Showing 45001 words to 48000 words out of 82877 words

Chapter 16 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2735

ta ke ta ji a zuciyarta tana ganin idan ta je ta sanar da Umman Mashkur Win to za ta Wanji nauyin maganar ya ragu a ranta.Bugu da ?ari ma ba ta so su ji a gari gwara su ji a bakinta, yanzu da magana ba Suya ta ke ba ko zance za ka ha?a rami ka binne sai ka tsinceshi a wani wurin.


Bayan sun gaisa su ka Wan tattauna, duk da Umman ta fuskanci kmr akwai damuwa a tattare da Ammin ko ta yanayinta ma, amma kuma sai ba ta nuna mata sbd wani lokacin idan abu na damun mutum in ka tambayeshi sai ka ?ara sosa masa inda ke masa ?ai?ayi ya ji damuwar ta dawo sabuwa fil.


Jim kaWan Ammin ta Wan yi shiru domin ta rasa ta inda za ta fara.


"Umman Mashkur da ma akwai wata mgn mai girma da nauyi da na zo mu tattauna amma kuma na rasa ta inda zan fara"


"Haba Ammin Zahra yanzu ni tsakaninmu har akwai maganar da za ki rasa mafarinta? Kawai ki fara ta ko ina, ni dama tun zuwanki na ga akwai wani abu"


"Wlh da ma Baffan Zahra ne ya... ya... ya...

"Wai menene na inda indar ni tsakaninmu har akwai abinda zai gagara a faWa min nan take? me Baffan na Zahra yace?"Umman Mashkur Win ta katse mata hanzarin ciccira maganar da ta ke.

"Abin ne na ke jin nauyin faWarsa wlh"
Dummmm gaban Umman Mashkur Win ya yanke ya faWi, duk da ba ta san me za ta ce mata ba amma ganin tana ?arfafa maganar alamar mai girma ce sai ta ji wani irin babu daWi a ranta.

"Ki faWa mini dan Allah"

"Aure ya Waurawa Zahra, da yaron da iyayensa su ka je rannan, nima sai bayan ya Waura ya kawo min sadakin ya sanar da ni"

Gigifffff, su ka ji ?aran zubewar mutum, ashe Mashkur da ke Waki kwance fitowarsa kennan wannan maganar ta sauka akan kunnensa shi ne ya yanke jiki ya faWi



"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"Su ka haWa baki wurin faWa tare da yin kansa ckn azama da tashin hankali.



SANADIN KISHIYA NE

>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...


PAGE 2?? 0??


*BAYAN SATI BIYU*


Lokacin Mashkur ya Wan warware daga rashin lafiyar da ya yi, dan har asibiti ya kwanta saboda rashin lafiyar da ya dinga yi a dalilin rashin Zahra.Tun daga ranar da ya ba ta zobe bai sake sanyata a ?wayar idanunsa ba haka itama Zahran.

Yanzu ya dawo wani iri baya fita hayan machine Win da ya ke, sannan wurin sana'ar tashi ma ba ya zuwa sai dai Ibrahim ke kula da wuri.Dan shi yanzu babu abinda ke masa daWi duk duniyar nan, hakan ya sa ya daina shiga ko ckn abokai ko da yaushe yana gida a Waki yana aikin nashi tunani da sanya damuwa ckn ransa.


Sallah kawai ke fito da shi zuwa masallaci ana idarwa kwa ya ke dawowa gida hatta abinci sai dai Umma ta matsa masa ya ke ci shi ma ba da wani kirki ba.Duk ya bi ya rame ya yi wani ba?i, shi ma ba a son ransa hakan ba ke faruwa yana so ya manta komai ya manta da damuwar da ke ransa ya cigaba da uzurirrikansa kmr da amma abin ya gagara domin abu ne na zuciya abu ne da ke ckn zuciya sai dai ya yi addu'a akan Allah ya yaye masa itama Umma da Baba haka su ke masa addu'a akan Allah kawar masa da damuwar rashin masoyiyarsa Zahra.



