Showing 96001 words to 98705 words out of 98705 words

Chapter 33 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt

11 Mar 2025

4319

na zauna a jikin Mabrooka dan ma Yayarta tazo daga Abuja, Ni kuma Daddyn su Ayaan da Ayaaz ya saka aka kai ni wani gidan shi ya turo min sakon na zauna kafin ya dawo dan zai kai kwana uku nan gaba, dake nazo da me renon yaran ban wani daga hankalina ba, haka muka kwana bayan na ga kayan abinci a cikin gidan, dafawa nayi muka ci, washi gari na wuce asibitin.


Ga uban masu kula da lafiyar mu ni da Yarana, haka muka koma asibitin wunin ranar muna asibitin dan ma na tafi da abinci.
Muna zaune Yayarta take bani labarin abinda ya faru.


"Wallahi tana cikin mota suka harbeta kuma sun gudu, amma insha Allah muna saka ran za a kama su nan da wani lokaci, yan sanda ma suna nasu binciken kuma wallahi wai dan kar ya zama sarki ake wannan rigimar"


Shiru nayi ina kallon ta, haka ya yi ta gaya min abinda yake faruwa.


.....
Tsayin kwana uku,.kafin aka yi addu'ar uku, da yamma ya gaya min yana hanya, dan haka kafin ya iso na gama kome, nasan idan yazo asibitin zai fara zuwa dan haka ya nutsu na gama kome, ga Umman mu sai waya take min na dawo.


Bai shigo gidan ba sai karfe bakwai na dare, murmushi na sake mishi sannan na kama hannun shi muka nufi dakin da nake da yakinin na shine na taimaka mishi yayi wanka, sannan ya saka kayan shan iska, haka na taimaka mishi yaci abinci, sannan yace min.
"Ina jin barci nagaji ko zaki taimaka min da tausa."


"Ok kayi hakuri na basu abinci sai na zo." Haka na nufi dakin yaran dan dama Umma ta koya min yadda zan kula dasu ba sai na shiga hakkin mahaifin su ba, kuma ta nuna min yadda koda ina shayarwa zan kula da lafiyar su, dan haka na shiga dakin da suke na basu nono har suka yi barci, sannan na dauki madaran da muke basu dan nonon yana kasa musu, na bawa Nanny din su.


Bayan na koma dakin da nasan...
7/19/21, 11:35 AM - Buhainat: 4️⃣5️⃣


Wanka nayi sosai, kafin na shirya cikin wasu kayan barci. Na nufi dakin shi, ina shiga na samu yana zaune a jikin allon gado, yana kunna fitila yana kashewa. Na jima ina kallon shi, kafin na haura gadon na kwanta a kusa dashi. Janyo ni yayi yana sauke ajiyar zuciya.
"Daddyn Ayaan!"
"Na'am" ya amsa min a sanyayye,
"Kayi hakuri nasan mutuwar aboki da zafi"
"Ba mutuwar shi nake ji ba, yanayin yadda kowa ya harzuka akan mutuwar shi ce, mutuwar da aka so Mabrooka tayi shine ya faɗa kanshi.


Buhayyah taya mutumin da ka yarda dashi zai cutar da kai? Taya mutumin da baka da biyun shi zai cutar da kai? Ko Abbana bai san Uncle Danrimi ne yake bibiyata ba sai yau da aka gama Addu'ar uku, yake cewa.
"Kamar Yadda na rasa d'ana sabida kai Aliyu sai na baka kyautar da baka zata ba, shi akan shi ya zata a ranshi yake fada,.sai gashi abinda yake ranshi ne yake fada. Kamar Mahaukaci haka yake ta surutu taya ba zan ji wani iri ba.


Kinsan Dr Tahir Aliyu Shamaki Kanin Papa su dan Rimi ne suka kashe shi, Mahaifin Halwani. Yanzun haka an dakatar da masu muƙamin cikin fadar. Turaki, Galadima, Wazir, duk an sauke su. An bar wambai, dan sarari, sai Abbana da aka bashi Gsladima. Ina cikin kewa na musamman. Domin na rasa abokina tun na Yaranta."


Daura kaina nayi a kirjin shi ina shafawa, kafin nace mishi.
"Kayi hakuri Insha Allah kome zai wuce."


