Showing 3001 words to 6000 words out of 98705 words
tausayin na kasa dasu, gani suke kamar Allah yafi kaunar su ne yasa ya basu arziki mu kuma talakawa baya kaunar mu ya haɗa mu da talauci. Dan haka na cigaba da tsayuwa a gurin, sai ji nayi an daki duwawu na.
A zabure na juya idanuna na cika da kwalla. Mijin Aunty widad. Kokarin rungumo ni yake, na kauce ya fadi. Ban san me yasa mutumin yake min haka ba.
"Buhayyah oya zo kusa dani."
Sake mikewa yayi tare da nuna alamar a buge yake, zai kuma rarumo ni na buga shi ya fadi sai anan idanun Aunty widad.
"Kan kutmar bala'i! Shegiya yar talakawa, karbi albashin ki Shegiya wacce bata san arziki ba. Kar na kuma ganin kafarki, matsiyaciya wacce bata san arziki ba, kin gama aikin gidan nan."
Dauka nayi jikina yana rawa, na fita da sauri dan na san babu abinda zai kuma, ajiyar zuciya na sauke. Sam garin Tankara babu mutane masu imani, shi yasa na tsani aikatau. Amma haka zan kuma niman wani, kafin Ramadan yayi na rasa abin yi. Matsalata halin da Innata take ciki shine damuwata. A hankali nake kallon yadda garin yake kara hada hadiri, tsare napep nayi tare da gaya mishi inda zai kai ni.
Cikin sauri na shiga da sallama na sami mata biyu, cikin sanyin murya nace musu.
"Barkanku!"
"Yauwa sannan yan mata"
Murmushi nayi musu, sannan na cigaba da kallon gefe, wata mota ce yazo da mugun gudu, dole muka bashi hanya napep din mu kamar zata fadi rami, tsoro ya kama mu.
"Tir da wannan wulakancin, Allah ya isa tsakanin mu da irin wannan Yaran!" Kallon shi nayi yana ta la'antar mutumin, matar da take gefe na tace mishi.
"Amma dai baka da Yara ne ko?"
"Toh baba idan ina dashi zan barshi ya lalace ne kamar Yarima Khamel? Gata da jin dadin rayuwa yasa basu san darajar mutane ba, taya zan bar d'ana yayi irin wannan rayuwar."
Ya faɗa a fadance, babu wanda ya kuma kula shi.
"Maman Balki don Allah ki taimaka mana gurin sami mana yan aikin, sabida Hajiya Maimuna suna gab da shigowa garin nan Azumi, dan haka don Allah a nima mana masu aiki. Masu tsafta da domin kin san rayuwar su baki daya a cikin turawa suka yi shi. Don Allah ban da marasa kunya."
"Insha Allah, Maman Uwani." Matar da take gefe na ta faɗa, sannan matar ta kuma cewa.
"Idan suka iya aikin da ya dace idan zasu koma Abuja ba mamaki su koma dasu. Kuma ga albashi me kyau basu da wulakanci, kinsan nice na zauna da matar Aliyu ta haihu Yar su Anoosh da kuma wannan da take goyo Anis, duk Ni nayi jegon su. Wallahi Karki ga yadda suka biya min kudin zuwa na London, daga can na wuce inda suke zama. Ina gama musu jegon Babbar Yar shi ya biya min aikin hajji, bayan na dawo ya saya min katon gida, ni kawai bana son a kai musu yaran da zasu bata min suna ne."
Haka kawai sai naji ina ma zan sami aikin, na rasa karatu. Domin Wallahi a matse nake na biya kudin wannan semetar din, amma gudun karsu zarge ni ya sani shiru har na tsaya a unguwar, na sauka sannan na biya kudin napep din har da nasu.
"Yarinya ayi haka ki biya mana kudin napep din."
Murmushi nayi sanan nace mata.
"Babu kome wallahi." Na juya tare da shiga cikin lungu uwar mu, ina me sauri sabida ruwan da aka fara, yar gida ce ma daidaiciya a tsakanin lungun, na tsaya tare da bugawa.
Budewa aka yi tare da jan tsaki, a hankali na shiga ina faɗin.
"Siyama ya aiki kwana biyu?"
Tsaki tayi tare da cewa.
"Yar mahaukaciya? Ashe ana nan ana bin maza kwararo kwararo. Kafin ayi abin kunya."
Ban iya fada ba, kuma bana son fada a rayuwata shi yasa na shige abuna, tare da cewa.
"Allah ya baki hakuri"
"Tsintacciyar mage har kin dawo ne? Yau naji uwar ki tana ta mata guggun ki leka dan babu wanda yayi shahaddar lekawa, sabida karta dake mu."
