Showing 66001 words to 69000 words out of 98705 words

Chapter 23 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt

11 Mar 2025

4309

motar shi.
"Turai! Ban sani ba ko bayan Nishat kana da wasu yaran a kasar waje ko? Wanda masarautan bata sani ba, kuma aka baka muqamin me nad'a sarakuna. Me zai faru idan na b'ankad'o wannan bayanin ga masarautan mu aka san waye Badar Turaki?"


Sannan ya wuce gurin motar shi tare da cewa.
"Kowa da ka ganshi Shaidani ne, sai dai idan bai saka kanshi ba, idan har Aliyu ya kwana lafiya, tabbas Zunnur da Abideen, koda yake ba zaka gane hakan ba sai ka kira su awaya ka tambaye Uwar su waye yazo mata hira minti talatin da suka wuce."


Daga haka Alhaji Ibrahim Amin Danrimi ya shiga motar shi.
"Kasan me? Wallahi ina sane da kome, bana son damuwa ce ya sa na dauke kai na, kamar babu ruwa na, idan ka sake na zama da ruwana tabbas wasar zata kayatu fiyye da da bana cikin shi. A gwada a gani"
Ya tadda motar shi a hankali zai bar gurin.


"Meye kake nufi? Me yasa baka nemi mulkin ba?" Dariya ce ta kwace Mishi. Sannan ya kalli Turaki.
"Idan na nemi mulkin ba zata zauna da ni ba, domin ita ke da alhakin Niman wanda yake tare da ita, balle kuma mulki irin na mutanen Tankara masu hadakar mulki da Aljanun, idan mulkin nake so, Ina da Yaro Bashir ina kuma raye zan nima da karfin tsiya, amma mulkin ta zab'i Aliyu ne tun daga ranar da aka haife shi na fahimci shine hasken da Tankara ta rasa na wasu karni da suka gabata."


Daga haka yaja motar shi ya bar gurin har yayi nisa, Alhaji Badar Turaki yana tsaye dawowa yayi tare da cewa.
"Ka dakatar da mutanen da suke bibiyar rayuwar shi, idan ba haka ba" bai karasa ba, ya bawa motar wuta, tabbas shima yasan Ana cewa Abbas tantirin mara mutunci ne bai taɓa yarda ba sai yau, dan haka ya d'aga wayar shi tare da cewa.
"Ku fita hanyar Aliyu domin Abbas yana mara mishi baya, idan kuma haka ta faru tabbas zamu yi kuka da kanmu"


Kome aka gaya mishi amma fuskar shi ya nuna damuwa sosai, dan haka ya kashe wayar shi ya shiga motar shi tare da nufar hanyar gidan shi.
***
Karfe goma sha biyu ya iso garin Abuja. Dan haka yana isa abinda ya fara Shine kiran Moddibo, yazo ya dauke shi. Bai samu zuwa ba ya turo driven gidan Ola.
Suka dauki hanya suna tattaunawa, har sunyi nisa Ola yace mishi.
"Sir ina son nayi fitsari ko zaka yi hakuri na tsaya."
"Ok zaka iya" ya cigaba da tura wasu bayanai ta wayar shi zuwa Laptop din shi. Ola na fita ya juya motar baya, sai ji kake "kauuuuuu tartsaaaa kiiiiiiii" wata mota da mugun gudu ta daki ta Aliyun da yake cikin shi, har sai da ta hantsila, da gudu Ola ya faɗa daji, haka motar Aliyu ya cigaba da wuntsile a tsakiyar titi kafin ya samu wani guri ya tsaya cak. Sannan ya kama hayaki kamar zai kone.
Wasu kartin maza ne suka tako har gurin suna waya.
"Oga mun rufe shafin Aliyu sai dai wani bashi ba"


Suka fada tare da haska mishi tocilar hannun su, yana jirkice jini na zuba mishi daga hanci da kanshi. Daukar hoton shi suka yi tare da bazama abin su da motar su. Suna tafiya ya lallubi wayar shi a hankali ya leka motar su tare da ɗaukar numbersu.


