Showing 36001 words to 39000 words out of 82877 words

Chapter 13 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2734

fa dama ba wai yana son auren nan bane,,, kawai dai dan babu yadda zai yi tunda Mubarak Win yana son kayansa.Kuma ma gasu talakawa amma sai rainin hankalin tsiya,,, duk da shi ma Wan talakawa ne amma baya son takalaka.

Ammi mi?ewa ta yi tana hararar Hauwa'u akan abinda ta yi a maimakon amsa sallama,,, kanta ta mayar ?asa ta cigaba da wankin.Mayafinta ta yafa ta nufo zauren.

"Wa alaikumus salam"Ta amsa sallamar ganin matashin saurayi ne,,, mamaki ne ya kamata ita da Zahra ta ce mata iyaye amma ta ga saurayi.


"Yawwa ina kwana"Yace yana binta da kallo.

"Lafiya"Ita ma Ammin ta ce tana haWe rai.


"Dama an ce ayi sallama da mai gdn ne"

"Ina wanda ke son ganinsa"

"Ga su can a waje"

"Ce musu su shigo"
Yana juyawa ta ?walawa Hauwa'u kira ta kawo mata tabarma ?atuwa,,, ta shinfiWa,,, gwara su shigo ta ji abinda ke tafe da su a yita ta ?are.

A kan wani dutsi da ke zauren ta zauna,,, sun shigo su uku,,, kallo Waya ta musu ta san masu hannu da shuni ne,,, sannan tana kallonsu ta shaida mutum Waya wanda ta ganshi a police station lokacin da suka je wurin Mashkur a matsayin mahaifin yaron da ya zo jiya.


Ta musu iso suka zauna akan tabarmar,,, duk da ba sabuwa bace tabarmar amma babu alamar ?azanta ko datti a jiki.An gaisa ckn mutumci anan ta gabatar musu cewa mahaifin yaran ya daWe da rasuwa,,, sai suka nuna mata ba su sani ba shi yasa ma suka nemi ganawa da shi.



A nan Waya daga ckn abokan Daddy ya shiga gabatar mata da bu?atarsu na nemawa Wan su auren ?arta tunda itace mahaifiyar yarinyar har suna faWa mata idan son samu ne suna so a Waura auren a yau,,, a faWawa kawunan yarinyar ko limamin unguwar in ya so sai a gabatar da bikin daga baya.

Tsabar mamaki ma Ammi kasa magana ta yi,,, shirun da ta yi sai ya nuna musu kmr ta amince ne,,, dan haka Daddy ya fara gabatar mata da matsayunsa da irin tarin dukiyar da yake da ita,,, da kuma irin abubuwan da zai ba su in aka yi auren da kuma irin daular da ?arta za ta zauna a ciki in ta auri tilon Wansa kakarsu ta yanke sa?a.Yana gama mata bayani ya fiddo rafar ?an dubu dubu guda 10 a ckn wata jaka miliyan Waya kenan,,, a matsayin kuWin nagani inaso da sadakin,,, har da cewa akwai sabuwar mota da gida da za su haWa da su. Ajiye kuWin ya yi a gaban Ammi tare da mata bayanin kayayyakin abincin da suka zo da shi.

Mamaki ne ya ?ara cikata ganin ana shirin yin cinikin ?arta,,, yo ciniki mana tunda neman siyanta suke a ganinsu dukiyarsu za ta sa ta amince da bu?atarsu,,, to ita ba haka ta ke ba farincikin ?arta ya fiye mata komai.


"?ata tana da wanda ta ke so,,, kuma shi za ta aura dan haka ina gdy da kulawarku da kuma ?aunar Wanku ga ?ata,,, ina masa ftn alkairi da kuma samun macen da ta fi Zahra koma"Tana kai ?arshen maganar ta mi?e tsaye.

Tumda ta fara maganar su ke kallonta da mugun mamaki,,, duk da talaucinta amma ko ganin miliyan Win nan da aka ajiye bai wani WaWarata da ?asa ba sai ta nuna halin ko in kula da ganin kuWin,,, kazalika kayan abincin da aka ambata.TaS lallai wannan matar na da wadatar zuci.


