Showing 54001 words to 57000 words out of 82877 words

Chapter 19 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2733

menene na damuwa da kyalekyalenta?!

Haka dai Ammi ta cigaba da nuna mata muhimmancin mijinta da kuma ha??o?insa akanta, babu ruwan ubangiji da babta son mijin, komai ta yi a rubuce ya ke, miji shine aljannar mace, miji ne zai Waga ?afarsa mace ta shiga aljanna, dan haka mace ko tana so ko ran ta baya so dole ne ta bi umarnin mijinta .


Sosai su ke kuka daga Hauwa,u har Zahra kukan nasihar Ammi da kuma kukan rabuwa da za su yi da juna, kukan yin nesa da juna bayan sun saba da rayuwa a tare kullum ana tare ayi faWa ayi daWi bare Haiwa,u mai shegiyar tsokana da abin dariya da tsiri da tsiwa Zahra kuma mai ha?uri da kauda kai, bare mahaifiyarsu mace ta gari mai sanin ya kamata da ?o?ari akan kula da tarbiyar yaranta.



Haka su ka zauna suna tattaunawa har dai dare ya raba su ka tashi su ka sallaci nafila tare da yin addu,o i akan alkairi akan auren Zahra da kuma nemawa mahaifinsu rahma.

An yi shagulgula sosai kmr ba gobe, da dare wajen ?arfe takwas da rabi aka zo Waukan amarya, motoci ne na gani a faWa su ka cika gaba Wayan layin tun daga farko har ?arshe.Mutane wanda aka gayyata da wanda ma gayyar soWi za su je kmr yadda ?an masar ke zuwa inda ba a gayyace su ba=??>?*?
?an SANADIN KISHIYA NE grp can na gansu hr turarreniya ake wajen shiga motoci, su a dole sai sun je sun ganewa idonsu gdn Zahra, wata tsohuwa sai cewa ta ke.


"Haba Wiyan nan duk motocin nan da suke wurin nan gasu nan abin bnza amma sai kuma gudu wurin shiga kuna neman yin turarreniya? Haba ku yi a hankali kowa ai zai samu wuri"Jinta kawai su ke amma kowa sai da ta ganta ckn mota mai ac sannan hnklinta ya kwanta, dan nadia ibrahim ga tsohon ciki amma haka ta totsu dk an matseta>?*?

Amarya tana mottlar da ta fi kowacce kyau da tsada su Umman Mashkur da Mairamun Baffa sun sata a tsakiya, sai wata mata a gaba.Haka motocin nan su ka jeru reras ba su zame ko ina ba sai a gdn amarya.


A bakin gadonta na Wakin da Auntyn Zee-zee ta sanya maganin nan can aka ajiyeta sannan kuma adede inda aka sa maganin.Kowa ya shiga ko ina ya ga gdn amarya sai sambarka ake da fatan zaman lfy da ?azantar Waki.Babu wanda aka bari dan ko ?awaye ba a bari ba sbd an daina siyan baki.?an sanadin kishiya grp sai tururuwar samun mota suke kar a gudu abarsu, an gama ganin ?wa?waf ana ta samabatu za aje a baiwa wanda basa cmmt labari dan su bandasu akaje, dan ko sunje mota bazat Waukesu ba sbd rashin cmmt=??>?*? Nadiya neman ?an niger take dan ita sai dana ?etaro boda.Tunda su ka firfita suka barta take ta kukanta dama tun lokacin da suke sallama da Amminta kuka ya?i tsaya mata, shi ne hr yanzu sai yinsa ta ke zubar hawaye kmr an buWe famfo.

Tana nan zaune bayan kmr minti ashirin sai jin ?aran tsayuwar mota ta ji, ana jiSawa kuma sai ta ji alamun an shigo gdn, jin an buWe ?ofar Sangarenta sai gabanta ya shiga buga mata.Wai yau itace da aure hr gata a gdn miji.Yatsanta ta kai jikin zoben da Mashkur ya bata, ta shiga murza zoben tana tuno da Mashkur Win, hawaye na cigaba da zubo mata tana tunanin halin da yake ciki a ynzu.

