Showing 15001 words to 18000 words out of 98705 words

Chapter 6 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt

11 Mar 2025

4299

domin bar ganin ƙatara dukiya ba."


Ya fada mishi haka tare da barin gurin. Kallon Bafaden Khamil yayi cikin zafin zuciya yace.
"Meye wancan ya gaya min?"
"Ai yana nufin kodan albarkaci shigowar ta masarautan nan bata cancanci duka ba, ka dake ta. Sannan abinda yake nufi na gama kai ma baka fi karfin Allah ya jarabce ka ba."


Rintsa idanun shi yayi tare da cewa.
"Duk inda kuka ga Yarinyar nan ku kawo min ita sai na bulata."


Ya fada yana huci tare da jin zafin jikin shi..
***
Kukan da nake tare da shasheka ya sani kasa musu bayanin me ya faru, shiru suka yi har ya shigo ya wuce abin shi.
"Zane ki suka yi? Toh me kika musu?". Cikin sabon kukan da yazo min nace.
"Aunty Mufeedah ban sani ba, kawai daga shigowa na, yasa aka fara zane ni"
"Karya kike munafuka, ina ce munafunci kika kulluwa Princess Natashah a Shamaki catering services, har Aunty Nafy ta baki sakamako mai kyau, So shine Ya Khamil yayi punishing dinki zaki zo kina bude baki kina acting like baki san me ya faru ba, stupid kawai" inji Sawwama.


Sake baki nayi ina kallonta, hawaye na zuba min kafin na mike a hankali na dauki kayana, zan fita.
"Ke zo nan" inji Moddibo,
Wani irin tsoron su da tashin hankali ne ka kuma kama raina, ban san lokacin da na matse kafana fitsari zai sauko min nace.
"Wallahi ba haka bane ni aikin daga yau na daina bana so zan koma gurin Innata"


Abin dariya ya ba Mai Kano yadda tayi maganar kamar wata Aroosh.
"Dalla stop dat childishly" inji Sawwama.
"Toh Ni nace bana son aikin ba tafiya zanyi ba." Na fada ina kuka. Saukowa Asad yayi yana kallon agogon shi.


"Kizo ki zauna yau zamu fara aiki kuma kice zaki tafi anya kinyi mana adalci." Kallon su nake sabida basu san yadda nake ji bane.
"Mother yarinyar nan ta daku fa, wallahi ku kaita ciki ku duba ta"


"Mufeedah wannan aikin kine ki kai ta ki duba ta."
"Toh zo muje!"
Haka ta bita dakin ta, tare da cewa.
"Off de outfit"
A hankali nake zare hijab dina, na cire shi tare da nad'e shi, zuge zip din rigar jikina nayi tare da barin shi iyakar kirjina.
"Juya min" a hankali na juya mata,
"Sai ina." Tana kallon farin bra din jikinta, duk da kayan jikinta ya nuna matsayin ta, amma tsaftar da take gani ajikinta ya burge ta.
"Don't worry am a doctor."
Ta gaya min, a hankali na zare d'aga skirt dina, mika min towel tayi na cire kayan, shigowa Sawwama tayi na ja hijab dina na rufe jikina.
"Me kike bukata?" Inji Mufeedah,
"Nazo ganin ciwo ne?"
"Of ana mutunta privacy din mutum ko ba haka ba?"


Fita tayi ita kuma ta Cigaba da shafa min magani.
"Shekarar ki nawa?"
"22 zan shiga na uku nan da three months"
"On August kenan, keda Yayan month dinku daya."


"Wani level kike?"
"N.c.e jiya na fada baki ji bane"
"Me yasa baki yi joining Unimed ba?" Ji nayi kamar ta zage ni. Tura mata baki nayi naki amsa mata, shigowar Maman su ya sani kallonta.
"Mother gaskiya sun fasa mata jiki, zan mata allur..." Wato ban san lokacin da na isa bakin kofar zan fita da gudu ba, kamar zan suma.


