Showing 78001 words to 81000 words out of 98705 words
Chapter 27 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt
dauko cabbage da kayan salat na hada yayi kyau, lokacin na zuba cus-cus din na rufe shi..muka wanke kayan da muka b'ata.
7/19/21, 11:33 AM - Buhainat: 3️⃣6️⃣
Haka ya saka ta a cikin motar suka nufi wani asibitin da yake gaba da garin tankara, suna shiga aka amshe su. Cikin gaggawa aka fara ƙoƙarin tsayar da cikin, abinka da tsohon likita shi yayi ta gaya musu allura da maganin da zasu saka mata, kafin aka samu jinin ya tsaya, lokacin ta farka.
"Don Allah ku tafi dani, na tsane shi na tsane shi mugu ne" haka nayi ya nanatawa, likitan da ya duba Ni gaya mishi da cewa.
"Sir idan aka yi tafiya me nisa da mota cikin zai sake fita, dan gaskiya tana bukatar hutu ne." Likitan na barin gaban shi ya kira privet jet na masarautan kano, bayan minti arba'in jirgin ya iso, dan haka airport suka nufa da Buhayyah, tun kafin su isa Kano ya kira yan shi da suke likitocin baki daya ya gaya musu gashi nan da bakuwa nan ba lafiya.
Bayan awa daya suka isa, kowa so yake ya ga bakuwar fuskar da aka tara su domin ita. Dan haka duk suka tawo, suna sauka aka je aka dauko su. Ita aka wuce da ita asibitin masarautan, aka fara bata kulawa, shi kuma ya wuce gida.
Sai da suka kwashe awa biyar akanta kafin suka yanke shawarar daure mahaifar, sannan aka kai ta dakin hutu inda zata yi awa ashirin da daya tana barci sabida karfin maganin zubda cikin.
Haka aka yi ta sintiri akan ta, kowa sai yazo yaga wacce Bakuwar fuska ce haka Lamido ya tawo da ita.
**
Lokacin da ya dawo yaga dakin alamar jini ya zuba amma bata cikin dakin bude kofar ban daki yayi yaga da gaske bata nan, dan haka ya fita zuwa gidan Mufeedah dan yasan kawarta ce,sai dai Mufeedah tana asibiti, kuma abinda ya dame shi, wayar Buhayyah na saman gadon,dan haka ya nufi asibitin babu ita babu alamar ta, ya zata ma ko rena mishi hankali tayi sai da tayi ta rantsuwa ya yarda,daga nan ya nufi gidan Innah Larai, aka ce bata nan ya kuma nufar gidan Aunty Nafy babu ita babu alamar ta, gidan Maman Uwani aka kai shi nan ma bata nan,kafin kace kwabo an rasa ta,ya kira Mother ya tambaye ta, bata Abuja dan haka ya kira Sawwama itama tace bata zo ba.
Wasa wasa hankalin Aliyu Asadullah ya tashi dan haka ya saka aka bazama niman matarsa, musamman favorite wife din shi, wacce yake masifar kaunarta, ya san saboda cikin da ya tab'a ta gudu. Toh amma me yasa ta aikata haka. Wallahi ya zata da wasa take mishi.
Dan haka yayi ta nimanta har aba zargin ko masu niman rayuwar shine suka dauke ta, babu ita babu labarinta,gashi ya roki Mufeedah karta gayawa Iyayensu abinda ya aikata, dake tana tausayin yadda ya shiga tashin hankali sai ta bar abin a ranta da zuciyar ta, amma gefe daya haushin sa take ji.
Abun kamar wasa aka kwana aka wuni babu labarin Buhayyah, zazzaɓi ne ya rufe shi Tare da danasanin kin sauraron ta, domin Mabrooka ma tazo daga Abuja amma wutar gabanta ta kashe bata damu da ya mutu ba ko ya rayu, domin kawai ya fifuta matan shi akan ta, haka kowa ya tawo ana taya Aliyu Asadullah jimamin matar shi amma ban da ita. Sai da Yayarta tazo daga Kaduna taga abinda take kamar farin ciki take Yayar tace mata.