"Dan Allah kar ki mana haka,,, wallahi Wana yana ?aunar ?arki idan ya rasa ta bansan halin da zai tsinci kansa a ciki ba"Daddy yace ckn taahin hankali ganin tana neman shigewa gida,,, dama wannan ne abin duniyar su kaWai ne abubuwan da ya dogara akansu Wansa zai samu abinda yake so sai kuma gashi matar na neman watsa masa ?asa a ido ta ma nuna abin duniya ba ya gabanta ?arta ta fiye mata komai,,, to yanzu ina ya kama ya ri?e???


"Kamar yadda ka ke son Wanka,,, ka ke kuma son farincikinsa da son ganinsa ckn walwala,,, to ni na fi ka son tawa par da bu?atar ganinta ckn walwala da farinciki,,, ku gaida gida"Tana gaa faWin hakan ta shigewarta gida ta barsu a nan suna kallon kallo.

A take zufa ta gama baibaye Daddy,,, dan wlh tashin hankalin da yake ciki ji yake kamar ya saki kuka,,, dan bai san yadda Mubarak zai yi ba idan ya rasa yarinyar nan,,, wata?ila ma ya kamu da ciwon zuciya,,, dan ya ga yadda Mubarak Win ke ?aunar yarinyar kmr ya shekara dubu da fara sonta.

"Dan Allah ya isa haka menene na Waga hankali a wannan calm down pls,,, ga mata nan kmr jamfa a Jos duk kalar da Muba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?rak Win zai so ya samu za a samu menene na damuwa dan ya rasa wannan ?ar talakawan mtsss"Abokin Daddyn Mubarak yace yana bubuga bayan Daddyn.


"Nima haka na gani,,, sai ka ce wata ?ar gwal za a wani dage a kanta,,, yarinyar da bata fi a bada 100k ba daga sadakinta har lefenta amma an kawo musu dukiyar da ko a mafarki ba su taSa gani ba amma suna wasa da damarsu da wasa da hankulan mutane"?aya abokin Daddyn yace shima yana mi?ewa tare da karkaWe babbar rigarsa.


"Ba za ku gane bane,,, wlh ba za ku gane ba,,, Mubarak Wina ya mutu akan son yarinyar idan bai sameta ba komai zai iya faruwa da shi,,, duk wannan lissafin ?an Satan da ku ke hankalinsa baya kan su,,, kun san zuciya da abinda ta ke so!"


Shiru su ka yi suna fitowa daga zauren gidan.


"Bazan koma gida ba har sai na samu labari mai daWi da zan jewa da Mubarak akan aurensa da yarinyar nan,,, idan son samu ne ma in je masa da albishir Win an Waura auren su"Daddy yace yana jingina jikin mota.


"Ikon Allah to yanzu ya ka ke ganin za mu yi"Cewar abokin Daddyn.



"Me zai hana mu yi tambaya ko Allah zai sa mu samu wani daga dangin yarinyar wanda ra,ayinsu zai banbanta ana mahaifiyarta,,, su ga abin hannunmu su bamu aurenta wanda su ke dolen yarinyar su ke da iko akanta fiye da mahaifiyarta,,, ina nufin kaman dangin mahaifi ko ma dai wani na gaba da mahaifiyarta iayayen mahaifiyarta wanda za su iya sanayata dole ta amince da bu?atarmu"Cewar Daddy yana binsu da kallo.


"Wannan shi ne abin yi tabbas ka kawo shawara"
Suka haWa baki wurin faWa.
Su na cikin haka sai ga wani mutumi ya fito daga ckn wani gida can Wan nesa da gdn su Zahra,,, amma dai a layin nasu ya ke,,, yana goge machine Winsa da tsumma su Daddy suka ?araso inda ya ke.


Sun gaisa da shi sai washe ha?ora yake yi ganin mutane masu mai?o-mai?o a ?ofar gidansa.Sun gabatar masa abinda su ke so suna masa nuni da gidan su Zahran.Ya gane tambayar ta su kuma tabbas yana da amsarta domin kuwa duk wanda ke unguwar nan babu wanda zai ce baisan Malam Abdullahi ba ?anin mahaifin Zahra ba,,, dan yanzu ne ma baya zuwa unguwar nan bayan mutuwar Wan uwan nasa amma lkcn yana raye ai kullum yana gdn Wan uwansa.Sun ji daWin jin maganar dan haka suka nemi ya musu kwatancen gidan Malam Abdullahin,,, sai ma yace zai rakasu har gidan Abdullahin.

