Showing 15001 words to 18000 words out of 95991 words

Chapter 6 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5395

bugu tana bugawa ne tareda kaunarka , Abas naroke ka karka yaudare kar..." Saurin katseta Abbas yayi tahanyar faWin "Aimanah ki manta da wata yaudara banzo nan danna yaudareki ba naroke ki kimanta da *Mustapha* da yaudarar dayai maki ki Wauki abin a matsayin kaddara da kuma dama can ba rabon aure a tsakaninku, bantaSa soyayya ba sai akanki kece first love Wina, uwar ya'yana insha Allah murmusa mana uhmm"

Dariya Aimanah tayi tareda saka hannu tarufe fuskarta tana dariya sosai, Abbas ya kalli agogon dake sanye a tsintsiyar hannunsa yaWago yana kallon Aimana wacce yanayin fuskarta ya canza, idanunwansa yabuWe sosai yana kallonta tareda Waga gira "Aimanah tafiya zanyi kinsan yau zan koma koma Abuja bana son tafiyar dare Hajiya faWa takeyi, kwara na tafi da wuri, nabaki amanar zuciyarki, ki kularmin da kanki please"

"Kema haka My Abas ka kularmin da kanka ka tsare idanunka, karka kalli ko wacce mace"

"Kallo?" kallofa love ai daga kanki nagama kallon wata Wiya mace kema kin sani nafaWa maki ba sau Waya ba biyu ba" sallama sukayi Aimanah ta wuce cikin gida shi kuma yahau motarsa yatafi, ahankali yake tuki cikin zallar nishaWi shi kansa yakasa gane shin wanne irin so yakewa Aimanah wani iri yakeji idan yana tareda ita jinsa yake kamar nan duniya babu kowa su kaWai suka rage lumshe idanu yayi yana murmushi tareda tuna ranar farko daya fara gani Aimanah, da wani yammaci da bazai taSa mantawa ba.


MUSTAPHA
Wata iriyar rayuwa yake shi Waya a india ko kaWan yaki sabawa da mutane ko yaushe yana gidansa idan ba makaranta ya shiga ba to zaka gansa manne da Sumayya wacce akoda yaushe sonta karuwa yake a zyciyarsa da wani irin matsanancin tsoronta dayake ji Yauma kamar kullum dawowarsa kenan daga makaranta yana shigowa gidan yaji kansa ya sara masa, saurin zama yayi a kasa yanajin Wakin na juya masa....
' [2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Tara*

*Assalamu alaikum masoya barkanmu da safiyar Juma'a, rana mai daraja idin musulmi, kar amanta dayiwa Annabimu salati a wannan rana haka ma kar a manta da karatun suratul khafi*


.......Abas agajiye ya sauka a gidansu can jigawa, bai sami Hajiya a gida ba bata nan taje wajan walimar bikin yar kawarta, bazai iya zuwa ya wuce batare daya ga Hajiyansa ba hakan yasa dole ya kwana a can ba damar komawa Abuja a ranar dole sai washe gari, baisami zama da Hajiya ba sai bayan sallar insha a gaba yasata da hirar Aimanah
"Abas ka zurfafa a soyayyar nan fa, ina jiye maka tsoron kazo baka aureta ba"
"Hajiya kima daina faWar haka dan Allah, daman Wazu wanta yake cemin yakamata na turo manya a tsaida ranar biki"
"Hmm jiya muka gama maganar nan da Alhaji, harma yabawa Alhaji Baita dama shida Alhaji Habu yaje suyi komai tunda baya nan"
"Masha Allah Hajiya naji daWi sai dai banso a saka lokaci mai yawa ni zanso ma asa wata guda, daman karatu ya hana komai kinga kuma yau kwana uku kenan da sukayi gradution"
"Duk bazai gagara ba daga garemu ba wata matsala sai daga su bansan ko sun shirya ba"
"Hajiya sun shirya nifa banason sumin komai zanyi komai da kaina ko Sangaran Amarya ma Aimanah kurum nakeso kuma ita kaWai nakeso su kawomin batare da komai ba, ni zan sai komai na gida"
"Hakan yayi Allah yasa yanda kake kaunar yarinyar nan kaima tana sonka haka" dariya kawai Abas yayi yana shafar sumar kansa,sallama yayiwa hajiyar ya wuce Wakinsa yai shirin kwanciya.

