Showing 84001 words to 87000 words out of 98705 words
Chapter 29 - ALIYU ASADULLAH Complete Book By Mrs Usman .txt
kaɗan, yana cikin wanke hannun Natashah ta shigo kamar an wurgo ta, kallon su tayi kafin tace musu.
"Da fatan babu abinda ya faru da ku.."
"Assalamu alaikum, Alhamdulillahi babu abinda ya faru." Inji Mufeedah tana shigowa falon..
"Babu kome fa" bai gaya musu asalin abinda ya faru ba, domin yasan su da kidima yanzun su haukata mishi gida, kai mata dai sai a hankali kai abu kadan zaka musu suyi ya korototo sai kace an zuba mishi dalma, bai kai ga gama tunanin shi ba Mother ta kira shi, nan ma amsar daya ce babu kome. Haka suka saka shi a gaba akan lallai su bar tankara.
"Ba zan iya barin garin nan ba, Mata na tana cikin shi ina zan tafi na barta? Nasan halin da take ciki ne? Ban sani ba, kuyi hakuri amma ba. Zan tab'a barin garin da Buhayyah take ciki ba, idan nayi haka wani abu ya same ya fa.....
7/19/21, 11:34 AM - Buhainat: 3️⃣9️⃣
I love my wify so much ba zan iya daukar kasadar tafiya babu ita ba, ita din wata shashi ce ta rayuwa ta, ina son Buhayyah ina kaunar Buhayyah, kowani motsi nayi ina jinta a nan dina, please ku barni na nime mata na, i love my wife so much, ina son Buhayyah.
Ina kaunar Buhayyah, ina kaunarta sosai ban san yadda aka yi nake banzan tunani akan ta ba, amma ina son matata ainun, ina mata so na hakika ba zan iya nisantar garin nan ba matuƙar tana cikin shi, dan haka zaku iya tafiya ni ina da abin ya rage min a nan, idan ban ganta ba zan zauna har ranar da zata bayyana, amma babu ina da zani"
Shiru suka yi suna kallon shi, yadda yake maganar zaka tabbatar daga ranshi yake fitowa, ba iya baki bane, a ranar daga Natashah har Mabrooka sun fahimci karfin kaunar da Yakewa Buhayyah, domin dai da suka je kwanciyar aure, bakin shi Abu daya yake nanatawa, Buhayyah ita kanta Mabrooka sai ta tayi kuka yadda yake tare da ita amma zuciyarsa tana ga Buhayyah, shi yasa ta kuma rike shi tana faɗin.
"INSHA Allah zaka ganta INSHA Allah zata dawo gare ka, muna sonka" ta kara rungume mijinta, tana kuka.
Haka suka kasance a cikin wannan yanayin, har kusan asuba. Sannan ya janye daga jikin ta, ya nufi ban daki yayi wanka,sannan ya tafi masalaci. Itama haka ce ta faru da ita tana tashi tayi wanka. Da sallah.
***
Yau satina biyar da dawowa cikin Ahalina sai dai kewar mijina ya hanani sukuni, kallon umma nake da take ta yanka min kankana, ina sha a hannun. Hannuna yana kan cikina.
"Aeesh" d'ago kai nayi ina kallon ta.
"Kina kewar Mijinki ko?" Gyada mata kai nayi kwalla na cika min idanuna,
"Me yasa zaki yi kuka?" Kai na ne ya fara sarawa, a hankali na zube a jikin ta, na kai tsawon minti talatin kafin ta tashi da mugun gudu tafita, gashi daga cikin gidan zuwa fada tafiya ce me dan tazara, dan haka tana isa fada tayi wani burgi, tana shiga bata tsaya ba,ta shake wuyar Galadiman tankara.
"Gargadi kuke miashi? Wato kuna mishi barazana kar ya bada auren da yayi niyyaku a ga Aliyu Asadullah? Toh ba Jikar zai bada ba Yar shi zai ba da, idan muka kuma ganin kafaffunku sai kun koma babu su. Kuma yanzun muka fara da ku, sai kun ficce daga yau zamu fara."
