sai ya koma ya jingina da kujera,,, yana jin faWuwar gabansa na tsananta,,, shi ba wai tsoron haWuwa da Zahran ya ke tsoro ba a'a shi tunanin irin yadda za ta karSi tayin soyayyarsa yake,,, tabbas ya san ya munanawa Yayanta (Mashkur) dan shi har yau ya Wauka Yayanta ne=?? amma duk hkn ya zai jure koma menene za ta masa indai za ta karSi soyayyarsa.

Iska ya sha?a ta tsawon da?i?u kafin ya fesar da ita da ?arfi,,, yana so ya ji ya daina jin abinda ya ke ji,,, wata iska ya fesar me zafi daga bakinsa wayarsa ya Wauko,,, ya ?ara mayar da ita ya ajiye,,, duk ya rasa ma abinda zai yi,,, shi da ke tun?arar ?anmata manyan ?anmata ma ba tare da fargaba ba,,, amma yau gashi yarinya ?arama ta sa yana jin fargabar tunkararta saboda tsoron sakamakon da zai samu.

Kamar an ce ya Wago kan sa ai kuwa ya hango abokin faWansa wato Mashkur sanye yake da wani dark blue Win yadi kansa babu hula,,, Yayan Zahra a cewarsa.Wani murmushi ne ya suSuce masa a ransa yana ayyan ya samu wanda zai masa jagora,,, ya kuma masa iso wurin Zahra,,, duk da sun yi faWa amma ya san yadda zai masa kota halin ?a?a sai ya yi yadda zai yi Mashkur Win ya amincw dashi duk da a baya ya nuna masa hali marar kyau amma yau zai nuna masa cewar son ?anwarsa ya canjashi.

Ganin Mashkur Win ya kusa ?arasawa gidan,,, hakan ya sa ya fito da sauri dan kar Mashkur Win ya shige.Da ?afarsa ya ?araso wurin lolacin Mashkur ya bashi baya yana tafiya zai shige gidansu Zahra domin mata wani Assigment da aka ba su.

"Barka dai malam" Mubarak yace lokacin da ya zo dai -dai bayan Mashkur Win.

Cakkk! Mashkur ya tsaya yayin da bugun zuciyarsa ya buga ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da mugun ?arfi,,, tabbas ba zai taSa manta mai muryar nan ba ko da kuwa daga sume ya falko bare ma idonsa biyu lafiyarsa ?alaw.Me ya kawoshi ?ofar gidan su Zahra??? Itace tambayar da ta fara zuwar masa a ransa, me zai sa ya masa magana da murya irin haka??? Tabbas akwai lauje ckn naWi,,, dan ba zai taSa mantawa ba cewa saboda Zahra ya masa afuwa,,, saboda Zahra ya janye ?aran da ya masa,,, saboda Zahra ya fasa yin shari,a da shi da kuma ?o?arin kaishi gdn maza dan kawai zalumci da son zuciya irin na su.Tabbas a matsayin Yayan Zahra ya Waukeshi wanda shi bai san cewa kusancin da yake da Zahra ya zarta na Yaya ba ya zama ya Wauki Zahra tamkar jini da hanta,,, sun zama abu Waya shi da ita zai iya Waukan matsayi da dama cikikwa har da na yaya bayan masoyi...


"Ina magana baka juyo ba,,, baka amsa min ba ,,, ina fatan dai ba har yanzu baka yafe min ba?"

Muryar Mubarak Win ta katse masa sa?ar jakin da ya ke.Idanunsa ya lunshe yana so ya danne mugun kishin da ya taso kamar guguwa ya mamaye masa zuciya,,, wani ?unci marar misali yana masa zafi a ransa,,, so ya ke ya juyo amma ya kasa,,, so ya ke ya furta lafazi

SANADIN KISHIYA NE



NA



MAMAN AFRAH



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Wannan page Win mallakin babbar Yaya ne,,, HAJIYA RUKAYYA ABUBAKAR>?p?>?p?>?p?