A hankali ya kira Mufeedah, ya gaya mata halin da yaƙe ciki, kafin ya fito a motar a hankali, domin yana jin kamar bayan shi ba nashi bane, jan kafar shi ya fara dakyar har ya gama fita a titin, kiran wayar shi Mufeedah tayi.
"Gani nan a bayan wata bishiya, karku haska ni" da gudu suka isa gurin shi.
"Wayyo Allah na" inji Buhayyah da taga lokacin da ya fito yana nufar su, da gudu ta fita motar ta rungume shi, kamar zasu fadi kasa, haka ta ruko shi suka shiga motar.
"Ina zamu kai na?"
Gaya musu inda gidan shi yake, sannan ya kuma cewa ta nimo likitocin da ba za a san yana raye ba, kuma ta kwantar da hankalin iyayen su. Kamar yadda yace.


Ko minti talatin me kyau basu dauka ba, suka isa gidan. Tare da niman kiran wani abokin ta likita, bayan kusan awa daya. Da ita da wasu likitocin uku suka rufa akan shi, har aka yi nasarar cire mishi glass, bayan shi kuma aka mishi dauri, bayan sun gama suka tafi. Suna zaune a jikin shi har gari ya waye, dake Buhayyah tasan gidan ita ta duba kayan abincin ta samu akwai dake baya rabu da zuwa gidan shi daya, haka ta shiga nima musu da zasu ci haka ya taimaka musu bayan sun yi sallah asuba, Mufeedah ta tafi gida, cikin nutsuwa tayiwa iyayen su bayani, sannan suka karya kafin suka zo ganin halin da yake ciki. Suna komawa aka baza sanarwar yayi hatsari, amma ba a ganshi ba, yin haka ya tab'a zuciyar mutanen da suka aikata laifin. Domin sun san ya mutu, kuma an bi sawun inda jinin shi ya diga ba a ga inda aka dauke shi ba.


Wannan abin ya saka zargi akan Ola da kuma wasu daga cikin members na emirates councilor na Tankara ai jiya Dan Rimi yayi musu kashedi basu ji ba, dan haka al'amarin ya girmama.


Aka shiga bincike kamar za'a raba ƙasar biyu. Sabida an kashe Aliyu me Kamfanin AA'S Bros. Haka aka yi ta niman Aliyu Asadullah, kuma na kara tsananta bincike, amma abin mamaki kamar goge kome suke sabida kar asan abinda suka aikata.


Natashah da Mabrooka hankalin su ya tashi tare da shuga rud'ani haka sukayi ta kuka, dan ma an gaya musu bai mutu ba, shina hankalin su ya kwanta amma ba a san inda yake ba, ana kan binciken shine. Amma fa suna cikin tashin hankali mara iyaka, domin b'atar miji tashin hankali ne da rashin nutsuwa.


___
After few weeks
Yana zaune tare amsar maganin da take bashi, cikin fushi da b'acin rai. Kawai dan ya nime ta ta nuna tana jin tsoron shine, shine yake fushi.
"Ki tafi gida bana son zaman ki anan, kije ki cigaba da jika kayan ki sha."
"Sir Aliyu"
"Karki yarda ki ce min tak, dan haka ki saka kai ki bar gidan nan kafin ranki ya b'aci" cikin rawan murya nace mishi.
"Sir"
"Out" zame hijab din jikina na fara tare da jin kwalla yana zuba min, rigar jikina na zame tare da nufar inda yake kishingide, na kwanta tare da lumshe idanuna.


"Su kuma Pant da bra din Ni zan cire miki idan baki so, zaki iya tashi ban miki dole ba, balle ki ce, ai na amshi kimar ki da karfin tsiya ne"


A hankali na kalle shi kafin na mike tare da balle bra din na cire pant din, ina kuka. "Na shiga uku. Idan baki so ki tafi mana da saka Ni a gaba kina kuka da hakkina tashi na gobe jeki dakin ki, ki kwanta bana bukata."
Fada min cikin fushi da b'acin rai. Na rasa gane mishi ga baki ɗaya ya sauya min ba halin nayi mishi laifi zai kama fada, wai dan na ganshi a zaune baya more rayuwar shi, idan nayi kuskure akan abinci yace min dan naga an hana shi wani abu ne. Yanzun jiya ina jin shi yana gayawa Mufeedah shi yana son kasancewa da iyalin shi ya kenan, shine tace mishi sati biyu kenan da faruwan hatsarin don Allah ya kara hakuri bayan ta haɗu nan da sati Uku, amma ya shiga mata fada.


