Showing 45001 words to 48000 words out of 98705 words
Chapter 16 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt
magana...
Book din na kudi ne 200₦ akwai Royal Diamond Group 500₦, Musu bukatar Complete Insha ALLAH 1k....... Am glad to meet you guys.....
Insha Allah 01-July-2021.....
And don Allah idan ba zaki fadi magana me dad'i ba karka karanta min book, don Allah domin ni nasan dalilin da yasa nayi haka....
7/11/21, 8:36 PM - Buhainat: 2️⃣2️⃣
Kasa musanta mishi tayi tana kallon yadda yake kara niman Alfarma, tana kuma Cigaba da kallon shi, ranta yana soya, bata kaunar wani abu mara dadi ya faru,domin itace zata sha kunya. Kuma kamar lalacewar sunan ahalin su ne. B'ata rai tayi sannan tace mishi."zan rike ta abisa sharadin, idan bai maka ba wallahi ba zan yi kaffara ba sai dai ta wuce ta nime danginta" cikin zakuwa ya kalle ta yana me jin sanyi a ranshi, kafin ya shafa kanshi. "Ina jinki Uwata!" Ya fada cikin ladabi da biyayya, murmushi tayi domin Tabbas ya bata mugun tausayi, tun yana yaro tasan abinda yake so ta san abinda baya so, kallon shi tayi sa sannan ta girmama al'amarin da zata iya mishi iyaka da Yarinyar ba dan kome ba, sai dan kaucewa fadawa sharrin shaidan, da kuma sharrin mutane da na wasu dangin ababen cutarwa. "Daga yau kar Na kuma ganin ka da ita! Sannan babu ruwanka da masu nimanta! Sai kuma ka shiga tsakanin ta da matan ka" idan ka sake na sami labarin ka shige mata wallahi da kaina zan ce ta shiga duniya ta nimo danginta" duk sharadin da ta gindaya mishi ba masu yiwa bane, amma kuma sabida ya amshi hukuncin a matsayin ta ba mahaifiyar shi sai ya kuma kaskantar da kanshi yana shafa kanshi. "Na amince" ya faɗa in cool Voice, wanda ya sata kara kallon shi. "Mufeedah ki kula da ita bari ya ajiye ni a gida," kallon shi tayi sannan tace mishi."Mr Cool zaka ajiye ni a gida?" Ta tambaye shi, a hankali ya mike tare da amsar jakarta, suka fita tare, "Asad!" Kallo kwayar idanun shi yayi yana kallonta, kafin suka nufi gurin motar shi, "kiyi hakuri Ummana" ya faɗa in sound tone, "ba kayi min kome ba, amma kamar na shiga cikin soyayyar ka ko?" Ta tambaye shi bayan ya shiga cikin motar, kallon mirror din motar shi yayi sannan yace mata. "Duk abinda zaki yi dan kin damu dani ne, kuma ba zaki TAB'A abinda zai cutar dani ba ko ita kanta yarinyar domin ke uwa ta gari ce, mai kaunar Ƴaƴan ta da na wasu ma" ya fadi haka yana me jin tausayina kanshi da kanshi, har suka isa gida basu kuma magana ba. Kuma bai dai sake cewa kome ba, tun a harabar gidan Halwani ya taso kamar zai dake shi. "Karka kula shi" "toh" ya faɗa mata, sannan ya wuce abin shi, har ya kai bakin kofar gidan shi Halwani ya tare shi da faɗa. "Ina yarinyar nan?" Bai saurarre shi ba ya saka kai zai shiga cikin gidan, "kai ina yarinyar nan nace Maka?" Ya fada da mugun karfi. Bai kula shi ba, "ina ka kai Buhayyah?" Sai lokacin ya kalle shi kafin ya sake murmushi, ya dafa handle kofar shiga falon. "Wallahi baka isa ba, dole ka bar min yarinyar nan banza jaki" yana shiga ya