Yanzu ba ya son duk wani abu da zai ke tuna masa da Zahra domin shi kaWai ya san yadda ya ke ji, ya so ace ya ganta ko sau Waya ne amma Umma ta hanashi zuwa a cewarta yanzu Zahra matar aire ce kuma ?ar?ashin igiyar wani ta ke.Hakan ya sa ya dangana amma hakan ba ?aramar azabtuwa ba ya ke na rashin ganin Zahra.Wayarta ma kullum a kashe, ya sa a ransa cewa da ma can Allah ya yi Zahra ba rabonsa ba ce sai dai har ya koma ga Allah ba zai taSa mantawa da Zahra ba, tabon son ta bai zai taSa gushewa ko kankaruwa daga zuciyarsa ba duk da Zahra ta yi aure amma ya san tabbas son ta Allah ne ya halittashi ya kuma sanya masa a zuciyarsa.Al?awari ya Waukawa kansa cewa duk runtsi duk wuya ba zai taSa daina ?aunarta ba, sai dai a binneshi da son ta a ?o?on zuciyarsa amma ba ya jin duk duniya akwai wata mace da za ta kama ko da yatsan kafar Zahra ne bare kuma ta taddota har ta samu gurbi a zuciyarsa tabbas ba zai taSa iya haWa son Zahra da wata ba!So ne na gaskiya ya ke mata so ne na ha?i?a da ba ya tunanin ko MAJNUN ya yiwa LAILA irinsa su ne dai masoyan da ake kwatance da su akan soyayya=?D?


Kamar ya warke hallaw ya cuta ta dawo sabuwa saboda damuwar da ke ckn zuciyarsa, hakan har ya haddasa masa aman jini sosai hankalin iyayen nasa ya tashi suka maidashi asibiti ckn ikon Allah dai ba ciwon zuciya sai dai likitan ya shaida musu cewa matu?ar bai daina sanya damuwa a ransa ba to dab ya ke da kamuwa da ciwon zuciya, dan haka sai an kiyaye Sacin ran nasa.Da suka masa bayanin damuwar tasa yace kawai idan da hali a nesantashi da inda yarinyar ta ke zuwa inda zai nesanta da ita hakan zai sa ya samu sassauci ya kuma manta da damuwarta.



Sosai su ka masa godiya da kuma ?udurin aikata shawarwarin da ya ba su, haka dai aka sallamosu daha asibitin kowa ransa da zuciyarsa babu daWi.Suna dawo wa washe gari Baba ya kira kaninsa da ke garin kano ya sanar masa Mashkur Win zai koma can da zama.Sosai Kawu Rabi'u ya yi murna dan dama ya daWe yana naci akan Yayan nasa ya bashi Mashkur amma ganin shi kaWai suka mallaka Yayan nasa ya hanashi.Baba ya sanar da Mashkur ya shirya gobe zai wuce Kano duk da ba ya so amma shima ya fi so ya tafi dan ba ya so ya zauna a garin da Zahrarsa za ta zauna zaman aure da wani ba zai iya jurewa ba.



Haka ya shirya kayansa a daren, amma kuma kwana ya yi bai runtsa ba, duk da dai dama baccin nasa ya zama asha ruwan tsintsaye daga ranar da ya san Zahra ta zama mallakin wani, amma kuma rashin baccin yau ya sha banban da na kullum.Yana yi ne mai wuyar fassaruwa yana yi ne da ya ke jin kansa tamkar ba nasa ba yana jin tabbas ya riga da ya rasa Zahra tun da gashi zai bar garin Zariya da zama zai nesanta kansa daga inda Fatima Zahra ta ke, wayarsa ya Wauka ya shiga rubuta sa?o kmr haka:


Tabbas zuciya halittace da ke ckn jikin Wan adam, ?aramar halitta ce da ke ckn ?irji a gefen hagu, sai dai tana Waukan abubuwa da yawa a cikinta.Abubuwan farinciki da na ba?inciki da na al,ajabi da ma abubuwa da dama makamantan wanda na ambata, tana da sashe -sashe a tattare da ita shi yasa komai ka cusa mata ta kan Wauka. Ha?i?a da sannu SO da ?auna ke shiga ckn zuciya tun SO yana ?arami har ya fara girma ya kai lokacin da ba zai iya fita ba domim babu ?ofa!