Gabana ne ya fad'i, na shiga dakin da sauri na duba tana kwance ta b'ata jikinta, da sauri na fito tare a daukar bokiti na fita dibo ruwa sabida ba zasu yarda na debi ruwan ba.
Sai da na fita wajen layin mu, sannan na dibo ruwa nan jikina yana rawa, nazo na d'agata da kyar, na kai ta ban daki. Inna Asabe ce ta fito.
"Karki sake ki b'ata mana ban daki da kamzanta domin wallahi ba zan yarda ba, maza kawo min kudin haya na"
Ajiye Inna nayi tare da komawa daki babu kudin babu dalilin shi, idanuna ne suka kayi jajjur.
"Inna Wallahi na zubda su"
"Kan kuturin bala'i. Toh ba a gidan nan ba, maza ki fita min da ita daga gidan."
Zuba gwiwa ta nayi tare da hade hannuna na fashe da kuka.
"Don Allah ki rufa min asiri kamar Yadda Allah ya rufa muku, Insha Allah zan nimo wani aikin domin an kore ni a gidan Aunty widad, kuyi min arziki" tsaki tai tare da cewa.
"Toh na kara miki nan da kwana ashirin." Ta shige abinta.
Ban dakin na shiga da innah nayi mata wanka, sannan na kwashe kayan na wanke tass, kafin na juya na kai ta dakin ta, na dawo na kuma ɗaukar bokitin na dibo ruwan na wanke ko ina, sannan na, zauna tare da bude laedar da na shigo da ita, na juyewa Inna abincin da nazo da ita.
"Innah sun kore ni a gidan" hawaye ne ya zubo mata, tare da dauke kanta, riko hannun ta tayi tare da kallon cikin idanunta. So take tayi magana amma ta ƙasa.
"Inna Kinga kudin da nazo dashi ya b'ata, naso kai ki asibiti."
Dakyar ta sarrafa bakinta tace.
" kin fito...., karki Kuskura ki bada kanki domin yawa Rayuwata, Allah yana kallon mu." Sake bude baki tayi harshenta yayi nauyi dan dole ta kuma yin shiru. Ban san me yasa baya son gaya min daga inda muka fito ba, kuma abin takaici daga sai taita zubda kwalla. Ban san ma'anar haka ba.
----
Washi gari da safe na wanke gidan sannan na dauki kayan Inna na wanke ina gamawa na shiga nayi wanka, sannan nace mata.
"Zan tafi niman aiki."kallona tayi kafin kwalla suka zubo mata, tabbas tasan darajar Buhayyah yafi karfin aikatau, amma taya zata iya gaya mata abinda ya faru na tsawon shekaru ashirin da uku, sam bata da halin girman kai ko wani abu.
Tana da sanyin halin da ko takata kayi zata baka hakuri, yarinyar tana tattare da boyayyen al'amari wanda daga ita sai Allah suka sani. Gyada min kai tayi na sake murmushi nace mata.
"Kiyi hakuri! Zan dawo idan na samu aikin na gaya miki." Na fada mata, sannan na juya na fita.
----
Bani da ko sisi haka na tafi gidan Baaba me riga, da ita muka fara shiga gidajen manyan masu kuɗi da yake G.R.A.
"Ke na gaji mu koma gida, gobe Insha Allah mu kuma fitowa." Ta faɗa min.
"Toh Baaba, amma zan tafi kasuwa koda gurin yan hotel din nan ne nayi aiki, idan yaso na samu abinda zamu ci."
Sake baki tayi tare da cewa.
"Baku da abinci ne?" Sosa kai nayi sannan nace mata.
"Toh ai nice nake kawo mana kuma kudin da na samu a gidan Aunty widad an sace." Na fada a hankali sannan na cigaba da cewa.
"Damuwata wannan zangon shine zan gama N.C.E, toh bani da kudin da zan biya, ga tsohon bashin da suke bina." Na fada a sanyayye kamar zanyi kuka.
"Insha Allah zan nima miki aiki yanzun ki zo muje gida kici abinci kuma ki rike muku, kuje ku ci da dare" kwallar da nake dannewa ne ya zubo min, nace Mata..
"Nagode sosai." Daga nan muka nufi gidan ta, anan muka ci abinci tare da zuba min na kai gida, na bawa Inna taci sauran kuma na rufe zuwa dare...
Ni baka ce, amma irin me hasken ba cam, sannan ina da tsayi babu laifi, hancina siriri ne amma Dan gajere ne, ina da cikar halittar jiki me kyau lokacin muna makaranta abokan karatuna cewa suke ina da karuwan jiki duk kayan da zan saka yana min kyau
Ga masu bukata su tuntubi wannan Number.+2347035133148
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Warning. This article contains pornography and sex warnings for girls and widows ...
