Showing 60001 words to 63000 words out of 82877 words

Chapter 21 - SANADIN KISHIYA NE Book Original by Maman Afrah.doc

30 Aug 2025

2749

Mummy ne suka sauka akan tafukan hannayen Zahra saboda, da ta kama sai taji wani ?ulu-?ulun abu data ri?e hannayen, idanunta ne suka firfito ta zaro su tamkar zasu faWo cikin kiWima ta saki hannayen da sauri sannan a ruWe tace



"Menene wannan a hannunki Fatima?"

Shiru ne ya biyo baya dan Zahra kukan zuci yaci ?arfinta, ta kasa furta komai dan jin yadda Mummy ta saki hannunta ta san tabbas idan tayi arba da fuskarta kuma sai dai ta ari na kare wato ta ruga a guje.


"Yana part Wina a upstairs "Zahra tace cikin muryar kuka.

Jin abin da tace yasa Daddy ya wuce cikin gidan ya bar su nan tsaye dan shi bai ga abin da Mummy ta gani ba na hannun Zahra, damuwarsa kawai ya ga lafiyar Wansa.


"Menene a hannunki Zahra?"Mummy ta tambayeta a karo na biyu idanunta na kawo ?wallar tausayin Zahran, duk da bata san menene ya sameta ba.


"Nima a haka naga ya fito min da safe"Tace har lokacin kanta acan gefe, idanunta na zubar hawaye har lokacin, amma sai taji girma da martabar Mummy ta ?aru a gunta ganin dai tayi tozali da hannunta mai kama da hannun aljana amma bata gujeta ba, gashi har lokacin tana jimami da jin tausayinta tabbas Mummyn ta cancanci yabo.

"Ya salam! Zo mu je ciki ki min bayani Zahra, amma me yasa kike Soye fuskarki?"Tace tana kamo hannayen Zahra.


A karo na farko da Zahra taji hankalinta ya kwanta, jin wacce ba mahaifiyarta ba taga yadda jikinta yake kuma ta ?ara taSa jikinta ba tare da ?yama ko tsangwama ba, ba tare da ta ?yamace ta ba.


"Duk jikina ne har fuskar"Cewar Zahra tana jinjina ?o?ari irin na Mummy tabbas tasan ko Amminta iya abin da zata mata kenan.

"Ya hayyu ya ?ayyum"Mummy tace tare da sanya hannu ta juyo da fuskar Zahra domin su kalli juna.


Itama Zahra hankali kwance ta juyo da fuskarta ta domin hankalinta a kwance yake kuma ta yarda Mummyn ba zata nuna mata ?yama ba.


"Subhanallahi!!! Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"Mummy da ta tsorata sosai da ganin fuskar Zahra ta faWa cikin tashin hankali, dan ita tun da take a duniya bata taSa ganin halitta mai ban tsoro ba kamar yadda taga fuskar Zahra ta koma.Da sauri ta maida kallonta ga ?afafun Zahran dan ance idan aljannu ne ana ganin kofato a maimakon farata (farce).


Ganin dogon hijab Win Zahran ya rufe har ?afafunta, ta sanya hannu ta Wago hijabin tare da taimakon Zahra suka cire hijabin.Mummy kawai kabbara take hawaye kwa kamar an buWe famfo tsabar tausayin Zahra daya gama cika mata zuciya, ganin gabaWaya jikinta babu wata masakar tsinke yasa ta kama hannun Zahra suka shige cikin gidan su duka suna kuka kamar an sanar dasu mutuwa.




*Daddy*


Da bibbiyu yake tsallake step Win gabaWaya hankalinsa a tashe dan baya jin zai samu nutsuwa, da salama har sai yayi tozali da tilon Wansa Mubarak.Yana hawowa saman ya shiga waigawa dan ya rasa ma a wane Wakin Mubarak Win yake.


"MUBARAK!" Ya buWe murya ya rangaWawa Mubarak kira, Mubarak kwa dake a tsorace jin an ?walla masa kira sai ya ?ara gigicewa, dan shi bai ma saurari muryar dake kiransa ba saboda tsananin ruWewa duk tunaninsa aljanar ce zata bayyana, shi yasa take kiransa cikin ?araji haka.


