Showing 90001 words to 93000 words out of 98705 words

Chapter 31 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt

11 Mar 2025

4317

Mai Martaba Sarkin Tankara ya kawo ni haihuwa.


Ya kira Mabrooka tare da cewa ta kai yaran Abuja maza ta biyo jirgi, tazo mu zauna tare. Natashah kuwa turata yayi Abuja ta zauna da su Umman shi, wani irin kulawa yake bani tunda ya san cikin yana raye a jikina,. Haka yayi ta ina ina sani, har Mabrooka ta iso, gidan shi da yake nan London dan bai sayar ba, ya barshi idan suka zo hutu su sauka a gidan, daya side din ne ya bada hayar shi, ba karamin dad'i yayi min ba, dan haka dakuna hudu ne a gidan.


Biyu a sama biyu a kasa, wani irin kulawa suke bani daga ita har shi, cikin kamar jira ake a san dashi kawai ya fito sosai. Kullum muna hanyar motsa jiki, idan ka ganni sai ka sha mamaki kayi wani irin kiba, gashi kun san Oga Aliyu babu sauki, yana samun faraga zai nemi abun.


Kullum muka zauna a falo muna hira Yana matsa min kafana, ita kuma Mabrooka tana kaiwa da komowa, dab abin tab'awa aikin ta kenan sai nace mata.
"Aunty zauna ki huta"


"Tab muna jiran twins zan zauna na huta ai nida hutu sai kin haihu sun kai wata biyar zan huta." Dariya nayi nake kallonta babu ruwanta yanzun.
"Wata biyar lallai akan me?"
"Sabida Yarana ne, Ni na dace da kula dasu."


"Toh wallahi ina haifan su, zan tattara miki kayan su, ku kare kalau"
"Sai dai na kuma loda miki wasu, tunda Allah yayi min lafiya nayi ta durawa mata ciki abina kema Mabrooka saura ke, ki gama hidimar ta na daura miki yan uku....
7/19/21, 11:35 AM - Buhainat: "Don Allah rufa min asiri, a haka ma ya nakare balle ka hada min zafi biyu kai ko tausayin mu baka ji, daukar ciki babu sauki fa, da maza ake bawa rikon cikin da ka sha mamaki domin duk wata tara zaka haihu"


Ta faɗa tana dariya, matsa min kafa yake yana murmushi.
"Queen Been, kinji ko? Wai wai duk bayan wata tara zan na ajiye mata yan dagwai dagwai, sai kace injin"
Daukar pillow nayi na maka mishi ina hararan shi, tare da cewa.
"Baka da kirki, wato mune zamu ta zuba maka haihuwa kamar awakai kai kuma kana gefe cikin mulki kana murmushin mugunta, toh ba damu ba, sai dai ka kara aure ka cika mana ta huɗu amma dukkan mu hutawa zamu yi sai ranar da muka dawo aiki"


Wani narka fuska yayi yana kallon mu.
"Yanzun hade min kai zaku yi?"
"Me zai hana? Tunda mu ma. Ba son iyayen mu suke ba, kaji ka da wani zance, babu mai maka haihuwa sama da biyar."


"Idan na kama ki sai na zane ki da bulaliya na." Ya fada tare da cire agogon shi, alamar zai shiga sallah.


"Aunty Mabrooka kinji shi ko?" Na fada tare da tura mata baki,
"Kyale shi can ta matse mishi" ta faɗa tana dariya,


Babu laifi amma zaman mun gwanin ban sha'awa, muna girmama junan, kuma ta gefen shi yana ƙoƙarin mana adalci, muna cikin haka Ya gaya mana Yaran da Natashah zasu zo.


Duk da ba wani abu bane, amma daga ni har Mabrooka mun ji babu dad'i, haka muka shiryawa zuwan su.


***
Shiru Bashir yayi yana kallon mahaifin shi, sannan yace mishi.
"Matsalar ba anan take ba, bana son damuwa wallahi kuma yana cikin binciken ake turo min gargadi akan babu ruwana da abinda ya shafi Asad, idan wani abu ya same ni kar nayi kuka da kowa nayi da kaina.


