Showing 54001 words to 57000 words out of 98705 words

Chapter 19 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt

11 Mar 2025

4312

ki nayi kokarin ganin na tsare kimarki, na kuma yi alkawarin kare darajarki.ba zan tab'a yarda wani mu'amalar banza ta shiga tsakanin mu, taya Ina da Y'a da kane mata da mata na,nayi wasa da rayuwar Yar wani. Dan haka tsakanina da Ubangiji na, nayi alƙawarin ba zan kusanci zina ba, dan haka idan baki son haka ki gaya min zan baki daman kiyi rayuwar da kike so" matsawa nayi kusa dashi tare da daura kaina a kafad'ar shi. "Ina tare da kai Sir Aliyu, ba zan tab'a maka abinda zai B'ata maka rai ba, kayi Hakuri ban san kowa ba sai kai." Matse hannuna yayi cikin nashi. "Insha Allah zan tsayawa rayuwar ki." Murmushi muka sakarwa junan mu, muna hira. Bamu bar gurin ba sai gab da Magarib, sannan muka nufi hanyar gida, tun a farkon tafiyar yace min, "ki saka belt din motar, ki saka karki sake mu bar garin nan baki saka ba" naga yana kallon bayan shi. A tsorace na saka tare da kallon shi. "Sir na saka" "good" ya faɗa yana karawa motarshi wasu abubuwan. Sannan ya figeta da mugun karfi. Aikuwa abinda yake zargi ne ya faru, domin kuwa sun kasa motar a guje. Suna binshi. "Kin tab'a gudun ceton rayuwar ki?" Girgiza kai nayi mishi, da mugun gudu muke ratsa kauyen har muka yi musu nisa, ashe sun mana kofar rago, domin muna isa gab bakin titi, tayar motar ta fashe duka biyu na gaba, hantsilawa muka yi tare da dungure gashi can gefen mu kogi ne, harbin motar suka fara, ya kalle ni.
"Karki damu, zamu fita amma ba zama dole ba." Ganin bana motsi ya sashi jijjiga ni. Amma ina sai ma jinin da yake zuba daga hancin ta, da bakin ta. Da gudu motocin suka daki motar shi ya faɗa kogin nan. Baki daya, yadda motar ta fadi nutsewa. Cire belt din motar yayi tare da dukar motar ya cire mata, nata sannan ya daki kofar motar, koda ya bude daukarta yayi tare fitar da ita, ya fara ƙoƙarin dawowa bakin gaɓɓar ruwan, sannan ya kwantar da Buhayyah, ya koma gefe yana dauke ajiyar zuciya, can bayan kamar minti goma ya koma kanta yayi ta matse cikinta har sai da ta farka, ya lalle ta. "Yanzun barin nan ya dace muyi ba zama domin" Dakyar na mike shima ya tashi, tafiya nayi zan zube ya tare ni, na zube a jikin shi. Daukana yayi tare da nufar dajin da mugun gudu. Kallon shi nayi kafin nace. "Kayi a hankali" "bazan iya nutsuwa ba sai na kai ki asibiti saboda wuyarki na Zubda jini." Daura kaina nayi a kirjina shi, hannuna na zagaye da wuyar shi. Sai da muka fito bakin hanya, Dakyar muka sami wata motar da zata kai itacce cikin gari. Ya dauke mu sai Shamaki specialist clinic, lokacin da suka gan mu, hankalin su ta tashi domin sun gani a labarai Yarimar Tankara yayi hatsari ana can ana Niman shi a cikin ruwa.