Machine Winsa ya tada yace su za su ke binsa a baya,,, su ka amince.Nazeer da ke hangensu ta ckn mota ya taSe baki.Su na shiga ckn motar Umman Mashkur da ta zo gidansu Zahra domin jin inda maganar zuwa wajen Baffan Zahra ina ta kwana,,, ta dinga binsu motocin da kallon mamaki jikinta har rawa ya ke,,, dan tabbas ta gane baban yaron nan da ya kulle mata Mashkur a police station,,, kuma yaron da Mashku ya ke faWa mata jiya sun haWu a gdn su Zahra.Jinjina kai ta yi ta juya ta shige ckn gidan,,, su kwa motocin tashin su akayi su ka tasarma gdn Malam Abdullahi domin gwada sa'ar su.



Umman Mashkur ta samu Ammi da Zahra zaune akan tabarma da alama ma idanun Zahra sun nuna ta yi kuka,,, Ammin kuma tana lallashinta ganin hakane yasa zaton da Ummar Mashkur Win ta ke ya ?ara tsaya mata a rai na da alama neman aure su ka zo ko dai wani abu mai kama da hakan.


?aki suka shiga suka bar su Zahra na ?arasa wankin,,, Sun gaggaisa ckn mutumci da tambayar bayan saduwa,,, Ammi sai jin babu daWi ta ke na ?in sanar da Umman Mashkur halin da ake ciki ba.



"Haba Ammin Zahra ya kuma na jiki shiru,,, babu labarin zuwa wajen Baffan na Zahra bayan kuma kinsan Babansa yana jiran jin amsa daga gareku"

"Wlh Umman Mashkur ina jin nauyi ne shi yasa ki ka jini shiru,,, yadda abun ya kasance ne babu daWin ji amma yanzu tunda Allah ya sa kin zo dole in faWa miki gskiyar abinda ya faru d...


"Haba Fa'iza ya za ku mana haka,,, duk da ban yi zaton wani abu marar kyau daga gareku ba,,, amma tun da na ji shiru jikina ya bani akwai abinda ke faruwa,,, sai gashi yanzu ma na ga mutanen nan a ?ofar gidan nan"

"Ya za ki min furucin daga gareki ba,,, haba Umman Mashkur,,, ko wani zai faWa miki wannan maganar ai bakya yarda ba,,, Zahra ta Mashkur ce insha Allah Zahra ba ta da mijin da ya fi shi,,, abinda ya faru shi ne...

Tiryan -tiryan Ammi ta bata labarin zuwanta gidan Baffan Zahra da abinda ya faru,,, kawo zuwan Mubarak da kuSa zuwan iyayensa maza da suka zo yanzu da abinda su ka tattauna.

"Allah sarki ni dama ina dai jin ba daWi a raina amma nasan ba za a taSa hana Mashkur Zahra ba,,, kuma tsakanin na da ke ya wuce hkn ai da kin min bayanin komai da tuni an yiwa tufkar hanci.Mu ai duk Waya ne babu wani Soye-Soye tsakaninmu,,, da kin faWa min ma da tuni ansan abin yi,,, ba wai lallai sai Baffan nata bane za a nemi aurenta a wurinsa ba,,, su ma waWan nan Wun son zuciya ne yasa suka zo"


"Wallahi kawai jin nauyinki ne yasa na kasa faWa miki,,, ace ?anin mahaifinta ya kasa bada aurenta ai abun da kunya wlh"

"Babu wani abin kunya,,, ai a duniyar nan babu abinda ba zaka gani ba indai kana raye,,, wasu mutanen watsi da zumunci ba komai bane a wurinsu"

Sun tattauna abubuwa da dama daga ?arshe dai suka yanke shawarar zuwa a faWawa Baban Mashkur Win ya san yadda za ayi tunda dole dai maganar maza ce dole Baban Mashkur Win ne zai yanke hukunci.




Daddy a dai - dai ?ofar gidan Malam Abdullahi su ka faka motocinsu,,, sun fito mai machine Win sai washe musu baki yake.

"Ranka ya daWe nan ne gidan"Yace cikin girmamawa.

