Showing 21001 words to 24000 words out of 95991 words

Chapter 8 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5407

ashe yayi barci, yagayamin yace wai ki zauna saiya neme ki, ki shirya yau ki shiga gidanki ki zauna shima yana ta shi zan tattara sa ya bar min gida kuje can kuyita zaman hakuri" Sumayya mirmushi kawai tayi batace komai ba duk da kuwa wani daWi daya ziyarci zuciyarta bata jima sosai ba ta koma sashin Amarya ta tattara nata ya nata ta koma gidanta.

Yau tun safe Abas ya kira Aimanah yana hanyar dawowa daga jigawa zai zo su gaisa a hanya yake zai koma Abuja, Cus cus ta dafa masa wanda yaji kayan lambu da zallar tsokar naman sa, sai jus na kwa kwa data haWa masa wanda yai sanyi sosai komai ta kai falon Daddy inda yake saukar bakinsa ta ajje sannan ta shiga wanka, sosai tayi kwalliya ta haWe cikin shuwariski lace Winkin street gwon wacce tabi jikinta kamar a jikinta telan ya haWa kayan babban mayafi tasa sanda ya kirata a waya ya ce gashi a waje
"To ka shigo" ta faWa a shagwaSe
"Uhmm uhmm kizo dai ki shigo dani" kashe wayan tayi ta gayawa Mah Abas yazo, tana fita compound yana shigowa gidan tsayawa tayi cak a inda take harya karaso wajan
"Barka da rana sarauniyata"
"Barka dai sarki mai mulkin zuciyar sarauniya" dariya sukayi alokaci daya suna kafe junansu da kallo, sun jima suna kallon juna irin kallon nan da bahaushe ke kira da kallon kuda, Aimanah ita tafara janye idanunta tayi gaba tana faWin
"Kashigo ku gaisa da Mahh" bayanta yabi suka gaisa da Mah sanan Aimanah ta masa jagora zuwa falon bakin Daddy, abincinta zuba masa kinci yayi dole saita basa da kanta
"Allah Kalbie bazan baka ba wancan karan ma saboda hannunka na baka yanzu kuwa alhamdulillah hannu ya warke, kariga da kasan haramcin hakan" hannu yasa yaWau cokalin yafara cin cuscus Win bayan yayi bisimillah sai santi yake mata tareda zuba mata surutu harya cinye bai sani ba=??saida yakai spoon bakinsa yaji ba komai ya kalli plate Win gabansa, atare suka kwashe da dariya, sun jima suna hira kafin ya mike zai tafi tayi masa rakiya har wajan gidansu inda yafaka motarsa, wata haWaWWiyar mota ce ta faka a kusa data Abas ma mallakin motar ya fito, gaban Aimanah ya faWi ta kafe wanda ya fito daga motar da kallo ganin yanda ya wani rame, Abas dake magana ya lura hankalin Aimanah baya garesa ya kalli inda take kallo da sauri yadawo da ganinsa ga Aimanah yaga dai har sannan gayan take kallon gyaran murya Abas yayi wanda yasa Aimanah saurin juyowa ta kalli Abas tana kokarin saita kanta ya watso mata tambayya
"Wane wannan Win" Aimanah tayi kasa da kanta jikinta na rawa ta kasa kallon Abas
"Kiyi magana mana kinmin shiru, ok na fahimta masoyinki ne Al'mustapha.....?

*Saura kiris adaina fitar da littafin Aimanah za'a daina posting Winsa a ko wanne group sai group na Aimanah real fans group 1 and 2 Idan har kinsan kina son cigaba da karanta Aimanah kuma kinsan zakiyi comment maza yi save Win wannan number 07039793439 da Mamin Humaidah kiyi mata magana ta whatssapp zatayi adding naki a group Win dazaki karanta hankalinki kwance batare da ko sisinki ba*
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha uku*

*Wannan page Win gaba Wayansa sadaukarwa ne ga masoya Book na Aimanah Musamman ?an Aimanah Real fans group two*