** Sai da aka gama kula da Buhayyah ya kira Bashir ya gaya mishi yana nan a raye, maza yazo. Bayan minti goma kacal sojoji suka cika asibitin. Bayan Iyayen shi sun iso tare da matan shi, yadda zaka san ana cikin damuwa da abinda ya faru. Har mai martaba sai da yazo ya ganshi.
Zama yayi a kusa dashi sannan tace mishi. "Ka fahimci abinda nake nufi ko? Kuma ɗan na gaya musu zanyi murabus tare da gabatar musu cewa kai zan bawa mulkin tankara, kayi hakuri nasan zan daura maka nauyi amma ya zama dole ka taimaka min, ban san lokacin da kome ya lalace ba, mutanen nan hatsibibai ne" shafa kanshi yayi sannan yace mishi. "Allah ya taimaki mai martaba, wannan shine hari na biyu da suka kawo mana, amma ina zargin akwai na kusa dani a tafiyar nan, dan haka Karka damu kome yayi tsannani maganin shi Allah."


Haka suka tayi ta tattaunawa har aka ce ga Bashir Ibrahim Amin Danrimi ya iso tare da Alhaji Ibrahim Amin Danrimi, duka shigo. "Sannun Yallabai Abbas, ALIYU Sannun ka auna arziki, lallai suna niman rayuwar ka, Allah ya takaita". Ya faɗa. Mik'ewa MaiMartaba yayi tare da cewa. "Yawwa Ibrahim Amin kaga yadda mutane suke kokarin ganin bayan kudirin Alkhairi, su shirya mu kuma a gurin Allah muke shiryawa, shi zai iya mana, ka kula da kanka da ita Yarinyar." Ya fada tare da barin asibitin. "Son Sannun dai, Allah ya tsare na gaba, Insha Allah sai munyi nasara, mutane basu da imani." Murmushi yayi tare da cewa. "Allah ya sansu." Haka suka zauna kafin su Mufeedah suka shigo. Nan ma suka jajjanta mishi tare da nufar hanyar dakin Buhayyah. Tunda suka shiga hankalin su ya kuma tashi domin kuwa ko motsi bata yi, dan haka suka zauna a gurinta. Washi gari. Aka wuce da ita Abuja, sai da tayi kwana goma sha tara sannan ta fara farkawa, shigowa yayi yaga tana motsi tare a girgiza kai. Alamar zata farka. Rike hannun ta yayi tare da sumbatar goshinta. Kwalla ne ya zubo ta gefen idanun ta, ya share mata da hannun shi. A hankali ta fara kokarin idanunta. "Buhayyah bude ido gani nan a tare da ke," haka yayi ta nanata mata har ta bude idanunta, shafa hannunta har ta kira sunan shi. "Sir Aliyu" murmushi yayi mata sannan tace mata."Yes Ma'a" lumshe idanun shi yayi tare da cewa. "Kaina da wuyana yana ciwo" "zamu tafi inda babu me damunki har sai kin ji kin yarda ni dake zaki zauna." Haka yayi ta shafa kaina.


Bayan awa ɗaya ya shigo tare wasu Nurse biyu, suka dauke ni aka sani a saman gadon, tare da fitar dani, aka nufi Airport. Koda muka shiga jirgin, sannan muka bar kasar baki daya. Yana rungume dani har muka isa garin Beijing. Shafa kaina yayi sannan yace min. "Daga nan muka fara daga nan zamu daura, I love your every thing."


***
Kura musu ido yayi sannan yace musu, "ba nazo bane dan mu sami sabani ba, don Allah ku kyale min D'ana tunda mulkin ne zai bar muku amma babu amfanin ku kasara min rayuwar shi." Kura mishi ido suka yi suma sannan suka ce. "Kana nufin abinda ya sami Asad mune muka mishi? Toh ka daina tunanin haka domin ido da ido muka gaya maka zamu illata shi. Ba mu tab'a shi ba dai, domin bamu ne muka tab'a shi ba"


Sosai abin ya basu mamaki domin kuwa, sosai suka nuna babu hannun su a cikin, abin ya daure mishi kai, haka dai ya bar masarautan bayan ya nufi gidan shi, ya kira Mai Martaba ya nime don Allah ya janye abinda ya bawa Aliyu ya barshi ya rayu da iyalin shi, haka bai mishi dadi ba, amma babu yadda ya iya, dashi. Haka ya zauna yayi ta nanata abubuwan da ya faru.