rufe kofar bai kuma bin ta kanshi shi ba, kallon shi Mabrooka tai sannan ta dauke kai, kura mata ido yayi sannan ya wuce abin shi, har yayi wanka ya sake fitowa Mabrooka bata ce MISHI cika ka ba, yana zuwa gurin Dinning babu abinci a fusace ya juya yana kallon ta. "Ina abincin na?" Cikin masifa ta kalle shi, sannan ta kuma ce mishi, "yana gidan yarinyar da ka ajiye domin bukatar kanka, ko Buhayyah bata baka bane? Na zata bayan ka gama kwakule ta zata dafa maka abincin da zaka ci ne? Ai Ashe ba haka bane toh zauna a gurin sai na samu damar da take dashi zan girka maka, ko tausayin kaunar da nake maka ba kayi ka rungume wata banza can ni gani nan jaka ban san me nake yi ba, Allah dai saka min, kuma ba zan yi girkin ba" ta faɗa tana kuka, zama yayi yana kallon ikon Allah, dan haka ya fice daga gidan ya nufi gidan su, yana shiga ya samu Hajiya Kaltumah mahaifiyar Halwani sun zauna sai kwashewa Buhayyah albarka suke ita da Natashah. Bai d'aga kai yayi musu magana ba, ya nufi gurin abinci ya diba tuwo miyar eguse, tunda ya fara ci ya fahimci girkin na Buhayyah ce, dan haka ya nutsu ya fara ci kamar babu mutane a falon. Saukowar Papa ya sashi d'agowa daga abincin da yake ci, "lion King" murmushi yayi sannan yace "Na'am Abbana" ya kira sunan Annan shi bayan ya mike daga kujeran da yake jikin Table ɗin. "Meke faruwa ne?" Zama yayi sannan ya korowa Mahaifin shi bayani abinda yake faruwa, sannan ya kara da cewa. "Abba ayi min alfarma daya yarinyar nan zan daina shiga harkar ta, matukar Natashah da Mabrooka basu kuma shiga nata ba, duk ranar da dayar su ya taba min ita, toh wallahi duk abinda ya zagayo ba zan iya dakatar da kaina ba, sannan ina son a shiga tsakanin ta da Halwani da Khamil, ya fita hanyar ta ko kuma duk abinda ya faru yayi kuka da kanshi. Yadda yake maganar zai tabbatar maka daga ranshi yake maganar, murmushi Alhaji Ahmed Amin yayi yana kallon shi musamman yadda yake ƙara jadadda abinda zai faru idan aka mishi ganganci. "Toh Aliyu amma kana son yarinyar ne? Idan kana Sonta sai ayi abu daya a hana ta kula kowa sai kai, amma nace zan hanata kula samari kamar nayi son kai ne, ka dai duba wani abu" shiru yayi sannan ya kara dakewa yana jin Hajiya Kaltumah tana cewa. "Alhaji Ahmed ban da fitina irinta Yaran yanzun ina Aliyu zai kai mata har uku, biyun basu ishaka ba sai ka kara da ta uku?"
Kura mata ido yayi tabbas tana son ya kafta mata rashin mutunci shi yasa take shiga hurumin shi. Mik'ewa yayi daga falon ya nufi waje domin ya cigaba da kallon abinda yake mishi zai iya mata tijara ba tare da ya fahimci abinda yake ba, ina shirin Fita Baban su yace mishi. "Kana son yarinyar ce?" Tsayawa kowa yayi yaji amsar da zai faɗa masu. Yace musu"A'a babu SOYAYYA a tsakanin mu, taimakon ta nake. " "Aliyu ASADULLAH kaji tsoron Allah kace baka son Buhayyah taimako ne a tsakanin ku?" "Eh ya faɗa yana barin gidan, ya rasa meke mishi dad'i, me ya kai shi wannan katob'arar. Haka yayi ta zaga gidan yana nazarin abinda ya kaita gashi babu halin yaje ya ganta.