"Wallahi ba zaku iya hanani ba, haka kawai ina jin zan iya kome kuce ba zaku barni na yi ba, sai dai idan Buhayyah bata cikin gidan nan matukar tana cikin shi zan gwada lafiyata " ya fada yana Bala'i kamar me sabida an hana shi buga iska. Shine yau ya saka ni a gaba, dan abu kadan zai haura min da masifa, ni kuma ban iya fada ba.


.... Ganin na daina kukan ne ya sashi matsoni sosai, sai lokacin na fara jin rawan jiki. "Zaki fara" ya tambaye ni. Girgiza mishi kai nayi ina me boye kuka na. A hankali shafani tare da matsar nonuwa na. Saukar wani abu naji a kasana tare da murdawa da cikina yayi, *Alhamdulillahi* nafada tare da kallon shi cikin damuwa nace mishi. "Sir na b'ata jikina da Period dina." A rikice ya kalle ni tare da cewa.
"Wato dan baki son na tab'a ki shine zaki kawo min wani abu na daban? Tashi ki fitar min a daki ki je ba zan kuma bukatar ki, idan kin gadama karki bani hakkina matsalarki ce ba nawa ba."


A hankali na mike tare da ɗaukar kayana, na bar mishi ɗakin. "Ka ji da masifarka tunda haka kake" na fada a hankali bayan na bar dakin, na shiga dakina tare da gyara jikina na fito na koma dakin shi na gyara mishi inda na b'ata mishi, ina jin karan ruwa na Fahimci yana ban daki ne, kicin na nufa bayan na gama abincin rana na kai Mishi dakin shi.


Ina fitowa muka hadu da Mufeedah.
"Barka da zuwa"
"Barka dai ya jikin na shi?"
"Alhamdulillahi" na ce ina kallon bayanta Abokin shi Bashir ne na gani, ban ji dadi ba. Amma na mishi Barka da zuwa. Sannan na koma dakin shi.
"Kayi bako, tare da Aunty Mufeedah suka zo"
"Ok bani keken nan na zauna akai" na isa gurin keken na bashi ya zauna domin baya jure tafiya a kafa,, yana zama ya tab'a wani gurin a jikin keken ya fita ina bin shi a baya, har falon.
"Ikon Allah! Dama kana raye?"
"Ga zahiri" ya faɗa yana murmushin jin dadi, "gaskiya akwai ban mamaki, domin yadda naga motar nan ban zata zaka yi survive ba, amma Al'amarin ikon Allah yafi gaban kome" inji Bashir,


"Wallahi kuwa gani nan dai tunda dai an kai min aka samu Buhayyah, aka kuma kai mana tare, wannan ma Allah ya nufa ba zata rutsa da ita bane shi yasa baki tafiya da ita, amma Alhamdulillahi masu shiri su yi shirin su, masu farmaki su farmake mu, ina sane dasu tsaf."


Ya gaya mishi yana murmushi, abincin da na jera na kawo falo sai lokacin Mufeedah ta mika mishi magani, tana faɗin.
"Wannan yana taimakawa sosai ka duba da kyau, sannan matsalar ka nayi Mag...."
"Me zai hana kiyi magana da shi a keb'ence? Tunda Kinga nan kamar publice tunda mun fi haka yawa." Na fada ina kallon ta..
"Yes haka ne, Amaryan mu kinyi gaskiya ai haka ne nan kusan cikin jama'a ne"
"Ina ruwanki da zaman mu? Ko kina cikin family issues din mu ne? Ban ce ke bare ba, sai Bro dina zaki kira bare, kinsan darajar ahali da dangi kuwa? Kar na kuma ji ko na gani kin shiga cikin harkokin family na, tsaya iya matsayin ki na bare matar Aliyu bayan haka bana son na kuma jinki a cikin wannan lamari."


