Showing 81001 words to 84000 words out of 98705 words
Chapter 28 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt
ita." Uwar ta faɗa tana kallon yarta.
Bata son abinda ake mata ba yadda ta iya ne kawai, dan haka tana ji tana gani aka shiga gyara mata jiki.
---
Yau Juma'a.
A sanyayye ya fito sanye da farrar shadda, yayi masifar kyau dukda kuwa ya rame sosai, amma haka bai hana shi fidda kyau na musamman ba, yana tafe da Anoosh da Anis, sai hira suke mishi, a cikin motar shi yana jinsu..
"Tauuuu" aka haife motar shi, sai da ya kwace mishi, dai dai gurin da yaran shi suke, suka zo da gudu. Kafin ya kwantar da yaran sun sake musu harbi, sai da na huda glass din motar, ya samu kan Anis, take yaron ya saka fadi ko shurawa bai yi ba, sai Anoosh, da ta razana ta suma, shi kuwa tsabar ya gigice bai san ya daki mashin din mutanen ba, sai da suka fadi a tsakiyar hanya mota tabi kansu. Shima kuma yaje yayi karo da wata mota, kanshi ya daki sitiyerin mota, jini na zuba ta hancin shi da bakin shi.
"Aliyuuuuuuuuu" na fada da karfi lokacin da na farka daga mugun mafarkin da nayi, a hankali na bude idanuna, Umma tana min addu'o'in, a hankali na fara rasa nutsuwata kafin wani lokaci na fara ihu, ina faɗin.
"Karku bari ya fita da farar motar shi, a kira shi gaya mishi zasu kashe shi kar ya fita"
Shigowa Yan uwan ta da Abban su yasa ta cigaba da gaya musu abinda yake faruwa a masarautan Tankara, dan haka a kira Aliyu a gaya mishi kar ya fita da farrar motar shi zasu kashe shi.
Akan lokaci kuwa suka kira shi.. bayan sun gaisa da Mai Martaba Sarkin Kano, nan yake tambayar shi ina zai tafi. Ya gaya mishi sannan yace mishi.
"Idan da hali karka dauki farar motarka ka dauki bakar akwai abinda nake son ka fahimta, sannan ka kira domin kana fita zaka ga abin mamaki,"
Haka yayi mishi sallama suna rabu, bayan sun gama ta kuma kallon Abbanta tace mishi.
"Wasu mutane zasu zo yau ka saka ido akan su. Daga masarautan suke, Yallabai ka saka surukinsa yayi sulhu mutanen nan mutanen banza ne, shekara ɗari da hamsin an yi Sarkin da ya same mu aka zauna dashi zama na Amana idan wani abu ya taso zai bamu damar mu tattauna dashi,
Bai tab'a gayawa kowa ba, sai da yazo rasuwa ya gayawa Galadima za Wazurin shi da kuma Turaki, sai wani na hudun su.
Dan haka ya gaya musu sirrin masarautan na had'akar mulkin mutane da aljanun, sunyi mamaki amma sai suka manta da zancen bayan mutuwar sarki sai na hudun su yazo mana da batun zai barmu muyi mulki amma sai mun bashi karfin mu da dukiya, muka ce mishi a'a ba zamu bashi ba, sabida yadda muka yi yarjejeniyar sulhu tsakanin mu da sarakunan masarautan, sai ranshi ya b'aci yana tafiya bayan kwana biyu ya kuma dawowa muka ki, daga nan ne yana dawowa na uku da wani shu'umin mutum ya kame mu, duk bayan shekara ashirin ake sake mu, a shekarar da za a sake mu, wasu daga cikin mu suke haifar da mugayen abubuwa na annoba da asarar rayukan al'umma.