"Murna kike dan matar shi ta b'ace? Kiga yadda kishiyar ki ta damu kullum akace sai tazo tana zama a jikin shi dan rashin Imani kina kallon shi."
"Toh ba shi bane ya nuna matan shi sun fini kome ba musanman Buhayyahr da yake daukar girkina ya kai mata"ta faɗa tana tura baki..
Cikin takaici da bakin ciki take kallonta kafin suka shiga magana na gaskiya, fada ta mata..
"Idan yazo baki sake mishi fuska ba ita kuma ya samu haka a gurinta ba dole ya kasance da uta ba, ke da kanki kika ce min yarinyar gwana ce a girki kinsan me yasa yake bayyana muku yafi ji da ita? Saboda tana iya b'ata lokacin ta a tare dashi ba tare da ta damu ba, ko bani ji da bakin shi yake cewa shi yayi mata laifi ta gudu ba, ai yasan abinda yake yi. Dan haka ki sake lale, domin matukar ya ganta ta dawo gare shi wallahi ta kare muku, a yanzun ma kamar zai mutu ina kuma. Ya same ta kina jin zai kuma yarda yayi abin da zata guje shi ne? Mata muke kashe damar mu, idan miji zai yi aure kyale shi yayi dauki sabon guri yake idan ya gama zai dawo gare ki, wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai ta mutuwar shi. Dan haka karki yarda mijinki ya ajiye ki a gefe sabida baki da hankali akan kishi, dan haka tashi ki kama mijinki ke fa kika gaya min baya tab'a miki fada a gaban su, dai a bayan idanun su, koda kuwa laifin zai kai girman yadda ba a zato ne, amma kin wani b'ata rai, mutumin da dan girman kusancin shi dake bai miki fada a gaban matan shi ba, sai yaushe kike son ki gane girman ki a gaban idanun shi? Amma ki cigaba da abinda kike, mata nawa maza suke cin Ubansu akan idanun kishiyoyin su, kuma su zauna ke fa daki ya kai ki yaki miki fada basu ji ba wawuya kawai, sai ki zauna yayi ta riritaki kamar kwai.
Lumshe idanunta tayi sannan tace.
"Shikenan shi baya laifi kenan sai Ni?"
"Kinga ko Amnah taga abinda kikewa dan uwanta zata ji zafi balle kuma sauran jama'a, dan haka ki nutsu ki gyara zaman ku da mijinki kafin ya fahimci yadda matan shi suke ya juya miki baya." Sam bata kawo akan haka ba, sai da yayarta ta tafi ta shiga Part din Buhayyah taga yadda kowa yake ririta shi da bashi baki, itama ta shiga tausassan mishi, har ya ɗan ci abinci.
Baki daya ta fara jin kamar ita tayi sakaci har mijinta ya kwace a hannunta da bata yi wannan shirmen ba ba zai samu da matan shi ba, amma by now ta shirya gyara alaƙar aurenta da mijinta da kuma kishiyoyinta.
Dan haka ta bashi shawara ya koma part din shi zai fi akan ana bude shashin Buhayyah, tunda bata nan kar a mata barna dan yara suna shigowa. Haka ta amince kuwa ana kara baza binciken akan Buhayyah.
***
Kano Emirater
A hankali na bude idanuna tare da yaye nikaf din fuskana ina kallon dakin da yake sauke da koren labule da farin paint, kamshin izal naji na kuma ware idanuna, a hankali na fara ƙoƙarin mik'ewa. Shigowar wasu mutane biyu, da sauri suka koma suna faɗin.
"Ya Ilahi!"
Can sai gashi kamar tururuwai, suka cika d'akin suna masu kallona, nima kallon tsoro na musu ina juya bayana.
"Na mutu ne?" Na tambaye su ina tab'a fuskana, kafin na juya na kalle su.
"Assalamun Alaikum!" Muryan matar ya ratsa mana kunne, kallon kofar suka yi, nima na kalli kofar. Tana shigowa idanuna kanta.