***
Babu shakka suna cikin damuwa domin tunda suka fahimci akwai boyayyen al'amari tsakanin Buhayyah da Aliyu take hankalin su ya tashi dan haka. Musamman Natashah da take mugun kishin mijinta kamar yadda take son shi.


"Mommy! Ina jin tsoron yadda yake shigewa yarinyar don Allah kiyi wani abu, domin bana son alaƙar su tayi nisan don Allah ki taimakawa rayuwata ina masifar son mijina. Gashi tunda ya tafi da ita Abuja wai zai tafi da ita China a duba lafiyarta duk likitocin nan basu yi ba, Mommy ko dakin na bai shiga ba, sai kan mayyar yarinyan nan" ta faɗa tana kuka, tare da daura kanta akan cinyar mahaifiyarta. Shafa kanta tayi sannan tace mata."karki damu dole na amshe ta, tunda Khameel yana Sonta sai mu dauke hankalintq akan mijinki.". "Don Allah don Allah ki taimaka min kar na rasa shi, domin shine rayuwata, idan na rasa shi mutuwa zanyi.". Murmushi tayi irin na isassun mata tace mata. "Ba zan tab'a barin ki rasa rayuwarki ba, Insha ALLAH sai na kwatar miki mijinki a hankali, kedai ki nutsu kiyi biyayya ni kuma zan kammala miki sauran aikin" haka Uwar tayi ta daura yarinyar akan gadar zare.


Idan akwai abinda ya dame Mabrooka bai wuce shan kan Aliyu da Buhayyah tayi ba, amma Tabbas zata dauki mataki, wanda ko da zata rasa mijinta ne dole tayi fada domin mijinta, ba zata yarda ta rasa shi ba, a yanzun haka alaƙar su babu aure ina kuma anyi aure ai sunan su kawai matattu. Haka kowacce su take raya abinda zai fishe ta. Domin suna ji suna gani ya dauke Buhayyah ya tawo abuja.


***
Tunda suka iso garin Baijing ake kai kawo akanta, domin kuwa aiki aka mata a gefen kanta, saboda buguwar da tayi da kanta a jikin glass din motar, shine Kwalba ya shiga cikin kunnenta da namar kanta, bayan an gama tana kwance ya riko hannunta. A Haka kullum yake kwana yake tashi, domin sunce zata kwana biyu tana kwance, shi yasa ya maida hankali akan jinyarta.


Sai da ta kwashe sati Daya kafin ta farka, shi yake kula da duk wata motsinta, yana kuma kara jin tana motsa zuciyar shi, yadda yake kaunar kasancewa da ita babu iyaka, bai tab'a nuna mata baya damuwa da iyalin shi ba, domin yana waya kullum da su, haka ya sa ta fahimtar yana cikin mazajen da suke iya boye sirrin gidajen su, bai taba nuna mata matan shi sun gaza mishi ne yasa yake manne mata ba, bai tab'a nuna kasawar matan shi ba, a kullum nuna mata yake matan shi Jarumai ne muka yana son su. Har wani lokaci tana jin haushin haka. Amma bai damu ba. Dan yakan ce mata. "Idan kinji haushi ki, addu'a zaki yi domin ni dai ba zan iya boye miki mutuncin mata na ba, kuma ba zan zage kiman mata na ba, dan haka your chance to get me! Idan kike sake suka fi karfinki har abada ba zaki same ni ba, dan haka kina da damar samuna kamar yadda suka same ni" a wannan yanayin maza idan suna niman aure bata ta gida suke, da miyagun kalamai da maganar banza akan matar gida bata kula da shi bai san dadin soyayya ba bai san dadin aure ba sai da ya hadu dake, karya ne gaba kece zai zaga da bayan son ta gidan da ya rabu da ita amma yana zaune da ita yana zaginta dake ke shashancin ya aure ki, ku nuna ai matar shi bata san darajar shi ba,ke da kika san darajar shi zaki aure shi dan ki kwace shi. For What? Malama idan namiji bai son mace ya san hanyar da zai rabu da ita ko baki nuna mishi hanya ba, balle namijin da ya jima yana zaune da matar shi yace baya samun kulawa karya ce kawai da yaudara irinta yan maza, idan kuma mika shiga cikin gidan zaki gayawa makotanku labarin namiji.