Dariya abin ya basu, aikuwa suka sani a gaba sai sun min allura, sun bani kulawa tare da sani na Kwanta sabida zazzaɓin da ya fara kama ni. Sai karfe biyu na tashi nayi sallah sannan muka shiga kitchen. Dake na tab'a aiki da wata balarabiyar Sudan,na koyi dafa shayi a gurinta. Mun yi nisa a aikin dake Siyama har tazo ta tafi nice dai zan wuni a gidan.


Tunda na fara hada kayan shanyin na dauko brown sugar na hada sannan na saka kayan kamshi dangin citta kanumfari, masoro, kajiji. Kirfa. Na'ana', habbatunsaudat, lemon grass, kwayar tafarnuwa, coffee tsabar shi iya shi na juye na nutsu akan shi na fara dafa musu sannan na maida hankali akan soya kosai da nake yi. Dake na taso naga ina tana soya kosai a bakin hanyar unguwar mu, na buga kosan sosai.


Kamshin ne ya cika kitchen, kallona Mama tayi tare da cewa.
"Wannan shayin zai yi dad'i, daga jin kamshin shi" dake sun tafi sallar la'asar, ni na rigasu tafiya.
Ciro kaza tayi tare da cewa.
"Miyar Papa ne tuwon dawa, idan ruwan yayi ki min magana. Ga kayan miyan nan". Murmushi nayi sannan.nace mata toh. A rayuwar duniya ina son baza fasahata a kan girki, wanke wanken nayi, sannan na jefa a cikin gidan. A hankali na fara na aikin miyar na hada mishi kayan kamshi dake tace min baya son yaji, sai na barshi da kayan kamshin musamman citta da kanumfari. Sannan na rufe tukunyar.


Na daura tukunyar tuwon dawa Aunty Mufeedah, tace.
"Allah Yarinyar nan kina da sauri. Wow shayin nan zai yi fa"
"Aunty Don Allah bani honey pure"
Dauko jakar zumar tayi tare da mika min, na diba tare da zubawa a cikin shayin. Sannan na koma kan miyana, sake dawar irinta kamfanin semo ce wata Dawavita! Ruwan nayi na tuka shi tsaf har yana wani fidda kamshi. Sannan na rufe shi.


Muka shiga aikin tuwon sahur, muna yi muna hira, har muka gama na juye shayin nan a flask uku da wani karami, sannan Mama tashi go,. Dama kunun tsamiya tayi tare da kallon abin da muka yi tace.
"Ina Mabrooka?"
"Tana can d'akinta."
Bata kuma magana na, ta saka hannu muka kwashe biski, miyar yakuwa. Sai pepper meat da muka yi, kafin karfe shida mun hada kome har da fruit salat, na fito lokacin Mabrooka ta shigo kitchen ɗin ya daura jallof din taliya, Ni kuma ina shirya abincin a dinning table.


Ina gamawa na nufi inda aka ware min kayan abincina a basket, lokacin Siyama ta shigo dan ance tana zuwa amsar abincin ta. Tana karb'an nata muka yi musu sai da safe.


"Kai Mother wannan yarinyar ko computer sai haka, wallahi ta iya girki ga tsafta. Kafin mu gama ta wanke kayan da muka b'ata, yanzun haka babu wanke wanke sai wanda zamu b'ata da buda baki da Sahoor." Inji Mufeedah,
"Wai yaushe kika fara yabo ne haka!"
Tsaki tayi tare da mai da hankalin ta a tafsirin Sheikh Ibrahim khalil, shigowar Asad ya kalle su yana cewa.
"Ku bani coffee saura minti biyar a sha ruwa"
"Sai dai kunun tsamiya" inji Mother, "ok" ya faɗa tare da haurawa sama, yayi wanka yana fitowa ana kiran sallah, dama yayi alola, dan haka gajeren wando ya saka da Jallabiya ya sauko, tea din Buhayyah suka fara sha musamman Mufeedah dan da kwadayin shi a ranta.
"Kai Jama'a amazing yarinyar nan karshe ce. Mother gwada sha" jan kujeran yayi ya fara shan kunun tsamiya sannan yace.
"A bani coffee."
"Wow kasha shanyin mana yayi dad'i"
Kowa a gurin idan ya sha shayin sai ya yaba, amma banda Asad dan dama shi haka yake bai cika son abinda ake zuzzuta shi,
"Sawwama hado min coffee" ya faɗa.
"Amma Ya Asad, shayin ma"
"I said coffee" ya faɗa a masifance, mik'ewa tayi tana tura baki, yaje ta dafa mishi bai nayi sosai ba ta kawo mishi. Karb'a yayi tare da kurb'a tsaki yayi tare da mik'ewa ya nufi hanyar masalaci.
"Wallahi na kuma kamaki kina waya da saurayi sai na karya hannunki, useless kawai wacce coffee ya gaggare ta dafawa"


