Showing 84001 words to 87000 words out of 95991 words

Chapter 29 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5405

laka tana katsina"
"Shikenan to Allah yabata lafiya, yanzu ki koma gidanku na nan baya ki share Wakin ki ki zauna"
"Ammi ya..." Ammi ta katse Mustapha da faWin
"Yimin shuru Mustapha, ka Wakko duk wani abu da kasan nakane kabar mata gidan ta zauna tana Wauke da cikinki har yanzu nauyinta na kanka har zuwa sanda zata haihu ta yaye Wan"
"Ammi bazan taSa barin jini na a wajan Wannan bakar kadarar ba, tana haihuwa zata bani Wana ko nononta bana bukatar ya sha bare ya gado wasu muna nan halinta" Sumayya dai mikewa tayi tana yiwa Ammi godiya tanan cikin gidan tabi kofar da zata sadata da gidan nasu, juyi tayi tai tsalle ta kwanta kan kujera ganin burinta nason komawa Mustapha yafara cika, lambar malam ta kira sai dai taki shiga jiki san yaye ta shiga Wakinta ta faWa gado tai kwanciyarta ba sallah bare salati daman tuni ta daWe da jingine sallah a babin rayuwarta, Ammi tasa Mustapha yaturawa Sumayya dubu Wari a account Winta danta rinka samun abu mai kyau tana ci,
Mustapha rai Sace ya dawo cikin gidan nasa yaWau duk wani abu daya san nasa ne ya maida sa Wakin Ahmad acan yagama week end Winsa safiyar Litinin yabi jirgin safe ya koma Abuja, sanda ya koma gida sai yaji gidan yai masa faWi shi kaWai ba motsin kowa, ko ina ya kalla sai moment Winsu da Aimanah ke faWo masa rayuwar da suke tare itada yara da yanda yake shiga cikinsu suyita tsalle tsalle wani bin harda tsairan gudu, hawayan fuskarsa ya share yana jin zuciyarsa ba daWi, ba shiri yabar gidan ya nufi wajan aikinsa, Sumayya tana ganin alart Win dubu Wari daga Mustapha har rawa ta taka tana cewa gobe sai enugu wajan malam, sai dai safiyar litinin Win Ammi tazo har gida tasata a gaba sukaje asibiti duk wasu abu daya dace ayiwa mai ciki shi aka mata sannan aka bata ranar dazata dawo awo, safiyar talata kuwa Sumayya sassafe tabi mota zuwa enugu, sai dai tayi rashin sa'a ta tarar bukkar Malam a kone kurmus a wajan wasu take jin labarin ai kawai gani akayi bukkar ta kama da wuta ta kone malam Winma a kone aka fito da shi wuta duk ta gama kone sa a haka aka bunnesa, ko kaWan bataji zuciyarta ta yi laushi ba saima cin alwashi datayi zata nemi wani malamin daga zarar ta koma kano.

Aimanah rayuwarta take ta jin daWi da walwala tuni ta koma B U K ta Wora da karatunta, ta koma gidan redion data ke aiki da taci gaba da aiki da su, yara na hannunta shi yasa hankali kwance take rayuwarta har kiba tayi ta kara haske, Yasar ya matsawa rayuwarta duk da ya koma Madina amma kullum yana nacin kira akan ta amince da soyayyarsa ta taimaki rayuwarsa a Waura masu aure ta biyosa madina su zauna, ita sam yanzu aure baya gabanta karatu da aikinta kawai tasa a gaba, koda zatayi aure ma batajin zata auri saurayi bare Yasar data ke ma kallon da kaWan ya girme ta a yanda take zato yasar bazai wuce sa'an Ma'aruf Win gidansu ba, har ?anbatta taje ta Wakko Gwaggo Fulani suka ci gaba da zama tare tana kula da yara, Mah na Saudiyya wajan mijinta Tuni suka koma har Ma'aruf da ya kamu da soyayyar Azinatu harma manya sun shiga an tsaida masu ranar biki, shiyasa Yasar yake ta mata nacin ta Amince sai ayi bikin tare danasu Yaya Ma'aruf Win, Mustapha tunda ya koma Abuja bai dawo kano ba sai da ya shafe watanni biyu sai dai suyi waya da Ammi yaransa ma yasa an kawo masu waya sabuwa dal a kwali Gwaggo Fulani ke haWasu da yaran su Sata lokaci suna hira, Aimanah na kallonsu wani lokacin har vidio call zata ga anayi, Musty yasha kiran wayar Aimanah bata Wagawa sai dai kullum kamar shan maganin bature sai ya mata tex messages sau uku a rana duk da bata taSa masa reply ba bai fasa ba, Maza da dama na zuwa wajan Aimanah masu santa da aure amma ko kaWan bata taSa bawa wani dama ba, wani Alhaji Sadam ne ma takan Wanyi waya da su kusan kullum shi tana ganin mutumchi da kimar sa yaransa biyu mata maman yaran ta rasu shekaru biyu kenan bai kara aure ba acewarsa yana neman wacce zata iya kula masa da yara bai samu ba sai da yaga Aimanah yaji a ransa itace wacce yake fata da burin ta zama matarsa yana ganin zata kula masa da yaran sa, ya mata alkawarin da zarar ya aure ta ta tawo da yaranta zai haWa duka ya rike su.....