*Mas'ud*
.......Gaba Waya bayajin daWin komai wani iri yakeji idan yaga Abas yazo wajan Aimanah ji yake kamar ya kore sa, haka kurum baisan Aimanah ta auri wani ba Mustapha ba, gaba Waya ya hana kansa barcin dare raya darare yake yana addu'ar Allah ya dawo da Mustapha hayyacinsa, yau bayan an fito daga masallaci sallar asuba yabi bayan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin da Mustapha ke ciki, Liman yayi jim kana ya ce
"Masa'udu shi wani bin asiri idan anyi wasu binne binne baya sakin mutum har sai anje an tone abubuwan da aka binne, irinshi ne mai wuyar karyewa gashi kace Mustaphan baya kasar nan da sai a haWa masa ruwan addu'a yasha mugani"
"Limana bazaiyu a haWa ba saina kai masa can kasar dayake" Liman yadafa kafaWar Mas'ud ya ce
"Kayi hakuri kaji kaci gaba da addu'a muma zamu tayaka, idan yadawo kazo ka gayamin akwai abinda zanyi" Mas'ud yayiwa Liman godiya ya wuce gida yanajin zuciyarsa ba daWi, yinin ranar haka yayi sa gashi nan shiba mai lafiya ba shiba mara lafiya ba, har aka tashi daga wajan aikinsu sanyi kalau da shi, ahanyarsa ta komawa gida kawai yasami kansa da canza hanya zuwa gidansu Mustapha bai shiga gidan ba yafaka motarsa a kofar gidan ya kira wayar Surayya kanwar Mustapha karamar ?ar Momy, yarinyar slantyly yana hango tahowarta ta gilashin motar sa, yanayin yanda take tafiya a nutse yaji wani abu ya daki zuciyarsa murmushi yayi tareda dukan sitiyarin motar, hannu yasa ya buWe mata murfin motar, bata shiga ba ta Wan durkusa cikin sanyin murya ta ce
"Yayanmu ina yini" haka take gayawa Mustapha shima Mas'ud sau tari hakan take kiransa,
"Lafiya kalau Sury, shigo magana zamuyi"
"Yaya dadai ka fito Ammi ta hanani shiga mota fa"
"Motar samarinki ba, niba saurayinki bane dan Haka ba zance nazo ba" dariya tayi ta shiga motar ta rufe fuskar ta
"Yayanmu ka bani kunya ina naga saurayi ni"
"To bani kunyar tawa na tafi da ita"dariya ta kuma yi tana sake saka hannunta daya sha jan lalle ta rufe fuskarta
"Sury kinsan halin da Musty ke ciki inata ?o?arin ganin na fitar dashi amma nakasa yau wani malami yafaWamin abun da zuciyata takasa nutsuwa" nan yagaya mata yanda sukayi da liman, shiru Sury tayi tana goge hawayan dake zubowa daga idanta
"Nifa ba kuka na kiraki kimin ba" Mas'ud yafaWa da wata murya da ban wacce shi kansa baisan yanada ita ba=??
"Yayanmu dole nayi kuka, jiya nan fa na shige ta kofar Wakin Amarya naji tana wayada Murjana tana gaya mata ta binne layar nan a kasan murhun mai kosai, kawai jikina yabani kan Yaya ne zasu binne layar" Sury tasake fashewa da kuka
"Sury please stop craying, zakisa zuciyata ta buga fa" da sauri ta Wago ta kallesa, yai saurin basarwa ya ce