Haka mazan suka tafi masalaci, kuka ta saka tare da shan coffee din taji babu laifi. Mabrooka itama ta mike, duk suka tafi sallah. Basu kuma dawowa ba, sai karfe bakwai, sannan suka sauke abincin a kasa aka fara sabin. Dake ba wani abu bane dai haka suka yi buda bakin suka tashi aka kwashe kayan abincin sannan suka nufi masalaci. Kafin ya fita yacewa matar shi.
"Ki dafa min coffee"
"Toh" a ranta kuwa haushinsa take ji ga shayi amma yaki sha. Haka ta nufi hanyar kitchen ta haɗa wuta amma babu coffee ya kare, kamar zata yi kuka haka ta kashe gas din ta fito.


Tunda tayi sallah ta manta da batun coffee, shi kuma yana can ya sami Bashir suna hira har zuwa karshe goma, sannan ya shigo gidan. Yana shiga yayi wanka tare da saka kayan barcin shi fari kal me laushi, yana gamawa ya fara aikin shi can ya fara jin ƙishin ruwa.
Kiran Mabrooka yayi tare da cewa ta kawo mishi coffee, bai tsaya yaji me zata ce ba ya kashe wayar shigowa tayi sanye da wata matsiyacin rigar barci, dan kyau yayi mata kyau, tace mishi.
"Daddy babu coffee nan ya kare" ta faɗa a tsora ce.
"Ai ho, waton ga dan iska ko? Shine kika ajiye ni ba zaki gaya min ya kare ba, toh wallahi jeki nima min abinda zan sha" ya kam masifa shi ta rena shi,


Shigowa tayi ta flask din shayi ya ajiye mishi, da kofi. Zata fita yace mata.
"Ni zan zuba? Ki kuma tafi da flast din" ya faɗa zuba mishi tayi a mug din sannan tayi ta fitarta, sai ya kalli shayin sai ya kauda kai. A ranshi kuwa masifa yake shi waye ya mutu waye ya dawo dole ya sayo machine din coffee,yana yi yana masifa. Can yayi nisa da aiki kamshin shayin ya daki hancinsa. Had'iye yawun yayi tare da kallon kofin. Kasadar dauka yayi sai da tsigar jikin shi ya tashi. Ya hakura, jin ance yar aiki ce ta haɗa. Ya sashi jin ƙyamar shayin indai wancan yarinyar da ya gani fuskarta kamar Akuya ta dumulo gari.


Can dai yayi kasadar daukar kofin ya saka a bakin shi yayi skiping shayin, lumshe idanun shi yayi tare da cewa a ranshi.
*Tsarki ya tabbatar ga Ubangijin talikai. Rahama da jin kai ya daddu akan wannan yar aikin*
Ya fada yana jan shayin, yana wani irin gyada kanshi cikin yanayi na musamman, tunda ya kafa kanshi bai d'ago ba, sai da ya shanye tass, sannan ya mike a hankali. Tare da nufar hanyar kasa.