'


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da Tara*

THE END

Al'Mustapha juyi yayi ya gyara kwanciyarsa, a hankali kuma ya buWe idanunsa bakinsa Wauke da addu'a, tashi yayi ya zauna tsakiyar makeken gadon nasa da yake ji ya masa faWi, a hankali ya sako kafafunsa ya sakko daga gadon ya shiga bathroom bakinsa Wauke da addu'ar shiga banWaki, kyakkyawar alwala yayi ya fito ya kabbara sallah, raka'o'i HuWu yayi a sujjadarsa ta karshe ya jima yana kuka yana rokon Allah kan ya masa zaSin Alkhairi
"Ya Allah na Ina rokonka idan Aimanah alkairi ce a gareni da rayuwata da addini, Ya Allah na roke ka da kawayan sunayanka Allah ka dawo da ita gareni" cikin kuka ya fara jero sunayan Allah sai da yakai karshe yana kuka sosai kana ya Wago daga sujjada, ya karanta tahiya da salatin annabi kana yayi sallama ya Wora da salatin annabinmu muhammad s a w, kur'ani ya fara karantawa har sanda ya jiyo an fara kiran sallah ya maida kur'anin ya ajje sa a ma'ajjinsa ya mike ya fita falo Sahur yayi kana ya wuce masallaci sanda yaji ana assalatu, daya dawo daga masallaci bayan sallar asuban kwanciya yayi barci yai kafin lokacin tafiyarsa office tayi, gaba Waya rayuwar Mustapha ta canza shi da kansa ya gano sakacin sa na rashin addu'a shiyasa abubuwa daban daban ke faruwa da shi, hakan yasa yamaida hankali wajan ibada sosai, azkhair na safiya da maraice baya wuce sa sai ya Wauki azumi yau in yayi gobe sai ya huta jibi yayi sallah bata wuce sa kullum akan lokaci yakanyi cikin jam'i baya tashi daga inda yayi sallah sai yayi addu'o'i sosai, ya dukufa akan Allah ya dawo da Aimanah garesa idan dawowar da alkhairi kullum addu'ar sa kenan hakan yasa a wannan karan bai zurfafa wa kansa ba baina baina yake komai shi yasa ya nisanci kano rabonsa da kano fin wata biyu kenan, yau kasantuwar juma'a ce kawai yatashi da kaunar zuwa kanon ganin yanda yaran suka matsa lalle yazo suna son ganin sa hakan yasa yau ya shiga garin da wuri wajan sha Waya na rana, ba kowa yasan da zuwan saba bai gayawa kowa ba daman Ahmad ne ke Wakkosa a airport shi kuma shida Alhaji Kamal suna cairo Alhaji yaje chaek up
Aimanah sauri sauri take ganin tabar stidio Win musamman ganin sha biyu saura minti goma, gashi Hadiza wacce zata karSe ta aiki bata karaso ba sha biyu dai dai ta mike tana kallon eng Sadik dake danna laptop ta Wan buga tebirin gabansa a hankali Wagowa yayi yana kallonta batare daya ce komai ba
"Eng dan Allah karasa rike min tashar nan zuwa Hadiza ta karaso munyi waya tana hanya yanzu zata iso, yara na makaranta suna jirana nasan yanzu sun ta shi"
"Amma journalist kina ganin kya tafi kuwa shekaran jiya da kika fita ma kafin lokacin ta shi da GM ya shigo bakiga masifar da ya rinka mana ba"
"Manta da GM masifar sa ta banza ce, nasan abinda yake wa, sabida wani uzurinsa bazan bar yarana a damuwa ba"
"To kunfi kusa asauka lafiya" Eng yafaWa yana dawowa kan kujerar data tashi, tafita tana murmushi motar ta ta shiga tafiyar mintina goma sha biyu yakaita makarantar faka motarta tayi inda ta saba tsayawa ta fito tana shirin shiga cikin makarantar ganin bata gansu ba a inda suka saSa tsayawa daga baya taji mai gadin makarantar yana mata magana
