Showing 93001 words to 96000 words out of 98705 words
Chapter 32 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt
ya dace sai da suka kammala shi a daren, kafin zuwa garin yawaye, an gayawa dangina da sauran mutane, dama tun wancan watan aka cire min robar bakin mahaifan. Saboda yadda na fara nakuda a tsayayye.
---
Kwanan mu hudu muka dawo Kano, dan Iyayena sun ce ba zan koma dakina ba sai an yi min biki kamar kowacce Y'a, shi yasa aka hada a sunan, sannan aka rike ni sai nayi arba'in abisa al'adar Hausa. Haka na cigaba da samun kulawa daga iyayena da yayuna.
***
Tankara.
Lokacin da ya dawo, kwanan shi biyar ya wuce Abuja, shi da matar shi, wacce kamar ya sani domin ya sara mata baki a hankali take laulayi, me cikin jiki.dan haka ya barta a Abuja tayi fama da kanta, shi kuma ya dawo Tankara, ya mai da hankalin shi kan Yanayin kamfanin da u bude, bayi zaman gida kullum yana fita.
Wani lokaci kuma sai dare yake dawowa. Ya gama kome na tunkarar mutanen da suka sako shi a gaba.
.......
Kallon Mother tayi sannan tace mata.
"Ina son zuwa gurin Yar uwata a Kaduna gobe Insha Allah zan dawo."
"Toh Allah ya kai mu, ince kunyi magana da shi?" Tambaye ta,.
"Eh munyi dazun jiya ma munyi"
"Toh Allah ya tsare"
Ta faɗa tare da mai da kanta gurin Alkur'ani da take karatun shi. Bayan tafiyar ko minti talatin ba ayi ba, aka kira Number Mother.
"Kece Surukar me wannan wayar?'
"Eh nice lafiya?"
"Hmmm! Yanzun aka wasu yan bindiga ne suka harbeta tana babban asibitin Abuja.."
Salatin da take yi ne ya fito da Moddibo daga dakin shi da shida Papa, suka nufi asibitin. A hanya suka kira Aliyu. Kamar zai haukace haka yake ji, ko awa biyu ba ayi ba, sai gashi nan ya iso garin Abuja.
Bai tsaya wata wata ba, ya dauki Bashir, suka tawo Asibitin.
Ganin halin da take ciki,.yasa shi lumshe idanun shi. Kafin ya bude akan Bashir suka fita.
Koda suka shiga mota murmushin takaici Aliyu yayi sannan yace Mishi.
"Ka gayawa Uncle ya isa haka? Mata ta da ciki yake niman rayuwarta? Meye aka yi akayi mulki? Uncle Dan Rimi yayi min abubuwa dayawa, dan haka bana son na harzuka balle na kai ga ramawa, mulkin Tankara kuwa bana bukatar shi saboda tsoron kar na rasa ahalina tunda abin ya koma kan Mabrooka."
Jikin shi ne yayi mugun sanyi, a hankali ya bude baki tare da cewa.
"Ya aka yi kasan cewa shi yake niman rayuwarka?"
Ajiyar zuciya yayi sannan ya kalle shi yace.
"Kana son na gaya maka ne? Ko kana son kaji abinda zai tarwatsa maka tunanin ka?"
Flash back...
In 1940
Kakan Alhaji Ibrahim Amin danrimi. Shine mutum na uku da ya tab'a shiga birnin ƙaisa,, garin da yake dauke da biranen aljanu.
Lokacin da ya isa fadan Sarkin Aljanun, aka mishi iso ya zauna.
"Barka da zuwa Bakon mu, meke tafe da kai?" Wani daga cikin manyan da suke tare da Sarkin.
"Nazo ne mu had'a kai muyi mulkin guri guda."
Kallon Sarkin su suka yi. Sannan suka ce mishi,
"A'a Bama bukatar haka mulkin kasar mu ya ishe mu ba sai mun hada da mutane ba,"
Kallon su yayi sannan yace musu.
"Zan baku damar nazari zan dawo idan aka kwana biyu."
