Showing 69001 words to 72000 words out of 82877 words

Chapter 24 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2732

dai sauran magungunan islam da Zahran ke amfani da su hakan na ?ara mata sau?i sosai a jikinta dan yanzu ?urajen ma sun mata sau?in yin zafi.


Zee-zee ce ta shigo falon rai Sace kuma a fusace tana faWa kamar zata hau su da duka.


"Wallahi ?aryarku tasha ?arya kunyi kaWan wlh domin ni b sa'ar yinku bace, dan haka wlh zaku ga abin da zai sameku a yau Win nan dama dan naga dama ne kuke zaune a gidan nan amma a yau ba sai gobe ba zaku gane cewa ?yaleku nayi"


"Haba keko me yayi zafi haka me aka miji da zafi da za kike maganganu mararsa daWu haka idan...


"Dakata dalla malama, koma menene waye yake shiryawa idan bake ba, nan a samu ciki amma saboda ba?inciki kuka shiga kuka fita ?arshe sai da naje haihuwa akace min wai ba Wa bane ?ari ne bayan kuma inajin motsi kuma ko scanning da aka mun ina ganin baby nah amma kuka san yadda kukayi a ranar haihuwata kuka sa aka canja Wan da wani abu da shi da Wanyen nama ma duk uban su Waya ina ji ina gani aka sanya abun a kwali aka je aka binne cikin da har yau ban ?ara samu ba to wallahi na gaji da ganinku cikin gidan nan yau za a yita ta ?are!" Zee zee ta katse Ammi tana huci ta faWi hakan.


GabaWayansu mutuwar zaune suka yi dan sun rasa bakin magana, dan su duk cikinsu ba su san abin da ya faru ba sai yanzu, dan su ce musu aka yi ta haihu Wan babu rai.


"Ikon Allah! Haba yarinya wa ya isa ya canja abin da ke cikin cikin mutum in ba Allah ba, mu ina muka isa muyi wannan abu ai rashin imanin ma yayi yawa"Cewar Ammi cikin taushin murya dan ita gabaWaya ma sai taysayin yarinyar ya kamata .


"Ku ne mana har ma kuna da bakin cewa ba ku bane"Zee - zee tace tana harare -harare dan dama ta san ba su bane dan Malam ya sanar da ita cewa aljannun da yasa su canja Wan daga ?ari ne basu canja ba dama shi ya ajiye ?arin a mazaunin cikin nufinsa idan zata haihu aljannu su canja mata da ko da Wan aljannu ne amma sai aka samu akasi.



"Ke kar ki nemi ki faWawa mahifiyarmu magana, dan ba a yi wanda zai yi hakan ba ya zauna lafiya ba"Zahra da Hauwa'u suka haWa baki wurin faWar hakan.


FaWin hakan ke da wuya Zee-zee tayi kukan kura tayi kansu, ta cakumi wuyan kowacce da hannunta ita kuma Ammi sai ta yi kansu domin ta rabasu, hakanyayi dai dai da shigowar Daddy, Mubarak, Mummy Zee-zee na jin hakan ta haWe ?afafunta da cinyoyinta ta matse su wuri guda, ledar jinin dake ma?ale a cikin pant Winta ta fashe a take ta saki wani razanannen ihu tare da yanke jiki ta faWi.


GabaWayansu suka yi kan ta suna kiranta a kiWime ganin jini na bin ?afafunta,Mubarak kant ya Waga ya Wora a cinyarsa yana sakin kuka mai cin zuciya.

"Mummy shikenan sun Saran mun da cikin da nake jin shine rayuwata"Mubarak yace yana fashewaa da kuka tare da bin su Ammi da kallo irin na tsana.


Ammi kam ta ma rasa abin cewa Zahra kwa zaunawa tayi hawaye nabin kumatun ta Hauwa'u kwa hannu biyu ta Wora aka ganin sharrin da ake son ?a?aba musu.