Wani gumi ne ya shiga keto masa a take suka shiga kokwawa da numfashin sa, du?un?unewa yayi a wuri Waya yana ta addu'o in da ba ya ?arasawa yake haWewa da ?arashen wata hatta addu'ar shiga banWaki sai daya karanta, dan tun lokacin yana ?arami sanda yana zuwa islamiya kafin ya kangare ya Wan iya wasu amma ba dukansu ba wasu farkon su ya iya wasu kuma ?arshen su.


Daddy kuwa jin shiru ba a amsa ba ya ?ara shiga damuwa dan shi tsoron da yake kar fa Zahra kashe masa Wa tayi, tun da auren dole ne aka mata, kuma ya sha jin labarin amaren da ke kashe angwaye a daren farko idan aka musu auren dole.Bare ma da ya ga yarinyar ta kasa haWa ido da su, kuma mai gadi ya faWa musu cewa yaji Mubarak yayi ihu a jiya da dare.


"MUBARAK!!" Ya ?ara rangaWa masa kira a karo na biyu.


"Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, dan Allah ku min rai, idan wani abu kukeso ku faWa min in muku, ku bani umarni amma kar ku cutar dani, ni indai Zahra ce ma kukeso in barta ku faWa mini, wayyo Allah na wayyo Daaddy wayyo Mummy ina jin dama gidan nan ba a sauke Qur'ani ba a cikinsa, muka tare gashi yanzu kwanan mu Waya amma har na fara gamo"Mubarak jin an ?ara kiransa ya faWa kansa sunkuye cikin gwiwar ?afarsa ya sanya hannu biyu ya dafe kansa, dan shi bai ma san ta inda sautin kiran yake fitowa ba.



Daddy kwa yankewa kansa hukuncin dudduba Wakunan yayi, ko zai ga Mubarak Win duk da zuciyarsa na cike da mugun tsoro kar yayi arba da gawar Mubarak Win.Dan ya san da ace yana raye to tabbas da ya amsa, dan ya san wannan kiran ko wanda ke ?asa zai jiyo shi bare kuma Zahra tace yana saman.


?akin dake gefen damarsa ya kama handle Win ?ofar ya kama ya murWa amma yaji ?ofar rufe ya murWa ya murWa amma yaji a kulle da makulli.Mubarak kwa jin an taSa ?ofar ana ?o?arin buWewa ya yi mutuwar zaune dan kaWan ya rage ya suma saboda tsananin tsoro.


Daddy kwa jin a rufe ya shiga duba duka Wakunan, sai dai su abin mamaki ba a kulle su ba da makulli, tsaf ya gama dubawa babu kowa a ciki, aikuwa tunanin sa ya karkata akan cewa tabbas Wansa yana rufaffen Wakin.Dan haka ya koma ya shiga doka ?ofar da ?afarsa.Mubarak jin za a Salle ?ofar sai ya shiga danna uban ?araji da ihu, yana ta sumbatu akan a kawo masa Wauki kar su Waukeshi su kaishi birnin sin ko kuma su kaishi kukar bulukiya matattarar aljannu.


Daddy jin muryar Mubarak sai hankalinsa ya kwanta dan ya tabbatar bai mutu ba sai dai kuma ya kasa gane kan sumbatun da yake da neman Wauki.


"Mubarak Daddyn ka ne fa nazo ni da Mummyn ka, ka daure ka buWe ?ofar"Daddy ya faWa jin Mubarak Win ya saurara da ife-ifen.


?iff Mubarak ya haWiye kukansa tare da tasowa yazo ya buWe ?ofar, dan ya ji muryar Daddyn sa ce, yana buWewa Daddy ya shiga binsa da kallon mamaki ganin gabaWaya a ji?e yake jargaf dan zuwa lokacin yayi fitsari yafi kala biyar sai wani uban zarni dake tashi daga jikinsa...




DAGA AL?ALAMIN
'?
'?
MAMAN AFRAH>?p?>?p?






SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS ERITER'S ASSO...


PAGE 3?? 0??


A hankali Daddy ya rungume Mubarak yana Wan bubbuga bayansa alamar lallashi, sosai yake jin tausayin tilon Wan nasa saboda ya san ba ?aramin abu bane zai sanya shi razana haka.


"Sannu son, ka yi ha?uri babu abin da zai sameka, ka cire tsoro da firgici a ranka"Cewar Daddy yana shafa sumar Mubarak Win.