Abba duk me bibiyar rayuwar shi yasan abinda yake yi, wallahi na razana. Domin kuwa sun gaya min abubuwa da yawa akan shi, don Allah Abba ku taimaka mishi, yadda ba zasu cutar shi ba."


"Nima na jima ina mamakin wanda yake bibiyar rayuwar shi, amma Insha Allah yana dawowa kome zai zama tarihi" karshe ya cigaba da rarrashinsa, tare da nuna mishi kome mukaddari ne, kawai dai hassada ce irinta mutane.
***
Ranar talata.


Da safe su Natashah suka sauka a garin London, duk da tana zuwa Dubai sai dai bata tab'a tsammanin haka London yake ba, koni zuwa sai da nayi kauyanci amma Alhamdulillahi. Daga zuwa na, na fahimci garin dake nuna fita sosai.


Nice na shiga nayi duk abinda zamu yi, na girki nace Aunty Mabrooka ta huta, duk da bata huta ba, tare muka yi ta aiki. Har suka iso. A hankali nake takawa ina saka yan kunne na. Suka shigo,
"Assalamun Alaikum."
"Waalaikumun Salam, barkan ku da zuwa.". Shigowa yayi tare da kallon zai min magana, kawai ban san me na taka ba, wallahi kawai na tafi zan fadi. Tare ni yayi ya na fada a kirjin shi, tare da sauke ajiyar zuciya.


"Alhamdulillahi, Ban fadi ba" na fada ina kallon shi.
"Kiyi a hankali mana, karki janyo min magana."
"Sannun ku da zuwa"
"Ashe an ganki a ina kika shiga?" Ta faɗa tare da kallona,, tana kallon cikin jikina. Murmushi nayi sannan nace mata.
"Kinsan kowa ya dora miya, sai ya nemi abin kad'i, balle kuma ni da nake da abin kad'awa har da girkawa." Na fada mata ina murmushi.
"Ai haka ne fa,Masallacin kura, ba a baiwa kare limanci."


"Hmm! Waye ya gaya miki birnin kura akuya bata talla, ai me abun fada shi ya shiryawa abin maidawa, idan kin gama ki haura sama dakin na biyu, shine naki zaki sami kome, Yarana ku nufi dakin can nawa ne, ku huta."


Na nufi kitchen, na dauki abincina da Aunty Mabrooka ta dafa min, murmushi nayi na nufi hanyar waje, zama yayi a kusa dani.
"Kinsan matsayinki kuwa?" B'ata rai nayi ina cin abincina. Daura hannun shi yayi akan nawa.
"Kina da da daraja da yawa, don Allah karki biye mata kusa mu matsala."
"Iskancin da aka yi min da ne ba zan dauka ba, idan da an dake ni yanzun babu wanda zai gaya min magana na kyale shi, Yawwa koma dan waye sai na tsayar mishi."


Na fada ina mik'ewa, "toh don Allah kiyi hakuri ban da rigima" cikin kunkuni nace mishi.. "rigima kan yin shi zanyi wallahi, sai dai idan mutum bai tab'a ni ba" na fada ina hararan shi.


Lallab'a ni yayi tare da raka ni d'akina, haka na yiwa yaran wanka bayan na basu kananun kaya sun saka nace musu.
"Ku haura first room zaku ga Mommy dinku"


"Toh Aunty Buhy" suka fada.
"Kids daga yau ita ba Aunty Bane, ita sunanta Mami, Maman Aanisah kuma Maama. Kunji yaran kirki maza kuje ku huta". Suna fita ya tako har zuwa gabana,
"Bee"
"Please bana son ciwon kai" na fada ina mike kafana, riko hannuna yayi tare da zauna dani,
"Me yasa kike jin haushina? Kiyi hakuri ba zan kuma ba kinji, nasan nayi laifi amma hukuncin yayi tsauri dayawa, wallahi bana jin dadin yadda kike horani a dakinki nan"


Rike hannun shi nayi, ina kallon shi kafin na janye idanuna a cikin na shi.
"Shi kenan ka bar bani hakuri, babu dad'i ne kawai daga zuwa zata haifar mana da damuwa,"


Rungume kaina yayi yana murmushi,
"Ina tare dake babu wanda zai haifar muku da rikici, karki biye mata, abokin magana take nima, don Allah karki bari shaidan ya tunzira ki."