"Yi shiru my son a yau zan kawo ?arshen komai tun da har kuka iya haWuwa kuka yiwa sirikata taron dangi kuka mata dukan da ya zama sanadiyyar zubewar cikinta"Daddy yace yana Waga murya kamar zai yi hauka.



"Alhaji ka saurareni haba ya ma za ayi ace mun mata tarom dangi ko da ace yaran nan za su aikata haka aini bai kamata ku sanyani a ciki ba bare ma babu wanda ya daketa itace ma ta tarki dukansu shi ne nazo zan...


"Ke saurara dalla!Duk irin halaccin da ake yiwa ?arki bakya gani, an zauna da ita babu wani amfani da take yiwa mutane a cikin gidan nan ?arshe gashi ta zama makauniya wa ya sani ma ko wani abun sharrin tayi yanzu kuma yake bibiyarta, dan haka duk hukuncin da naga dama shi zan yanke yanzu"Cewar Daddy yana bin su Ammi da kallon tsantsar takaici.


"Haba Daddy Mubarak bai kamata ka yanke hukunci ba, ba tare da ka ji daga garesu ba kuma ina yiwa Ammi da yaranta kyakkyawan zato ba za su aikata hakan ba kawai dai...


"Ke saurara min wallahi idan kika ?ara wata magana a bakin aurenki!!!"Daddy ya dakatar da Mummy ta hanyar daka mata tsawa.


Shiru Mummy tayi tana kallon su Ammi da sigar tausayin abin da ake zarginsu da shi.



"Mubarak ina baka umarni duk da nasan kaima umarnin hakan kake jira ka saki yarinyar nan saki uku sakin da babu wani aure da zai ?ara haWaku!"



"Na sake ki saki uku!!!"Mubarak yave kamar dama jira yake.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"Mummy, Ammi Hauwa'u suka haWa baki wurin faWa ita dai Zahra a zuciyarta ta faWa.


"Ku haWa ya naku ya naku ku bar gidan nan yanzun nan, ba tare da Sata lokaci ba dama haka kuka zo tun da ku baku san mutunci ba"Daddy yace yana yatsina fuska.


Idanun Ammi ne suka ?an?ance tabWi lallai Wan adam tabbas komai zaka nema ka nema a wurin Allah tabbas Wan adam wataran sai ya maka gori duk da ba duka aka taru aka zama Waya ba.

Ammi ce ta kama ?a?anta ta rungumesu tare da cewa Hauwa'u ta Wakko jakar kayanta haka Hauwa'un ta Wakko akwatin kayanta, dan banda jakar Zahra mai wayoyinta sai ?aramar akwati data zuba mata kayanta haka suka fito Mummy na kuka tana basu ha?uri ji take kamar ta nitse a ?asa saboda kunya.Amma Ammi tana nuna mata babu komai.Ta dai buWe jakarta pose ta fiddo takardu da makullan gidan da aka basu ta mi?awa Mummy dan dama basu koma gidan ba sannan gorin da Daddy ya yi yanzu yasa Ammin jin komai ya fitar mata a rai.Har sai da Mummy ta ga Ammi na zubar da hawaye sannan ta karSa.





Zee-zee kwa ji take kamar ta tashi daga kwancen da take ta taka rawa saboda murna da farinciki,haka aka kwasheta zuwa asibiti da yake dama sun haWa baki da likitan tun a waya hakan yasa yace cikin ya Sare duka babu wani wankin ciki da za a mata magunguna aka rubuta mata kawai data farfaWo.



Ammi dai duk da auren nan ba wani son shi ake ba amma sai da ta ji babu daWi a ranta sosai taji abin ya taSa mata zuciya sai dai tana fatan hakan ya zama alkairi a garesu baki Waya.