"Amma Daddy baku ga aljanar ba lokacin da kuka shigo"Mubarak yace yana waige-waige kamar wanda ke tsoro bayyanar wani abu.


"Aljana kuma?"Daddy yace cike da mamaki.


"Eh Daddy wlh aljana ce ta firgita ni, ni ban ma san aljana bace har dafata na yi"


"Ah gaskiya kam mu babu abin da muka gani, ko dai mafarki kayi?Amma babu kowa a gidan nan sai matarka dan itace ma ta buWe mana ?ofa muka shigo"


"Itace Daddy, Zahra ce aljanar ai"


"Lafiyarka kwa Mubarak ko dai gamon kayi da gske, har ya fara taSa maka ?wa?walwa?"Daddy ya faWa idanunsa na fitowa waje.


"Wallahi Daddy yadda naga Zahra da fuska da jikinta duk na aljanu, ina tunanin ma dama can Zahra ba mutum bace"



"Gaskiya ka samu matsala babba ma kwa, yarinyar da yanzu ma ita ta buWe mana ?ofa amma kana haWata da jinsin aljanu?"


"Shikenan Daddy inaga gizo take min"Mubarak ya faWa ganin Daddy ba fahimtarsa zai yi ba shi kuma ya matsu a fitar dashi part Win ma gabaWaya.


Hannunsa Daddy ya kamo suka sakko ?asan domin yaje ya yi wanka, dan jikinsa sai Wigar fitsari yake.Suna sakkowa Mubarak ya toge a step Win ?arshe yace bazai sakko ba, ganin Mummy da Zahra zaune a falon sai sharar hawaye su ke da alama dai Zahran wani abu take faWawa Mummyn.


Daddy da bai lura da abin sa Mubarak ya gani ba yace.



"Ka zo kaje part Winka ka watsa ruwa ko ka daina zarnin fitsarin nan, amma shine ka tsaya ka ?i gaba ka ?i baya"


Da hannu Mubarak ya shiga yiwa Daddy nuni da Zahra da ke zaune kusa da Mummy kanta sunkuye sai share ?walla take.



"To waye ba?onka a cikin su Mummyn taka ko kuma matar taka?"Cewar Daddy yana kallon Mubarak ganin duk ya wani ruWe.


Ganin yanayin da ya shiga yasa Daddy Win tsayawa da nasa idanun akan su Mummy wai ko zai ga abin da Mubarak Win ya gani, ko kuma aljanar yake gani a kusa da su Mummyn.Idanu ya zaro ganin Zahra kamar wata halitta da ba, ta mutum ba halittta mai ban tsoro dan baka ganin komai a jikinta da fuskarta sai manyan ?urajen nan gashi tayi wani ba?i kamar ta shafa ba?in gawayi.


"Mummyn Mubarak!!!" Daddy ya faWa da ?arfi ganin Mummy tana zaune kusa da Zahra a tunaninsa ko ita bata ganin abin da su ke gani.


Mummy ce ta Wago kanta, da idanunta da suka mata jawur saboda kukan tausayin Zahran, ta saukesu akan Daddy da ke ?o?arin furta wata kalma amma ta?i fitowa.


"Ba...kya...ganin abin da ke gabanki"Daddy yace yana binta da kallon mamaki, sai yanzu ya yarda da maganar Mubarak da ke cewa Zahra ce aljanar.


"Ina gani mana Zahra ce Allah ya jarabceta da fitowar ?uraje a jikinta"Tace tana Waga masa hannayen Zahra domin ya hango yadda jikin ya koma.



"Ke yanzu kin yarda cewa mutum ce? itace fa duk ta firgita mana yaro fa kiga yadda duk ya fita hayyacinsa ba gudunta ma fa yayi"



"Ta faWa min komai, shi me yasa bai yarda da ?addara ba? ?addarar da ta sameta a cikin gidansa"


Shiru Daddy ya yi yana nazarin kalamanta, can kuma sai ya sakko daga kan matakalan, a hankali ya ?araso wurin da suke zaune ya ?urawa Zahra idanu yana kallonta cikin mamaki da al'ajabi


"Wai kina nufin Zahra ce wannan?Ba wai aljana bace, ta yi shiga da kamarta?"