"Yanzu Amarya tana nan?"
"Bata nan ta fita tun safe sai Murjana"
"Yawwa kiramin Murjana nan amshi wannan ki goge face Winki, duk kin Sata kwalliyarki da hawaye sai saurayinki yazo yaga fuskarki a haka yamaki dariya"
"Yaya Nifa Allah vana da saurayi"
"Najib fa?" Saurin amsar hankacif Win tayi ta fita tana dariya, yaWan jima a motar kamar yatafi jin shiru Murjana vata zo ba, yana kokarin tada motarsa ya hangonta ta fito ko mayafi bata saka ba yana hannunta ta rikesa, kai tsaye ta buWe motar ta shigo bako gaisuwa ta ce
"Surayya tace kana kirana"
"E! dan Allah mai kike so namaki nima inada abinda nakeso kimin" shiru Murjana tayi alamar tana nunani can taWago ta kallesa
"Kafara faWar abinda kakeso na maka saina faWi nawa daga baya sabida nawa yanada girman daba lalle ka iyasa ba"
"Nima nawa babba ne"
"Zan maka komai kake so matukar zaka aure ni" dam gaban Mas'ud yafaWi yaWago ya kalleta ta kashe masa ido Waya
"Naji zan aure ki indai zaki min abinda nakeso"
"FaWi kawai ko menene zanyi"
"So nake ki rakani inda kuka binne asirin da kuka yiwa Mustapha"
"Waye yafaWa maka wannan maganar?"
"Narida nasan komai wallahi indai aka tone tona rantse maki zan aure ki" Shiru tayi na mintina can ta ce
"Zan tone komai yau da daddare kasani inka yaudare ni komai zai iya faruwa"
"Ba abinda zai faru sai alkhairin aure na dake" fita tayi a motar ta koma cikin gida yana kallo harta shiga gidan yatashi motarsa yanajin nutsuwa a zuciyarsa, Surayya tana gayawa Murjana Mas'ud na kuranta ta wuce Wakin Ammi, ?ar Wakin Ammi ce sosai kusan komai nata yana Wakin Ammi, zama tayi saman kujera rufe idonta ta Wora Hankacif Win da Mas'ud yabata a fuskarta tana shakar daddaWan kamshin turaran Mas'ud, wani bakon yanayi takeji a zuciyarta gameda Mas'ud
Mas'ud koda dare yayi kasa nutsuwa yayi har saida yakira lambar Surayya wacce har varci yafara Waukarta cikin mayan barcin tai picking call Win
"Hello" tafaWa da muryar barci
"HaWani da Murjana ko ki bani lambarta"
"Bani da lambarta, naga fitarta Wazu wajan tara na dare"
"Ok" kawai yace ya kashe wayar, Ammi dake zaune kusada Surayya ta kalli Surayya ta ce
"Dawa kike waya?"
"Yaya Mas'ud ne Murjana ya ke tambayya" Ammi dafe kirji rayi tareda zaro idanu
"Wayyo ni Saudatu shikenan shima ya shiga komar su wayyo Allah na"
"Ammi vana tunanin wani abu tsakanin Murjana da Mas'ud akwai dai abinda yakawo sa wajanta inaga akan Yayanmu ne" Ammi ta sauke numfashi ta maida kanta ta kwantar jikin filo,Murjana dare tabi ta tone komai batareda Amarya tasani ba saida ta haWa dukkan abubuwan da suka binne ta kira Mas'ud, yazo ya karSa cikin dare ya kone gaba Waya layun.