Ko Zahra ma maimakon ta ji daWin sakin tun da ba son auren take ba sai ita ma ta dinga jin ranta babu daWi, haka suka koma gida Ammi ta cigaba da musu nasiha da nuna musu su yarda da ?addara dan abin sosai ya dami Hauwa'u ma ba komai ke musu zugi da suka ba illa dalilin yin sakin sharrin da aka musu sai dai sun yarda kuma sun san cewa Allah yana tare da su.



_Bayan wata guda_


Abubuwa sun caSewa Zee-zee dan yanzu gabaWaya ta kasa gane kan Mubarak kullum abu Waya faWa da hantara kamar wacce ya tsana ga yawon club da hotels ana kawo mata labarin irin tsiyar da yake shukawa a gari, dan ko Neesa ita ma da ka yi bikinta yanzu ba daWin Nazeer Win take ji ba duj sun juya musu baya.


Abin da ya kawo jagulewar lamarin Malam yace dama bai ce ta fitar da Zahra daga gidan a cewarsa kawai ta mata wani sharrin amma dama idan aka saki Zahra to komai na asirin da aka yiwa Mubarak Win zai karye dan shi yasa ma yanzu yake iya kusantar wasu mata ba kamar a baya ba da a wurin Zee-zee ne kawai yake namiji.




SANADIN KISHIYA NE




NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



PAGE 3?? 5??




Ammi ta tashi tsaye sosai akan Zahra basa bacci su duka sun du?ufa da yin addu'a ba dare ba rana dan ganin Allah ya bata lafiya.Yanzu sana'ar yin gugguru take yi mutane suna sara, sai ku shago da ta buWewa Ibrahim abokin Mashkur da yake yanzu an zama Waya hakan yasa aka siyar da sar?a da Wankunnen Zahra na gwal aka kama shago tare da zuba kaya a ciki sai Allah ya sanya albarka yanzu babu abin da suka nema suka rasa.




Cikin hikima da ikon ubangiji sau?i na samuwa sosai dan yanzu ?urajen sai suke motsewa da kaWan -kaWan,gashi yanzu abin da ke zuba Win ma yanzu babu ko alamarsa Allah ya Wauke mata shi sai godiya ga Allah.



Tun washe garin sakin Zahra Ummar Mashkur ta kirashi a waya ta sanar dashi abin da ke faruwa, dan dama bata taSa faWa masa wani abu game da Zahran ba dan bata so ya shiga damuwa, shi kuma ba zuwa yake garin ba dan tun da ya koma kano tsawon shekara biyu da wani abu sau biyu ya taSa zuwa Zariya shi ma shigowar magrib yake yi sai ya yi tafiyar sassafe shi ma dan zuwan ya zama dole amma baya son zuwa garin kwata -kwata saboda idan ya kusanto garin yana jin kewar Zahra sosai ya kan ji sonta ya dawo masa sabo dal.



Wayar da Umma ta yi masa ta sanya shi a cikin tashin hankali jin cewar an saki Zahransa abin da ya Sata masa rai ma shi ne auren ko shekara uku bai yi ba amma aka saketa, shi da yake da burin idan ya aureta sai ko mutuwa ce za ta raba su amma yanzu ga wani banza can ya ci moriyar ganga ya yada korenta.


Lokacin yana busy dan haka bai samu damar zuwa Zariyar ba, domin yanzu kasuwa ta cigaba sai albarka ke ?aruwa dan shi yanzu ma ba ya jin ko aikin gwabnati ya samu zai yi saboda sabo da kasuwanci.Tun da aka faWa masa an saki Zahra yake jin abubuwa guda biyu abu na farko haushin sakin da aka mata abu na biyu kuma wani abu mai kamar farinciki dan tun sanda Umma ta sanar masa ya ji duk wani nauyi da ya daWe a zuciyarsa ya sauka, yana jin kamar ya zama tsuntsu yaje ya ga Zahra, domin itace kaWai a zuciyarsa dan ko a Kano ya haWu da ?an mata da yawa wandansu da kan su suke cewa suna son sa ya aure su amma wani abi sai dai yayi murmushi kawai dan baya jin akwai wata mace da zai iya bata gurbi a a cikin zuciyrshi.Tashin hankalinsa Waya jin larurorin dake tare da ita.