Haka yayi ta rarrashina, tare da gaya min magana me dad'i, har muka iso inda ba zan iya hana shi ba. Sai dai kash cikin jikina yayi min cikas domin baya barinsa ya dake dani ainun.


--- bayan sallah la'asar muka fito, shi kuma ya nufi dakin Natashah.
Kallon shi tayi tana shirya Yarta,
"Sai yanzun yar Sarkin Kano ta Barka ka fito? Na zata rike ka zata Yi baki daya, sai naga ashe duk jarabarta haka zata barka" ta faɗa tana gyarawa yarinyar ta, zaman kayan ta, sannan ta fasa mata turare suka fito, bai ce mata cikanki ba, haka suka fito. Na samu yaran sun ci abinci har sun fita wasa, itace dai bata ci abincin ba sai da muka fito.


Kallon juna muka yi da Mabrooka,
"Maman Uku"
"Insha Allah kece zaki dauki uku bani ba," na fada ina zama a kujeran da ta ja min, mamaki ya kama Natashah, ganin yadda muke hira tare da tattaunawa. Haka muka ci abincin baka jin maganar kowa sai ta cokali, muna gamawa muka dawo falon anan ne yayi mana nasiha da kuma muhimmancin rayuwa da zaman lafiya, kuma Alhamdulillahi mun fahimce shi.


Nan ya raba mana kwanakin mu, sannan ya fara daga kan Natashah, bayan mun gama abincin dare nida Mabrooka, muka zauna a falo muna kallon tare da hira. Tun bayan sallah isha da ya jamu, suka shiga cikin basu fito ba sai karfe tara saura, lokacin munci abinci mun bar musu.


Namiji dan baban shi, babu ruwan shi, sai dai daga Yadda yake cin abinci zaka Fahimci yana mugun jin yunwa, sai da ya cika cikin mu, aka cigaba da hira tana gamawa ta wuce sama, babu wanda ya damu da ita sabida kuwa kowa takanshi yake, hira muka bude domin yaran mu sunyi barci.


Nice na fara mik'ewa lokacin da ta fito tana kallon shi da wata Mahaukaciyar rigar barci. Tsaya mishi tayi a kai tana magana.
"Ya Asad kasan dare yayi kuwa?"
"Eh na sani"
Mik'ewa Mabrooka tayi tare da nufar hanyar d'akinta, kafin kace me duk mun watse mishi, dakyar ya mike tare da bin bayanta.


Tunda suka shiga suke Abu daya, baki daya ya gama gajiya, kamar ya gudu ya bar gidan, haka har gurin asuba, kafin ya damu barci. Natashah irin jahilan mata nan ne,.marasa tsoron Allah, tunda taxo ta cika cikinta da magungunan mata, bata san kanta take cuta ba.


Dan haka tayi ta addabar shi da jaraba, ko ya dauka sai ta kuma tab'a shi yadda zai sake mik'ewa cur, kafin karfe hudu dai da ya haɗa mishi coffee, a nan ta zuba mishi wani maganin da ta sashi karfi har kusan Asuba kafin ta kyale shiga barci, dakyar yayi Sallah Asuba ya dauko ya gudu dakin shi.


Ita damuwarta matukar zai cita toh bata da matsala dashi, dan haka a kwana ɗaya da yayi mata, ba karamin matsanancin ciwo bayan shi yake ba.


Domin kuwa bayan shi yayi mugun ciwo na fitar hankali, haka ya sauka a dakin Mabrooka, ranar barci yayi domin ya gaya mata bayan shi na ciwo, haka ya gama kwana dayan shi da zazzaɓi me zafi, sakamakon wancan maganin da Natashah ta saka mishi, ranar girkin Buhayyah kuwa.