MMN Abbah,,,d'? Jiddarh,,,=؛? and Saadiq=ؚ? alkairin Allah ya kai miki a duk inda ki ke,,,, zaman lfy tare da kyakkywan ?arshe,,, Allah raya zuri,a=?O?=?O?=?O?

PAGE1?? 5??


Har lokacin Mashkur ya kasa kataSus bare har ya juyo,,, a ransa ya ji baya bu?atar ya haWa ido da wanda yake ji a ransa akwai ?wayar zarra na son masoyiyarsa Zahra a ckn ransa.Bare kuma ave wata magana ta haWa yawunsa da nasa yawun ta hanyar bashi amsar da yake tambayarsa.Har yana wani neman sanin shin ya yafe masa ko bai yafe masa ba??? TabWi ya ma zai yi ya yafe masa,,, zai yafe masa komai amma ba zai taSa yafe masa son Zahra da ya sanya a ransa ba.

Zahra tasa ce dan shi kaWai aka halicceta,,, baya jin akwai wani malu?i da zai ?aunaci Zahra bayanshi,,, kuma babu sau?i,,, babu rangwame,,, babu yafiya,,, bare afuwa ga duk wanda ya kamu da son abar begensa Fatima!!!

"Dan Allah kar ka yi mini zaton hali irin halin da na nuna maka a baya,,, yanzu wannnan ba Mubarak Win da ka sani bane a baya,,, ha?i?a son Zahra ya canjani irin canjin da ba zaka taSa zaton zai sameni a kwana kusa ba" Yace har lokacin yana bayansa kamar yadda shi bai juyo ba haka shima bai matsa daga inda ya ke ba.

Mashkur jin ya ambaci son Zahra a take wani duhu ya giftawa ganinsa,,, sai runtse idanunsa ya yi tare da jim?e hannunsa duka biyu,,, yana sauraron irin bugun da ?irjinsa ya shiga masa tamkar ?aran cidar da ake yayin zubar ruwan sama.Tabbas yau da ya san zai saurari wannan mummunan kalamin da bai tunkaro gdn su Zahra ba bare ace ya ji wannan mugun jin marar misali.

"Nasan na Sata maka a baya amma ka bani dama domin gyara kuskurena,,, dan Allah Yaya kar ka cigaba da fushi dani domin hkn zai kawo rauni da na?asu a ckn Soyayyata da Zahra,,, kasan ance babban wa shine uba,,, ina ftn zaka amince min na shiga sahun masoyan Zahra ina ftn kuma ni ne zan yi dace in zamo mai nasara,,, ta fitar dani abokin rayuwart...

"Ya isheka! "Mashkur yace yana sanya hannu ya warSar da hannun Mubarak da ya Wora masa a kafaWa,,, juyowa ya yi a mugun fusace yana faman huci tamkar kumurcin maciji.Idanunsa da suka kaWa sukayi jawur saboda tsanin Sacin rai da kishin da ya tsinci kansa ciki wanda shi kansa bai san yana da kishin ba.


"Kai! ya isheka kuma,,, shin na bu?aci ka nemi yafiyata ko kuma k...

"Dan Allah ka min rai,,, dan wlh nasan ko da ace Zahra ta amince dani idan baka yarda ba,,, ba lallai ne abin ya je ko ina ba bare har ta kai ga munyi aure cikar burinmu"Mubarak ya katse Mashkur daga abinda yake son faWi,,,yana mai kama hannun Mashkur Win duka biyu idanunsa duk sun kawo ruwa yana tunanin kamar Mashkur Winne damarsa da kyma tsanin da zai bi domin zuwa ga muradinsa kuma cikar burinsa Zahra.

"Kai idan har barci kake ya kamata ka falka daga nannauyan barcin da ya Wauke ka,,, idan kuma taSin hankaline ya sameka ya dace ya gaggauta zuwa asibitin mahaukata domin ba wai abinda kake tunan...