"Sannu da zuwa Hajiya, babu sauran yara a ciki kowa anzo an Wauke sa" gaban Aimanah ne yabada wani ras da sauri ta juyo jikinta har karkarwa yake
"An Wauke su kuma Baba, amma fa ni ke zuwa Waukar yaran nan kullum kun rigada kun sani inba ni nazo ba sai Ahmad ko Shaheed gaba Wayan su kuma basa nan"
"Inaga fa Ahmad Winne yazo" mai gadi yafaWa yana kallon Aimanan, juyawa tayi ta koma cikin motarta hannunta har karkarwa yake wajan danna lambar Yah Ahmad wacce kamfani suka shaida mata lambar na kashe, Gwaggo Fulani ta kira ko an maida yaran gida, Gwaggo ta shaida mata basu zo ba, hankali tashe ta kira lambar Ammi tayi sa'a bugun farko ta Waga kiran
"Ammi ko kinsa azo a Wauki su Aslam a school nazo ance Ahmad yazo ya Wauke su".
"Ahmad kuma" Ammi tafaWa hankali tashe
"Haka gate man yace kinga kuma ai Yaya Ahmad baya nan" Aimanah tafaWa cikin kuka,
"Yi shuru Aimanah Yara ai bazasu Sata ba, tunda kikaga sun bisa koma wane sun san sa kuma kinsan suma makaranta bazasu bawa wanda basu san shi ba, ki nutsu ki tawo gidana nima gani nan zan baro makaranta yanzu zan karaso," kai kurum Aimanah ta iya Wagawa kamar Ammin tana ganinta ta katse kiran ta kifa kanta saman sitiyarin motar tana kuka sosai,
"Ina kuke yarana waye wanda yazo ya Wauke ku Allah yasa kuna cikin aminci yarana" tafaWa cikin kuka, saurin lalubo lambar Mustapha tayi jikinta na mazari sosai ta danna masa kira, Al'Mistapha dariya yayi sanda yaga kiran ya shigo wayarsa zuciyarsa tai wani irin sanyi karo na farko bayan rabuwa Aimanah ta kirasa, picking call Win yayi tareda sauke wata ajjiyar zuciya a hankali yayi mata sallama
"Mustapha na shiga uku banga yaran nan ba, wai wani yazo school ya Wauke su"
"Ke wanne irin sakaki ne yasa kika kasa zuwa Waukar su da wuri har wani ya rigaki, duk abinda yasami yarana dake zanyi kuka," Musty yafaWa a zafafe
"Kullum fa akan lokaci nake zuwa yaune kawai aka sami akasi ban tashi a aiki da wuri ba"
"Aikin yafi yara ne, yanzu kina ina to"
"Ina bakin makarantar"
"Gasu nan suna waje na" katse kiran Aimanah tayi a zafafe take tuka motar harta karasa gidan Ammi zuciyarta na mata wani irin zafi, ita Mustapha zai rainawa hankali yazo ya Wauki yara bai sanar mata ba, tana shiga gidan taga Ammi da alama itama shigowarta kenan ko futowa daga mota batayi ba,
Aimanah ta wuce Ammi ta shige cikin gidan, yaran sun saka Mustapha a tsakiya suna shan RUFAIDA YOGHOURT Islam na saman cinyarsa harya canza masu kaya da alama ma wanka ya musu
"Bani yarana maiye tsakaninsu da kai da zaka Wakko min yara a makaranta ka Waga min hankali" Aimanah tafaWa tana jan hannun Islam data kankame babanta Aslam da Tasnim sun mike tsaye suna kusa da Aimana a tsaye,
Ammi tsaye tayi a bakin kofa tana kallon yanda Aimanah ke jan hannun Islam da Mustapha ya rike ta kam a jikinsa
"Ammi kice yabani yarana, yariga da ya barmin su tun tuni"
"Saki yarinyar nan Mai babban suna" Ammi tafaWa