Aimanah takasa cewa komai haka ta kasa haWa idanu da Abas batayi aune ba taga harya shiga mota yana kokarin tada motansa, da sauri ta buWe front seat ta zauna batare data rufe murfin motar ba
"Fita fitarmin a mota Aimanah" Wagowa tayi tana kallon Abas dayake fitar da huci kamar wanda yayi dambe, tuni idanunta suka soma zubda hawaye
"Haba Kalbie shikenan daga na kalli wani waje sai kace wani nake kalla, abar shi ma wani nake kalla shine mai, nidai nasan kaine nake so ba wani ba, kada kallon wani ya Sata mana wannan lokacin, kai nakeso kaine a zuciyata, bazan taSa kallan wani kallo irin na soyayya bayan kai ba, Abas kanada matsayi mai girma a zuciyata taya zan iya kallon wani kallon soyayya bayan kana kusa dani?"
"Aimanah ki fitarmin a mota" yafaWa a zafafe, Aimanah rufo mirfin motar tayi ta gyara zamanta cikin motar tana kallon cikin idanunsa wanda bata hango komai ciki sai zallar rigima da Sacin rai
"Abas ni kake kora a motarka"
"Na korekin kije kici gaba da kallon masoyinki gashi can ya shiga gidanku"
"Shikenan" Aimanah tafaWa ranta Sace, kokarin buWe murfin motar tayi amma yaki buWuwa ta lura ansawa motar scurity,
"Ka buWe na fita" hannunsa yasa saman hannunta, lokacin da hannunsa ya haWu da nata taji wani ?ar a gaba Waya jikinta
"Aimanah yanzu saiki iya tafiya ki barni a wannan yanayin?"
"To yaya zanyi dakai Abas na gaya maka gaskiyya kaki fahimta, ka buWe min na fita"
"Hayatie zuciyata tana maki wani irin mahaukacin so wanda ni kaina bazan iya misalta maki kalar saba na riga na faWa irin sosai Win nan, zuciyata tayi wata irin bugawa a sanda naga kina kallon wani bayan gani a tsaye gabanki, shiyasa nan take zuciyar tawa ta bani Mustapha ne, ina da kishi sosai akan abinda nakeso ki kiyaye karki sake kallon wani namiji inhar muna tare"
"Bazan sake ba Hayatie kaine rayuwata gaba Waya, bazan sake Sata ran masoyi naba wanda ya wanke duk kan wata damuwa a zuciyata, Hayatie ina tsananin so da kaunarka kaunar danake maka takai matakin da bana iya kallon ko wanne Wa namiji, Kasani a raina kai nasa ba wanda nake gani, ko ruwa na Weba ciki zan sha kai nake ganowa, kaine mahaWin rayuwar da duk zanyi kasan sai da kai, hannunsa dake cikin nata ya damke sosai yana kallon idanunta
"Muyi alkawari Hayatie duk runtse duk wuya Wayanmu bazai rabu da Wayansa ba"
"I promise"
"Yes Hayatie I promise" hannu suka haWa tareda jinjinawa, ta zare hannunta a hankali daga nasa
"Idan katafi yau sai yaushe?"
"Sai ranar Waurin auranmu"
"Haba dai dafa saura dayawa"
"Sati uku yayi saura ai, bazan ma iya ba abaya ma bana sati banzo kano ba bare yanzu da naga ana neman yi min fin karfi"
"Ka kwantar da hankalinka ba wanda zai iya kwace maka ni"
"Na kwantar irin kamar kayi bako ya mutum Win nan" dariya suka yi sosai kafin Aimanah ta fito da wayarta taWan masa kusa da shi kaWan ta masu picture, guda Waya tayi masu ta sake saita wayan tana kallonsa
"Captein smile" murmu sawa yayi ta masu hoto ta maida wayanta kan cinyarta
"Amma zaka halarci dinner Win Uncle Yunus"
"Bazan zo ko wanne event ba amma zanzo wajan Waurin aure"
"Shikenan ka sauka lafiya" tafaWa bayan ta buWe door na motar ta fita tana Waga masa hannu harya yice daga layin.