Sanan ya bar su, shiru Sarkin su yayi sannan ya zauna yana nazarin da muhawara tsakanin su.
"Zamu yarda da bil Adama a cikin mu ba, domin basu da amana, kuma karshe zasu yi amfani damu ne gurin mulkin su"
Inji wasu daga cikin manyan fadan,
"Insha Allah ba zamu basu hadin kai ba, koda ya dawo" suka fada tare da yanke hukunci.
A cikin fadar akwai munafukai, dan haka suka zame jiki suka nemi Alhaji Amin Dan Rimi,.suka yi magana dashi. Shi kuma ya kuma zuwa bayan kwana biyu.
Zama suka yi bayan.ya gaishe su yace musu.
"Yau ma kamar wancan karon na dawo muku"
"Kayi Hakuri ba zamu iya hada mulkin mu da kai ba, sabida haka kamar wancan karon ba mu amince ba"
Mik'ewa yayi ya tare da cewa.
"Toh shikenan." Ya fada tare da barin garin baki daya.
A lokacin yana son karfi da yaji a bashi mulkin tankara nez shi yasa yake ta bin hanyar da zai samu, da shi da wasu manyan mutanen cikin fadar tankara suka koma garin akan musu magana na karshe su kuma aljanun suka razana su, tare da koran su.
Abu yayi musu ciwo, dan haka suka zauna tare da shawarar yadda zasu kama su a hankali. Haka kuwa ka yi suka samu wani shaidanin boka, ya kama musu aljanun baki daya, cikin shirin kota kwana bayan an bautar dasu. Ta hanyar amfani da karfi sai dai kuma duk da haka, bai basu mulki ba, sai ma wahala.
Bayan sun kame su, sai ya kasance sun samu karfin mulki na fitan hankali, su basu mulki amma suna da damar nad'a duk wanda yayi musu, sai abun ya zama kamar Tsinuwa ce, domin kuwa babu wani da zai tunkari mulkin matukar basu son shi sai ya mutu.
Haka suka yi ta gadar da mugun nufinsu akan jinin su, ga bin bokaye da malamai, a garin binsu sune suka samu labarin mulkin zai fita a hannun mutane a suke so, zai koma hannun mutanen da suka yarda da Allah.
Bayan shekaru masu yawa, har zuwa yanzun da Sarki Abbas ya gabatar da Aliyu a matsayin shine majiran gado, haka ya mugun daga musu hankali.
..... "Tun daga lokacin da aka hana Zuri'ar mu mulki na fara bincike sai na samu daga cikin dalilai akwai bautar da Aljanun da ake yi,.sannan na biyu Zuri'ar dan Rimi sun fi kowa aikata laifukan cin zarafin wasu jinsin halitta,dan haka na fara bincike akan Zuri'ar Shamaki, anan na gano cewa idan har zasu kwana su wuni babu me yarda suyi mulki.
Uncle Danrimi yana amfani dani ne dan bukatar kanshi, ban tab'a sanin cewa yana da hannun akan abinda ya faru da mu da kuma abinda ya faru da ni kwanakin baya ba, sai bayan da na kama ola, ya gaya min shi yake sakawa yana Aikata min mugun aikin shi, sannan na kuma fahimtar baya kaunar dukkan abubuwa da yake min kawai Pretending yake. Wannan abin yayi min zafi, yanzun kuma mata na da ciki?
Ka gaya mishi ya isa haka, nasan baka sani ba, kuma baka da hannu akan abinda ya faru dani, shi yasa ranar da Mufeedah ta kawo min kai gidana da yake can naga mamaki akan fuskarka.
Sannan ban kuma tsinkawa ba sai da naji ashe har aurenka da Mufeedah ya haramta aurenku bai ishe shi ba, ya tafi har Kano yayiwa Sarkin Kano gargadi, Ashe ya ma rigada ya amsa min auren Yar Sarkin kano.
Me Fahimci baka da hannu a cikin abinda yake faruwa dani ne ta hanyar gane haka ne, yasa na kuma damka maka binciken, sai na fara Fahimtar Mahaifinka yana bibiyarka, tare da tura maka sakon ka fita daga binciken da kake min.