Daga falon ya fara jiyo sautin kukanta da take rerawa a hankali, hakan yasa ya ji babu daWi a ransa, wani abu ne ya daki zuciyarsa da ya tuna kodai kukan ?iyayyarsa ta ke yi"Allah sarki son ma so wani"Yace a ckn ransa.


. Babbar rigarsa ya cire ya Wora akan kujera, ya ajiye ledar da ya shigo da ita a falon da ya ke manyan faluka ne guda biyu, sai bedroom guda uku da toilet sai kicin.A can step ma Wakuna ne birjik babu abinda babu.?akin da yake jin sautin kukanta na fitowa ya nufa jikinsa sanyi ?arai dan bai san halin da zai isketa ba, kuma baya son ya sameta ckn damuwa, dk zumuWin da yake sai ya ji murna na neman koma masa ciki, dk da ance idan aka kai kowace amarya ma tana kuka amma sai ya ke ji a jikinsa cewa kukan tasa amaryar ba na rabuwa da gida da iyaye bane kawai, akwai ma rashin son mijin da bata yi...

MMN AFRAH
SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?

NA





MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

PAGE2?? 5??


"Assalamu Alaikum"Ya shiga Wakin bakinsa Wauke da sallama.
?iff ta yi da kukan nata kmr ruwa ya cinyeta, ta daina wasa da zoben ta maida hannayen nata ckn mayafin tare da sanya su saman fuskarta ta shiga share hawayen da ke kwance akan kyakkyawar fuskarta.Sannan ckn sha?a??kiyar muryarta da ta ci kuka ta ?oshi ta ce.

"Wa alaikumus salam"
Wani daWi ne ya ratsa zuciyar Mubarak Win jin ta amsa sallamarsa dan a yadda ya yi zato ma ko magana ba za ta yi masa ba.
Akan bedside drower ya zauna, sai ma ya rasa ta ina ma zai fara yi mata magana.Kallonta kawai ya ke ta cikin mayafin na ta, ya na jin wani shau?i na ratsa zuciyarasa, so kawai ya ke ya ga ta buWe fuskarta ta kalleshi da kyawawan idanunta ma su rikitar da shi a kowane lokaci idan ta kalleshi da su.

"Barka da shigowa sabuwar rayuwa, rayuwar aure mai tarin albarkatu, ina miki albishir da samun kulawa a wurina da sauke dukkan ha??o?in da ke kai na"Ya faWa har lokacin idanunsa kafe a kan ta.

"Nagode"Ta ce cikin sanyin murya.

Shiru ne ya Wan biyo baya, kafin ya ?ara yin ta maza ya ce.

"Ki buWe fuskar ta ki mana, ko na ga kwalliyar da aka yi domin ni"Cewar ango Mubarak cikin za?uwa ganin wai yau gashi ga Zahrarsa a gida Waya a Waki Waya a matsayin ma,aurata har yana magana tana maida masa martani.

Kamar ba za ta buWe ba sai kuma ta tuna nasihar Amminta, anan take ta sanya hannu ta yaye lulluSin, a take kyakkyawar fuskarta ta bayyana a hasken ?wan lantarki, amma har lokacin kan ta a sunkuye ya ke.

baki kawai Mubarak ya saka yana kallon ta, dan sai yau ne ma ya ?ara ganin tsananin baiwar kyau da Allah ya yiwa Zahra.