Sai dai a haka magabatan mu, sun ce za a wani gari a ƙarshen mulkin da za a kawo yarinyar da zata sama mana yanci ta sanadinka, bamu yarda ba sai da aka sace ta aka kawo ta inda aka binne sarki Saminu, anan muka rab'e ta dan haka muka fara bincike da son sanin wacece ita, sai muka gano kaddara ce ta kawo ta Yankin tankara, shi yasa muka fara kokarin bude mata ido amma tana da karfin ibada da na addu'a, sai muka koma gefe, a yanzun ma sabida za a cutar da mijinta muka shigo jikinta.
Don Allah ranka shi dade ka taimaka mana ba zamu tab'a cutar da kowa ba. Insha Allah."
Shiru yayi yana kallonta, kafin yace musu.
"Toh na yarda zan taimaka muku amma idan aka samu labarin kin cutar da wani meye zan muku?" Ya tsare ta da ido,
"Idan ka sami wani abu bayan wannan ka mana hukuncin da zaka iya shafe mu mun amince domin mun gaji da ukubar da suke mana, da kashe mu suka yi da yafi mana, dan adam shu'umin mutum ne muma basu bari ba balle junan su. Ka taimaka mana zamu rayu cikin yanci da walwala"
"Shikenan ku tafi zan yi magana da Shi Aliyun Insha Allah zai saurarra muku sannan zai tsaya muku har sau kun sami yanci,. Allah ya sa mu dace."
"Amin Ya Allah Mungode" daga nan.ta sake atishawa.
Kafin ta kwanta sai barci. Shafa kanta yayi yana tofa mata addu'o'in.
"Toh ni wallafa gaskiya ba zan iya barin A'ishah ta koma ba, ina tsoron Allah kar a kashe min ita."
"Karki damu Allah yana sane da ita, wayon ki da hikimar ki ba zai hana wani abu ya same ta ba, sai Abinda Allah ya tsara mata, dan haka ki mikawa Allah kome, Insha Allah zai tsaya miki, itama Addu'a zamu taya ta dashi. Nasa ana bincikar halin da yake ciki, dan haka karki wani d'aga hankalin ki domin babu inda zai kai ki sai damuwa."
Haka yayi ta rarrashin uwar har ta hakura sabida ita yaki kiran Aliyu akan Buhayyah ba dan kome ba, sai dan yaga yadda take yawan ce mishi yanzun haka "zaka dauke ta maida mishi ita ki jin dumin ta, bayan muna ba mu gama jin duminta ba, ta b'ata a jaririya ta dawo da girman ta shine zaka maida mishi ita don Allah karka gaya mishi domin ina mugun son jinta a jikina."
Wannan dalilin yasa ya kasa kiran Aliyu amma tabbas zai gaya mishi dan kar ya zama karamin mutum, ace matar mutum ta b'ata baka gaya mishi ba, bayan yasan yadda ake magana akan batun auren tsakanin masarautun guda biyu, ajiyar zuciya na sauke sannan ya mike ya bar d'akin,yana nazarin yadda zai sami Aliyu da batun, ya kuma san zai tambaye shi inda yaji, so kawai gwara ya sanya shi yazo sai ayi abun a gaban shi, domin matukar ba haka ba, zai dauka kamar yana tilasta shi yayi abinda bai shirya bane, dan haka gudun zargi ta sa shi ajiye maganar a gefe. Yana me niman yardan Ubangiji a cikin kome ya saka a gaban shi domin babu wanda zai tsaya musu sai Allah.
Kuma shima yasan mutanen basu da kirki ko kadan shi yasa yake tausayawa Aliyun,
Wannan kenan...
7/19/21, 11:33 AM - Buhainat: 3️⃣8️⃣
Tun daga ranar, nake yawan shiga damuwa sabida Aliyu ina yawan mafarki da Aliyu, kuma cikin tashin hankali, haka yasa na saka su a gaba da rigima na daina cin abincin gani nake kamar any moment za a sami labarin mutuwar shi..
***
A tankara kuwa, lokacin da Mai Martaba Sarkin Kano ya kira shi, suka yi magana bai yarda da abinda ya faɗa mishi ba, sai dai ya dauki wata motar Mabrooka ya fita da ita, bai tsaya ko ina ba sai fadar sarki, ya same shi a wani babban falo ya zauna cikin nutsuwa. Kan shi a kasa.