"Amma fisabilillahi Ammi yaushe rabona da yaran nan, itafa tai wasarai rai da yaran badan naje na Wakko su ba haka zasuyi ta zama a bakin makaranta kowa na kallonsu"
"Amma to kizo mu koma gidanmu mana basai ku rinka ganinmu ba ko yaushe ke da Abie, Yusrah kawata fa kullum Daddy Winta ke zuwa yana Waukarta mu kuma sai dai ke kirinka zuwa kina Wakko mu kina kai mu mudai daga yau Abie kai zaka rinka kaimu ko Aslam" Islam tafaWi haka tana kallon Aslam, Mustapha Wagowa yayi yana kallon fuskar Aimanah yaga a wanne yanayi take, sakin hannun Islam Aimanah tayi ta juya zata fita,
"Amma zanbi ki" Tasnim yafaWa yana biyo bayanta hannunsa rike da Rufaida yana sha
"Aimanah koma ki zauna" Ammi tafaWa cikin bada umarni
"Muta ne na maza kuje wajan Mom ku gaidata" Ammi ta faWa tana kallon yaran, fucewa sukai daga Wakin cikeda nutsuwa suka nufi sashin Momy
"Abinda kukai gaban yara dai dai ne, maine haka kuke yi kamar wasu kananun yara"
"Ammi maine haWinsa da yarana yariga da yace yabar min su nasan yanda zanyi da su, Ammi korar mu fa yayi ya maida mu boys kwatas na gidansa yamaida mu da yara yace yabar min su nayi duk yanda zanyi da su" Aimanah ta faWa tana shashshekar kuka da alama tuna abin ya taSa mata zuciya
"Aimah kiyi hakuri da abinda yafaru a baya kin rigada kinsan komai basai na faWa maki ba, nai nadama Ammi dan Allah ki amince mana mu maida auranmu ko dan yaran nan, idan har Aimanah tai gangancin auran wani to tabbas tasa a ranta bazan taSa bada yara na ga kowa ba da gatan su baza suje suyi agolanci a gidan wani ba" Mustapha na gama faWar haka yasa kai yafita daga Wakin, yabar Aimanah tana kuka sosai
"Yi shuru Aimanah barsa kishi ke damunsa, ba wanda ya isa ya rabaki da yaran nan matukar ina raye, jeki Wauki yaranki ku koma gida, zan sama masu driver Win da zai rinka kaisu makaranta yana dawowa da su" Aimanah batace komai ba kuka take sosai ita kaWai tasan mai take ji a ranta, sai da tagama kukan ya isheta sannan ta mike tayiwa Ammi sallama koda ta shiga sashin Momy ta shaida mata yaran sun fita tareda babansu, Aimana jiki sanyaye ta koma gida, sallah tayi ta kwanta lamo kamar mara lafiya ta rasa inda Mustapha ya dosa ko ina yakai mata yara oho, barci ne yai gaba da ita, ba ita ta tashi ba sai da akayi la'asar sannan Gwaggo Fulani ta tasheta wanka tayi tai sallah ta fito babban falo inda Gwaggo ta ajje mata abinci, gaba Waya damuwa ta cunkushe mata ciki ta kasa cin abincin na kirki haka ta maida sa kicin ta ajje, wajan biyar na yamma tana saman kujera tana danna laptop taga sulaiman yaron gidan yana shigowa da manyan kwalaye da buhunan kayan abinci, ta kalli tarin kayan ta kauda kai taci gaba da abinda take a laptop Winta
"Sulaiman Munir daman yana gari ne"
"Ba daga shi bane, Alhaji Mustapha ne suka zo da yara" gaban Aimanah ya buga jin an ambaci Mustapha kafin Sulaiman yabar falon Mustapha da yaran suka shigo tare
"Sannu da zuwa, yau a gari" Gwaggo Fulani ta faWa tana murmushi
"Yau a gari inji maki bako ba, Mun same ku lafiya Gwaggo" Mustapha yafaWa yana zama kan kujerar da Aimanah ke zaune wacce bata ko Wago ta kalle su ba,