Zahra na kamu da SO akan ki nasan menene SO na tabbatar da menene ?auna har ta kai da ina jin ba zan iya rayuwa ba in babu ke=??



To amma dama Ubangiji ya gama tsara mana rayuwarmu tun kafin mu dira a duniya, dan haka dama cannke ba matata ba ce rashin sanin gaibu da kuma ?addara wacce ake kira da ta riga fata, su ne sunka haWamu, ina baki ha?uri ina kuma ro?onki da ki daure ki jure ki cireni a ranki ki yi zaman aure, ki bi mijinki ki masa biyayya domin mijinki shi ne aljannarki, sai ya Waga ?afa sannan za ki shiga aljanna dan haka ina so ki masa biyayya kar ki taSa yarda ki saSa masa.




Sannan ina sanar da ke a gobe zan bar garin Zariya zan koma Kano wurin ?anin mahaifina da zama, ina fatan kiyi rayuwa mai albarka, ina fata ki dace ina kuma fatan wannan mijin da kika aura ya zama alkairi a gareki NAGODE NAGODE NAGODE>?? SAI WATA RANA>?r?=?-?


MASHKUR ne=?L?=?L?=?L?

Yana gama tura sa?on ya fitar da layikan gaba Waya biyun yankarya su, ya juya ya kwanta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.Allah sarki ko ni mmn afrah sai da idona ya cika da ?walla=?? Allah sarki MASHKUR.


*WASHE GARI*


Wajen ?arfe goma ya shirya tsaf ya Wauki jakarsa ya yiwa iyayensa sallama, su ka masa fatan alkairi da kuma fatan sauka lafiya.Yana juyawa Umma ta shige Waki ta shiga share hawayen tausayin Wanta Allah sarki uwa da Wa, tausayinsa ta ke ji gashi yau sanadin soyayya za su yi nesa da juna, tana fatan Allah ya sa haka ne mafi alkairi amin.


Yana fitowa ya sanya glases a fuskarsa saboda duk idanunsa a kumbure su ke gashi har lokacin ba su washe daga jan da su ka yi ba.Machine ya tsaida ya hau ya faWa masa ya kaishi tasha, yana ji yana gani haka mai machine Win ya biyo ta unguwar su Zahra domin nan Win ya fi kusa da tashar da zai kaishi, shi kuma bai hanashi ba hasalima tun da ya hau machine Win bai yi magana ba.



Sun zo dai dai ?ofar gidan su Zahra kawai ya ganta za su shiga gidan ita da Hauwa'u da sauri ya kauda kansa gefe tare da runtse idanunsa domin wani irin faWuwar gaba ne ya ziyarceshi.Su kuma su Zahra daga ma?otan bayan layinsu su ke inda akayi mutuwa su ka je sutura, acan su ka baro Ammi, dan haka ba su ga Mashkur Win ba ma shi ne ya gansu.


Yana zaune ckn motar ana jira mutane su cika motar a tafi sai ga Ibrahim an saukeshi a machine, dan yanzu ya je Baba yace masa har Mashkur Win ya tafi shine ya biyoshi tasha, dama jiyan da ya je da yamma ya ji zancen tafiyar tasa Kano.



Sun Wan tattauna yana bashi baki akan ya manta da komai, suna nan har motar ta cika, suka yi sallama motar ta tashi su na Wagawa juna hannu, shi ma Ibrahim har da ?wallar tausayin halin da abokin nasa ya kasance ya yi, kafin ya juya ya bar tashar cike da kewa.