Amma kuma wani abin mamakin Umma tun tana sa ran ganinshi har dai ta cire rai abin ya Waure mata kai sai dai babi yadda za tayi ne, har dai ta fara tunanin ko dai dan Zahran ta taSa aure ne amma kuma a iya saninta Mashkur ba zai fasa son Zahra ba dan kawai ta taSa aure tun da dama ko bayan auren Zahran ta san har yau bai daina ?aunar Zahra ba rashinta ne ma yake hanashi zuwa garin.


Bata tunanin wata mace za ta Wauke masa hankali aka soyayayar Zahra duk da Wan adam na canjawa ako yaushe kuma a kowane lokaci, musammman ma da ake cewa kuWi da kuma mace na canja namiji a kowane lokacin amma dai tana yiwa Mashkur Win kyakkyawan zato akan soyayyar da yake yiwa Zahra.


Ko Zariyar ma ba ya maganar zuwa ko gida ma da ya siyawa su Ummar Ibrahim kawai ya aikowa kuWin aka siya musu har suka tare a gidan amma bai zo ba itama kuma Ummar ko da sun yi magana a waya bata sake masa magana akan Zahra ba ta barshi ne ta ga iya gudun ruwansa duk da bata san dalilinsa ba kuma bata so ta sani, amma ita a tunaninta a ranar da ta faWa masa zai iya yiwa Zariya tsinkaye a washe garin ranar in ma bai shigo a ranar ba.


Wasa - wasa sai da aka kwashe watanni uku amma babu Mashkur babu labarinsa babu alamar zuwansa garin Zariya.

Zahra ma tun da aka saketa take sanya ran zuwa Mashkur garin ko dan ya zo ya dubata dan ta san dai Umma ba za ta kasa sanar masa halin da take ciki, duk da ta san ba lallai ne ya zo dubata ba sanda tana gidan aure akwai kuma igiyar wani akanta amma kuma yanzu ai bata da aure.Kullum kunnuwanta a buWe suke hankalinta akan ?ofa tana sauraren da wanda zai shigo gidan domin har kullum cike take da begen jin muryar Mashkur Win tun da ta san yanzu dai bata da idon ganinsa.


Amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, tun tana sauraron ringtone Win wayarta in an kirata ko za ta ji ance Mashkur ne tun da ita ba gani take ba amma sai dai ta ji shiru babu kira ko da a waya ne.Hatta Ammi ta san Zahran na cikin damuwa duk da bata faWa mata damuwarta ba amma ta san tabbas akwai lauje cikin naWi, kuma itama Ammi a nata Sangaren tana mamakin rashin zuwan Mashkur Win duba Zahra ko da ace ya canja she?a ma'ana ya samu wata wacce ya canja ra'ayi ta Wauka zai zo ya duba Zahra ko dan zumuncin su da mahifiyarsa amma shiru.

Zahra ita har ta dangana da zuwansa ta sanyawa ranta ha?uri da dangana dama Mashkur ne take sanya rai akan sa cewa duk runtsi duk wuya ba zai taSa rabuwa da ita ba, duk lalurar da ta sameya zai iya zama da ita ashe dai ba haja bane tun da gashi wata uku da sakinta amma bai ma tuna inda take ba bare ma ya tako ya zo inda take.Hakan yasa ta cire rai da wata aba soyayya bare ?auna dan dama yawanci mutane suna son mutum ne saboda wasu abubuwan zarar ya rasa abubuwan to su kwa sun daina marmari son sa bare har su ?auna ce shi hakan yasa ta sanya a ranta cewa tun da ta samu lalurar ?uraje da makanta to dole ta sanya a ranta cewa babu wani da zai ?auna ce ta musamman da Mashkur ya manta da ita haka ta ringa baiwa ranta da zuciyarta ha?uri akan hakan.