7/9/21, 8:00 PM - Buhainat: *_ALIYU ASADULLAH♡_*
```The Lion of Monarchy```
MrsUsman400
Chapter0️⃣3️⃣
بسم الله الر حمن الرحيم...
Lokacin idan suka fadi haka dariya nake musu, shi yasa ban cika ado ba, na taso cikin kuncin rayuwa, Malam Umaru shine mutumin da ya taimaka mana har muka zauna a gidan shi. Malam Umaru yana da iyali wasu suna aure. Sai Ya Khamis yana aiki a Kaduna. Sai Yaya Haruna yana sabon unguwa da matar shi.
Sai kanwan su Siyama Sa'a tace, a hankali na kai hannu kofar gidan, Ni kaina ba zance ga inda muka fito ba, gashi ko kadan bana kama da Inna. Wallahi ko kadan bama kama. Haka yasa mutane kiran mu da sadaka yalla. Kasancewar nafi Inna kyau nesa ba kusa ba. Wani abinda yake faruwa shine mutane suna min wani irin kallo. A duk lokacin da saurayi yazo gurina yau gobe ba zai kuka zuwa ba, idan kuwa aka tambaye shi cewa yaƙe.
"Wallahi matar manyan mutane ce, ko sarakuna ba irin tamu bace."
Haka ya saka ko fita nayi bana samun wasu samari, kuma Alhamdulillahi Yaya Haruna yana ƙoƙarin dauke mana dawainiya musamman ni, daga baya innah larai, ta hana shi dake yana biya min aboye aka gaya mata shine ta mishi iyaka dani. Shekara daya kenan, shi yasa yanzun ya daina. Tun daga lokacin na fara aikatau, nayi aiki a gidaje dayawa, amma kusan matsalar da nake samu daya ce mazan yan iska ne shi yasa bana wuce wata uku zuwa huɗu na bar aikin sabida tsira da mutunci na. Dake malam Umaru ya rasu shekara biyu da suka wuce, amma ko ni kaina ba zan bada shedan yadda muka kasance a gidan shi ba, dan dai na taso na gansu ne ina da sanyin dayawa, shi yasa bani da abokin fada, gani da dan banza tsoro kamar farrar kura.
Hakurina yasa lokacin muna islamiyyan malamai sarkin hakuri, zan iya cewa sabida rashin son magana ta, zan iya wuni na kwana ban ce maka Sannun ba. Kawai abinda na sani daga abinda yake gana bana son hayaniya, koda zamu yi sauka. Bani da kudin biya, malaman mu suka hada min kudi suka biya min, har anko sabida nice na zo na daya maza da mata, shi yasa malaman suke masifar kyautatta min, Asabar da Lahadi ina shiga makarantar ina koyarwa a shashin yan yadda. Albashin dubu uku ne, shima kuma yana tafiya a sabulu da man shafawa.
Kaya kuma Allah yana taimakona idan na tafi gidan aikina ina samun kunce, shi yasa bana rasa sutura.
A hankali na shiga da sallama, tare da kallon su. Suna cin namar kaza, dauke kai nayi sannan nace musu.
"Barkan ku da gida"
"Barka dai gantalalliya" inji Siyama. Murmushi nayi sannan na wuce dakin na zauna tare da zuba ma Inna abinci tana gama ci na wanke mata jikinta sabida fitsarin da tayi na kaita ban daki nayi mata wanka. Sannan na kuma dawo da ita na gyara dakin. Yau muna zaune a gidan ne sabida malam yayi babban furuci akan matukar ba dangin mu, suka bayyana ba ko nayi aure ba, ko mutuwa ba bai yafe ba idan muka bar gidan ko yaran shi suka d'aga mu.
Gyara zama nayi bayan nayi sallah na gayawa Inna yadda muka yi sannan na dauki Alqur'ani ina karatu,.har aka kira magarib. Ina idarwa na zauna nayiwa innah alola itama tayin sallah.
👑👑👑
Seoul
Na kasar Korea ta kudu, a tsaye yake sanye yake da wani English sweate sai jeans me shegen kama jiki, yayi kyau ta baya, yalwataccen gashin kan shi ya sauka a bayan shi.
"Asad! Amma maganar gaskiya dole ka koma Abuja ni ban ji dadi da Daddy yace wai ba ku koma Tankara ba, dan iska idan ma wani abu ka binne a can zaka sani dan banza mara mutunci."
Banza yayi dashi yana kallon cikin garin, bai san ƙaddarar da ta kawo shi gurin Bashir Ibrahim Amin danrimi ba.
"Ali Ghaji!"
A zafaffe ya juya tare da kafe shi da manyan idanun shi masu matukar kyau da kwarjinin, zama yayi cikin fushi kamar wanda aka mintsine shi ya mike zai fita.