Aljanun suka fada da mugun karfi yadda sai da fadar ta amsa da mugun amo da hauhawa, toshe kunnen su, suka yi tare da fita da gudu, cillar da Galadima tayi tare da faduwa kasa, a sume.
Aamil ne ya dauke ta, sabida jinin da ya ɓalle mata, aka nufi asibitin masarautan da ita, ana bata taimakon gaggawa, abun tausayi. Haka suka samu da kyar jinin ya tsaya, sannan aka duba lafiyar Babyn yana nan lafiya lau, kamar babu abinda ya faru dashi, jinin ne kawai ya zuba, tunda bakin mahaifar a rufe yake.
***
Shiru Mai Martaba yayi yana jin shawaran khalifa, babban dan shi dan dakin Fulani Aina'u wacce tayi sanadin b'atar Buhayyah. Gyara zama yayi sannan yace musu.
"Kuyi hakuri da abinda Umman mu ta aikata, amma ina rokon mai Martaba ya sanarwa mijin Aeesha tana nan, sabida yadda kome ke faruwa, sannan kuma sai a san yadda za a bullowa matsalar masarautan su.
Ita kuma Aeesha a maida ta d'akinta, wallahi tana kewar mijinta, na fahimci haka ne ta hanyar rubutun Status ɗinta.
*With You am somethings without You am not somethings*
Ya cigaba da cewa,.
"Tana fushi da shi, domin ko maganar shi ka dauko mata ba zata amsa maka ba, amma idan ta zauna ita daya zata yi ta tunanin shi. Don Allah ku duba al'amarin babu wasa a cikin shi."
Yadda yayi musu bayanin duk sun gamsu, dan haka Mai Martaba ta kira sarki Abbas ya gaya mishi abinda ya faru, sannan ya kuma tabbatar mishi ya bawa Aliyu Yar shi Aeesha da ta b'ata ta dawo, kuma ba zai yi danasanin bashi ita ba.
"Toh Yallabai yaron nan yana cikin damuwa, domin matar shi ta uku ta b'ace, wallahi duk ya birkice mana, mun yi iya yin mu amma baki daya."
"Toh kace mishi yazo Kano jibi ina son ganin shi.".inji Mai martaba Sarkin Kano.
"Toh Insha Allah zan mishi magana, Allah yasa ya amince dan wallahi baki daya ya fita hayacin shi, sai dai yawan tunanin matar shi."
" Karka damu kace yazo ni nace ina son ganin shi"
"Toh Allah yasa ya amince." Ya fada a sanyayye, haka suka yi sallama, ya kalli Yaran shi.
"Shima Aliyun yana can yana damuwa da halin da matar shi take ciki, yana nimanta.
Amma nace yazo, idan ma rigima suka yi, zasu daidaita kansu bana jin dadin ganinta cikin wannan yanayin." Ya fada tare da kallon dakin da aka kwantar da ita.
Bayan fitowar Dr Adeel da Dr Aamil, sai Dr Sadiya.
"Abba babu abinda ya samu cikin, jinin ya zuba ne kawai." Suna fada tare da nufar dakin canza kaya.
Haka suka zauna har Fulani Yahanasu tazo, ta shiga taga halin da take ciki.
"Muna zaune da ita fa? Kawai ta fita da mugun gudu, shi kenan sai gata kuma a kwance a gadon asibiti."
"Eh toh a tunani na, aljanun masarautan ke bibiyarta, kuma basu son abinda zai tab'a mijinta, shi yasa suke yawan tashi ai ko zuwan ta faɗa, sabida kawai sun ce na janye batun auren Ummu da Aliyu ne shi yasa suka zo, amma idan mijinta yazo aka yi wani abu a gaban shi tayu, idan aka yi a gaban shi haka zai zaka shi fahimtar inda matsalar yaƙe."
"Mijinta ka kira? Kace zai zo ta rabani da Ita bayan shekarun da tayi tana tare da su, don Allah Karku rabani da Yarinya ta," ta faɗa cikin tashin hankali da damuwa. Rike hannunta yayi yana faɗin.