Aimanah sanda ta shiga gida Al'Mustapha ta tarar tareda Mah tana duba lesika da alama shiya zo mata da su, Aimanah Mah kawai tayiwa sannu da gida ta wuce tana gafda shiga Wakinta Mah ta mata magana
"Zo nan Ummu Aimanah" dawowa Aimanan tayi ta zauna kasan carfet gaban kujerar da Mah ke zaune
"Mah gani" Mah bata kulata ba taci gaba da duba lesukan gabanta can tayi magana
"Sunyi kyau Al'Mustapha, tagaya maka kuWinsu" Al'Mustapha ya shafi kansa kana ya ce
"Mah na biya kuWin gaba Waya harna Anty Hasanah"
"Masha Allah Musty muna godiya Allah yakara arziki mai albarka ya cika buri"
"Ameen ameen" Mustapha yafaWa yana kallon Aimanah, Mah kallon Aimanah tayi kana ta maida ganinta ga Al'Mustapha
"Wai banga kun gaisa ba, ince dai ba gaba kuke ba" Aimanah Sata fuska tayi tareda kautar da kanta can gefe batace komai ba
"Mah Aimanah ta daina kulani rannan dana zo ma kofa ta rufe ta hanani shigowa"
"Aimanah mai kenan gaba kike da shi"
"Mom ni..." kuka ne kawai ya kwace mata ta mike da gudu ta shige Wakinta, shiru Mustapha yayi, har can cikin ransa yakejin kukan nan na Aimanah, Allah Allah yake Mah ta tashi a wajan ya shiga Wakin Aimanah kamar kuwa Mah tasani ta mike ta faWin
"Mustapha bari na adana kayan nan a Waki nasan Hasana tana gafda zuwa gidan nan tun safe ma nake saka ran zuwanta kilama gajiya ce ta hanata fitowa ta sha zaman jirgi" Mustapha baice komai ba yabi Mah da kallo harta shiga bedroom Winta, yana ganin shigarta kamar wani Sarawo ya yi wuf ya shige Wakin Aimanah, kwance ya sameta saman bed tana ta faman kuka kamar ranta zai fita, tsayawa yayi kofar Wakin yana kallonta har kasan ransa yake jin kukan nan nata, harya shigo Wakin ya zauna gefan gadon bata sani ba tana faman kuka kukan daya rasa na menene
"Aimaah daina kukan nan please na gaya maki bana son kukanki" da sauri ta Wago tana kallon sa batace masa komai ba ta maida kanta taci gaba da kukanta, saman gadon ya hau sosai ya zauna harya saka hannu zai taSata ya tina haramcin hakan da sauri ya mike ya sauka daga gadon, saboda wani abu daban da zuciyarsa ta Warsa masa
"A'uzubillah" yafaWa a hankali yana kokarin fita daga Wakin sai dai kuma yakasa fita Win saboda yanda yakejin zuciyarsa ya tsaya baki kofa
"Aimahh dan Allah ki daina kukan nan na roke ki, ki tsaya muyi magana naji ya yarda yanzu bakya sona ai ko ba soyayya daman can ni Wan uwanki ne"
"Ni kafita bana son ganinka" bai sake tsayawa yace komai ba yasa kai ya fita yayi sa'a Mah bata falon hakan ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yabasa damar fita daga gidan gaba Waya, tun daga wannan ranar Aimanah bata sake saka sa a idanunta ba har aka fara bikin Uncle Yunus, Uncle Yunus kanin su Mahh ne babansa wan babansu ma ne, a gidansu yata shi wajan Ana, ana ita ta rikesa bayan rayuwar iyayansa sanadin haWarin mota tun yana Wan shekara goma sha biyu.