"Ya Mashkur ina yininku"Hauwa'u da ta dawo islamiya ta gaishesu,,, dan bata ma lura da yanayin da su ke ciki ba.Mashkur ne ya warce hannayensa daga ri?on da Mubarak ya masa,,, ya juya ya shige gidan ba tare da ya kalli Hauwa'u ba bare amsa gaisuwarta,,, da kallon mamaki ta bishi,,, yana shigewa ckn gdn ta Saida kallonta kan Mubarak dake tsaye wurja- wurja.Baki sake ta ke kallonsa dan da alama bata ma taSa ganinsa ba balle ta san shi.Amma kana kallon yanayinsa da yanayin shigar jikinsa kasan hutu ya zauna a jikinsa kuma da alama Wan gdn masu hannu da shuni ne duba da irin suturar da ke jikinsa.


"Dan Allah kin san Zahra???" Ya katsewa Hauwa'u tunanin da ta lula.

"Ya Zahra kuma???" Ta tambayeshi da mamaki a maimakon ta bashi amsar tambayar da ya mata.

"Yauwa ehh ita fa ko kema ?anwar wanda ya shige gidan naku ne yanzu???"


"Eh,,, amma me yasa ka ke nemanta ko ta maka wani laifi ne???" Ta tambaya a Wan tsorace.


"Tabbas ta min laifi babba ma kuwa"


"Laifin me ta maka dan Allah???" Hauwa'u ta tambaya kmr zatayi kuka dan dai tasan faWa da aljani ba riba,,, tunda dai yanzu wannan da ganinsa suna da dukiya to inkwa laifi Ya Zahran ta masa lallai ta sanyasu ckn matsala.


"Sata ta mini???"

"Sata???" Ta faWa tana dafe ?irji duk da ta san ba halin Yayarta bane amma ko sharri aka mata ai an Sata mata suna,,, ko shi yasa ta ga ran Ya Maahkur a Sace ko gaisuwarta ma bai amsa mata ba.


"Zuciyata zuciyata,,, zuciyata ta sace min,,, wallahi ta tafi da zuciyata na kamu da tsananin son ta ki taimak...


"Haba malam ai sai ka bari ka faWawa wacce ta maka satar,,, duk ka saniba ruWani na Wauka wata muhimmiyar magana ce,,, ashe ba a banza ba na ga ran mijinta wanda za ta aura a Sace ashe maganar da ta ?ona masa rai ka faWa masa.Yo maganar da ta ?ona masa rai mana dan jin wani yama son Zahransa tamkar bomb ka saka masa a ransa ko kuma wu?a ka caka masa a ?ahon zuciyarsa"Tana gama faWin haka ta shige ckn gdn ta barshi da baki sake,,, kan sa har wani juyawa yake yi,,, a take ya ji wani haushi da ?unci sun mamaye masa ruhi zuciya.


"Kenan ba Yayanta bane??? Kenan shi ne ma mijin da ake sa ran zai aureta???Kenan ma saurayin Zahra yasa ?an sanda suka saki???Ashe shi yasa yake ta nuna min wasu halaye da ya ji na ambaci Zahra.Haka ?wa?walwarsa ta yi jefo masa tarin tambayoyi ,,, yana jin wani ?unci na masa dabaibayi a ckn zuciya,,, ashe shima son ta yake,,, da ya san hakane wlh da bai isa ya tunkareshi da wata magana akan Zahra ba.Amma duk da haka...


"Ni ne nan mijin Zahra,,, Zahra bata da wani miji sai ni ko me zai faru sai dai ya faru wlh ba gudu ba ja baya"Ya faWa tare da marawa Hauwa'u baya zuwa ckn gidan=?(?=?3?