Alhaji Habu da abokinsa sukaje suka zo kano aka tsaida auran Abas da Aimanah nan da wata uku...
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Goma*

*Wannan page Win gaba Wayansa sadaukarwa ne ga Chamsiyya Louwali Rabo (Mrs Sadauki) Mafiya*


*Mustapha*

.....Idanunsa yabuWe waWanda yaji sunyi masa wani irin nauyi zabura yayi ya fisge kanula Win karin ruwan dake hannunsa yamike yana kiran "Aimanah! Aimah!!!" yafaWa da wani irin sauti da yai amsa kuwa a cikin asibitin, nan da nan likitoci sukayo kansa, wani jirin ne yasake Wibansa yai luu zai faWi kafin ya kai kasa Waya daga cikin Nurse Win dake Wakin yai saurin tare sa yafaWi a jikinsa
Sumayya gefe ta koma ta Wora hannu aka ta fashe da kuka ta fita waje ta kira Amarya a waya "Wayyo Amarya na shiga uku shi kenan na kaWai komai ya warware muna asibiti Mustapha ya birkice sai faman kiran sunan Aimanah yake, Mama dan Allah ki koma wajan boka tsito komai fa ya ruguje"
"Sumayya garin yaya kikayi wannan gangancin?"
"Mama banida masaniya akan komai kawaifa yadawo gida yafaWi na kira asibiti suka zo suka Waukemu yanzu kuma ya farka yana kiran sunanta"
"Bari na shirya naje wajan Tsito muji wannan masifa daga ina da rana tsakan nan"
Sumayya ta koma Wakin da Mustapha ke ciki ta tarar har anyi masa allurar barci cikin turancin daya daga cikin Likitocin yake gaya mata ta zauna nan kusa da shi ta kula da shi yana tashi ta kira su, Mustapha ya kwashe awanni yana barci kafin yabuWe idonsa karaf idanunsa kan fuskar Sumayya saurin mayar da idanunsa yayi ya rufe yai shiru kamar mai barci, komai yasoma dawo masa a kwanyarsa "Nooo!!!" yafaWa da i??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hu tareda mikewa duka a lokaci Waya, wuyan Sumayya ya shaka
"Ke kika ja komai ina Aimanah ina Ammi?" Sumayya idanu zare ta kasa magana saboda shakar dayayi mata wanda takeji kamar za'a zare mata rai magana takeso tayi ta roke sa yayi hakuri ya kyaleta amma ta kasa, dan kansa ya saki wuyan nata tareda haWata da bango, gefan gadon ya koma ya zauna tareda dafe kansa yana fitar da numfashi da sauri sauri
"Ina wayata?" yafaWa yana kallon Sumayya data koma can gefe ta tsugunna har sannan tana rike da wuyanta, mika masa wayan tayi ta koma nesa da shi ta tsaya tana kallon sa, lambar Ammi ya loda sannan ya danna call, bugun farko Ammi ta Waga wayan gabanta na faWuwa ganin kira da wata lamba ta wani kasa
"Ammi kiyafemin" abinda Mustapha yafara faWa kenan bayan Ammi tai picking call Win
"Mustapha kaine Alhamdulillah Allah na gode maka" Ammi tafaWa da muryar kuka
"Ammi ina Aimah"
"Tana nan kalau"
"Ammi gida zan tawo"
"Mustapha ka zauna ka karasa abinda yakaika India kwanki fa suka rage maka"
"Ammi Aimah fa bazan iya zama anan ba Aimah ba" hmmm Ammi taja numfashi tana goge hawayan tausayin Wanta dasuka zubo mata
"Karka dawo Mai babban suna ka zauna kamar yanda nace maka Aimanah tana nan har kadawo"
"Shikenan Ammi zan zauna ki turomin lambar Aimah na kira naji muryarta" Ammi ta katse kiran ta Wora kanta saman kujera ta fashe da kukan tausayin Mustapha, "Mustapha kadawo hayyacinka a kurarran lokaci yamzu Aimanah tazama ta wani" kuka tayi sosai sannan ta mike ta fita daga Wakinta zuwa na Momy, Mustapha yamaida kansa ya kwanta saman bed na asibitin yanajin zuciyarsa kamar zata fasa kirjinsa ta fito, wata iriyar soyayyar AIMANA ce ketasowa tun daga kasan zuciyarsa
"Ammi bazan iya ba, bazan iya jure zama anan ba Aimah ba, mikewa yayi yana kallon Sumayya data haWa kai da gwiwa ta zafga tagumi
"Ke kisa a sallameni gida zan koma" asanyaye tamike ta fita shi kuma ya koma ya zauna yana tinanin irin hukuncin da zai yankewa Sumayya, saki shine babban abinda zuciyarsa ta amince dashi

A can gida kano kuwa gaba Waya hankalin Amarya yatashi da kyar ta lalubi hijab Winta ta saka tana kokarin fita daga Wakin Murjana ta shigo Wakin, kallo Waya Amarya tayiwa Murjana ta Wauke kai tana tsaki
"Mama ina zaki?"
"Wajan boka Tsito zani komai ya warware"
"Mama dama kin zauna basai kinje ko ina ba ni na tone komai"
"Na shiga uku" Amarya tafaWa tana Wora hannu aka "Murjani ke kika mana wannan Wanyan aikin, na shiga uku ni naja'atu Allah ya wadaranki Murja" Amarya ta fice fuu daga gidan gaba Waya.

Aimanah da Abas soyayya suke sosai da sosai ko yaushe suna manne a waya ayyuka sun masa yawa sosai sakamakon karin girma daya samu a wajan aiki hakan yasa bai zuwa kano sosai sai da waya, tuni Aimanah tafara aiki a Waya daga cikin gidan redion dake cikin garin kano, sosai tamaida hankali wajan aikinta, yau agajiye ta dawo daga wajan aiki gaba Waya bata jin daWin jikinta kamar mai zazzaSi haka takejin jikinta wanka kurum tayi ko abincin dare bata tsaya taci ba ta wuce Wakinta zata kwanta barci, harta gama addu'ar kwanciya barci ta lulluSa da blanket taji alamar shigowar sako wayarta, da sauri ta Wauki wayar tana murmushi "Abas farin Masoyi" tafaWa afili tana kokarin cire key na wayar
_"Fatan alkhairi tareda fatan kina cikin aminci ina mai neman afuwa bisa tarin Wimbin zunubin dana aikata a soyayyarki_ mamaki tayi ganin bakuwar lamba da bama ta wannan kasar ba goge massages Win tayi taja tsaki ta koma ta kwanta tana mai cewa kilama saSanin number aka samu, Abas ne ya kurata suka sha soyayyarsu har tayi barci sannan ya kashe wayarsa ya kwanta.