Gobe ne yinin biki wanda Ana zata gudanar a wani babban wajan taron biki dake nan cikin garin kano, gaba Waya ?a?a da jikoki muna gidan Anah anata shan chatter mun cika falon Ana da surutu baka jiyo muryar kowa a wajan sai tawa data Rumaisa babbar Wiyar Anty HASANA da kaWan na girmi Rumaisa yan shekaru ne na bata, tamu tazo Waya sosai shiyasa duk sanda suka zo nageria muna jone, Ammi ta fito daga bedroom Win Ana tana mitar mun cika masu kunne
"Ai ga kaji can guda hamsin Alhaji muntari ya aiko dasu daga kasuwa suje su gyara" Anty Hasana ke faWar haka da itama ta fito daga Wakin Anan, da sauri Anty Ruma matar Yaya Muneer ta mike zata fita, Anty Ummi ta ruko hannunta tana dariya
"Wallahi bazaki fita ba dake za'ayi aikin nan, haka Wazu ma daga Mah tace mu Wora abincin rana kika gudu gidan, Zeenatu saida aka gama sannan kika dawo ci"
"Kai Anty Ummi harda sharri" Ruma tafaWa tana kallon Ammi data tsare su da idanu, gaba Waya su Aimanah suka fita wajan gidan inda Ana ke wanke wanke a hankali suke gyara kajin sunata hira ana tsokanar Aimanah itama yau bikinta saura sati biyu, Aimanah Wago kan dazatayi taga shigowar Al'Mustapha shida Yaya Mas'ud sai Surayya a bayansu tana rikeda manyan ledoji guda biyu, Mas'ud da Al'Mustapha sunyi kyau sun haWe cikin Blue Win shadda sai walkiyya take a kallo na farko inkayi masu zaka zata ?an biyu ne sai ka sake kallonsu sannan zaka banbance kamaninsu, kallo Waya nayi masu na kauda kai ina taSe baki, Rumaisa ta taSoni na Wago ina kallonta ta nuna min su Mas'ud
"Kalle su Yah Aimanah sun birgeni sunyi kyau sosai"
"Ke kikaga haka ni basu birgeni ba, ni rukemin nan" na mika mata naman dake hannuna muka cigaba da wanke su da lemon tsami, ina jiyo sun Mustapha da Anty Hasana sunata hira nayiyo an kama sunana yafi a kirga a maganar tasu har muka gama wanke kajin muka shiga dasu gidan Hajja Kande wacce ita aka bama aikin abincin bikin gaba Waya, washe gari aka Waura aure muka sha hotuna da ?an uwa da abokan arziki na kusa dana nesa, Abas bai sami halartar Waurin auran ba mundai yi waya da shi yana hanyar zuwa kano, wajan karfe biyu anata tafiya wajan yinin kusan kowa ya tafi gidan shiru Aimanah kaWai da Rumaisa suka rage a gidan suma jiran karasowar Abas suke, wayan Aimanah tayi kara harga Allah tayi zaton Abaa ne amma tana kallon screen na wayar taga Uncle Yunus ne tai picking call Win ranta Sace
"Yauwa Aimanah ga wata mota nan a waje nayi mantuwa a Wakina ki duba zaki ga babban leda fara da kaya a ciki ki Wakko ki kawo za'a taho min dasu, badan taso ba taje ta Wau ledan ta fita, mota Waya ta gani a layin hakan yasa ta nufi motan ta kwankwasa glass na motan aka buWe murfin motar ganin ba wanda ya fito a motar an barta tsaye da leda a hannu ranta ya kara Saci daman cike take fam da rashin shigowar Abas garin da wuri, juyowa tayi zata koma cikin gidan da sauri Mustapha ya fito daga motar yana jinjina taurin kan Aimanah so yayi ta shigo motar yatafi da ita,
"Aimah" cak ta tsaya jin ankira sunanta da Aimah tasan ba kowa bane sai Al'Mustapha, ledar hannunta ta dire a wajan ta shige cikin gidan da gudu, Musty dariya yayi tareda karasawa ya Wauki ledan ya koma mota yana dariya ganin shirin su baiyi ba, wajan uku na yamma Abas ya zo wayanta kawai ya kira Aimanah itada Rumaisa suka fito, motoci biyu suka gani a wajan da sauri wani soja ya fito daga motar dake gaba ya buWe masu murfin kofar motar suka shiga, Abas na hakimce a bayan babbar motar sai dariya yake ganin yanda Aimanah ta Sata ranta, ya kalli Rumaisa yana dariya
"Barka da shugowa naija mutanan Qatar"
"Yawwa barka Kalbie" Rumaisa ta faWa tana dariyar itama, Abas leka fuskar Aimanah yayi yaWan Sata rai kaWan
"Sorry Hubbie na Sata lokaci ko, jokob ne baya taka mota sosai har saida fa na karSi tukin na rinka gudu kamar zan kifa"
"Kai ko" Aimanah tafaWa tana kauda kanta gefe, sanda suka isa wajan atare Abas da Aimanah suka jera zuwa ciki, sojoji guda biyu na gefansu dama da hagu, gaba Waya hankalin kowa yayo kansu, Al'Mustapha ma akan idanunsa suka shigo har suka zauna yana kallonsu, a cikin idanun Abas yaga tsantsar so da kaunar Aimanah, yanda yake kulawa da motsinta kaWai abin burgewa ne, yana kallo ya buWe mata lemu ya mika mata kaWan tasha ta mika masa sauran ya shanye duka, kasa kasa suke magana suna dariya a kallo daya inkayi masu zaka gano su Win masoya ne na hakika take zazzaSi ya rufe Al'Mustapha harya soma ganin duhu duhu Shaheed ya kira ya basa car key Winsa yace ya kaisa gida, Shaheed ya maida sa gida ko zama baiyi ba ya koma wajan bikinsa, Mustapha na shiga gidansa Sumayya tayi sauri ta tashi zata tare sa hannu ya Waga mata ya wuce Wakinsa ya rufe da key ta ciki, wani iri yakejin kansa kamar zai raSe biyu saboda azabar ciwon dayake masa, magani yasha ya kwanta barci yayi gaba dashi bai farka ba sai ana kiran sallar mangariba shima bugun kofar da akeyi ne yatashe sa, kofar ya buWe Sumayya ya gani tsaye a bakin kofa tana sanye da hijab da alama sallah zata tada,
"Naji ana kiran sallah ne shiyasa na buga maka kofa" tsaki yaja ya koma ciki ya shige bathroom ya Wauro alwala ya fice masallaci, bai dawo daga masjid ba saida akayi sallar insha ya shiga gidansu, ya tarar tini Ammi ta dawo, gaidata yayi kana ya zauna kusa da ita yayi shiru
"Da aka tashi na neme ka ban ganka ba da wuri ka tawo kenan?"
"Kaina ke ciwo Ammi" Ammi kallon Wan nata tayi tausayinsa fal cikin ranta, akan idanunta taga tahowarsa wanda ta tabbata saboda ganin Aimanah da yayi da wani ya haddasa masa barin wajan harma da ciwon kan,
"Allah ya sauwake kasha magani?"
"Nasha" yabata amsa da kyar yana dafe kirjinsa da lokaci Waya yaji ya masa wani irin nauyi, gyaran murya yayi ya buWe baki zaiyi magana wani amai yatawo masa na zallar jini, gaba Waya Ammi ta ruWe hankali tashe tayi wajan Al'mustapha wanda jiri ya Webesa ya zube kasa.....
' [2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha huWu*