"Amma mun dawo" Aslam yafaWa sanda ya ke kokarin zama a kusa da ita
"Aslam mai yayi ruwana da dawowar taku da kun sani kuyita zama acan inda kuka ga yafi maku, banda damuwa" Aimanah ta faWa a kufule
"Kefa uwar Wakina kin fiye rigima maine lafin su dan sun zauna wajan Abbansu" Gwaggo Fulani ta faWa tana dariya Aimanah rufe laptop Winta tayi ta mike zata bar wajan sai da taje kofar shiga Wakinta kana ta Wago tana kallon Mustaph
"Ka Webe kayanka bama da bukatar komai naka, kafin kazo ai bamu mutu ba gashi kazo ka tarar da mu a raye, dan haka kasani ko babu abincinka zamu rayu" tana gama faWa ta shige Wakinta
"Kayi hakuri Mustapha bansan maiya shiga kan Aimanah ba kwana biyun nan masifa take ji da shi" Murmushi Mistapha yayi ya mike ya cire hularsa ya rike a hannu ya nufi Wakin da Aimanah ta shiga, lokacin daya shiga Aimanah tana kwance saman gado ta kifa kanta rabin jikinta na kan gadon rabi kuma na kasa da alama kuka take ma, karan kofa dataji baisa ta motsa daga yanda take ba saima magana da tayi a fusace
"Ku fitar min a Waki badai kun zaSi Abie Winku ba kun barni ku bisa kuje can ku rayu tare kuje ya kaiku wajan matarsa ta rike ku na bar masu ku nima Allah yabani wani" ta faWa cikin kuka, kamshin turaran dataji ya cika mata Waki yasa ta Wago da sauri, yana tsaye jikin kofa ya sarke hannuwansa a kirji yana kallonta haWe da wani zazzafan Murmushi dayake aika mata, ahankali yake takawa harya karasa kusada ita ya zauna gefan gado yasa hannu ya Wago ta ya haWata da jikinsa ya sumbaci leSSanta
"Aimah I love you so mach, kina tunani ko zaton zan nisance ki ko, ko kaWan zuciyata bazata iya nesa da ke ba Aimah, a lokacin da numfashi na suka haWu da naki lokacin ne ni nake iya numfashi dai dai Aimanah indai ina raye soyayyarki bazata taSa iya barin zuciya ba, tabbas zan iya komai akanki, idan nace komai ina nufin komai, soyayya bata taSa mutuwa haka soyayya bata tsoron mutuwa, soyayya bata tsufa, Aimanah karki mana ganganci da rayuwarki na riga da na sani kema kin sani jiya yau gobe da jibi zuciyoyinmu nasan juna bazasu taSa canzawa ba,"
"Bakada sauran wasu kalamai da sukai saura waWanda zaka iya rinjayata, a yanzu ba soyayya ce a gabana ba, koda ace auran soyayya zanyi kasani a yanzu bakai a zuciyata" Aimanah na faWar haka ta kwace daga jikinsa ta faWa bathroom, tsayawa tayi a cikin banWakin tana karewa kanta kallo ta cikin madubi dafe kirjinta tayi data ji zuciyarta ta buga da karfi
"Mustapha ko sonka zaiyi ajalina bazan komawa gidanka ba mai cike da kayoyi da bala'ai daban daban" kuka tasha sosai har sai da taji Gwaggo na kwaWa mata kira sannan ta fito, ranar dai haka ta karashe ta cikin damuwa da kunci, washe gari asabar batada aiki hakan yasa ta Webi yaran da Gwaggo suka tafi gidan Ana su mata yini, idar da sallarta kenan ta la'asar taji yara na tsalle suna ihun ga Abie ga Abie, muryarsa ta jiyo a falon Ana suna gaisawa, da gudu Tasnim yazo ya ce
"Amma Ana tana kiranki"
"Gani nan ta faWa tana mikewa ta linke daddumar ta maidata ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login