Da gudu na bar falon tare da shiga daki na banke kofar ina kuka afujajjan, domin kuwa ya gaya min gaskiya kuma ya gaya min abinda ya tab'a kima ta, dan haka na kulle kai na.


"Amma gaskiya baka kyauta ba, Allah ka daina threating ɗinta ta wannan hanyar, babu dad'i kai da kake da dangin me suka maka? Sai niman halaka ka suke ta hanyar amfani da mulkin banza mulkin wofi, gaskiya ta faɗa a halin da muke ciki meye dangin suka maka sai ma niman hanyar kashe da suke gaskiya sai na gayawa Mother ta san halin da Matarka take ciki tunda ka zama dai sai Du'ai masu laifi da ban ita kake saukewa masifar da kake ji.....
7/14/21, 5:31 PM - Buhainat: 31**** "karki min rashin kunya Mufeedah tafi ki bani guri" "na rashin kunya bane ai gaskiya na gaya maka, ita yarinyar da take zaune da kai ka san yadda take ji ne mutum ya zauna sai masifa, sai na bata maganin barci ta wurga maka cikin ruwan shan ka zaka gane baka da kirki."


Harararta yayi yana faɗin. "Kana ganin rashi mutuncin da take min ko Bashir?" Cikin in-in-ina yace mishi.
"Kayi Hakuri," ya faɗa mishi a sanyayye, nan suka shiga tattauna duk wasu bayanai da ya dace, sannan Bashir ya mike tare da kallon shi.
"Ka kula da kanka"
"Insha Allah"
Ya fada bayan sun sake musabaha, tunda Mufeedah tayi musu sallama, yake raba ido ko zai ganta, amma bai ganta ba. Wasa wasa har aka yi magarib bata fito ba.


**
Tunda na shiga nake kuka ban kuma fita ba, dan haka ina zaune har magarib, koda na fito baya falon na shiga kitchen, ina cikin hada abincin dare naji shi ya rungume ni. Hawaye ne ya zubo min daga cikin idanuna zuwa kan hannunsa.


"Kiyi hakuri mana"
Janye jiki nayi ina kallon shi kafin nace mishi.
"Sir baka min kome ba, nice zan baka hakuri saboda na maka katsalandan, kuma hadisi ne guda karka shiga abinda ba ruwanka, kayi hakuri ba zan kuma ba kaji"


Yana daga cikin abinda yake kara mishi kaunarta. B'ata rai yayi sannan yace mata.
"Bana son iyayi da gulma kin samu ma nazo zan baki hakuri, common hug me"


Kasa motsi nayi ina kallon shi..
"Nace" ya faɗa tare da bude hannunsa, a nutse na karasa tare da fadawa kirjin shi, na sake kuka, har da shesheka, buga bayana yake a hankali tare da cewa. "Shiiiii" ya faɗa yana lasar kunnena, a hankali na furza da kukan.
"Ya isa haka mana, bana son haka. Bana son kukan banza" ya faɗa min, yana matsa mazaunina. "Ina son wannan abin" kifa kaina nayi a kirjin shi tare da sake dariya, domin ya fara min chakulkuli. Ban san lokacin ba na rike shi ba, muka k'amk'ame juna.
"Baby" cak ya tsaya, tare da d'ago kai na.
"What?" Kara rufe fuskana nayi ina me fashewa da dariya, nace mishi.
"Sir Aliyu yaji nace mishi baby, dama kai Babyn Mama ne"
Na fada ina me tura shi gefe, tare da duba girkina, sumbatar wuya na yayi nayi maza na juya tare da rike hannun shi muka fito falo.
."Zauna a nan, kar na kuma ganin kafarka tunda har ka zami lafiyar da zaka dam...." Zuɓewa nayi a jikin shi cikin mutuwar jiki, tare da kallon shi.
"Sir" cilla min harshen shi yayi cikin bakina, ban san lokacin da na rike rigar shi ba. Wani irin banzan kiss yake min wanda ya sani sake wasu tagwayen ajiyar zuciya, ina kara cusa kaina jikin shi.. ilove my mr Cool, ya iya tafiya da zuciyar mace, kamar bashi ba, lokaci guda ya haɗa min zafi da sanyi, Aliyu gadanga kusar Yaki. My Haidar, Dear Abuturab.
"Me yasa kike kallon cikin idanuna haka?"
"Sir ban sani ba, amma qaddara ta da taka a hade yaƙe"
"Ban zaci haka ba, domin lokacin da na nemi aurenki ban dauka zan iya ba, yau gashi ina ribarta abata a hankali zan cigaba da gurguranki"