"Alhamdulillahi! Kuga wani irin kama" ta faɗa tana kallona.
Haka ta shigo cikin ɗakin, kafin kace me suka sauran sun zagaye ni, sai tambayana ake ina basu amsa.
"Ina iyayenki?"
"Innata ce kuma... Kuma ta rasu."
"Me yasa zaki zubda cikin jikinki?"
"Fulani Yahanasu a barta ta huta mana, Aamil zoka dibi jininta, domin wallahi ina jin Aeesh tace a nan"
Da sauri mutumin yazo wanda muka hadu a Jamus.
"Kece"
"Laaa kai, ina matar nan?"
"Ai Abba itace muka hadu da ita A Jamus ban gaya maka ba." Murmushi yayi sannan yace musu.
"Ka nutsu da kyau ka gwada jinin nima ka diba nawa." Kallon su nake.
"Autar Fulani me zaki ci?" Inji matar.
"Yawun bakina ne ya tsinke, nace mata dan wake."
"Kuma ya ishe ki ko a hada miki da wani abu?"
"Har da kosai da bread."
"Ikon Allah Fulani kamar yadda kika yi lokacin cikinta. Dan haka maza a. Kawowa Shalele!"
"Ku bani guri na mata wanka," haka suka fita ni da ita muka shiga ban daki, tana min wanka tana kuka, nima kuka nake.
"Taya kika sami cikin jikinki? Ke din Jinin Sarauta ke yawo a jikinki don Allah karki b'oye min kinsan ciwon da uwar da aka sace Mata yaro take ji kuwa? Bayan shekaru ashirin da biyu yau gashi ina wanke ki da hannuna, Aeesh."
"Toh me yasa aka sace ni. Innata tace mishi Ni yar masarautan Ka daga nan ta rasu me yasa aka rabani da ku?"
"Sabida kece kawai Ya mace da aka haifa cikin masarautan nan, babu wata mace sai ke, sai ƴaƴan yan uwan. Kishi ya sa aka fitar min dake."
Haka tai min wanka ina kara jin kaunarta a raina, har ta gama.
Muna fitowa aka kawo abincin tare da babban capter, aka shimfid'a na zauna a hankali. Sannan aka fara bani abincin, ina ci ina kuka.
"Cikin jikinta ince dai na aure ne?"
"Kai Musadeeq." Kallon shi nayi kafin na gyada mishi kai na.
"Cikin yana nan? Bai zube ba? Don Allah da gaske babyna yana raye."
"Little sister Babyn mu yana raye, sai dai yayi weak ne, ayi ta yin abu a hankali kar wani abu ya same shi ko"
"Toh Uncle din baby," na fada ina tauna abincin a hankali. Hawaye ne ya kuma zuba min,
"Daga wani gari kike yanzun?"
"A tankara aka tawo da ita baka ji hausarta ba."
"Mijinki yana can ne?"
Shiru nayi ina kuka tare da cewa.
"Don Allah Karku gaya mishi ina nan zai zo ya tafi dani na fasa auren shi ma,"
"Toh me yasa kika tsaya aka miki alluran nan baki san tana tab'a zuciya ba? Da badan Abba bane ya kawo ki sai na zane ki"
Kallon Abban nayi kafin na fashe da kuka.
"Abba wai zane ni zasu yi?"
"Babu me dukar gimbiyar Abba, amma karki kuma shan wani abu ina son ganin jikana, kinji Babyn Abba"
Wani abin ne ya tsaya min a rai, haka ina cin Abinci har Yaya Aalim ya kawo sakamakon ana ta murna, take Abba ya saka aka baza an same ni, nan aka bude wata irin walima, matan yayuna suma sun zo, kamar da nake da Umman mu yasa aka yarda nice dama tun haihuwa na nake kamar da Umma.
Habawa haka na kwana goma a asibiti muka koma gida, ina shiga cikin gidan, muka yi ido biyu da wata mata,gabana ne ya fadi ta mike tana faɗin.