Karfe takwas Moddibo ya dauko mu, ina kwance a jikin Sit abin duniya ya dame ni. "Buhayyah dama baku soyayya da Ya Aliyu Asadullah?" Kamar wacce baka mintsine ni na tashi zaune ina zare ido. "Babu kome a tsakanin mu" na fada ina kallon Aunty Mufeedah, "toh ai bamu ce akwai kome ba, soyayya muka tambaya tunda babu shikenan" ta faɗa tana kallon hanya Itama. Har muka isa gida ban san me suke ciki ba, sai da na shiga cikin gidan na samu ana kuma maimaita abinda ya faɗa d'azun ko dan sun ganni ne oho. Gaishe su nayi sannan na nufi hanyar d'akina, na zauna a bakin gadon. Ina jin babu dadi a raina.. shigowar Natashah ne ya sani mik'ewa ina kallonta. "Toh karya mara zuciya bari kiji abinda Hubbyn ya gaya mana akan ki!" Haka muryan shi ya fito tar sunkuyar da kaina nayi ban san lokacin da murmushi ya subuce min ba, ina wasa da yatsuna. "Toh nagode" na fada mata ina me nufar ban daki, riko wuyar rigana tayi tare da Hadani da bango. "Wai Ni kam meye nayi miki ne kika tsane ni? Me yasa ba zaki je gaban mijin ki, kokarin riko wuyar shi ba, dalla sake ni" na kwace kai na, juyar dani yaxa mare ni, na kare kaina kwalla na cika min ido, marin hannu tayi tayi, har da cire takalmin ta. "Wai ke Natashah baki da hankali ne? Kishi hauka ne? Zaka kashe musu yar mutane ne? Duba yadda kike dukarta da dunduniar takalmi, gaskiya kin b'ata wayonki" inji Mama tana fisge takalmi. Kowa na gidan sai da yaji babu dad'i. "Kiyi hakuri Buhayyah Mufeedah don Allah kula da raunin da taji, karku bari Asad ya san abinda ya faru." "Ai ba gidan Ubanta bane wallahi dai ta bar gidan nan ko kuma na kira Abbana na gaya mishi cin zarafina da kuke" ta fada tare da riko rigana ta nufi Hanyar waje dani. Tana hankad'a ni. "Fita mana a gida slut kawai, bar magana gidan Mijina" dakyar aka riko ta, tana ihu tana masifa lallai sai na bar gidan, saukowa yayi daga falon shi na sama ya fito, yaga abinda yake faruwa. Kifa mata mari yayi sau daya yasata dauke wuta na hucin gadi , na wasu dakikai kafin ta dawo hayacinta, ta wani fashe da kuka tana shafa hancinta da yake zubda jini, kusan Yaran manyan ba kowa yake hukunta dan shi ba, dan haka ya d'ago Buhayyah ba tare da ya kalle su. Ya rike hannun ta, tare a nufar cikin gidan shi."wallahi ba zan yarda ba, sai na kashe ta." Bai kula ta ba, kuma babu wanda yayi yunkurin dakatar dashi, sabida yadda ya dauki matakin cikin gaggawa. Falon shi ya wuce dani. Ya zaunar dani tare da dauko goron ruwa ya mika min. "Meye ya hadaki da ita?" "Ban san meye nayi mata ba, don Allah ka barni na koma gurin Aunty Nafy" wani irin duba yayi min irin baki da hankali ne? Sunkuyar da yayi tare da fashewa da kuka. "Ni kam ba zan zauna ba ka kai i gurin Aunty Nafy nace" na fada da karfi ina kuka. Mamaki ne ya kama shi. Abinda ya kuma kara bashi dariya bai shirya ba shine ganin yadda take bori, har da niman faduwa a kasa, bai san lokacin da ya tare ta ba, idanun ta na zubda kwalla. "Da alamu a gidan ke yar auta ce abinda kike sai an auta sakaltattun yara." Jin tudun kirjina a nashi ya sani sauke wata irin ajiyar zuciya, tare da manna kaina a kirjin shi ina jan majina. "Ke yar baby ce?" Tura baki nayi ina son saka mishi kuka. "Kika sake kika yi min kuka sai na baki mamaki. Ki shirya kayanki zaki koma tankara kamar yadda kike so" ware idanuna nayi tare da mik'ewa sai kuma na sake murmushi ina gyara gashina ina ajiyar zuciya na sauke sannan na ciro tissue na goge jinin bakina, "sir zan iya tafiya?" Nuna min hanya yayi yana tsugunne, fitowa nayi tare da nufar step din. Ban san ya akayi ba, sai dai na ga wutar gurin ya dauke tare da jin an tura ni daga bakin step din. "Sir Aliyuuuuuuuuu" na kira sunan shi da mugun karfi ina gungurowa daga step by step. Da gudu ya bude kofar tare da kunna wutar gurin, cike da wani irin Fargaba ya hango jinin da yake malala daga kan Buhayyah. Uku uku yake tsalle step din har ya isa gurinta, daukar ta yayi tare da ficewa daga gidan. Lokacin wata mota baka tayi mishi horn, kurawa motar ido yayi yana hango Natashah ce a cikin motar, tana me fita a gidan. Wani irin bakin ciki ne ya kama shi, da sauri ya nufi gidan su da Ita tana kwalawa Mufeedah kira. Dukkan su haka suka fito.