?angaren Zahra tun bayan da Ammi ta dawo daga gidan su Mashkr ta ga alamar damuwa a tare da Ammi alamar ta sanar da su Mashkur halin da ake ciki, sai hankalinta ya ?ara tashi ta ji damuwarta ta ?aru domin tana tunanin halin da masoyin nata zai shiga domin ta san yadda ya ke bala'in ?aunarta kmr me.Sosai tsananin zafin zazzaSinta ya tsananta sai duk su ma su Ammin su ka ?ara shiga damuwa da ganin halin da ta ke ciki.



Hakan ne ya sa tun daga wannan ranr da ta kashe wayarta ba ta ?ara kunnawa ba, ba ta son abinda zai sanya Mashkur Win cikin damuwa ta dalilin jin Waurin aurenta kuma ta san matu?ar wayar a kunne dole zai kira ko da ace ya jure bai san sanda zuciya za ta Waukeshi ya kira ba domin zuciya ba ta da ?ashi.



A ranar sai da Ammi su ka kaita asibiti saboda zazzaSin ya yi tsanani ga kuma ba ta cin komai kumanko da ace ruwa ta sha sai ta amayo da shi. An sanya mata drip tare da mata allurori aka kuma rubuta mata magunguna da magriba aka sallamesu da drip Win ya ?are su ka koma gida.



Cikin ikon Allah Ammi na mata nasiha, da ba ta baki ta ke Wan watsar da komai kuma tana yin hakan ne sbd Ammi da Hauwa'u dan ganin damuwar da su ke ciki ta dalilinta.Hakan ya sa ta barwa zuciyarta halin da ta ke ciki domin ita kaWai ta san irin azabtuwar da take ta rashin Mashkur.


Ko da daddare tana likimo ne kmr me bacci amma ko runtsawa ba ta yi, in ta ga Ammi ta Wan falka har munsharin ?arya ta ke, dan ma dai Ammin tana tashin su, su yi nafila da dare su yi addu'o insu dan sun fawwalawa Allah komai, hakan ne ya sa abin ma ya zo da Wan sau?i ba kmr yadda su ka tsammata ba, addu'a maganin ?unci da damuwa addu'a maganin komai.





Tun washe garin zuwan Baffa Abdullahi ranar da aka aki Zahra asibiti tun a ranar Mubarak ya zo da daddare, Ammi ba ta nuna masa komai ba ko a fuska da ya gaisheta ta amsa masa ba yabo ba fallasa dan ita ba ta ganin laifinsa da na ubansa ta fi ganin laifin Baffan su Zahra domin shi ya ba da auren.


Shi ma kuma Mubarak Win bai tambayi Zahra ba da ya ke tana Waki, itama Ammi ba ta ce masa komai ba.Haka ya ?ari zamansa akan bencin da ya yiwa kansa masauki da yake bencin a wurin ya ke ko yaushe. Da ya tashi tafiya ya ajiye wata leda da ya shigo da ita yace "A ajiyewa Zahra" Ammi ta ce "Madalla" Dan ba ta so ma wata doguwar magana ta shiga tsakaninsu dashi, shi yasa ma ba ta ce ya koma da ledar ba bare kuma yanzu da Zahra ta ke matsayin Satarsa yana da ha??i ya bata duk abinda ya ke so.





Shi dai ya tafi ransa fari ?al dan tunda dai Zahra ta zama tashi ko bai ganta ba ya san dai lokaci ?alilan ya rage, ta dawo kusa da shi dawowa ta har abada ma kwa.