"Ba zai yiwu bane, mijinta yana can ya damu da halin da matar shi take ciki na rashin ganinta kice wai kar mu gaya mishi wannan ba adalci bane, son kai ne murarran , sannan kin bincika halin da yarki take ciki? Mijinta yana can ya gigice b'atar matar shi, don Allah karki so kanki da yawa mana"
Tabbas ya gaya mata magana masu kama hankali, sai dai kewar Yarinyar da tayi na shekaru masu yawan gaske yasa ta gaza fahintar yarta, dan haka cikin sanyin hali irin nata tace mishi.
"Shi kenan, amma ba zai tafi da ita ba ko? Domin naga cikin jikinta bai yi kwari ba, don Allah yayi hakuri idan ya shiga wata shida sai ya tafi da ita, amma duk yadda kace haka zan yi."
Takowa yayi gabanta cikin nutsuwa, sannan ya rungume ta, tare da kifa kanta a kirjin shi. Yana shafa bayanta.
"Ina sonki tun ranar da na fara ganinki, ina sonki tun lokacin da aka bani ke, ina kaunarki tun ranar da kika haifa min Sagir. Ina jinki tun ranar da kika haifa min Aeesha, ina tausayinki tun ranar da aka sace ta, ba zan daina tsaya miki ba, a duk inda halin haka ya samu ina tare dake mata ta". Hannunta takai bayan shi tare da rungume shi tana kuka na wani irin farin ciki. Tana kara jin lallai Ubangiji ya sota da rahama ya bata miji irin sarki Lamido shi yasa yake tsaye a koda yaushe domin ita, yake jajjircewa domin ta.
Tabbas idan babu Lamido da ba zata kai labari ba, Lamido shine farin cikin ta, shine nutsuwarta shine kome na ta, kokarin janye jiki take ya kuma kara rungume ta.
"Ina zaki? Kin tuna lokacin da aka bani ke? Cewa kika yi baki son namiji me mata, gudun kar mata na tafi karfina ne"
"Amma ai dariya kayi ta min a ranar, har kana ce min kwaila" cizon kunnen ta yayi sannan yace mata.
"Amma ai ranar da bakinki kika ce min ke kinyi karama da auren gwandarerre irina, na cika girma kamar wani basamude"
Dariya yayi yana kallon yadda take dariya.
"Toh wallahi zan gyara wannan bakin da yake zaro magana kamar me"
"Na nawa kuma.ai gyara kayi shi daura na ganin d'an A'isha."
Haka suka yi ta hiran su har an kawo abinci, suna nan zaune a gurinta. Sai kusan isha ta farka tayi mika da Hamma.
"Umma ina jin yunwa?" Ta faɗa tana mik'ewa a hankali,
"Toh tashi kiyi wanka sai yi sallah ko"
Saukowa nayi ina kallon d'akin. Shafa cikina nayi ina dan danna marana, naji zafi. Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa.
"Cikin yana nan ashe"
"Dama an ce miki ya fita ne? Cikinki yana man sai dai.muyi fatan auta ta sauka lafiya."
Ban daki na shiga nayi wanka tare da tsarki domin jinin ya dauke kamar babu shi, nazo na sauke sallah kai na baki daya, kallon Umma nayi ta zuba min abinci ina ci muna hira.
"Mijinki zai zo!" A razane na kalle ta,
"Umma Abba ya gaya mishi ina nan ne?"
"A'a kawai an ce yazo ne, dan haka ban san wani irin miji gare ki ba, idan har yana cikin maza masu tsananin bukata dole zai yi hakuri ba zan bashi ke ba, kuje ku ture cikin jikinki ba."
Kunyar ta ya sani sunkuyar da kaina, nan tayi ta baro min zance da yadda xan kula dashi matuƙar haka ya faru, da yadda zai kiyayye cikin jikina, Wallahi Umma wayayyar mace ce. Once ta gaya min yadda zan magance matsalar mijina da na rayuwata, ba iya shi ba, da yadda zan tattala mijina, tace min.