"Asadullah akwai abinda yake damunka?" Inji Mai Martaba, kasa yayi da kai cikin girmamawa, da tarin damuwa yace mishi.
"Abba mata na yau satin da biyu da b'ata, yanzun Mai Martaba Sarkin Kano ya kirani akan kar na fita da farar motana, ina fitowa waje naga wasu mutane akan mashin, Abba ina jin tsoron matsayin da kuke nima na amsa, don Allah ku hakura idan na sami Buhayyah zan iya amsar sakon ku"
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace.
"Tunda baka yarda da take taken su ba, yaci a ce yanzun ka fahimci abinda yake faruwa. Duk cikin fadar nan babu me kaunarka, ba zan maka ishara da wanda yake bin ka ba. Amma zan gaya maka wani kuskuren da kayi da ya bani mamaki. Shin ka tab'a bibiyar wanda ya daki Yarinyar nan a gidanka?
Ka tab'a bibiyar mutanen da suka turaku a ruwa? Aliyu zamanka na dan kasuwa ba yana nufin Zaka sake rayuwar yarinyar da kake so ya tafi a banza bane, nasan kana mata so na hakika, amma kafin ka tsaya da tunanin ka, dole ka iya sarrafa abubuwa guda hudu. Na daya Mulki, Na Biyu Dukiya, Uku mace na hudu Jama'ar, duk inda zaka shiga da wannan abun matukar zaka same su baka da sani akan su zaka wahala.
Yana da kyau ka iya nazarin yadda zaka sarrafa su. Amma ka sake gidan ka yana shirin gauce maka, ka sake matar ka tayi b'atar dabo, ka sake Jama'a suna mana kallon mutumin da bai iya rike gidan shi ba taya zai rike Al'ummar gari guda? Mutumin da bai iya kare mutuncin gidan shi ba taya zai kare mana na Al'ummar mu. Matar ka bata b'ata ba, nata raye sai dai abinda kayi har ya tafi ta Barka lallai ba karamin abu bane, domin babu macen da zata same ka ta Barka a bakin Natashah naji haka.
Tace kai mutum ne me sa'a, shi yasa Allah ya basu kai a lokacin da basu zata ba kai kamar ruwan sanyine a cikin sahara, sannan tace soyayyar da kakewa Buhayyah da ace zata sami kad'an shi sai tayi hakuri da abinda kayi mata, shi yasa yake maka kallon waliyi, ni kuma nasan dadinka ta sani dukkan su matanka basu san wahalar ka ba sai Ita Buhayyah, ta zauna da kai na tsawon watanni, bata tab'a gudunka ba ka san me yasa? Sabida duk cikin matan ka babu wacce ta same ka a tsada kamar ta. Shi yasa take hakuri da halinka.
Idan yadda Khamil ya gaya min halinta tabbas kai me laifine a gare ta, idan yadda na Fahimci halayyar ta kai ba ka kyauta mata ba, domin mace irin su masu iya boye damuwar su sabida mazajen su, wallahi ba zata tab'a yarda ta matsa a tare da kai ba.
Aliyu mace da kake ganinta kashin harkarkari ce idan ka matsa zaka lankwasa ta karyewa zata tayi, haka kwana kin baya sai da na ci karo da Natashah tana kokarin bayyana rashin adalcin da kakewa Uwargidan kan Aliyu baka kyautawa. Itace ya kamata ka daraja, ba wai ka wofantar da ita ba, ita ya dace ka girmama ba sauran ba.
Kayi Sa'a matanka suna sonka, kuma wayayyu ne, masu ilimin addini Musulunci da na Zamani, basu da kazaman buri a tare da su, babban damuwarsu. Taya zasu kyautatta maka. Kasan sabida me yasa? Saboda kai namijine a tsaye baka da sauki. Mata kuma suna son namiji irinka, baka basu fuska ba, balle su ci daman cin tuwo kanka.