Tunda naga ya wuni bai fito ba abinci ma dakin ake kai mishi nace mata.
"Kinga ya zauna a dakinki sai yaji sauki ni kam babu abinda zai min."


Bata so ba, amma naci karfinta da baki, wasa wasa sai da muka dangana dashi ga asibiti fa, anan suka gano maganin karin karfin maza ya sha, kallon shi muka yi cikin mamaki muke kallonshi.
"Yaushe ya fara sha?"
"Baya sha, sai dai idan an bashi yasha matar shi ta dafa mishi tea cikin dare dan anan tabar kayan, nice na gyara kitchen ɗin"


"Allah ya kyauta nace mata," haka muka gama tattaunawa tare da zama jikin shi, tabbas wannan shine tashin hankali, haka dai abin babu dad'i.


Komawa muka yi gida, tare da kwana washi gari.
Tare muka kawo mishi abinci.
"Barka da safiya Honey"
Inji Mabrooka, murmushi ya sakar mata, sannan ya mika mata hannu, ta girgiza mishi kai tana faɗin.
"Ban san ya akayi tayi barci ba amma ta gini buƙatar ka" ta faɗa tana nuna mishi ni.


Bude min hannun shi yayi. Na isa gurin shi har da guntun hawayena.
"Ya isa mana"
Ya fada tare da shafa bayana.
"Sannun kinji"
"Ya jikinka?" Inji mabrooka,
"Da sauki sosai"
"Allah ya baka lafiya" inji Mabrooka, haka muka wuni muna ririta shi, sai yamma Natashah suka zo da Mai Kano, da Yaran, haka muka yi ta hira, zuwa wani lokaci suka ma sallame shi. Muka dawo gida.


Daga nan na mishi bayanin yanayin shi, da kuma kiyayye maganin da aka bashi, bai ce kome ba amma yasan Natashah ce zata bashi ya sha.


Da dare bayan ya kwanta ta biyo shi dakin shi.
"Baby kayi hakuri wallahi ban san cewa zaka samu matsala da maganin ba da ban saka maka ba."
"Dama ina zaki sani? Tunda ba lafiyarki bace, kinci darajar Abba tabbas da na gama zama dake kenan, kuma daga yau idan zaki sha maganinki ya tsaya iya kanki karki kara min abinda zai kashe ni, bana so karki kuma"


Kamar da gaske taji shi amma sam bata ji fadar ba, kawai haukarta take yana gamawa ya fita tana bata rai, tana isowa falo.
"Duk bakin cikin dan kaza bai zai ci dan shawo ba, duk abinda zayi da kalan dangi da zaku yi sai ku nida Aliyu mutu karaba"


Bamu d'aga kai ba balle ma har mu fahimci wai damu dake, sai da ta tafi sannan na sake murmushi ina bin bayanta da ido, Umma na tayi gaskiya da tace ba zata bani maganin mata ba, domin ba rike min aure zai yi ba sai tashin hankali. Nasan ina cikin mata mabukata, amma bana jin a raina zan iya shan wani abu da zai cutar da lafiya ba, har da lafiyan mijina.


----
Haka muka koma amsar duty tunda koda ta bangare na ne, ba wani abu muke yi ba, sai ma kamar gudun mu yake, yi.


Abinda bamu sani ba, shine maganin ta kasara lafiyar shi fiyye da yadda baku zato domin. Sai ga namiji har namiji toh alkalamin shi baya aiki, itama kuma kamar zata haukace domin ita gama shaye shayenta, babu abinda zai tsoma mata haka ta fara fushi da fada ita zata bar garin tunda bai da wani amfani, idan ba rashin adalci ba ai ba haka yakewa matan shi ba itace da baya kaunar.....
7/19/21, 11:35 AM - Buhainat: 4️⃣3️⃣
Ai ba haka yakewa matansa ba, kawai dan baya kaunarta, shi yasa baya kwana da ita amma matan shi da yake kauna ai biyo shi dakin shi suke dan haka a fusace, ta bar dakin tare da alkawarin bata kuma shiga turakar shi ba, (hmm maji magani matar maji taki taki fadar maji)


Da hasken gaske ciwo ne ya kama Aliyu, domin kuwa sai da aka mishi aiki a mafitsaran shi tukun.
Satin shi biyu aka sallame shi, ya dawo gida, bayan nan ne Natashah ta koma Nigeria, muka cigaba da kula dashi tare da bashi duk wani kulawar da ya dace.