Yana sauka ya nufi kitchen, ya kuma cika kofin ya haura zama, yana aiki yana sha yana aiki, shanyewa yayi tare da sake sauka yaje diba suka haɗu da Mufeedah dan shi flast din ya dauka zai wuce tace mishi.
"Ya haka? Ya Asad, kawai ajiye mana" ajiyewa yayi tare da zuciya zai bar gurin.
"Don Allah ban san zaka yi fushi ba ɗauka ka tafi dashi" b'ata rai yayi tare da cewa.
"Ki zuba min ina sauri ne" dan kar ta kawo mishi hari. Da sauri ta zuba mishi tare da mika mishi. ya juya tare da barin gurin.
Dariya ya bata, tana cewa a ranta.
*Zaka ji da gulmar ka"
Haka ta zuba nata ta bar kitchen ɗin.


Shi kansa dariya kanshi yake yadda ya b'ata rai kamar zai yi wani abu, haka ya sha shayin. Kafin ya kwanta.
-:-
Lokacin da muka isa gida, na zubawa Innah kunun tsamiya tasha sannan na shiga ban daki nayi alola da wanka nazo na gabatar da sallah, domin muna hanya aka sha ruwa, ina idarwa na shiga kokarin cin abincina muna hira. A hankali nake bata labarin abinda ya faru. Amma ban gaya mata an dake Ni ba, sabida kar ranta ya b'aci. Bayan na gama na zauna ina mata karatun Alqur'ani, ina karatu tana kuka.


Haka da asuba ma muka yi sahoor, kwanciya nayi bayan sallah Asuba.
-:-
A gurin Sahoor raba ido yake a gurin shayin aka zuba mushi, bayan ya sha ya fara kokarin cin abincin. Aka juyewa Papa tuwo dawar shi miyar kuka sai kamshi yake.
"Papa zanci tuwon dawa nan"
"Amma dai yau kai zaka ci tuwon dawa?"
"Papa kaji su ko? Cokali daya fa zanyi"


Tura mishi warm yayi tare da cewa.
"Bismillah"
"A'a muci tare."
"Ok!" Daukar spoon yayi tare da gutsira tuwon a hankali, ya dauki tuwon ya saka a bakin shi, wani irin lumshe idanun shi yayi..
"Alhamdulillahi masha Allah. Wow perfect..." Ya cika bakin shi da tuwon......
_Warning. This article contains pornography and sex warnings for girls and widows ..._
7/9/21, 8:02 PM - Buhainat: 0️⃣9️⃣
بسم الله الر حمن الرحيم...


Duk da sun san shi mutum ne da baya boye abu idan yayi mishi amma yaba girki ba nashi bane, ko sau nawa Mother zata yi baya tab'a yaba mata balle kuma ya nuna jin daɗin shi. Sai gashi wannan lokacin yana yaba abincin yar aiki. Mutumin da duk inda ya shiga yana da kwararrun masu mashi girki na musamman. Sabida rena mata da yayi.


Yana ci yana gyada kai sai da ya cinye tsaf yace.
"Rabona da cin abincin nan tun hajja Falmata tana raye gashi nan yau na kuma ci."


Kallon Mother yayi sannan yace mata.
"Umma don Allah wannan ya zama abincin sahoor din mu." Ya fada tare da nufar sama, tare da ɗaukar katon jug din shi na tea ya haura.
"Prince Aliyu Asadullah da kanshi yana daukar kaya ba zai bari dauka mishi ba"

Banza yayi musu dan baya son magana, dake akwai sauran time na sahoor ya dauko project din shi ya shiga yi yana shan shayi, saura minti goma kacal ya shanye shayin.


-:-
Washi gari.
Dankalin turawa muna gyara bayan na gama taya Siyama wanke wanke, dan yayi mata yawa kuma gashi bata saba ba, muna gamawa na kama aikin gyara dankalin tayi min sallama, ta tafi, tana tafiya aka kawo kayan cikin saniya, na zauna na gyara tsaf sannan muka zuba wasu a deep freeza, sauran muka daura farfesu.


Ina cikin tafasa namar na wurga mishi yankakken lemun tsami, kamshi ya cika ko ina. Na mai da hankalina akan aikin Ta shigo.


Kallona tayi tare da da kama aikinta, nima kuma tun da na d'ago kai naga fuskarta a daure tsoron ta ya kamani.