"Buhayyah duk macen da tace miki mijinta yana wulakantatta ki bincika ita ta fara wulakanta kanta, duk namijin da ya dauko ki ya kawo ta gidan shi yayi haka ne dan yana kaunarki, amma sabida samun duniya zaki ga wasu matan sun wulakanta kansu. Sannan mazan su daura akan nasu.
Bari na gaya miki matan masu kuɗi kishin su ƙalilan ce, idan kina niman inda ake kishin hauka ki samu matar malam bahaushe da yake nima dakyar,. Sau dayawa matan da suka samu duniya suke hana shiga hakkin mazajen su. Sannan suma mazan marasa imani suna wannan abun. Dan haka ina baki shawara, karki zama mara adalci da rashin girmama kanki, an ce ku uku ne a gurin shi. Karki sake duniya ta gaya mishi baki da kirki, kiyi hakuri da shi da kuma abinda ya ajiye ku, ba zan baki maganin mata ko na baki rubutu ba, amma zan gaya miki karki manta da Allah, idan kika rike shi a sallah walaha zai rike ko har zuwa tashin alkiyama, idan kika rike shi a sallah kiyamul layli, zai rike ki har ranar tashin Alkiyama, Kinga aljanna kyauta ce free mode ce, amma wuta tsadar tsiya ce da ita.
Idan kika ce zaki rama abinda namiji yayi miki, toh zaki wulakanta, sannan society ba zasu duba laifin shi ba, laifinki za a gani, sabida shi namiji ne, idan kika sake ya kai ki ga sayan wuta toh babu shakka kin fada kuskure, duk Muminin kwarai an sanshi da hakuri, da sanin ya kamata dan haka karki sake ya kaiki ga aikata laifukan da ba zaki yafewa kanki ba, kiyi hakuri da zama da dangin shi. Domin kuwa suma wasu abubuwan ne dake karawa zaman aure lafiya da daidaito.
Idan kika sake kika b'ata alaƙar ku, shi kasansa bai da ikon sawa su soki, amma ke zaki iya sawa su soki, karki yarda abin hannunki ya rufe miki ido, karki bari su tambaye ki yadda zasu samu abu a gurin dan uwansu, ki tuna mishi yan uwan shi suka bukatar kyautattawa daga gare shi ba sai sun tambaya na, ki gaya mishi iyayen shi da makotakan shi suna bukatar kyautattawa daga gare shi, karki manta ki tuna mishi girman mutanen da suke kiran shi daga garin shi, kar duniya tasa ki samu abu ki manta da mahaifan shi da yan uwanshi. Iyayen rikon ki idan kin zamu ki kyautatta musu, Buhayyah duk wanda kika ji yace Ayya wancan tayi sa'ar miji.......
7/19/21, 11:34 AM - Buhainat: 4️⃣0️⃣
"Ba kome bane yasa ake ganin haka sai dan yadda ta zauna suka fahimci juna, karshe idan tafiya tayi nisa sai kiji ana cewa tayi mishi asiri ya zama mijin tace. Ba haka bane kyautattawa ce ta janyo haka. Duk namijin da ya kai matsayin samun mace wayayya zaki ji ana cewa malam wane ya more mata, ba dan kome na sai dan yadda ta fahimce shi ya fahimceta, zaki samu ko rigima suka yi yi basu jimawa sun shirya, ba kome ya kawo haka ba sai iya tafiyar da rayuwar aure tafarkin addinin Muslunci.
Kyautatta zato a tsakanin juna, kyakkyawar mu'amala da juna, girmama juna, tsare cikin shi da dukiyar shi, tsare amanar shi da hakuri dashi, gaskiyar mutum bai tab'a karewa ba, amma karya yana karewa, duk abinda kika ga hakuri bai baki ba rashin shi ba zai baki ba.