Mustapha gaba Waya baya cikin nutsuwarsa gaba Waya hankalinsa yayo gida kano nageria, sam yafita harkar Sumayya ayanda yaso tun acan zai yanke igiyar auransu gaba Waya amma yakasa saboda tausayinta da yaji ya jinkirta sai yadawo gida,yau cike yake da murna da Wokin gobe zai bar india zaiyi ido huWu da sarauniyarsa Aimanah murmushi yayi sanda ya tuna Aimah ya tina tilin tex masaages daya ke aika mata amma bata taSa dawo masa da reply ba, shi duk azatonsa fiahi tayi baisan cewa batama san shi bane, ita kuwa Aimanah ko sau Waya bata taSa kawowa wai Mustapha nw ke aiko mata da sakonni ba waWanda tana ganin shigowarsu wasu ta karanta wani ma ko buWewa batayi zatayi delate Winsa, dan yanzu ba kowa a gabanda da zuciyarta sama da Abas wanda takewa wani irin so, sosai take son Abas a yanzu a cewar Aimanah yanzune tai soyayya, soyayyar Mustapha datayi a baya ba soyayya bace idan ta haWata da ta Abas,
Abas Wan soyayya ne ya iya soyayya da tattalin mace kusan ko yaushe suna jone a waya motsi kaWan ya kirata ya ce yayi kewarta, yau Aimanah ba inda taje kasancewar lahadi ce tana gida bata fita, azaune suke a falo itada Mahh suna kallon Arewa 24 Aimanah na tsotsar alawa ahankali kamar wata karamar yarinya Mahh ta kalli Aimanah tai murmushi
"Hmm Abas zai sha yarinta dan Allah jibi yanda kike ta tsotsar alawa mai tsinke kamar wata yarinya" Aimanah ta Sata fuska kamar mai shirin kuka
"Mahh nifa yarinya dika shekaru na basufi goma sha bafa"
"Kice ma baki shekara ba" Mah tafaWa tana maida hankalinta kan shirin da ake haskawa a arewa, wayar Aimanah tayi kara alamar shugowar kira kallo Mah tay taga hankakinta ba akanta yake ba hakan yasa tai pickin call Win
"Hello Masoyi" Aimanah ta faWa a hankali tana satar kallon Mahh
"Masoyiya ya kike, kawau naji kewarki na kiraki"
"Kewa niko bana kewarka saboda ko yaushe kana ma?ale a zuciyata"
"Nima haka, gabana faWuwa yake Masoyiya yanzu Kanol ya kurani zamu shiga daji, tsoro nakeji gabana faWuwa yake Aimanah ji nake kamar wani abu zai sameni nifa gani ma nake kamar mutuwa zanyi....=?0?
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Goma Sha Waya*

"Mutuwa kuma? haba masoyi tabbas mutuwa wajibi ce akan dukkan mutum bawa mai numfashi amma bazaka mutu yanzu ba, masoyi bansan ka da sarewa ba kaida kake karfafawa wasu gwiwa kuma yau kazo da wannan maganar insha Allah nasara ke tare da kai, katashi kai shiri ka haWa rundunarka ku tafi Allah yana tare dakai Masoyi"
"Na gode masoyiya kin karfafa mun gwiwa, duk na sare inda zamuje ba sarvice kwana uku zamuyi ki kularmin da kanki, ki adanamin soyayyata can kasan zuciyarki, kiyi barci sosai banda tunani mai yawa, Ina fatan duk sanda kika tina ni kimin addu'ar samun nasara"
"Insha Allah nasara na tare damu" kashe wayar yayi naja ajjiyar zuciya ina Wago kaina muka haWa ido da Mah wacce bansan tsawon lokacin data shafe tana kallona ba
"Masoya, in anyi magana kice ke yarinya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login