Janyo ni yayi kirjinshi sosai.
"Amma ba zaki koma ba kin dawo kenan?" Ya tambaye shi yana sumbatar bakina.
Rike fuskar shi nayi, a hankali na hada bakin mu guri daya, ina jin wani irin kewar mijina. Sannun Sannun sai da na biya tsawon wata guda da kana biyar da nayi a gida babu shi, wallahi sai da naji gabana kamar ba a jikina yake ba, domin Aliyu ya dawo min da giant din shi, har cikin mara ta nake jin shi, haka daren nan ya raya shi a jikina, dab Asuba ya janye daga jikina. Muka yi wanka tare. Bayan na fito yace min.
"Karki daura kome, zan mana odan shi." Ya fada tare da kallona. Shiryawa yayi sannan ya nufi masalaci.


Dakin Yarana na nufa nayi musu wanka da sauya musu kaya, sannan na basu nono suka sha, na kuma kwantar dasu. Sannan na dawo nayi sallah kamar yadda na saba, haka ma yau na musu addu'a kafin nayiwa mahaifin su, sannan na kuma daura da nimawa Mabrooka lafiya, sannan nayiwa kaina da ƙasata da iyayena.


Ina cikin azkar ya shigo ya zauna muka yi dashi, karfe takwas muka kwanta, bamu tashi ba sai goma an kawo abin karyawa. Daga gidan Hajiya Rumaisah, ashe ma muna kusa dasu ne, dan haka aka gaya mana wai takai wani asibiti, wanka muka sake sannan muka fito tare da zama muka ci abinci, sannan muka shirya domin yau xan koma. Sai bina yake da ido. Kamar kai na tafi, haka muka nufi asibitin daga nan ya kai mu airport.


Ina rungume a kirjin shi. Sai kalamai yake gaya min.
"Nasan zanyi kewarki, kuma nasan zan kasa hakuri da rashin ki ko zan bi ne?"
"Babu damuwa sai na saka ka a cikin jakata" haka muka yi ta hira.


A hankali nake kallon shi bayan na sumbaci kumatun shi, lokacin da jirgin Kano yake kokarin kiran fasinjojin shi. Haka muka tafi muna d'aga mishi hannun.


***
Bayan wata guda, yau aka mai dani d'akina, sakamakon laulayin da ma fara, jikin Mabrooka taji sauki sosai, har sun zo min kano. Sai da nayi wata biyu aka dawo dani bayan an yi bikin mai dani kamar me. Sannan na dawo na fara laulayi ni da Mabrooka, dama dama ita da sauki, Natashah ma tana nan amma bata da cikin


.... Yau ake bikin Mai Kano da Siyama bamu san lokacin da aka shirya ba sai dai ji muka yi kawai an saka rana, sai Nishat Badar Turaki, itama an hada da Moddibo, sai Mahirah da Kanin Bashir. Mai suna Miqdad, anyi bikin karshen jagorancin Mai Martaba Sarki Abbas, aka sha biki. Aunty Nafy sune akan gaba.


Sati daya a tsakanin muna tsaka da shirin dawowa Abuja ranar wata Jumma'a, bayan an gama Huduba, aka yi sallah. Aliyu yana sanye da farrar shadda, ya mike kawai fadawa suka zagaye shi. Ana fadin gyara kintsi. Kafin ya ankara an mishi duk wani abinda za ayi na nadin Sarautan, aka saka mishi alkyaba.
Aka shiga mishi kirari, kuka yake tare da tuno Bashir.
*Wallahi tunda suka baka Yarima suna nufin kai ne Next King of Monarchy don Allah karka d'aga hankalin ka akan shirmen da ake yin mulkin da kanshi zai nad'aka*
Idan ya tuna da wannan maganar kuka yake, haka aka fitar da sanarwar bikin nadin sarautan nan da kwana uku. Yayinda Gwamnati Tankara ta bada hutun kwana ukun nan, gidan mu babu masaka tsinke.


Ga Aljanun da suka tashi a kaina, lallai sai an nimo shi anyi sulhu. ai kuwa haka aka yi suka yi magana sosai sannan aka ajiye yarjejeniyar sulhu a tsakanin su, ba zasu kuma dawowa ba. Suka tafi abinsu.


Sai da nayi kwana biyu, ina jinya, kafin ma amshi mijina, na bashi kyautar sabuwar kaina a matsayin farin cikin samun damar zama sarki.


Ranar na uku akayi bikin bashi sarki wanda yayi daidai da haihuwar Mufeedah,an yi hidima sosai. Sati na zagayowa Sawwama ta haihu. Kamar zamu tashi sama, Mufeedah ta haifi mace aka sanya mata sunan Hajiya Balaraba, ita kuma Sawwama aka sanya mata sunan Hajiya Khubrah, mahaifiyar Halwani.


Aka bar mu da namu kananun cikin.


Bayan wata bakwai, Mabrooka ta haifi danta namiji, aikuwa aka saka mishi Muh'd Bashir, wata nan su uku na haihu inda na kuma samun yara maza biyu aka saka Abbas da Abubakar.