"Alhamdulillah, masha Allah"Yace a cikin zuciyarsa.Kallonta kawai ya ke yana lura da ji?ar gashin idanunta alamar kukan da ta yi, wani iri ya ji a cikin ransa, dan ba ya son ko kaWan ya ga Zahra cikin damuwa amma yana ganin komai ya zo ?arshe tunda ta dawo kusa da shi zai yi duk yadda zai yi ya ga ya hana damuwa ko da raSarta ne bare kuma har ace ta shiga cikin zuciyarta, balle uwa uba kuma ace shi ne zai yi sanadin shigarta damuwa ko Sacin rai ba ya fatan hakan.

Cikin kalamai ma su taushi ya dinga jan hankalinta tun tana gyaWa kai wajen bashi amsa, hat ta dawo ta Wan saki jiki da shi.Hakan ne ya sa ya umarceta da ta je ta yi alwala dan gabatar da nafila domin nuna godiyarsu ga Allah S.W.A.

Bayan sun idar ya dafa kan ta ya mata addu,ar da Mummynsa ta koya masa ana yiwa amarya ranar da aka kai ta Wakinta, saboda shi ya taso a sangarce ba ya son zuwa islamiya bare har ya koyi wasu abubuwan.Ledar da ya shigo musu da ita ya Wakko ya buWe, ita sai lolacin ma kam ta sunkuye tana wasa sa yatsun hannunta, duk kunya da nauyinsa ta ke ji saboda ba ta taSa kaWaicewa da wani namiji a Waki Waya a irin wannan lokacin ba.Ta san dai ta taSa shiga Wakin Mashkur lokacin da su ka je duboshi ita da Ammi da Hauwa,u, amma ba irin wannan kaWaicewar ba domin dai wannan har hannu ya sa ya taSa kan ta, duk da kasancewrsa miji a gareta amma sai ta ji duk ta takura.

Da?er ya samu ta kurSi lemon da ya zuba mata, sai kuma ya yago tsoka daga jikin kazar zai kai mata bakinta, da sauri ta Wago kan ta aikuwa a take idanuwansu su ka sar?e da na juna, kallon kallo ake, wanda tsabagen sakin baki da Mubarak ya yi a lokacin da ya sanya idanunsa cikin nata, bai ma san ya saki tsokar da zai ba amarya a baki ba>?-? babu sabga haba ango kar ka bada maza mana tun ba aje ko ina ba=??

Zahra ganin abinda ke faruwa da angon nata ya sa dariya ta kusa suSuce mata, a hanzarce ta maida ?wayar idonta ?asa domin ta fahimci itace silar ruWewar ango Mubarak Win>?#?

Sunkuyar da kan da ta yi shi ya nusar da shi abinda ya yi, murmushi ya kuSuce masa, kallon naman da ya faWi a ?asa ya yi sai ya jijjiga a ransa ya ce.

"SO"

?aukewa naman ya yi ya ajiye akan takardar da ke kan plate Win, ya sake gutsuro wani ya nufi bakinta, da shi cikin lallami ya sa ta buWe bakin ya saka mata ta shiga taunawa a hankali cikin kunya tana kare bakin nata da hannunta.Murmushi ya saki yana bin ta da kallo.



KaWan su ka ci, ta haWa ta sanya a frige, ta je ta wanke bakinta ta fito.?akinsa ya mata umarni su ka ta fi can, cikin kunya da jin nauyinsa amma a haka ya rabata da duk abinda ke cikinta cikin kiWima ya tsinci kan sa a wani yanayi mai ban tsoro wanda hakan ya tada hankalinsa sosai, ganin jikinsa kamar ba nasa ba, gaba Waya babu wani kataSus da zai iya yi a matsayinsa na namiji.Ya yi, ya yi amma jiya i yau babu sauyi tamkar lagwanin fitila haka jikinsa ya koma, a take wasu hawaye ma su zafi su ka shiga kwaranyo masa daga idanunsa.Wani ihu ya dage ?arfinsa ya ?walla na tsabar takaici...



A yi ha?uri da wannan afrah da munib ba lafiya=??=?? muna bu?atar addu,arku ngd


MAMAN AFRAH>?p?
SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?