"A toh babu komai Nazeer fito ka je ka mana iso"Daddy yace tare da fiddo kuWi kimanin 50k,,, hannun mutumin har rawa ya ke ganin kuWin da Daady ya mi?o masa.Rabon da ya ri?e kuWi mai yawa haka har ya manta,,, bai fi ya ri?e 5k ba amma gashi ckn lokaci ?an?ani da yayi rakiyar da bai fi man machine na naira 100 ya ?ona ba amma an bashi kuWi me yawa haka.Godiya har da tsugunnawa,,, daga ?arshe ya hau machine Winsa ya tafi cike da murna,,, ya bar Daddy da fargaba da tunanin yadda za ta kaya tsakaninsu da wanda aka ce ?anin mahaifin Zahra ne.



Mairamu tana ta fama da Malam Abdullahi da ke zazzaSi akan ya tashi ya sha magani,,, amma ya ?i sai jan bargo ya ke yana rufe jikinsa har kansa,,, dan sai karkarwar sanyi yake,,,zazzaSin ne ma ya hanashi zuwa kamfani wurin aikin gadin da ya ke sai yana jaraba akan abi ci komai ba ba zai sha magani ba.Ita kwa Mairamu ce masa ta ke ga Wumamen safe nan da bai ci ba ya tashi ya ci,,, yana cewa idan ba abu mai Wan daWi ba ba abinda zai sa ya ci tuwo ba.

Suna ckn wannan tababar ne su ka ji ana rafka sallama.


Malam Abdullahi yana daga cikin bargo yana karkarwar sanyi ya ke cewa.


"Wallahi ko ma waye indai ni ake nema babu inda za ni,,, da dai ma za ace wani ne ya kawo min zakka to kwa da na je,,, amma haka kawai azo a cika mutum da surutun banza,,, ke in ma kin ji masu bina bashi ne ki ce na yi tafiya"

Ita dai mairamu ba ta ce komai ba ta ajiye maganin da ta Sallo masa,,, tare da janye kwanan tuwon gefe,,, ta mi?e domin zuwa ta ji wanda ke rafka musu sallama da tsakar ranar nan.Dan lokacin sha biyu ta daWe da wucewa.


"Alaikumus salam,,, wai waye"Ta ce daga can cikin Waki kafin ta fito,,, shiru Nazeer ya yi har sai da ta zo zaure haba wa tana ganin Nazeer yanayin shigarsa da kuma wata tafkekiyar wayarsa ri?e a hannunsa,,, a take duk ta rikice ta fara washe baki.


"Wa alaikumus salam,,, a toh Wan samari kai ne mai sallama dama?"

"Eh"Yace a gadarance.


"Ikon Allah,,, Allah dai ya sa nan gidan ka ke nema ba wai Satan kai ka yi ba ko kuSa tambaya ka ke yi ba"

"Eh fa ina da tabbacin gidan nan nake nema"

Sosai mairamu ta washe baki tana nuna zalamarta a fili,,, da son abin duniya.


"Me gidan yana nan"

"Eh wlh ya...na...nan" Ta ce cikin rarraba kalamanta,,, duk ta rikice tana fatan dai Allah sa su sami kuWin shinkafa a wurin mutumin nan dan da ganinshi akwai ?amshin mai?o mai?o,,, ga me gida dama ba lfy idan aka samu shinkafa ai an warke.


"Ki sanar da shi alhazai ne su ke sallama a waje"Ya ce yana haWiye dariyarsa ganin duk ta ruWe da jin ana nemansu da ganinta irin mutanen nan ne masu son abin duniya.


"Alhazai! A ?ofar gidan wannan?"Ta ce tana Wan zaro ido tare da haWiye wani yawu,,, shikenan kakarsu ta yanke sa?a.

"Eh suna waje a manyan motoci,,, in...

Ai kafin Nazeer ya ?arasa magana Mairamu ta yi ciki da mugun sauri har tana haWawa da gudu.


"Malam! Malam!! Malam!!!"Tun daga falon ta ke rafka masa kira da uban ?arfi.


Cikin rawar sanyi har ha?oransa na haWuwa da juna ya ke cewa


"Wallahi babu inda zani,,, sai ki koma ki ce na tafi gona"

Hannu Mairamu ta kai za ta yace masa bargon aikuwa ya dage ya danne bargon.


"Ta...shi...maza...attajirai na kiranka a waje,,, da manyan motoci da a...