Haka Allah ya saka Albarka a cikin rayuwar mu, ana cikin haka Siyama ta haihu aka saka sunan Yarinyar Umma, Firdausi, suna kiranta da Nana. Nishat ma ta haifi namiji Suka sa mishi Aliyu takwaran mai martaba.


Mahirah ma ta haihu itama sunan Baban ta aka saka mata....
Dan Rimi da Galadima, da Turaki da Wazir an wayi gari ne aka nime su aka rasa su.


Ana cikin haka naji barci ya kama ni, haka na kwanta.
A wani alkarya na bude idanuna, rike hannun wasu mata suka yi aka kai ni wani daki na alfarma, na zauna kafin wata kyakyawan mata tazo, kallona tayi sannan tace min.
"Matar Sarki ce a gaba?"
Murmushi nayi domin bani da bakin magana.
"Toh duk da ina son na sanar miki ne, ba wani abu bane.
Jan hannuna tayi muka fita hankali. Ta kai Ni can wani gidan Yari a karkashin kasa, anan na hango Uncle Danrimi ana basu azaba.
"Anan zasu dawwama harsu mutu, sun cutar damu."
"Allah ya huci zuciyarki, idan da hali abarsu da tabon da zasu rayu dashi, yafi a Barsu anan iyalan su, suna can cikin damuwa. Ki duba magana ta"
" Shi kenan Aeeshatu Buhayyah, me kike bukata a cikin kasar mu?"
"Nagode Umma na, duk abinda aka bani zan karba da sama yadda ake zata"
"Allah ya miki jagora a rayuwar ki."
"Amin Ya Allah"
Babu abinda ya burge ta kamar yadda na bata matsayin uwa, haka ta kai ni dakin gwala-gwalai, ta zuba min sannan ta haɗa min shatara na arziki, tace min.
"Idan kika farka zaki gansu a gaban ki, idan kina son gani na, ki kwanta kawai Zamu zo gare ku Insha Allah. Ina sonki sosai Buhayyah."


"Nagode sosai Ummana"
Haka ya rungume ni, sannan muka yi bankwana, lokacin da na farka da sauri na ware idanuna sabida kayan da na gani a gabana, sai kamshin turaren ta da yake rab'e a jikina, murmushi nayi sannan nace.
"Ina sonki sosai Umma" daga baya naji sautin murmushin ta, juyawa nayi naga bata nan.


Kayan na kai d'akina, na adana su.
Da dare nice. Dakin mai martaba, yana kishingide kaina a saman jikin shi.
"Yallabai! Insha Allah za a ga su Waziri very Soon"


Shiru yayi sannan yace min.
"Wallahi abin ya dame ni, domin ina zargin aljanun nan ne suka dauke su "
"Babu batun zargi laifi suka yi aka biya abiya bashin sai ta zama laifi? Sun tab'a."
Matsa nono na yayi yana faɗin.
"Ban ga laifinsu ba"


Ya fada tare da ciro kayan lambun shi ya shiga matsawa, "Yau a falo nake son ganin mun yi zancen mu"
Dariya nayi domin ya bani dariyar.
"Toh gani nan sai ka cinye ki ai"


Haka muka cinye juna kamar babu gobe. Ina son mijina domin shi daya yasan darajata, kishiyoyina bani da matsala dasu, sai Natashah ne da muke yawan samun sab'ani da ita, shima sai da aka mata warning ta fita hanyata.


Ina yawan zuwa Kano gurin iyayena, kuma ina jin dadin rayuwa dasu, anan tankara Aliyu ya nima min jami'a, na fara karatun degree dina.


Kamar da wasa na fara, sosai na maida hankali.
Bayan wasu abubuwan da na farin ciki da na bakin ciki sun faru. Na kara fahimtar zaman auren mu da sauran kishiyoyina.


Mabrooka yar ko oho ce, duk yadda aka yi abu matukar bani ce zan nuna mata amfanin shi a gurin mijinta ba, ba zata yi ba haka Allah yayi ta kuma tana mugun son mijinta, gashi babu laifi tana mishi biyayya, kawai haka take da kayan ban haushi. Natashah, bata da aiki sai na kayan mata, amma kuma tana da wata dabi'a, idan na cire kishin mijinta, Natashah babu ruwanta da ita ta haifi Yaro ko d'anka ne, dukkan su Abu daya ne a gurinta.


Amma mayyar kayan mata ce, ita daya ke sha, karshe idan tayi karo dashi, Ya kure mata lafiyarta karshe gudu take..dan ya lura ita kayan matan shine rayuwarta.