"Yanzun sai da wannan yarinyar ta dawo? Toh wallahi sai ta koma, sai koma hahaha"
Ta fito tana dariya, abin da ya basu mamaki, hauka tuburam ta fara, tana tonawa kanta asiri iyayena kuwa kukan farin ciki aka fara, domin abinda ya faru.
Yayuna maza goma sha biyu ne, na Ummana bakwai na Matar da tayi hauka biyar, lokacin Abba yana mugun son Ya mace, shi yasa yace musu duk wacce ta kuma sami cikin mace zai mata kyauta a kuma abubuwan da zai yiwa Yarinayr da zata haifa, ita matar itace Uwar gidan, umma Amarya dan haka ta shiga fadi tashin har ta samu ciki ya lalace, sai Umma ce ta samu cikina,haka aka yi ya renon cikin har haihuwa.
Ranar da aka haife ni, Ranar aka sace ni, wannan maganar ya fito ne daga bakin Abban mu, kuka nayi tayi inawa Allah godiya, ya dawo dani cikin Ahalina, kewar mijina kadai nake ina jin a raina me yasa yaji min haka. Bayan kome ya lafa. Suka tambaye inda muka zauna.
Gaya musu nayi tare da basu adireshin Ya Haruna, dan haka washi gari. Abba ya tura har can aka tawo da su.
Karku ga Murna a gurin Siyama da Inna larai, haka dai suka yi ta murna, kafin bayan nan suka tambayi Innah larai, ta gaya musu abinda ta sani, tare da musu kwatancen Innah ta.
"Ai na gaya mata Karime ce domin itace na bari a ranar."
Gyara zama Innah Larai tayi sannan tace musu.
"Ta gaya min dalilin da yasa ta gudu da ita. Domin an zo za a kashe yarinyar ce ta dauke ta ta gudu da ita. Bawai dan an biyata ba,ceton rayuwar ta tayi.....
7/19/21, 11:33 AM - Buhainat: 3️⃣7️⃣
Haka ta gaya musu irin rayuwar da muka yi da,, kuka kowa yake a farkon tare da jajjanta min da ita kanta matar da ta sace ni, sannan ta kawo musu yadda aka daura aure na da Aliyu.
"Ikon Allah! Toh faduwa tayi daidai da zama, sai dai ba zamu nime shi nan kusa ba sabida yanayin da muka tsinci ta.
Domin bamu san abinda ya haɗa su ba, ta fito da karamin ciki tana zubda jini, kuma a yadda na fahimta Aishat meye ya haɗa ki da mijinki?"
Zaro ido nayi na fara yarfe hannu, ina cewa.
"Abba kayi hakuri, ni.... Ni...."
"Keke meye?"
"Inji Babban yayan mu dan a ƙalla ya haife ni, shine Baban Ummi da zasu bawa Aliyu. Kuka na saka ina faɗin.
"Kawai bana son cikin ne"
"Shine kike son kashe KANKI Dan baki son cikin jikinki? Wallahi ba dan cikin ba sai na zane ki, wanda gobe wani yace zai cire cikin shi sai tsoro ya kamaki, shegen rashin kunyar banza, mun gode sosai baiwar Allah."
Ya fada yana kallon Innah larai, itama godiya da kunya ce ta kamar, wayyo Allah naga gata da tarerayyar, yadda aka tattara soyayyar duniya aka daurawa cikin jikina ya masifar sanyani jin kamar na dawwama cikin dangina.
Haka ake ririta Ni, ko ina bayi ne da masu kula dani, ga Ummana. Ga matar Abba Amaryan ci wacce take bin Umma itama maza ne babu mata, wani irin kauna nake gani akan idanun yayuna da kanena, kayan ciye ciye kuwa kamar zasu fasa karamin frig din dakina.
**
Tankara.
"Da gaske saura kwanaki ƙalilan yaron nan ya zama sarki kuyi wani abu da?" Inji Turaki,
Shiru yayi yana kallon su, kafin gsladima yace musu.
"Ba zai sabu ba, idan muka bari meye zamu amfana shi, dan haka zamu dakatar da abinda yake faruwa, idan yana raye ne zai yi mulkin tankara idan ya mutu shi kenan."