"Kai Sir" na fada tare da guduwa na barshi ina me tura baki, haka kawai.
"Sai kace goriba"


Daukar apple yayi tare da kallon yadda nake b'ata rai, yadda ya gama lashe apple din sannan yayi mata wani irin gutsira ban san lokacin da na arta da gudu zuwa kitchen ba na banko kofar ina dariya.


"Mara kunyar karya da kinzo na nuna miki karshen rashin kunyarki" ya faɗa tare da d'aga murya, yana dariya.


** Bayan na gama na jera mishi, yana zaune akan sallah. Ina ganin lazumi yaƙe. Da na gama na koma daki nayi wanka tare da saka riga armless iya gwiwata, sai yar karamar bomshort, na shirya tare da fitowa falo ina kamshi. Zama nayi ina kallon shi, yana karatun Alqur'an, lumshe idanuna nayi tare da bin shi muna tare, yana tsayawa na cigaba da yin shi.


"Jazakillah bil janna"
Ya fada min, murmushi nayi tare da cewa.
"Food is ready"
"Zuba min ina jin yunwa"
"Ok Baby sir"
Na fada ina kunshe bakina, dariya yayi sannan yace min.
"Idan na kama ki zaki gaya min dalilin dariyarki" ya faɗa min,


"Toh sir meye nayi kuma? Dariya kawai nayi meye laifina?"
"No baki da laifi idan na kama wancan fararren cinyoyin, hmm" ya faɗa tare da kallon yadda nake saka mishi, kallon yatsun hannuna yayi sannan yace min.
"Ya baki saka lalle irin na Mufeedah, yadda suke fararren nan zai kara kyau da inganci."


Mik'ewa nayi na zuba mishi ruwa ina gyara gurin, kamar wani wanda yake da wani abu sai ji nayi ya kai min duka a duwawun. Sai da na zabura.
"Sir Baby"
"Well ba zan daina ba" ya faɗa min, nima kuma na cigaba da tsokanar shi, har ya gama cin abincin, sai lokacin muka zauna muna kallo, kan shi yana kan cinyata, ina wasa da gashin kanshi.
"Queen Been!"
"Na'am sir"
"Thank You"
"Nima haka"
Rike hannuna yayi tare da sumbata, haka na kifa kaina akan fuskar shi ina murmushi, tare da mishi jiran shirme, sai dariya yake min zaka dauka wani abun arziki nake bashi labarin nan kuwa abin dariya ce kawai da shirme.


Koda muka je gurin kwanciya, gyara jikina nayi, tare da shigewa jikin shi, ina sauke ajiyar zuciya, ga wani kamshin turaren da yake kara rikita min lissafi, sai ajiyar zuciya nake.


Can muka yi shiru, kafin na gyara kwanciya ta nace mishi.
"Sir Aliyu, don Allah na tambaye ka mana"
"Ina jinki" ya faɗa tare bada janyo ni jikin shi. Tare da kallon yadda nake kyafta idanuna..
"Ina jinki"
"Sir Aliyu, wannan shine karo na uku da ake kawo maka hari meye yasa suke bibiyarka"


"Saboda mulki, duk wani abinda za a min ko a miki saboda mulki ne." Gaya min yana kara shafa fuska na,
"Sir Aliyu, kana nufin sabida Yarimar Tankara da aka baka ne suke wannan abin?"
"No Baby girl sabida sarki Abbas Muhammad Al-Amin zai yi murabus ne suke wannan abin, kuma ya gabatar da ni ne sarki na gaba idan ya sauka shi yasa suke bibiyata"


"Sai nake ganin kamar ba akan haka bane akwai wata Ɓoyayyen ajiyar da suke son kare shi, gabbanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login