"Mufeedah!!" Hankalin su a tashe suka kuma fitowa, ganin yadda Jini yake saukowa daga kanta yasa Mother ta cire hijab ɗinta aka daure kan, sannan aka nufi asibitin da ita, tun karfe tara suke tsaye da gaban kofar har zuwa karfe biyu na dare sannan, likitan ya fito alamar an gama aikin, turo ta aka yi a gadon.
A tare suka sauke ajiyar zuciya, sannan suka Kalli mufeeda da aka yi aikin da ita. Yanayin fuskarta kawai ya saka su fahimtar kome dan anyi nasara. "Mufyy" ya kira sunan ta a sanyayye, "Alhamdulillah, babu wani abu buguwa ce a goshinta sai jin ciwon da ya hadu a gurin amma taya haka ya faru?" Cikin takaici yace musu. "Natashah!" Zaro idanu suka yi, "ita ce ta wurgota?" Cikin takaici ya fallawa Sawwama harara, "karya na miki? Nace karya na miki? Idan ba ita bace waye? Ko kin ajiye wani da zai turo ta ne?" Shiru tayi kanta a sunkuye, "amma ai bata fadi haka dan wani abu ba, idan ka duba gidan ai akwai Mabrooka, ko bata san abinda ya faru bane?" Shiru yayi tare da kurawa Mother ido, sai yanzun abinda ya faru ya dawo mishi lokacin da zai fita dauko Buhayyah, haduwa suka yi tana mishi kallon jin haushi da takaici. Dafe goshinsa yayi tare da cewa. "Toh idan ba Natashah ba sai dai Mabrooka ce" ya faɗa a masifance, "toh idan ba ita bace fa?" Allah Sarki duk sai ya zuba musu ido, "zaku kashe ni" ya faɗa kamar zai zubda kwalla. "Bamu kashe ka ba, amma ya kamata ka bincika wanda yayi laifin ba wai ace wannan wannan ba, idan na zaka iya tsayawa a gidan ka ba, me zai hana ka bar masu so da gaske suyi rayuwa da ita ba wai ka zauna kana kame kame ba, yarinyar nan dai kowa ya san ba aurenta zaka yi ba, toh don Allah ka barta ni da Khamil mu shiga nimanta." Kurawa Halwani ido yayi sannan yace mishi" dadina da kai dakikanci, uwar ka zanyi da ita?" Basu tab'a jin zagi a bakin shi ba, amma yau da yake a fusace yake sai gashi yana aunawa. "Karka kuma zafin Mahaifiyata?" "Uwarka gwal ce fa ba zan zage ta b...." Saka hannun Mother tayi a bakin shi. "Ni kake zagi fa" tashi yayi tare da naushin bango dai da kashin hannun shi yayi kara, cikin fushi yace"Ya kuke so nayi? Ya kuke son nayi da rayuwa na? Yarinyar nan tun kafin ta shigo cikin mu ake samun matsala da ita, tunda ta kasance mara magana da fada kowa ya rena ta, meye yarinyar kayi da aka son a cutar da ita saboda kishi Me yasa?" Ya fada da karfi tare da zama yana huci. "kayi hakuri mana" inji Mufeedah, saka kai yayi ya bar asibitin dan matukar ya cigaba da zama asibitin zai daki kowa ma, haka ya nufi gida, lokacin da ya isa gida ya shiga Part din Mabrooka, yana shiga ya same ta kwance tana barci. Tab'a ta yayi ta farka. "Lafiya?" Ta tambayi shi, "duk abinda yake faruwa baki sani ba?" Kallon shi tayi irin kallon mamakin nan, "kamar ya duk abinda ya faru ban sani ba, ina