Domin a cikin kundin tarihin halin shi, ko shafin Farko baki samu damar karanci shi ba balle shafi na biyu. A tsarin Aliyu shi mutum ne da bai iya kananun magana ba, shi yasa bai damu da idan suka mishi Iskanci ya kula ba, tattara kome yake ya watsar dan yafi fahimtar nutsuwar shi dama da kullum yana kallon ki , kina b'ata mishi rai. Zai yi wuya ya d'aga hankalin shi yayi fada, amma kuma idan zai yi faɗan Toh na gaske yake shi yasa Mabrooka take mugun shakkar shi bata son abinda zai hada su kuma bata son wata halitta na mace ya shiga tsakanin su. Dan tasan baya son ta, amma kuma ba zata yi kasa a gwiwa ba gurin kame kanta ba, dan shima yana da wani shegen hali matukar ta nuna damuwa akanshi tattara ta yake ya ajiye a gefe, sai dai idan jaraba ta ciyo shi zai yi kamar zai cinye ta babu kayan Hadi.


*** Shafa kanta yayi tare da gyara mata kwanciya, bayan ta goge mata jikinta. Sannan ta sumbaci hannunta yana murmushi, barci take domin tunda ya gama gefe mata jiki barci yayi gaba da ita.....
7/13/21, 4:45 PM - Buhainat: 2️⃣6️⃣


Abuja.
Sun dawo gida, amma har yau bawai suna fahimtar kome bane, daga Mabrooka har Natashah ba wani shiga harkan juna suke ba.
Kuma abin dariya zasu hadu a cikin gidan, amma kuma ba su magana da juna, shi yasa duk wacce tasan yar uwanta na cikin gidan bata shiga sai ta fita, saboda wani irin gasar da suka sakawa kansu. Zaune take a gaban Surukarta cikin damuwa ta kalle ta sannan tace mata.. "don Allah ki ce ya auri yarinyar mun amince, da akan yayi wannan rayuwar da ita, idan kika duba yana da matan shi da yaran shi, wallahi zuciyata ba zata dauki nauyin tashin hankalin da nake ganin shi yana niman fadawa ba, don Allah kiyi wani abu."


Murmushi Umman tayi sannan tace mata. "Tunda kike dashi ya tab'a aikata wani abu mara dadi?" Girgiza kai tayi tare da rungume Yaranta da suke kwance a Jikinta. "Aliyu ba zai tab'a aikata abinda zan zarge shi ba, Aliyu Asadullah ba fasiki bane, mutum ne na gari, tun ranar da yaga yarinyar yace yana Sonta, sanin cewa ya kawo zab'in shi muka amince mishi, bayan rasuwar Uwar Yarinyar ranar da aka yi addu'ar ukun mahaifiyar yarinyar ya nemi aurenta a hannun Mutanen da suke rike da ita, sun bashi auren ta, kuma an daura auren, Dan haka ki ajiye maganar zai yi wata mu'amala mara kyau da ita, matar shi ce tun farko ya dace a gaya miki. Amma kika nuna kishin mijinki tafi ki saurare mu, so wannan kar ya dame ki domin matar shi ce.