Ina son naga namiji da mata s suke hauka akan shi, ba irin wanda kana ganin shi, ya zama . Idan matanka suka dawo gare ka, ka rike su da Amana karka dake wani yaga gazawar. Kuma na baka aiki ka nimo min mutumin da ya fita a mota aka ture ka baka bibiyi bayan shi ba.
Mutanen da suka turaku a dam bai bibiye su ba, Aliyu mu kuma muna son ka zama sarkin garin nan amma kai baki daya ka gaza fahimtar mu, sannan ka kasa gane waye ke bibiyarka mu da muke shiryawa rayuwar ka cigaba ka kasa gane yadda muke son ka.
Yanzun gashi abin ya kai inda ya kai ana Niman rayuwar ka, bayan an san kai ne zaka iya fita da wata mota me kala kaza, me yasa Sarkin Kano ya kira ka? Saboda shima daga nan fada an sami mutanen da suka je akan ya dakatar da aura maka jikar shi.
Har yau bai ce kome ba, Aliyu akwai mutanen da suke raye domin kai! Akwai mutanen da suke Niman yanci domin kai, Aliyu masarautar nan tana Niman Adalin sarki ne, wanda baya karshen ikon kowa sai na kanshi, wanda zai iya daukar nauyin al'ummar shi, wanda zai iya tinkarar duk abinda yazo mishi wanda zai murza gashin bakin shi da idanun shi ya kalli mutanen da suka kawo mishi farmaki ya gaya musu abinda ya fito bakin shi!
Allah ya jikan Mahaifina Muhammad Al-Amin na uku, kafin kakanku, shi ya fara daukar ka lokacin da ta ya shiga garin London, yayi maka huduba sannan ya kalle ni yace.
"Abbas ga Zakin Masarautar tankara nan yazo! Ga King of Monarchy yazo, wannan shine ake kira lion King of Monarchy, kuma daga yanayin ka da girmanka naji a raina kai ne muke addu'ar Allah ya kawo mana kai, yau gashi nan kazo. Makiya da magauta sun hanaka ka amsar wannan damar. Hmm Aliyu Asadullah, idan har ba zaka amsa sunan zakin Allah ba, babu amfanin saka rai da tsammanin zaka kawo mana karshen abinda yake faruwa a cikin Masarautan nan.
Ba zan tilasta ka sai kayi yadda nake so ba, amma zan baka shawara ka tashi daga barcin da kake, su kuma mutanen yanzun haka an rufe shafin su, tunda na kudiri aniyar ka zama sarki, yasa na Nime taimkawar Ubangiji, kaga gaya min ni kuma na tura maka da sakon gaggawa, ko cikin dare ne ka fita kayi yawo a cikin tankara babu abinda wani zai maka Allah yana tare da kai, Ubangiji ya a maka jagora, ina alfahari da samunka a matsayin D'a daya tamkar da dubu, tashi kaje kayi ƙoƙarin nimo inda Matarka take. Allah ya bayyana maka ita, ka tashi da addu'a. Karka yarda rashin matar ka ya kasaraka. Makiya abinda suke nima kenan, kuma idan suka samu ba iya ni ba hatta wanda suka saka rai akanka zasu sare gwiwar su. Don Allah Karka saka mu jama'ar da muka saka rai da kai mu sare mana."
Yayi mishi nasiha ya kuma dawowa mishi da tunanin shi akan abinda yake faruwa. Sannan yayi mishi hannunka me sanda da wasu abubuwan da suke gab da faruwa, kuma dake mutum ne me kaifin basira sai gashi yana kallon Abubuwan kamar ba zai faru ba, dan haka bayan sunyi sallama, ya mike tare da nufar masallacin juma'a. Anan ya hadu da Baba Danrimi.
Bayan sun fito sallah jumma'a, suka tsaya a waje suna gaisawa.
"Ya har yanzun babu labarin Buhayyah?"
"Eh wallahi, amma muna kan hanyar gano inda da take Insha Allah." Ya fada yana karamar murmushi.