Wallahi ban tab'a jin ko dar na cutar da kai ba, sabida kai abokin yaranta nane, sai dai na fahimci yana amfani da kai sanin abinda nake, shi yasa zaka lura da janye maka da nayi, Mahaifinka ne amma sabida kai na d'aga mishi kafa, idan ya kuma wani ganganci akan Iyalina zan haukace idan na haukace kuwa ba me taro ni sai Allah, shi yasa bana son haukar ta kamani dan bani da dad'i sam, idan da Mabrooka ta mutu me zai ce min?
Yazo min ta'aziya ko me? Bayan shi yasaka aka kashe min mata ta? Wallahi na sha mamaki da na gane Uncle Danrimi shine yake niman hanyar halaka ni sai naga kamar kashe kaina nayi da kaina, me yasa bai gaya min mulkin yake so ba, amma lokaci guda ya sauya daga yadda nasan shi zuwa yadda yake. Koda yake jini yafi ruwa kauri, zai yi haka ne domin gadar mishi da abinda aka yi, ba zan lamunci cutar da Iyalina ba, ba zan dauki gangancin ba, duk abinda zai yi yayi amma ban tab'a min mata na da Yarana.....
7/19/21, 11:35 AM - Buhainat: 4️⃣4️⃣
Bana son abinda zai raba zumuncin shi yasa nake gaya maka, shi kuma Mahaifinka ne, duk lalacewar shi naka ne, idan wani abu ya same shi ta sanadina ba zaka yafe min ba.
Amma ni waye zai bi min hakkina? Waye zai gane abinda Ake min zalinci ne? Mata na da Yaron cikin ta na four weeks ya zaka ji idan kai ne? Bana son abinda zai tab'a zumunci, shi yasa na gaya maka amma billahi azim zan dauki kowacce irin mataki akan shi sabida bana tsoron kowa sai Allah.
Idan kuma yaga ba zai daina ba, tabbas mai laya ya kiyayye mai zamani, dan zan bashi kyautar da bai zata ba." Daga haka ya fita a motar domin ranshi ya kai kololowar baci. Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Karka damu zan duba kome a tsannake, amma ya fita a rayuwata." Ya fada tare da juyawa ya koma asibitin. Yana shiga ya nufi dakin da yake kwance ya zauna a kujeran da yake kallonta, ya riko hannunta.
Ya sumbata sannan ya cigaba da kallon yadda take zubda kwalla ta gefen idanunta.
"Insha Allah zaki samu sauki, ina tare dake, ba zan tab'a juya miki baya, ina son ki sosai"
Tausayin rayuwarta yake, baya son ya rasa uwar Ya'yan shi, kwalla ce ta zubo mishi. Kamar yadda yake jin har abada ba zai samu macen da ta kaunace shi kamar Ita, ba zai tab'a samun macen da ta zauna dashi babu soyayyarta a zuciyar shi sai ita.
Yasan shi da Buhayyah lokaci guda suka fada kaunar juna, amma ita wannan tana ganin shi taji a ranta ta sami abokin rayuwarta, bai tab'a kawowa yau zai zubda kwalla ba sai yau, da yake kuka domin ya rayu ya gaya mata yadda yake kaunarta. Kamar ba namiji ba yayi kuka saboda kaddarar shi ya kawo shi inda bai zata ba, bai tab'a kawowa yau sabida mulki zai rasa farincikin shi ba sai akan fuskar ta.
Koda Buhayyah ta b'ata bai yi kuka ba, amma yau ganin halin da Mabrooka take ciki, yasa shi kuka sosai, dan haka ya kira mai martaba ya gaya mishi abinda yake faruwa, baya son d'agawa Iyayen shi hankali. Amma kuma ALLAH yana tare da shi.
Haka ya kira Buhayyah ya gaya mata. Domin an sanyawa yaranta sunan Ahmad da Muh'd, suna kiran su da Ayaan da Ayaaz, yana gaya mata, kuka ta saka mishi. Haka ya kashe wayar.