Ni kuwa babu abinda ya dame ni,mijina yafi min kome, kuma idan ma samu zandariyar shi ta zungure ni zan kwana na wuni ban ji kome ba, a duk lokacin da na tuna da zandariyar wallahi sai naji har tsigar jikina mik'ewa yaƙe, ina son mijina da kayan dadin shi, sharbebiya da ita gwanin ban sha'awa, yana cika yana matsa maka nono, I love my Sweet Aliy, haka nake jin babu wanda ya kai ni sa'a.


***
Bayan wasu yan shekaru, soyayya da mutumtaka ce ta karu a cikin gidan Aliyu ga Zuri'ar shi da ta yadu, ina rike da Mimi yar karamar yarinya ta da na haifa, aka sa mata sunan Ummana Yahanasu, muna kiranta da Yohais, wani irin dad'i kake ji idan naga yarinya nan, kwanan mu talatin da biyu. Mama Uwani ce a gurin mu, dan haka ina farkawa na samu ta yiwa yarinyar wanka ta shirya ta cikin kaya pink color.


"Sannun Maman Uwani, Sannun kin yiwa Princess wanka."
"Allah Sarki, karki damu Allah ya baku lafiya dai."
"Amin Nagode"
Kallon ta nayi sannan nace Mata.
"Maman Uwani, ga wancan jakar naki ne daga Kano Ummina ta aiko miki dashi, wannan kuma nawa ne ki dauka, inji Mai martaba Sarkin Tankara yace a baki wancan kyautar."


Zuba gwiwar ta tayi zata min godiya na bata rai.
"Ni abinda kika min ba zan tab'a Mantawa dake ba, dan haka dauki kome nima Yarki ce, don Allah ban da yawan godiya " ya faɗa kamar zanyi kuka.


Haka ta mike tana kara share kwalla, Alkhairi kenan kayi shi yau ka same shi gobe, waye yasan yarinyar da ta taimakawa ta bata abincin ta mata gata ta kawo ta gidan da ya zame mata madubin gobenta? Zata mata irin wannan Alkhairin? Waye yasan cewa yar sarki ne mai karfin mulki? Allah kadiran Allah manyasha'u, Allah Kenan..


Bayan tafiyarta, na tashi nayi wanka tare da gyara dakin fess, har yau nice nake kome nawa na kaina, bana yarda a yi min ban ga amfanin hutun ba, tunda dai nayiwa wasu babu amfanin na mike kafa ban sami ladan kai na ba. Aure nake ba zaman hutu ba.


Rayuwar aure ba nake da ibada ban zo rayuwar jin dadi ba, akan me zan mike kafana? Bayan na san cewa ibada nake. Mijina bai fi kowa ba, amma kuma bana fatan ya zarce yadda zai fi wasu.


---
Haka rayuwar mu ta mike, yana adalci a tsakanin mu, kuma yana kokarin kamanta kome a tsakanin mu, dole yasa muka hade kan mu.


Yarana biyar maza biyu, mace daya itama sai da na jima kafin na sami cikinta, Natashah yaran ta biyu ta haifi namiji, Mabrooka yaranta Hudu biyu mata biyu maza.
Yara goma sha daya, ba karamin kulawa muke samu ba, da kanshi ya bamu shawara amma ya tuntube mu yace ko zamu fara sana'a?


Toh ni dai na ce ina son na fara kiwon dabbobi ne dan haka yasa aka ware min wani katon fili aka gina min gidan kiwon kaji da kifi.


Mabrooka kuwa ta ce ita a bude mata gurin Saloon da gyaran jiki, sabida tana masifar kaunar gyaran jiki, manyan mata Natashah kuwa cewa tayi a bude mata boutique, inda aka zuba kayan kece reni.


Haka ya zuba mana da manyan manyan kudi bayan an watsa mana ma'aikata. Haka muka cigaba da farin ciki a rayuwar mu, mijin mu ya dauke mana kome, kuma Alhamdulillahi bamu da wata damuwa. Yaran mu sun girma kome nasu iri daya idan ba ka bincika ba, ba zaka tab'a gane dan waye wannan, mu uku muka tallafi al'amuran mijin mu.....


Alhamdulillahi anan na kawo karshen ALIYU ASADULLAH abun nayi daidai Allah ya bamu ladan wanda nayi kuskure Allah ya yafe min masu kananun magana tun labarin bai fita ba Thank You Nagode idan babu ku ba zan rayu ba..... Ubangiji ya Hada mu a free book Tambarin Shaharah...... Insha Allah ayi hakuri da yadda labarin yazo very short Story, darasin rayuwa na labarin ya dace a duba 👏

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login