"Look dude by now ya dace ace kasan abinda kake bai dace ba, idan ba, Tsakanin ka da Allah meye yasa baka son zama da Mabrooka? Sannan kai kana kudu ita tana arewa wannan ba adalci bane Wallahi, a yanzun yaran ku biyu, Anis da Aroosh,kaga suma yaran suna son ka basu lokacin ka, amma idan zaka ci Yar mutane ka mata ciki baka tuna cewa kana gudunta shege mayen mata."
A hankali yake jin duk abinda yake fada mishi amma zunzurutun mugun hali irin nashi na rashin son magana ya sa shi yin shirun dole.
"Lion King!"
D'ago sexy eyes din shi yayi tare da watsawa Bashir banzan kallon"
"God forbids, na ga mace nace ina sonta. Su kuma Yan matan garin ku idan suka ga namiji binshi suke, so ina da type na mace da nake so. Bana son macen da zata ganni tace tana sona, sannan ita Mabrooka ita ta fara shiga rayuwata, kuma da rabon yaran nan so zan zauna zauna da ita ne sabida Amnah da yarana so bayan iya bana jin zan kuma kara wani auren dan na tsani hayaniya a gidana, i hater haukar da mata suke da sunan kishi."
Kallon shi Bashir yake domin ko babu kome yayi dogon magana, bai kai da gama nazarin ba kuwa yaga ya rike kanshi, alamar yayi magana da yawa, har kan shi ya fara ciwo.
"Ita mata ta biyu ba tsarinka bane tsarin Ubangiji ne, idan ya so sai kaga an baka wata daga cikin Family."
Mik'ewa yayi tare da ɗaukar wayar shi da kome nashi, sannan ya kalli Bashir da yake dariya, yace mishi.
"Ba zan tab'a auren macen da bata waye ba, Na zauna da Mabrooka ne sabida tana da wayewa da ilimin me zurfi domin yanzun haka zata koma master din ta ne, kaga kenan."
"Ubangiji ya karya alkadarinka!" Banza yayi mishi. Wai dama shine har yayi dogon magana. Aliyu ASADULLAH ba za a kira shi da matashi ba muka ba za a kira shi da me shekaru dayawa ba, mutum ne da bai cika son tara hayaniya ko son shiga cikin hayaniya, Aliyu bai da wata burin a duniya sama da kasuwanci, sannan irin mutanen nan ne da basu damu da mace ba, kodan bai sami wacce take so bane.
A cikin matasan Afrika masu ji da arziki da dukiya, Aliyu yana cikin su. Idan aka lissafo Maleek na cikin Kome da lokacin sa, Mahir na Mah-Noor, sai Aalim na cikin Ruwa biyu, shine mutum ba uku da Allah yayi mishi baiwar sarrafa kowacce haja kuma a samu nasara. Mutum ne da yake da zurfin ilimin addini da na Boko, amma Bature ne ba bugawa a jarida.
Aliyu yana da ra'ayi, musamman akan rayuwar shi ta malam bahaushe, sam yaki jinin yaji maganar kara aure, kuma tun kafin yayi aure ake fama daga domin kin auren yayi, sai da Mabrooka ta gan shi kamar zata yi hauka, har da ciwo. Dan shi mutum ne da bai da lokacin kanshi balle na wani, shi yasa yake gudun aure tunda ba iya sauke hakkin iyalin zai yi ba.
Koda aka yi auren shi da Mabrooka, tasha wahala kafin ranar da ya b'are ta a leda, tun daga lokacin bai cika niman ta ba, sai ya shafe wata guda ko biyu.. amma duk ranar da ya kusance ta tana ji a jikinta namiji yayi tarayya da ita, har Allah yasa aka sami cikin.
Salimah wacce suke kira da Aroosh, bayan ta haife ta haka suka ci-gaba da rayuwar kurame, abinda ya fahimta. Yana son zama da mutane, amma bai san yadda zai mu'amalantar su ba, sannan ko yan uwan shi ba cika shiga hidimar su yake ba, duk lokacin da yazo sallah Tankara toh insha Allah. Sai anyi Mishi tallar yaran mata a cikin dangin su kai har da yaran sarakunan kasar Hausa. Amma haka yake dauke kanshi yace baya so.
Mutum daya ne yasan halin shi, Bashir shine kawai yake iya saka shi magana, bayan nan kuwa babu ruwan shi da kowa. Bai cika son yawan zuwa gidan su ba, dan yasan yana zuwa za a mishi maganar Tankara, ya tsani mutanen garin da kome nasu. Yana son rayuwar yanci da farin ciki.
Gashi nan karfi da yaji sun saka shi ya kuma buɗe wani karamin kamfanin a tankara, bayan sallah za a bude shi..
Sau dayawa yana kallon kanshi kamar bai da lafiya,