Idan yayi miki ki rike girmanki, idan bai miki ba ki sake su rena ki, na dai tabbatar shi ba zai rena ki ba, domin kuwa ya san darajar uwar Yaran shi." Kuka take sosai kafin tace mata. "Lallai na zama mara gata, tunda har Aliyu zai auri mace kishina mara amfani ya gaza fahimtar dani abinda yake faruwa, bani da wata amfani. Nagode da gaya min gaskiya da kika yi." Ta mike tare da kwasar hannun yaran ta, ta fita da su. Alhakika Uwar mijinta ta tausaya mata, amma kuma idan ta duba wasan da tayi da damar ta, sai taji babu dad'i domin tana son mijinta. Kuma tana kaunar mijinta. Bata san yadda zata sama mata Aliyu Asadullah ba, mutumin da iya girki kawai ya dauke mishi hankali, meye kuma zai rage mishi.


--- tunda ta shiga d'akinta take kuka, ta kira Yayata da take aure a Kaduna ta gaya mata halin da take ciki, itama ta tausaya mata ta kuma bata shawarwarin da zata rike ya dawo mata da mijinta, amma dake tana Bala'in kishinsa kawai tace mata.. "wallahi na fita harkan shi har abada, ba zan kuma shiga cikin rayuwar shi ba, yaje ya rike Buhayyah da Natashah." Ta cigaba da kuka tana gaya mata ita ta hakura dashi zata yi zaman Yaranta. Tunda bai dauke ta da kima ba, haka dai tayi ta bata hakuri dan ta fahimta amma fir taki. Natashah kan a cikin matan da aka kawo da su, akwai daya daga cikin su da take mata gyaran jiki, ana ta dura dure ana jiran miji ya dawo. Tayi kyau ta kuma cika dake ana kawo mata kayan gyaran jiki daga Tankara gurin mahaifiyar ta, haka ya sa take da aniyar duk ranar da Aliyu ya dawo zai gane cewa mata suna suka tara.


*
China.
A hankali ya riko hannunta tare da saukar ita daga gadon, kallon shi tayi tana murmushi. Ban daki ya shiga da ita, ya cire mata pant da rigar Jikinta sannan ta fara mata wanka, dakyar yake mata wankar kamar zai cinye ta d'anye, yana fito da ita ya cire hular da yake kanta sabida kar ruwa ya tab'a kunnenta. "Sannun kinji?" Murmushi tayi sannan tace mishi. "Nice zan ce maka Sannun tunda ka bada rayuwar ka domin ni akan me ba zan baka rayuwata ba? Sai dai ina da wata rokon da zan maka don Allah karka rabani da kimata a wata duniya, ka amshe shi a inda zan yi mutunci da daraja." Na fadi haka ina wasa da hannuna. Shafa kaina yayi bayan ya rungume ni. "Insha Allah ba zan miki abinda zaki ji babu dad'i ba, zan mutuntaki bayan an miki duk abinda akewa wata Y'a mace" ya faɗa yana kara matse ni a jikin shi. "Amma zaki gane ranar da aka turo ki a sama? Shin mutum ne ya turo ki zaki iya gane wanda ya turo ki?" Da sauri na d'ago kai na ina kallon shi. Kafin na ce mishi. "Na dai ga mutum ya fito ta dakinka but ba san ya aka yi ba, lokacin da ya turo ni ya kuma komawa dakin da gudu." Riko face ɗinta yayi yana kallon kwayar idanun ta. "Ranar da kuma muka je gidana meye ya faru dake?" Kwantar da kaina nayi a kirjin shi. Ina sauke numfashi a hankali. "Sir Aliyu idan na gaya maka dariya zaka min, domin da idona naga bishiyoyin gidan suna min dariya, grass capter sun rike min kafaffuna, so kamar Imagination ne ba reality bane" na fada ina wasa da hannuna a kirjin shi.


"Zaki iya taimaka min da wani abu idan muka koma" ya tambaye ni, juya idanuna nayi tare da cewa. "Of course I will did" sumbatar goshinta yayi yana son kwarin gwiwar ta, yana jin dadin yadda take bashi kwarin gwiwa, dan haka ya shiga lulawa da ita wata duniya na daban, wanda shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login