NA





MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE ?IN NAN SADAUKARWA NE GA MUNIB & AFRAH TARE DA DUK WANI MUSULMI DA BASHI DA LAFIYA, UBANGIJI YA BASU LAFIYA MAI ?OREWA
=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?


PAGE2?? 6??


Ihun da Mubarak ya ?wala ne ya sanya Zahra razana tare da buWe idanunta da suke a rufe ruf saboda sauraron abin da ke shirin faruwa da ita na abin da da Mubarak Win ke shirin aikata mata.Ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba sai ganinta ta yi a zaune Waram, tana ciccira ido abin da ya fi ba ta mamaki ma shi ne ganin Mubarak dafe da kan sa yana wani kuka kamar dai an ce Mummynsa ta mutu.


Waige -waige ta shiga yi wai ko za ta ga abin da ya yi saurin canja yanayinsa har haka, wanda ya sa ya shiga halin ?a?anikayi halin tashin hankali wanda ya yi saurin canja dariya zuwa kuka.Amma kuma iya ganinta ba ta ga komai ba, da sauri ta Wauki kayanta ta suturta jikinta sai da ta gama sanya kayanta sannan cikin sanyin muryarta ta ce

"Halan wani abun ya faru da kai ne?"
Jin tambayar da ta jefo masa ya sa ya daure tare da cije leSensa dan sautin amon maganarta ma ba komai ya ?ara msa ba illa damuwa da ?ara sanyashi cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa sai dai kuma yana ganin babu wata mafita da za ta sa ya samarwa kansa abinda yake so domin fita daga yanayin da yake ciki hakan ya sa ya danne wani kuka da ke shirin ?ara fito masa ya ce

"Babu komai Zahra"

Shiru ta yi tana nazarin kalamansa kafin daga bisani ta ce

"Allah kyauta to"

"Ki kwanta kawai "Ya faWi hakan cikin Wacin rai da ?unar zuciya.

Wani lalataccen murmushi ne ya suSuce mata, jin ya ce ta kwanta kenan duk taraddadin da ta shiga a sanadin abin da yake shirin aikatawa ya fasa shikenan.Ita dama kwata -kwata saboda matsayinsa na miji a gareta ya sa za ta bashi ha??insa amma ba wai dan ranta yana so ba kuma ma ta san abu ne mayuwaci ace ba ya aikata saSo saboda ta san an ce mata Zee-zee?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta san shi a matsayin namiji duk da ba tabbatarwa ta yi ba amma abin yana mata yawo.Sai da ta ba da tazara mai yawa tsakaninsu ta hanyar komawa can ?arshen gado sannan ta ja blanket ta rufa tana jin wani daWi a cikin ranta duk da ita ba ta san dalilin Mubarak Win na fasa abinda ya yi niyya ba.


A nan ya raba dare zaune ya na ta faman kuka, da jin raWaWin abin da ya sameshi, abun bai masa daWi ba ko kaWan yau gashi ga Zahra amma kuma ba labari wannan shi ake kira ga bikin zuwa amma babu zanen Waurawa.Haka ya zauna yana bin Zahra da kallo da ke rufe da bargo ruf abinta har kan ta ta rufe.Ko a ransa bai ji ya zargi Zahra da aikata masa haka ba, duk da ya san ba ta son sa, amma ba ya jin za ta aikata haka a gareshi, amma dai tabbas akwai lauje cikin naWi tun dai shi ya san lafiyarsa ?alau tunda ba wannan ne karo na farko a gareshi ba bare ya ce can ma haka Allah ya halicceshi.


Kayansa ya maida ya kwanta yana jin hawaye ma su zafi su na kwaranyo masa abun takaici ne ace yana ango kuma ga amarya amma kuma...