***
Bayan wata uku.
Cikina ya tsufa sosai, dakyar nake cire kafana.
"Sannun Kinji" murmushi nayi musu sannan nace musu.
"Yawwa." Ina shan kankana,
"Ina son na idan kin haihuwa ba zaki wuce kwana biyar ba zamu koma gida, Abba yace a Kano za ayi suna"


Kallon shi nayi kafin nace mishi.
"Allah ya kai mu lokacin"
"Amin Ya Allah, kinsan cikin ina ganin sabida abinda ya faru ne yasa ya koma baya, shi yasa Yanzun ne ya cika wata takwas."


Hararan shi nayi domin ya fara bani haushi, na tsani ace min wai cikin ya koma baya.
"Babu bayan da ya koma kawai dai lokacin shine bai yi ba, amma idan yayi Insha Allah zan haife shi, ina jin yadda nake kokarin zama dakyar tashi da bismillah zaka ce ya koma baya, ko gaba ne Insha Allah na kusan haifan shi."


Sake baki suka yi suna kallona, kafin Mabrooka tace mishi.
"Masu ciki basu cika son ana gaya musu haka ba, dan haka a kiyaye gaba."
"Ai na gama fada bani kuma." Dauke kai na nayi daga gare shi, wallahi na gaji da cikin jikina, kawai babu yadda na iya ne fa na cire shi na huta, shima kuma ya fahimci haka ko nace sun fahimci na gama gajiya da cikin.


Matsa min kafa yake idanun shi yana kai na.
"Me yasa kafaffunki suke kumbura?"
"Sake min kafana" na gaya mishi ina hararan shi. Sakewa yayi yana murmushi tare da cewa.
"Allah ya baki hakuri"
"Amin" na fada a zafaffe. Murmushi yayi sannan yace min,
"Kome nayi haushina kike ji?"
Ban kula shi ba, na mike tare da barin falon na koma daki na kwanta, ƙarfe takwas na dare na fara jin ciwon baya kad'an kad'an.


Tun ina daurewa, har na kasa amma ban fita ba haka na cigaba da zama. A d'akina koda ya shigo ya same a kwance bai kawo a ranshi nakuda nake ba haka ya sumbaci gefen hannuna ya gyaran min kwanciya ya fita, yana fita kamar ya dawo da ciwon na fara bala'in ciwon kamar xan mutu.


Har kusan karfe hudu lokacin naji wani irin ruwa ya zuba da karfi,. Dakyar na mike ina jin kamar kafana ba zata motsa ba, naja dakyar na bude kofa. Bakin kofar shi na nufa na buga da karfi, lokacin ina jin wani abu na shirin fasowa ta kasa na, sake buga kofar yasa shi fitowa babu shiri, yana bude kofar ina rike kafar shi da mugun ƙarfi na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya, wanda yayi daidai da fadowar abu daga kasa na, tafiya nayi zan zube ya kuma rike ni, sake wani jin wani murɗa yasa Ni cizon bakina, tare da k'amk'ame shi, a hankali wani babyn ya kuma fadowa, kallon juna muka yi, lokacin da na sake wata ajiyar zuciya. Da Karfi ya kira sunan Mabrooka, itama ta fito afujajjan. Ta sauko.tana zuwa ta dauki koma d'akina ta dauko kayan da zamu tafi asibiti, shi kuma ta rike Ni tare da shigar dani dakin ya dauki wayar shi ya kira Number asibitin, kafin mintinan ƙalilan sun iso har cikin gidan, suka zo aka gyara min jikina da na yaran. Allah Sarki baya taso hankalin shi yana kaina,.har nayi wanka tare da shafa min mai da bani tea da magani, na kwanta.


Duk wani abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login