*"*
Lokacin da ya gaya min abinda ya faru, kuka nayi ta mishi ina ji kamar nice a halin da yake ciki.
Ajiye su Ayaan nayi tare da cewa.
"Ummana Mabrooka an kai mata hari don Allah ki taimaka min na isa gurin su, wallahi yana cikin kadaice sosai. Yana bukatar wani kusa dashi. Kuma nasan ni ce na dace na zauna a kusa dashi."
Ganin yadda nake kuka yasa ta ce min.
"Zaki amma zaki dawo, domin gaishe su zakinyi sabida har yanzun jikinki bai yi kwarin da zaki tafi wani guri ki zauna ba."
Gyada mata kai nayi, sannan shiga hada kayana, ina kuka sabida tausayin mijina, kai jama'a umma tace.
"Kiyi hakuri mana, Insha Allah zaki tafi ai ba kwana nace zaki yi ba da kike hada kayan ki da na yaran" d'ago kai nayi na kalle ta cikin kuka nace mata.
"Wallahi na rude ne, Ummana yana cikin tashin hankali da damuwa shi yasa amma na nutsu."
Murmushi tayi sannan tace min.
"Karki damu Allah yana tare su, ki daina damun kanki."
Gyada mata kai nayi kawai, amma tabbas mijin da kishiyata suna cikin damuwa, dan haka na zauna na ci kuka. Sannan na kwanta a kusa da yarana.
*"*
Cikin kuka ya kifa kanshi a jikin motar shi, yayi kuka ya kuma yin kuka, domin bai tab'a zaton Mahaifin shi yana cikin masu yunkurin kashe Aliyu ba sai yau, duk da yasan cewa mahaifin shi yasha tambayar shi, ina Aliyu yake.
Ina zai je, me yake yi yau, irin wand'anan tambayoyin ya zata kawai sabida damuwar da yayi da Aliyu ne ashe sabida zai kashe Aliyu ne.
Yayi kuka karshe kan shi yana sarawa ya ja motar shi ya bar gurin.
Bai san inda yake tafiya ba, kawai tuki yake, sai da yaji kamar an kwace motar a hannun shi, ko kafin ya dawo hankalin shi ya afka mummunan hatsari wanda kafin kace me motar ta kama da wuta. Dakyar aka samu yan kwana kwanan da suka kashe motar, aka dauke shi ya gama jikata aka nufi asibiti da shi.
Koda suka isa Rai yayi halin shi, A labaran Duniya Aka saka hoton motar da kuma yadda aka yi hatsarin take hankalin Alhaji Ahmad ya tashi babu shiri ya nufi asibiti shi ya kira Alhaji Ibrahim Amin Danrimi ya gaya mishi hatsarin. Zasu dauki Bashir zuwa Tankara, yana fadar haka ya kashe wayar.
*"*
Zaune suke Galadima, Turaki, Waziri da Danrimi.
"Yaron nan ya kamata mu ga bayan shi" inji Galadima.
Kallon su Yayi sannan yaji wayar shi tayi kara, dubawa yayi sannan ya dauka.
_Abba Me yasa ka aikata abin zai sani jin kunyar ALIYU ASADULLAH? Abba meye Aliyu Asadullah yayi maka? Don Allah Abba ka kyale shi tunda yasan kana bibiyarshi Abba matar shi suka harba me yasa kake aikata laifukan cin amana a boye? Yau Aliyu da bakin shi ya gaya min yasan kai ne kake aikata mishi haka amma ya kyale ka sabida ni! Don Allah karka kuma cutar dashi babu ruwan shi, don Allah ka rayu cikin aminci da salama mana, Abba ka yafe min Nagode sosai Allah ya huci zuciyar ka_
"Sai na kashe Aliyu yau ni zai kunyata a gaban Bashir? Yaron nan bai tab'a sanin halina ba amma lokaci guda Aliyu ya gaya mishi nike bibiyar shi, yaron."