"Amma kuma idan baka ganta ba, ka hakura da ita mana ai babu dole sannan irin wand'anan Mata basu dace da irin ka wanda ya fito babban gida ba, dan basu san darajar shi ba. Sannan yarinyar nan ba wata kamun kai ne da ita ba, haka naji labarin ai ko lokacin da ka maida ita Abuja da aurenka take tsayuwarta da Halwani da Khamil."
"Ita kanta bata san da maganar auren ba, kawai daga sama takai ta ji labarin Dan haka babu amfanin da iya zartas da hukunci, sannan ni nasan halin matata, domin ni na dauke ta a budurwarta, kuma Alhamdulillahi ina kan niman ta, domin nasan darajar ta. Batun auren yan babban gida ba shi bane aure na kwanciyar hankali, Babban kwanciyar hankali ka samu matar da take sonka ta damu da kai, Nagode da tunatarwa."
Daga haka ya barshi a gurin sake da baki, yana nufar kofar gidan shi ya samu yan sanda suna bincike sakamakon kashe wasu yan ta'adda da aka yi a kofar gidan shi, dan haka sun tambaye shi yace bai sani ba shima dawowar shi kenan.
Lokacin da ya shiga cikin gidan ne yaga Iyalinsa hankalin su a tashe, da gudu yaran suka fada a jikin shi.
"Dad mun ji karar gun, a kofar gidan nan Mom ta na ta kiranka baka dauka ba, shine Uncle Khamil ya zo yace karta fita you are safe, dad ka mai damu gurin Granpa." Ta faɗa tana kuka, daukarta yayi suka shiga cikin dakin uwar su. Tana zaune a tsakiyar gadon shi, ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta.
"Baby" ya kirata a hankali, da sauri ta cire kanta tana kallon shi, ajiye yaran yayi tare da mik'ewa ya bude mata hannu, da sauri ta sauka tare da fadawa kirjin shi, tana kuka me tab'a zuciya.
"Asad na razana, na tsoro ta sosai. Na zata karshen rayuwata tazo ne, ban tab'a tsammanin kana raye ba, Alhamdulillahi. Asad ka mai dani Calfonia idan kome yayi sauki ka dawo dani ina jin tsoro."
Kara rungumeta yayi yana shafa bayan ta.
"My princess babu inda zaki, kina tare da Lion King zaki gudu. Babu abinda zai kuma faruwa Insha Allah, mijinki Jarumin gaske ne ba rago ba, mijinki ba irin su bane, karki sake tsoron wasu ya tsaya a ranki bayan muna da Allah." Ya fada mata yaba shafa bayan ta.
"Asad"
"Na'am. Baby" ya faɗa yana kallon yadda take kuka.
"Ince basu kuma dawowa ba?"
"Insha Allah ba zasu kuma dawowa ba, duk wanda ya dawo ma mutuwa zai yi, domin tab'a Aliyu da matan shi ba sauki ne ba, dan haka karki kuma zubda kwalla nan domin tsada ne dasu kinji. Ina son kwallar ya zuba ina tare dake, bana son su zuba bana tare da ke, kwallar ki ajiye min abuna lokacin da ya dace domin ina bukatar abu na lokacin da nake matse ki ina shanye dadinki." Bubbuga kafa tayi a kirjin shi tana kukan dad'i. Yau ita Asad yake gaya mata ta ajiye mishi kukanta yana da amfani, wow tana kara jin kaunar mijinta, sake makale mishi tayi tare da cewa.
"My sugar boy,"
Ware idanun shi yayi tare da cewa.
"Hmm, zaki sani a uku. Bari naci abinci yau zaki gaya min waye sugar boy, ina laifin Sugar Man. Gaskiya yau din nan"
Dariya tayi lokacin da ta ga ya hakikance zai kamata ta yayi mata chakulkuli, yana pretending ne kawai amma yana masifar kewar Buhayyah, haka ta riko hannun shi suka fito falo ta zuba mishi abinci yaci