Allah sarki kowa yana da ?udurinsa hakan yasa ake so kar ka yankewa mutum hukunci ba tare da ka ji ta bakinsa ba, yin hakan zai sa ka munanawa wani zato akan kuma yana da kyakkyawan ?uduri a zuciyarsa domin Allah kaWai ya san abin da ke cikin zukatan mutane!

A ranar da Zahra ta cika wata uku da kwana Waya ana washe garin gama idar ta, da misalin ?arfe biyar da rabi na yamma, yammaci ne mai cike da tarin ni'ima babu zafi sannan babu sanyi sai dai yanayin ya dace da yadda kowa zai ji hakan ya masa daWi.Dan dama ace zafi yayi yawa ko ana sanyi mai shiga gaSoSi shine za ka ga an samu banbancin ra'ayi na yanayin wani yace zafi, yafi wani kuma yace sanyi ya fiye masa.


La'asar ce sakaliyya tafe yake a cikin motarsa da bai daWe da siyanta ba, a hankali yake tu?i sai dai jin ransa yake kamar ana sanya masa ?an?ara saboda wani sanyi da ke ratsa ran nasa da kuma tarin farincikin da ke cikin zuciyarsa.Ga kuma karatun qur'anin da yake suararo daga sudais shi ne ke ?ara sanyaya zuciyarsa yana kuma sanya mishi nutsuwa.


A dai -dai ?ofar gidan ya tsaida motar a hankali ya Wago kansa tare da sauke akan gidan kallon gidan yake tamkar a yai ne ya fara ganin gidan, rabon da ya biyo layin nan ma tun ranar da zai koma garin Kano da zama, tun daga wannan ranar ko da wasa bai yarda ya biyo layin ba amma a yau sai gashi bayan lokaci mai tsawo ya dawo ba ma layin kaWai ba har gidan zai shiga ji yake kamar a wancan lokacin da yake tsaka da zuwa gidan a kowacce rana domin yin tozali da kyakkyawa kuma tauraruwar zuciyarsa.


Cikin natsuwa ga buWe ?ofar ya fito, sanye yake cikin dark blue Win shadda Winkin tazarce babu hula a kansa dai dai gashin kansa da yake kwance luf a kan nasa domin bai kasance mai tara gashi ba, sai sajen fuskar da ta matukar yiwa kyakkywar fuskarsa ?awanya ga girarsa mai yalwa da ba?i da gashin idanunsa masu tsawo, sai sajensa wanda ya zagaye har bakinsa sai dai babu gemu a haSarsa.

Fatar jikinsa da tayi matu?ar yin kyau sai she?i take farinsa ya ?ara bayyana idan ba wansa ya san Mashkur sani na ha?i?a ba idan ya ganshi ba zai shaidashi ba dan gabaWaya ya sauya ga hutu da ya ?ara bayyana a tattare dashi sai ?amshi turaruka da ke tashi daga jikinsa masu matu?ar ?amshi.?ofar ya maida ya rufe tare da sanya key ya rufe ?ofar, gidan ya durfafa cike da shau?i marar misaltuwa.


Zahra ita kaWai ce cikin gidan Ammi da Hauwa'u sun fita za su je gidan suna a can ciki anguwar, dan haka ita kaWaice a gidan, tashi ta yi tana so za ta shiga bayi sandarta ta lalimo a hankali ta shiga dafa bango tana lalumawa haWe da neman ?ofa da sandarta ta.Sai dai Ammi tace Hauwa'u ta zauna amma Zahran tace su je tare tunda ita Hauwa'u ?awarta ce me haihu ita Ammi maman yarinyar ce suke zumunci.Dan haka ma Zahra tace su je babu komai za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login