Haka suka yi ta kullu munafuncin su, tare da shirya yadda zasu kashe Aliyu.
--
Gabaki daya ya watsar da kome, idan ka ganshi sai ya baka tausayi, gashi ba wani cikakken lafiya ne dashi ba, shi yasa ya zauna a Tankara ko zai ganta, haka yayi ta Bin lungu da sako ana niman ta, suma.matan shi sun kara tabbatar da cewa mijin su na Buhayyah ce.
Idan babu ita ba zasu tab'a samun shi ba, shi yasa Mabrooka ta mike sosai, gurin mai da hankali a niman Buhayyah.
.....
Kamar zata yi kuka haka take kallon shi tare da cewa.
"Muma muna bukatar ka, idan ka ce zaka cigaba da mana irin wannan horon zamu shiga halin rayuwa, ka dubi girman Allah ka yi hakuri ka ci abinci. Ubangiji yana son masu hakuri idan yaso sai ya dawo maka da Ita akan lokaci, idan kuma kace kai zaka nimo ta sai ya Barka da iyawarka, don Allah kayi hakuri" ta faɗa mishi muryana yana rawa, rike hannunta yayi tare da daura kanshi a kan cikinta.
"Karki kuma yin amfani da abin hana haihuwa laifina ne, da ban saka an cire mata cikin jikinta ba da ina tare da ita, ina son Buhayyah sosai.
Ban tab'a kawowa zata iya fushi da ni ba, sabida naga tana da hakuri da biyayya. Duk abinda na mata zata yi hakuri dani, B'ata tab'a nuna ta gaji da dani ba, asalima kamar jiran umarnina take. Na mata laifi amma kamar bata damu da abinda nayi mata ba. Har kwanan gobe ban tab'a ganin macen da duk yadda na mata zata ce min nayi hakuri. Kin tab'a ganin ta rama abinda kike mata?
Haka take bata iya fada ba, tana da sanyin hali sama da yadda nake, tana da juriya sama da yadda nake tsammanin, takan maida kanta kamar yar shekara goma a gabana dan ta sami nutsuwa ta, idan zata yi Shirme sai ta zama kamar yar karama sosai take shirmen nan.
Ina mugun kewar ta, ina mugun kaunarta, Ina son Buhayyah ban boye miki ba na gaya miki gaskiya, amma itace first love ɗina i love her, tana da kome na rayuwa ta iya zama da kowa, ta iya zama da duk yadda kazo mata, kai zaka mata laifi ita zata baka hakuri, samun mace irinta yana da wahala. Tayi hakuri da ke tun bata san kome akan ki ba, tayi hakuri da Natashah tun bata san zan aure ta ba, wallahi da mutuwa tayi sai Allah ya kamani domin sai na kare rayuwata ina danasanin mara amfani, yarinyar nan tayi ta rokona da Allah kar na cire mata kamar zata zauce, amma naki sauraron ta. Sai da tayi ta kuka amma yarinyar nan tace min ita ba zata tsane ni ba, amma zata nisance ni.
Wallahi da nasan haka zai faru, ba zata iya tafiya ba. Nayi laifi na kuma laifi na ki kulata bayan an mata alluran na tsallake ta na bar ta, Me yasa ban saussauta mata ba? Me yasa ban hakura ba lokacin. Me yasa?" Ya kifa kanshi a hannun shi, tare da lumshe idanun shi, domin kuwa bai tab'a jin tsanar kanshi, domin kuwa ji yaƙe kamar ya bar kasar baki daya ko zai huta.
***
Gyaran da aka mata bai saka ta sami nutsuwa ba, kallon Yarinyar ta me suna. Aanil yarinyar kyakyawa kamar uwarta,
"Mommy Ni kam a bar maganin nan haka sai abinda hali yayi, wallahi baya cikin nutsuwar da zai kula mace." Ta faɗa kamar zata yi kuka.
"Zaki min shiru ko sai na sab'a miki, ai ba wani abu bane domin kuwa idan kika shige mishi zai manta da