Ina dauke farfesun na kashe gas din sannan na nufi waje dan na takura.
"Yawwa Buhayyah yanzun Moddibo zai kawo fruit Baban Aroosh ya aiko shi ina ga ki raba biyu kiyi nama fruit salat irin na jiya, dan ma bai sha ba. Amma yana son fruit salat."


"Toh Mama!"
"Buhayyah don Allah idan akwai berries don Allah kin iya shaka kiyi mana"


"Toh Aunty!" Na ce mata.
Ina zaune aka kawo kayan, na fara a hankali Ina aikin ina bin karatun da aka saka a gidan tv, tana aikinta ina nawa, tana kallon lokacin da na zuba zuma da madara a fruit salat din.
"Waye ya gaya miki kowa ne yake shan irin wannan haɗin?"
"Kiyi hakuri wallahi ban sani bane, dake nayi aiki da Larabawa sai nake ganin kamar is normal."


Tsaki tayi tare da Cigaba da aikina, shigowar Aunty Mufeedah taga na hada shaka yayi kyau nayi na defference colours, na fruit. Abun ba karamin burge ta yayi ba, dan haka ta shirya su a freeza, sannan na ce mata.
"Kuyi hakuri yanzun ban san yadda zanyi da wannan fruit din ba na saka mishi madara da zuma, sai dai ko zan markada shi "


"Duk yadda kika yi za a ci ai baki ga yadda ake ta santin shayinki na jiya ba." Kallonta nayi sannan nace mata.
"Shayin yan Sudan ne, maybe da zaki ji wakar al laila bi laileh, ai shi suka koɗa"
"Laaa wakar da suke cewa Nassi sharahali, mahuwa bimazahar intar sukar" murmushi nayi naga itama yar kara'i ce dan haka muka markad'a muna aikin mu, Matar Yayar su sai fushi take tare da masifar da babu gaira babu dalili musamman da yarinyar tazo muna aiki tana hira na dauke ta na ajiye ta a kitchen ilanda, kawai ta kama masifa kamar zata dake ni tsoro ya hana Ni magana sai da Mama ta shigo ta sallame ni sannan ta juya ina barin gidan.
"Kinsan bana son sakarcin banza. Meye nufinki? Meye yarinyar tayi miki?"


"Mother!" "Ban haifi dan da za ayi kazamin kishi akan shi ba, dan haka ki kama kanki aiki tazo yi idan ta gama ba zaki kuma ganinta ba, bana son yada kai sannan ban da fitina ai Natashah zaki fara rigima da ita ba wannan ba, wato mara gata ko? Ita kuma Natashah yar babban gida ba a fada da ita dan kar a tsane ki? Da ita xaki yi kishi ba da Yar da bata san mijinki ba, dan bata tab'a ganin shi ba balle ya dame ta, Kinga ko Mazan gidan ta damu ta san su ne? Mace kenan wacce uzurin gabanta shine nata ba nawa Ni ba"


Bayan an sha ruwa da ruwan Shayin yayi buda baki yana jin wani irin nishadi a ranshi, har ya tafi masalaci ya dawo tare da ɗaukar fruit salat din zai sha tace mishi.
"Yar aiki tayi fa, ba Umma bace tayi." Kallon Mufeedah yayi tare da cewa.
"Ya tsafta me aikinku dan naga wata yarinya da uban lipstick din bakinta kamar an tsoma kan akuya a gari,"


Cin abinci take cikin kwanciyar hankali tace mishi.
"Wallahi Ni dai ba gamsu da tsaftarta idan ka cire tsoron bala'i da Allah ya daura mata bata iya ko fada ba, balle wani abu. Kai Umma da Allah ya yoni a namiji wallahi sai na auri yarinyar, domin tana da nutsuwa da halayyar zamantakewa."


"Toh aci abinci dai."
A hankali yake shan fruit salat din, yana lumshe idanun shi yana jin wani azazzaben dad'i. wanda har kunnen shi yana motsi, a hankali yake sha har ya gama bai kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login