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shi Ammi keta ambata hankali tashe, Alhaji Kamal da shugowansa gidan kenan yaji salatin Ammi atare suka shigo Wakin shida Momy, cak Alhaji Kamal ya Wauki Mustapha hankali tashe yayi asibiti da shi, Ammi da Momy suka bi bayansa a motar momy dan Ammi batada nutsuwar dazata iya tuki duk hankalinta yatashi gani take ma kamar kafin suje asibitin za'ace ya mutu.

Murjana ta fito shirye tsab cikin shirinta na fita unguwa tana kallon Amarya batace mata komai ba har takai bakin kofa Amarya ta ce
"Murja ina zakje ne yauma jiya fa baki kwana a gida ba"
"Amarya ina ruwanki da inda zani gari zan shiga kuma jiya da ban kwana a gida ba naga ina gidan Kawarki maman Salim can na kwana tare da shi kinsan sun shigo kano" Amarya ta washe baki jin anyi maganar Salim
"Masha Allah ?ar albarka abinda nakeso ki gane kenan, yawwa kiWan masa wayo irin naku na yammatan zamani ki samo mana yan kuWin jiya nace wajan boka kiri kiri yakimin aiki wai saina basa dubu saba'in"
"Bakida damuwa Wari ma zan kawo maki gobe inna dawo"
"Yawwa ?ata shiyasa nake alfahari dake kin fuye min waccan Sumayyan data kasa taSukawa kanta komai" Murjana sa kai tayi ta fita wajan gidan inda wata haWaWWar mota ke fake, shiga tayi cikin motar, Salim yatashi motar yana aika mata da kallo
"Kinyi kyau kaunata, yau dai ina fatan za'a bani dama na shiga koramar nan da jiya aka hanani shiga aka barni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login