barci me zan iya sani" "mutuwa kika ba barci ba, ban da tsabar Iskanci ki turo yar mutane a sama kice barci kike?" Ya daka mata tsawa da yasa ta fashewa da kuka. "Wallahi ban turo Natashah ba" "kaniya ce ba Natashah ba, nace kaniya ce ba Natashah ba, akan Buhayyah nake magana na akan wata can ba." Ya fada da karfi. Bakinta sake take kallon shi bata san lokacin da kukan ya tsaya ba, tace mishi. "Wallahi ban san me kake nufi ba meye ya sami Buhayyah?" Wani irin dauke wuta yayi. Yana kallonta. Kafin ya juya ya fita daga dakin, ya nufi sama, washi gari.. Natashah tazo gidan domin daukar kayanta yasa aka kama mishi ita, kallon shi tayi cikin mamaki, "meye nayi maka?" "Idan kika isa station zaki musu bayani." A tsorace ta kalle shi tana girgiza kai tace" don Allah ka gaya min meye nayi indai akan dukar Yar aikinka ne wallahi ba zan kuma ba karka zubda min kimata da ta Masarautan da na fito." Ta faɗa tana zuɓewa a gaban shi. "Ba akan dukar bane akan furucin sai kin kashe Buhayyah ne, har kika yi nasarar turota daya daga sama". "Ni!!!" Ta faɗa tare da rufe bakinta ya kuma fashewa da mugun kuka tana faɗin."nasan nace zan kashe ta amma billahi azim ban shiga gidan ba, wallahi ban mata kome ba, na rantse da Allah bayan na dake ta da naje gidan Hajiya Rumaisah fada tayi min ka kirata ka tambaye ta, na rantse ban mata kome ba, akan me zan turo ta, don Allah karka zubdawa mahaifina mutuncin shi" ta faɗa tana me hada hannunta dukka biyu. Tana kuka me matuƙar ban tausayi, d'agawa hannu yayi cikin damuwa. "Sir mu barta ne?" D'aga kai yayi wanda yake sara mishi kamar zai fadi. *Toh waye ya turo Buhayyah daga sama?*.ya tambayi kanshi.
7/11/21, 8:41 PM - Buhainat: 23***"Something happens ba tare da na sani ba, waye yake bibiyar inuwata, tabbas wani yana bibiyar rayuwata, amma ba a tsaya a kaina ba sai akan Innocence lady" ya faɗa yana sosa goshin shi. A hankali ya nufi cikin gidan shi, yana sallama securitys din, ya shiga cikin gidan shi ya zauna tare da harde hannun shi yana kallon hoton shi na nadin sarautan da akayi kurawa hoton yayi ido, kafin ya mike ya kuma shirin ya nufi asibitin dake shi yake jan motar, lura yayi da wata mota tana bin bayan shi, shiru yayi tare da gangarawa daga samar titin zuwa gefen hanya, yaga motar me kiran toyota hilux 4×4 ta wuce da mugun gudu. Lumshe idanun shi yayi yana tuno Number mota, kafin ya kira BASHIR ya gaya mishi.
"Iko Insha Allah yanzun za a bibiye motar."
Ya fada mishi, lumshe idanun shi yayi yana kallon yadda motoci suke tsalla gudu, shima ya bi bayan su a guje, yana jin ina ne zai samu wanda yake harin Buhayyah. Koda ya isa asibiti ya samu Mahaifiyar su da Mufeedah , zama yayi tare da dafe goshinsa."na rasa wanda ya ture Buhayyah daga sama, Mabrooka tace ba ita bace sannan Natashah tace