Da sallama ya shiga gdn,,, tun daga ckn zauren gdn ya ?ara fahimtar gdn masu ?aramin ?arfi ne,,, da ace ba dan soyayya ba in acan baya ne kafin ya fara son Zahra ai ba zai iya shiga gdn nan ba ko da kuwa akan mota ne bare da ?afarsa.Tsayawa suka yi suna kallonsa gaba Wayansu ba ya Ammi ma da bata yi zaton ganinsa ba dan shigowar Hauwa'u kenan bata kai ga basu labarin ba shima ya shigo.


Ammi ce zaune akan tabarma a ?ofar Waki,,, sai Hauwa'u da ta shigo yanzu ta zauna a kusa da ita,,, Mashkur na zaune akan benci dan Ammi ta lura akwai wani abu dake damunsa.Tunda ya shigo ya zauna ya gaisheta bai sake cewa wani abu ba.Itace ma ta tambayeshi Ummarsa,,, ganin haka sai ta ?yaleshi,,, ita kuma Zahra tana ckn Waki zata Wakko wayarta dan dama tunda ya mata waya zai zo ta zauna ckn shiri.


Mubarak ?arasawa ya yi har gaban Ammi bai yi la,akari da farar sabuwar shaddarsa ba,,, gwiwoyinsa duka biyu ya zube a ?asa ya shiga gaishe da ita.Dan a yadda yake ji zai iya komai akan Zahra ko da a ckn kwata akace ya dur?usa ya gaishe da Mamanta ko kuwa zai yi jkn inda hkn zai sa a mallaka masa Zahra.


Amsawa ta yi har lokacin mamaki shimfiWe a fuskarta dan ta shaidashi,,, tun ganin da ta masa a police station.Duk hararar da Mashkur ke jifansa da ita hankalinsa bai kai wurin ba,,, Ammi na shirin tambayarsa dalilin zuwansa sai ga Zahra ta fito daga Waki.Sanye ya ke da doguwar rigar jar atamfa mai manyan pattern,,, Winkin ya matu?ar mata kyau,,, sai mayafinta da ya dace da atamfar sa?ale a kafaWarta,,, fuskarta babu kwalliya amma Waurin Wankwalin tamkar akan nata yake dama.Sosai kyanta ya fito,,, tun da ta fito ya manta da Ammi a wurin ,,, gaba Waya hankalinsa akan Zahra tamkar yau ne ya fara tozali da ita,,, kallo yake mata mai cike da ma,anoni da dama ji yake tamkar ya je ya rungumeta ji yake dama ace an mallaka masa ita a matsayin matarsa.

Ganinsa yasa gabanta mummunan faWuwa,,, bare ma gashi dur?ushe gaban mahifiyarta gwiwa a ?asa,,, duk jijji da kan nasa,,,dan ita har ga Allah bata ji sallamarsa ba,,, bare ta san ya shigo gdn,,, ganin sun haWa ido da kuma irin kallon ?urillar da yake mata yasa ta sunkuyar da kai ?asa ta ke wasa da yatsunta.Mashkur ne ya tashi tsaye a harzu?e jin wani abu me kama da taSarya ya tsaye masa a ma?oshi,,,a sukwane ya ?arasa gaban Zahran yace

"Wuce mu je"Yace yana nuna mata hanyar zaure inda suke hirarsu.


"Babu inda za ta je dan nima wurinta na zo"Mubarak yace yana mi?ewa tsaye yaje yasha gaban Zahran.

Ammi gaba Waya ta rasa bakin magana binsu kawai ta ke da kallo,,, Hauwa'u kwa sai dariya ta ke dan ita abin ya ma daina bata haushi,,, lallai Yayarta ta zama ?wallo an sanyata a tsaka mai wuya.


"Wai kan ka Waya kwa???"Mashkur yace ckn harzu?a dan ya ga Mubarak Win yazo dab da Zahra hkn yasa ya ji wani kishin ya taso masa fiye da na Wazu.


"Kai dai za a tambaya kan ka Waya,,, kar ka manta yarinyar nan fa ba matarka bace ,,, allura ce ckn ruwa kuma insha Allah ni ne mai rabon da zai Wauki Zahra a matsayin matars...