Kafin ta kai ?arshen bayanin Malam Abdullahi ya wangame bargon,,, kafin ta ankara sai ganinshi ta yi ya yi wata adungure mai haWe da shala ya wuntsilo daga kan gadon.


"Attajirai masu mota???"Ya ce yana Waukan hularsa tashi da ?wawa ya sakata,,, ko daidaituwa hular bata yi ba ya fara goge furkarsa da wani tsumma.

"Hankali dai kai da baka da lfy"


"Wane bani da lfy ai na warke,,, kina sanar dani na ji na warke,,, Allah sa su bani dubu uku wlh yau da shinkafa da taliya zan siyo mana"

"Amin ya Allah"Tace lokacin da ta rakoshi ?ofar Waki yana saka takalmi.

Yana fitowa ya ga abin da ya so Wauke masa hankalin ckn ?wa?walwarsa,,, manyan motoci da mota mai lodin kayan abinci ga alhazai dai duk da sun bashi baya amma ya san tabbas sai dai wani gdn su ke tambaya ba gdnsa ba.Dan Nazeer Win ma fitowa ya yi lkcn da Mairamu ta shige ckn gdn.

"Sannunku bayin Allah"Yace ckn Wari-Wari yana Wan lelle?a fuskokinsu,,, suna juyowa ya yi tozali da Alhaji mai kamfanin da ya ke gadi.

"Yawwa sannu"Su ka haWa baki wurin faWa.

"Alhaji"Malam Abdullahi ya ce yana kallon Daddy.Daddy da bai shaidashi ba sai yanzu da ya masa magana tabbas wannan mai gadin kamfaninsa ne,,, lallai abu zai zo da sau?i.


"Malam Abdullahi"Ya ce wani murmushin farinciki yana suSuce masa,,, ganin kazarsa za ta kama tarko,,, saboda sanin Malam Abdullahi da ya yi da son kuWi da kuma son abin duniya.


"Na 'am Alhaji in ce dai ko wani wuri ku ke nema"Yace ckn girmamawa,,, dan dai yasan bashi da matsayin da mutane kmr waWannan za su zo gidansa.


"Wurinka mu ka zo"Daddy yace yana baiwa masu motar kayan abinci umarni akan su fara sauke kayan nan su shiga da su ckn gdn Malam Abdullahi.

Idanu Malam Abdullahi ya zaro kan murna yana godiya har ?afafun Daddy ya dur?usa ya kama yake godiya.?ago dashi Daddy yayi yana nuna masa wannan ba komai bane.

Mairamu tana ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye,,, sai sallamar samari ta ji suna shigowa da kayan abinci,,, sakin baki ta yi ita dai ta rasa bakin magana sai idan Malam ya shigo ya bata bayanin daga inda wannan zakka mai dimbim yawa take Haka suka shige da kayan abinci sai lodawa sukayi wasu kan wasu.


"Da magana mu ka zo fa"Daddy yace dan ya ga duk Malam Abdullahi ya rikice ya san yanzu da wuya ya ?i amincewa da bu?atarsu.


"Mu shiga daga ciki bismilla"Yana faWa ya fara yin gaba ya fito da tabarma ya ajiye musu a zaure duk da zauren ba wani girmane da shi ba.Da ya shiga sai son jin labari Mairamu ta ke yace ta bari su tafi.

Bayan sun zazzauna Daddy ya fara gabatar da bu?atarsu,,, Malam Abdullahi da ke kan takalmansa zaune dan cewa ya yi ba zai zauna tabarma Waya ba da su Daddy ba.Tun da Daddy ya fara magana Malam Abdullahi ya saki baki jin irin abinda Ammi ta musu lallai matar nan ta samu matsala yanzu mutane kmr waWannan ta yiwa haka.

Babu Sata lokaci,,, ya ce ai aure kmr anyi an gama domin yarinyar ba ta da uban da ya fishi,,, dan Daddy na cewa da a yau ma za a Waura auren,,, a take Malam Abdullahi ya amince,,, Daddy ya fito da kudin nan miliyan Waya ya ajiyesu a gaban Malam Abdullahi,,, Malam Abdullahi kmr ya yi ?aramar hauka dan rikicewa da ganin tsabagen kuWin.

Goro da alawa masu mugun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login