"Tabbas itace a wayewar yau wannan abin ya sameta a cikin gidansa amma saboda ya nuna halinku na maza shine har ya fara nisanta kansa da ita, shine har ta zame masa dodanniya"Mummy tace tana share hawaye da bayan hannunta.


"Gaskiya na tausaya mata amma ke kanki idan kika kalli yarinyar nan ba ?aramin tawakkali da imani ne zai sa ki zauna a kusa da ita ba, saboda yadda gabaWaya jikinta ya koma"


"Hakane amma bai dace ace ya mata haka ba in bai rungumi ?addara ya lallashi matarsa ba, ai ba ya gujeta ba har ya shiga Waki ya rufe"Mummy tace tana juyawa domin hararar Mubarak Win, amma abin mamaki babu shi babu alamarsa a wurin.


Shi ma Daddy juyawa yayi domin ganin inda Mummy ta kalla, shi ma wayam ya gani babu Mubarak babu alamarsa.



"Wai saman ya koma"Ya tambaya da mamaki.

"Ya fita daga part Win"Zahra ta bada amsa kanta a sunkuye hawaye na zuba a idanunta, dan ita ta ga lokacin da ya fice har da gudu-gudu ya haWa.

"Ikon Allah"Mummy da Daddy suka haWa baki wurin faWa.




*HAUWA'U*



Sai shiri ake domin ziyartar amarya Zahra dan dama sun ce za su je ita da su Hannatu ?awayen amarya, bayan ta gama shirinta tsaf ta yiwa Ammi sallama, Ammi ta bata hisnul muslim Win Zahra da ta manta, domin karantawa saboda samun kariya da tsari.Cikin jakarta ta saka ta fita tana sauri kar su tafi su barta dan lokacin ?arfe Waya ma har ta kusa.



A ?ofar gidan su Hannatu ta samesu har sun firfito, Hannatu ce sai wasu ?awayensu guda biyu, napep suka tare guda biyu suka faWa masa inda zai kai su.


A ?ofar gidan ya ajiye su suka sallameshi ya ja napep Winsa ya tafi, su kuma suka tura get Win suka shiga, me gadi suka samu zaune kan benci, sun gaishe dashi tare da gabatar masa da kan su ya basu izinin shiga.Abin mamaki ?ofar da zata sada su da cikin gidan a buWe take, haka suka shiga kansu tsaye, part Win amarya suka nufa suna ?o?arin shiga da sallama suka ga wani mutum ya fito da hanzari a fusace, shi kwa Daddy da ya fito da niyyar bin bayan Mubarak bai ma ji gaisuwar da suke masa ba.



Da kallo suka bishi, suka juya suka shiga falon da sallama.Mummy ce ta amsa musu suka shigo kowa baki a washe kamar gonar auduga sai murnar ganin amarya suke.Tun da suka shigo Zahra bata Wago kanta ba kanta yana sunkuye hawayen jin zuwansu ya cigaba da kwaranyo wa daga idanunta da basu da maraba da garwashi saboda kukan da ta sha yi yau.



Suna shiga Hauwa'u a guje tayi gun Zahra cike da murna da farinciki ta rungumeta, a hankali Zahra ta Wago fuskarta aikuwa itama Hauwa'u ta Wago fuskarta sai kuwa idanuwansu suka sar?e da na juna.Wani irin zaro idanu Hauwa'u tayi cikin firgici da razana tace


"Ya Zahra"




"Hauwa'u"Ita ma Zahra ta kirata da sha?e??iyar muryarta.


Su Hannatu kwa mutuwar tsaye suka yi ganin yadda jikin Zahran yake da ba a san da me za a kirashi ba.




"Ya Zahra me ya sameki kuma?"Hauwa'u tace tana ?ara rungume Zahra tare da fashewa da wani kuka mai taSa zuciya, ganin halin da ?ar uwarta take, ba dan Zahra jininta bace kuma ko da Zahra mutuwa tayi ta dawo ba zata taSa gudunta ba, da ba Zahra bace a kusanta ba, ba lallai tazo ba amma dama masu magana na cewa in kaji kana cewa ba zaka iya ba to bai sameka ba.



"?addara"Zahra tace tana goge hawayenta, ita kuma Hauwa'u na tattaSa ?urajen tana hawaye.