"?arya ka ke wlh,,, Zahra matata ce bata da wani mijin da ya fin..


"Haba Mashkur menene hkn kuke shirin yi,,, ya kuke abu kmr wasu ?ananan yara ne,,, halan kun manta ina ckn gidan nan??? Duk kishi ya rufe muku idanu ya kamata kuyi abu na hankali"Ammi da ta taso daga inda ta ke zaune ta faWa ganin abun nasu ba na ?are bane.

Gaba Wayansu sunkuyar da kai sukayi kowanne zuciyarsa na tafasa,,, yana jin haushin Waya.

"Ammi ki masa mgn babu shi babu ita,,, ya barmu mu tafi uzurinmu kar ya ?ara shiga gabanta" Mashkur yace yana hararar Mubarak.


"Wallahi baka isa ba,,, ai ba matarka bace"Shima Mubarak ya faWa a harzu?e.


"Zahra koma Waki"Ammi ta ce ckn bata umarni.A hnkali ta fara takawa tana jin kmr ?wai ya fashe mata a ciki,,, shin menene hkn ya ke son kunno kai ckn rayuwarta??? Wace ?addara ce haka,,, tabbas wannan ba ?aramin abu bane a gareta da yakeson dagula mata lissafi.


"Dan Allah Ammi ki barta mu gana ko na minti biyu,,, wlh na gama sawa a raina yau zanyi mgn da Zahra"Mubarak yace kmr ya fashe mata da kuka ganin Zahran har ta kusa da Waki.


"Na gama mgn"Ammi tace tana juyawa suka shige Waki ita da yaranta suka bar su nan tsaye.

"Sai kaja ?afarka ka bar musu gida,,, a tunaninka ni ban gana da ita ba kai za ka gana da ita,,, ya kamata ka bi wani sarkin ba wannan ba,,, dan sbd ni aka halicci Zah...

"?arya ne wlh,,, ka dai shigo rayuwarta ne kawai amma ni ne na dace da ita" Mubarak ya katseshi yana masa mugun kallo.


"To mu zuba mu gani"


"Aikwa za ka gani Win,,, dan kana nan za ka ga I.V card na aurenmu,,, kuma dama ina ?aleka ne,,, sbd na Wauka kai Yayanta ne,,, da nsn hakane da har yanzu kana can a Waure,,, Waurin da har sai igiya tayi saura!

Mubarak na kai ?arshen maganarsa ya juya a fusace ya fice daga gdn.Mashkur kwa rasa ma me zaiyi ya yi shima marawa Mubarak Win baya ya yi,,, yana fitowa ya ga har ya figi motarsa,,, a hankali yake tafiya yana jin jiwa na neman kayar dashi,,, ga wani duhu da ke giftawa ganinsa lokaci lokaci,,, kafin ya isa gida har an kira sallar magrib,,, soyayyar da yaje ya yi ta wannan yammaci bata samu ba sai tarin ba?in ciki da kuma ba?in kishi da ya tsinci zuciyarsa a ciki.


Ammi suna shiga Wakin suka zauna shiru babu wanda yace ?ala,,, kowa da irin tunanin da yake,,, ita Zahra dama kan gado ta hau ta juya bayanta tare da runtse idanunta tana jin wani abu na mata kai kawo a zuciyarta wanda ta kasa tantance menene shi.Ammi kwa tagumi ta rafka tana alhinin wannan sabon abun dake shirin shigowa ckn neman auren Zahra da Mashkur,,, dama har yau ta kasa faWawa Umman Mashkur takamaiman abinda ke faruwa na abinda kawun Zahran yace game da zuwa wajensa neman aure.Yanzu idan ta ji wannan magnar sai tayi zaton ko wano abu ne daban,,, duk da akwai kykkyawar fahimta tsakaninsu.

Kiran salla ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login