Duk gidan ma'auratan da zaki leka zaki samu ana ƙwarya ƙwaryar zaman lafiya, amma da zaki bincika yanayin zamantakewar zaki samu babu dad'i, saboda ana samun kananun magana a tsakanin juna, amma idan zama yayi zama namiji ya tsaya da kafarshi babu macen da ta isa kawo kananun magana a cikin gidan bai dakatar da ita ba. Ta wannan gurin nake jinjinawa Mijina, saboda bai tab'a bamu fuskar da zamu shigo mishi da kananun magana cikin gida ba,. A haka muna kishi. Amma mai ma'ana, sannan shima da ya gane haka bai tab'a kawowa mana abinda zamu b'atawa juna rai.
Mijin mu yayi adalci a tsakanin mu, kuma ya bamu yanci a zaman mu dashi, bai tab'a yanke wani hukunci ba dai da taimakon Yaran shi, Sabida lokacin da na aure shi babban danshi ya girme ni, amma a hankali na fahimci dan ya ajiye wannan yaron ba zai hana shi yayi yadda yake so ba, mutum ne adali mai adalci,.ya zauna damu kamar yadda ake zama da abokai. Bai dauke mu matan shi ba sai da ya maida mu kamar yan uwan shi da abokanshi, yayi hira damu a zauna mu ci abinci tare.
Mahaifin ku yadda ya mu'amalance mu, indai haka mijinki zai mu'amalance ki wallahi kin cab'a, karki yarda wani mugun nufi ya fito a ranki akan abokan zaman ki, domin sune shaidar ki na farko bayan kin mutu, karki yarda abokan zamanki suyi murnan mutuwar ki.
Buhayyah rayuwar duniya cike yake da ban mamaki da ban tsoro, duniyar bata da wani auki sai tarin damuwa da tashin hankali, Buhayyah Kinga namiji, idan baki samu mutumin kirki ba zai ja ki zuwa wutar jahannama, Buhayyah idan baki zama ta gari ba, dan cikinki zai ja ki zuwa jahannama. Buhayyah duniya babu kome a cikin shi sai tarin tashin hankali, idan kika dauke kanki daga tashin hankali sai ki zauna lafiya, Buhayyah namiji komi kankantar shi shi girma yake so da girmamawa, namiji nason kulawa sosai, a damu dashi, ko cikin abokai ne zaki Fahimci namijin da yake samun kulawar mace ne ta hanyar kalaman shi, duk abinda zai yi zai kira sunanta yafi sau dari.
Duk abinda fada sai ya kira sunanta yafi sau dubu, idan aka fadi abu zai ce da wancan ne abinda zata min sai yafi haka. Namijin da ya samu kulawar mace hatta nutsuwar shi daban take a cikin al'umma. Namijin da ya samu mace idan zai fita fuskar shi cikin farin ciki yake, kuma idan namiji ya sami mace kika kuskura kika ajiye maganar zaki hadu da shi, toh wallahi ki kama gabanki domin.kafin ya fito daga cikin gidan ma duniya ce. Balle kuma ya samu mace ta haɗa aji, iya kwalliya, girki, da tsafta uwa uba Ibada, idan tana karanta Alqur'ani kamar tana rera mishi algaita, kice ya rabu da ita? Ai babu boka babu malam, ba maganin mata ba kome ta kwace mijin kawai.
Sai dai kiji ana cewa. Ai matar wane uwar gidan ta zama Allah sarki, ko kuma kiji ana cewa matar wane ai Matar ta zama abin tausayi sai yadda Uwar gidan tayi da shi. Buhayyah idan maza suna da laifi a rayuwar mu, sai mu duba hanyar da zamu ganar dasu kuskuren su. Mafiya yawan lokuta muke jefa mazajen mu aikata laifukan marasa dad'i, wani namijin kuma rashin godiyar Ubangiji ce duk abinda mace tai mishi sai ya rena, duk kokarin ta burge shi sai ya gwatsele ta, wallahi akwai mata da yawa da gidajen auren su ya koma tamkar makabarta, suna rayuwa ne amma tamkar da matattu suke, sun zaune a guri guda tamkar marasa lafiya..suna son Farin ciki amma bakin ciki ya hana su motsawa, mazajen su na gasassu kamar masara.
Karki yarda ki