Har gidan Baffa Abdullahi ua je ya masa shatara ta arzi?i, sosia Baffan ya yi ta rawar ?afa da murna yana ganin ya samu sirikin da zai ke SanSarar kuWi daga jikinsa, anan ya ke tambayarsa yana zuwa gidan wurin matarsa sosai Mubarak ya ji daWin wannan tambaya saboda an sosa masa inda ya ke masa ?ai?ayi, anan kwa Mubarak Win ke shada masa yana zuwa sai dai ba ya ganin Zahra shi kuma nauyin tambayar Ammi ya ke ji shi sa bai tambaya ba Ai nan fa Baffa ya shiga bashi ha?uri kmr ya dur?usa masa akan kar ya damu daga yau yana zuwa zai ke ganinta kuma za ta ke saurarensa.



Haka ya bar gidan Baffan cike da farincikin kalaman Baffa Abdullahi.



Baffa kwa a ranar ya yiwa gidan Ammi dirar mikiya, ya yi ta zazzaga masiga da bala'i yana kiran Ammi za ta kashewa yarinya aure dan haka ma ranar tariya zai saka yarinya ta tare a Wakin mijinta ya ga tsiya.Ita dai Ammi ba ta tanka masa ba haka ya sha bambaminsa ya tafi bayan ya korawa Zahra kashedi akan rashin fitowa ta saurari mijinta dan haka daga yau matsawar ba ta fito sun gana da Mubarak Win ba to komai zai iya faruwa!



Haka ya tafi duk da ya shaida musu cewa su kasance ckn shiri domin ko yaushe za a iya tarewa tunda dai ko cokali ba su za su siya ba.



Mubarak ya cigaba da zuwa gidan su Zahra kuma Zahran na fitowa dan ba ta son abinda zai Satawa Amminta rai, dan ta san ko sama da ?as za su haWe Baffan ba zai yarda cewa ba Ammin ke hanata fita wurin Mubarak Win ba.Haka zai zo ya yi ta zuba kmr ruwan famfo duk da ita ba magana ta ke masa ba iyakarta ta gaishe da ahi ta ja bakinta ta yi shiru>?? yana hirarsa ita kuma tana tunanin yadda ?addara ta jujjuya al'amuranta, wani lokacin ma sai dai ya ga hawaye na kwaranya daga idanunta idan ya ga haka sai ya sallameta ta shiga gida shi kuma y tafi.



*Zee-zee*

Tun tana ha?uri akan maganar antynta na ta share Mubarak har da abin ya zo yana damunta, domin ba ?aramin ?o?ari ta ke ba wajen jure rashinsa ba.Duk ta yi ba?i dan ba ta da nutsuwar shfa man bleching Win nata ma duk ta yi glass a fuska.



Idan ta samu Antyn nata da maganar ta kan ce mata ta ?ara daurewa komai ya kusa zuwa ?arshe, domin kuwa duk sanda aka mata abun sai ta yi alfahri da hakan,Wannan dalilin yasa ta ke danne duk wani raWalin so da sha'awar Mubarak Win dan tana so itama ta kawo ?arshen yarinyar da ya mareta akanta.


Ita yanzu fitar ma wahala ta ke mata, dan ko Neesa sai dai ta kawo mata ziyara.


Nazeer ne ya kira Neesa ya a waya ya bata labarin auren da aka Waurawa Mashkur da Zahra, a gigice ta ke tambayarsa ya kuwa tabbatar mata da gaskiyar lamarin.



Wayarta ta Wauka hannunta har wani karkarwa ya ke, a haka ta kamo no Zee-zee ta danna mata kira, wayar sai ringin ta ke amma ba a Wauka ba.




"Ki Wauki waya mana Zee" Ta ce tana ?ara danna mata wani kiran ji ta ke kmr ta rufe idonta ta ganta a gdn su Zee-zee Win.




A Sangaren Zee-zee kuwa lokacin da Neesa ke kiran wayarta tana Wakinta da ke saman bene a kan gado a kwance sai juyi ta ke, ta rasa duniya me ya ke mata daWi, dk ba jin daWin komai kawai so ta ke ta ga Mubarak Winta ko kuma ta ji muryarsa, kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login