"Toh ya kama ta kan kaci kaniyar shi"
"Wai dan a. Harbi matar shi ne ya tsare BASHIR shima da rashin sanin ciwon kai yake damuwa akan shi.". Ya fada tare da jin faduwar gaba me mugun karfi.
Har aka yi magarib suna kulla Sharri sai ga kiran Alhaji Ahmad, akan zai kawo Bashir. Bai yarda ba sai da ya tabbatar mishi da cewa tabbas Bashir ya mutu. Nan ne ya fashe da kuka, tare da zaman dirshan yana tuna abinda ya gaya mishi.
"Abba a duk lokacin da naga kana yawan tunani sai na ga kamar kana cikin mutanen da Allah yayiwa baiwar fikra ce, don Allah Abba kayi ta nusar damu hanyar da ta dace"
Ire-iren waɗannan maganganu idan ya tuna kuka yake sosai, a daren aka kawo gawar BASHIR, kuma a daren aka mishi sutura, washi gari Da Aliyu aka kai shi gidan shi na gaskiya. Lokacin da aka binne shi, daga Danrimi sai Aliyu ne zaune a jikin kabarin.
"Na zata kana son mulki ba zaka yi kuka akan rashin mutumin kirki irin BASHIR ba? Na zata ba zaka damu da mutuwar wanda bai san kome ba? Na zata kaunarka da duniya ta kai ta hanaka kukan mutuwar Bawan Allah. Na yarda da kai sama da yadda na yarda da kaina, bana jin maganar kowa sama da naka, Ashe hauka nake, ina ta nan waye yake don kashi ne ashe kai ne? Ina niman waye bibiyata ashe kai ne?
Amma ga damar nan na baka, domin nasan har yanzun zucuyarka na zata yi sanyi ba, sai ka ji labarin gawata tana dab da shiga rami, wallahi ban tab'a kawowa zaka iya cutar da rayuwata har haka ba, amma babu kome na Barka da Allah"
Ya fada tare da barin makabarta, yana share kwalla, domin yasan ya rasa aboki na gari, mutumin kirki. Mutum me addini da sanin ya kamata, mutumin da alkhairi ne ya haɗa su ba sharri ba, shi ya fara gaya Mishi ya auri Buhayyah kar Iblis yayi nasara akansa, shi ya bashi shawaran bincike sosai akan wanda yake kokarin ganin bayan shi har ya amshi binciken.
Shi ya gaya Mishi ya tsaya a tankara har ya sami matar shi tana da muhimmanci da daraja a rayuwar shi, shi ya bashi shawarar fita da Buhayyah waje lokacin da aka dake ta, shi ya bashi shawaran tsayawa akan matsayin shi namiji ya tafi da Buhayyah idan aka kwana biyu ya dawo da ita lokacin da bai da lafiya, shi ya gaya mishi ya ji tsoron Allah kar ya b'ata yar mutane shima Ya haifi mace, shi ya gaya mishi yayi hakuri da abinda matan shi suka yiwa Buhayyah wata rana sai labari, ya gaya mishi abubuwa yawan.
Ko jiya da zai rasu da yake gaya mishi abinda Danrimi yayi mishi kura mishi ido yayi domin wallahi bai zata haka ba, yana ganin yadda kwalla yayi ta zuba a idanun shi. Bashir ya rasu ya bar mata da tsohon ciki. BASHIR aminin arziki ne ba mutumin banza ba, haka kawai yaji kwalla da wani irin tsoron Allah ya cika mishi zuciya.
Haka ya suna a family house din su har aka wuni, yana yi yana waya da Buhayyah. Da ta isa abuja. Kawai wani irin tsoro ne ya cika mishi zuciya yana gudun kar a tab'a mishi mata da Yaran shi.
Haka ya kira ta lokacin sun shiga asibitin. Ajiyar zuciya ya sauke tare da Hamdalla ga Ubangiji da yatsare mishi mata da Yaran shi, dan haka yana zaune ya tura sakon a kai ta gidan su, idan ta gama zaman asibitin.
----
Tunda na isa Abuja na samu labarin Mutuwar Bashir na tausayawa matar shi da iyayen shi, sannan