Da asubar fari Zahra ta farka daga Sarawon baccin da ya Wauketa, dan idanunta biyu tana tunanin Amminta da ?anawarta Hauwa,u sannan lokaci- lokaci ma Mashkur yana faWo mata, gabannin asuba ne baccin ya sace ta.Yanzu kuma jin kiran sallah daga masallacin kusa da su ya farkar da ita.Da lalume ta kunna fitilar Wakin gani ta yi babu kowa a Wakin sai ita kaWai, a ranta ta ke tunanin masallaci ya tafi ko part Winsa ua tafi?Da haka ta dinga ?are wa Wakin kallo ganin tsaruwa da haWuwarsa.
A haka ta buWe ?ofar bayi domin yin alawala ta gabatar da sallah, da addu,a ta shiga ta maida ?ofar ta rufe.Kallon bayin ta ke gwanin sha'awa sai dai da ta zauna a wannan gdn gwara a ce Mashkur ta aura ta gwammace ta zauna a gdn ?asa zagaye da langa-langa.Kan toilet ta hau domin yin fitsari bayan ta gama fitsarin sai kuma ta ji wani abu da ban na zubowa wanda ba fitsarin ba ne, mamaki ne ya kamata jin abun na zuba tsiyy jarunta ta ara ta le?a kawai sai ganin jini ta yi na zuba daga jikinta mamaki al,ajabi ne su ka mamaye zuciyarta lokaci guda saboda tasan ba ta fi sati guda da gama priod Win ta ba to amma me zai maido mata al,adarta yanzu?A tsorace ta sake le?awa sai dai wannan karan a ruWe ta mi?e tsaye ganin abin da ke zuba daga jikinfa kwata-kwata bai yi kama da jini ba dan ba?i ne wuluk kamar ba?in gawayi gashi yafi jini kauri, floshing tayi sai kuma ta zauna bisa toilet Win domin wanke na jikinta.



Amma abin mamakin tana wankewa yana ?ara fitowa kamar ma hankaWoshi ake, ganin ba zai daina zuba, ba ya sa ta buWe ?ofar ta fito a kiWime domin abun ya mugun tsorata ta.Jakarta ta hannu ta Wakko ta fiddo ?aramar wayarta da ta kasheta tun ranar da aka Waura mara aure, kunnata ta yi domin kiran Ammi ta faWa mata, tana kunna wayar sai kuma ta fara tunanin kar ta tadawa Ammi hankali da asubar nn gwara dai ta sanya pad duk da tana tunanin ba ma lallai pad Win ya ri?eta ba.

Kafin ta gama wannan tunanin sai ganin messages ta yi su na shigowa, har za ta kashe wayar sai ta fasa ta shiga buWe messages Win.Wasu daga kamfanin Mtn ne amma sai kuma ta ga wani guda Waya da sunan da ta yi sarving number Mashkur, hannunta har rawa ya ke ta buWe sa?on ta shiga karantawa, cikin tashin hankalin ganin kalmomin da Mashkur Win ya yi amfani da su masu tsada cikin kalmomi masu motsa tsohuwar soyayya.A take ruwan hawaye su ka shiga kwaranyowa wasu na bin wasu...
Tana cikin wannan halin sai ji ta yi kamar an tsikareta da allura a wuyanta, tana kai hannu wurin sai ta ji wani ?aton ?urji ya fito mata a wurin, ba ta gama mamaki ba ta ji duk jikinta ana tsikare ta sai ta duba duka jikinta duk inda aka tsikare ta sai ta ga wannan ?urajen ya fito, kafin meye wannan jikinta gabaWaya ya haWe da wannan manyan ?urajen...


"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN"Itace kalmar da ke fitowa daga bakin FATIMA ZAHRA


MMN AFRAH>?p?


SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?

NA





MAMAN AFRAH



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE 2?? 7??


Jikinta ne ya shiga karkarwa kamar mazari, ganin gabaWaya ?urajen sun gama mata jiki hatta fuskarta babu masakar tsinke duk inda ta shafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login