"Ku yi ha?uri dan Allah komai ya samu bawa daga Allah ne"Mummy tace cikin muryar kuka ga tausayin yaran d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a ya cika mata zuciya.


"Hannatu mu zamu wuce sai kun taho"?awayen Zahra suka haWa baki wurin faWa, kafin Hannatu ta basu amsa har sun dangana da ?ofa.Kai ta jijjiga cikin sanyin jiki Hannatun ta nufi wurin su Zahra, suka rungume juna su duka ukun baka jin komai sai sautin kukansu.



MAMAN AFRAH>?p?=?
?=??

SANADIN KISHIYA NE
>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?



NA




MAMAN AFRAH


FIRST CLASS ERITER'S ASSO...


PAGE 3?? 1??



Mubarak na zuwa part Winshi ya samu wayarsa tana ringing kallon inda wayar take ya yi ya Wauke kai dan shi halin da yake ciki ba ta waya yake ba.Yana shirin shiga bedroon ya ji wayar ta cigaba da ruri har zai shige sai kuma ya dawo Baby nah shi ne abin da ya gani a jiki, a take yaji kan sa ya wani sara masa a maimakon ya Waga wayar sai kansa ya dafe saboda tsananin sara masa da yake.



Wuri ya samu ya zauna amma har zuwa lokacin kan nasa bai bar sara masa ba, sannan kuma wayar bata daina ringing ba da kiran ya katse sai kuma wani ya ?ara shigowa.A hankali ya mi?a hannu ya Wakko wayar yana mai danna ok ya kara wayar a kunnensa.


"Ka manta dani ko?"Ya tsinci muryar Zee-zee a ckn dodon kunnesa.A take yaji kan nasa ya daina sara masa sai wani farinciki da ya mamaye masa zuciyarsa saboda muryarta da ya tsinkaya.


"Kiyi ha?uri ban manta da ke ba, ni kaina bansan mai ya Waukeni ba na kasa tunawa da ke sai yanzu da naga kiranki a take naji wata sabuwar soyayyarki ta sokeni a zuciyata" Yace yana jin wani nishaWi da jin muryar Zee-zee.


"Ba wani nan bayan kayi aurenka kana can da amaryarka ka manta dani"


"Ke dalla wa yake ta amarya, amarya ko jidali"



"Kamar ya?"


"Ki bari kawai Baby, ai ni wannan auren nayi da na sanin yinsa"

Wani mugun daWi ne ya rufe Zee-zee jin kalaman Mubarak sun tabbatar mata da komai ya tafi kamar yadda Malam ya tsara kasancewarsa, domin alamu sun nuna cewa babu wani abu daya faru tsakanin Mubarak Win da Zahra, sannan kuma ta fahimci cewa son Zahra da ke cikin zuciyar Mubarak Win ya dan?are wanda hkn duk cikin aikin Malam ne.Ga kuma uwa uba yace bai manta da ita ba lallai komai yayi dai -dai sai aure kawai ya rage tsakanin su.


"Da na sani kuma"


"Eh ke dai bari kawai"


"Amma na jajanta maka haWaWWen guy kamar ka amma yake da na sanin yin aure"


"Bar maganar nan, ki shirya zan shigo da la,asar mu fita mu Wan huta"

Wani irin ihu Zee-zee ta saki jin abin da Mubarak yace, sannan ta maida wayar kunnen ta tace


"Ina jiran zuwanka"

"Ok bye"Yace tare da kashe wayar, shi ma yana kashewa ya mi?e tsaye tare da naushin iska yace
."Yess"

Ji ya yi an banko ?ofar da ?arfi, Daddy ne ya shigo a fusace yace


"Wai Mubarak me yasa baka da hankali ne, ya zaka bar yarinyar mutane da lalura kana gudunta maimakon ace yanzu kana neman yadda za a yi a nemo mata magani ko ta samu lafiya amma sai kuma kake wasu abubuwa kamar mai taSin hankali"Daddy ya ?arasa faWa cikin Sacin rai.


Mubarak sanyaya muryarsa ya yi saboda Daddy yaji tausayinsa yace


"Dan Allah Daddy ka yi ha?uri nifa ba wai gudunta nake ba ya za ayi na guji matata, amma Daddy ka duba yadda jikinta yake wlh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login