Showing 6001 words to 9000 words out of 95991 words

Chapter 3 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5377

yamasa bayani Abas da abinda zai kawosa gidan, Mansur yayi farin ciki sosai duk da daman Ummi ta gaya masa haWuwar su da Abas Win a Shoprite harma da kiran dayakewa Aimanah bata Wagawa duk yasani zuba mata idanu kawai yayi yana jiran Abas yakawo kansa, Yaya Mansur ya kalli Anty Ummi yace
"Masoyiya inada bako fa mai zaki shirya masa?"
"Duk abinda kace Masoyi"
"Ok asamar masa abu mai sauki na snack yana hanya, yanzu Mus'af yafaWamin Abas zai zo" yafaWa ahankali yana kallon inda Aimanah take itada yara saboda karta ji abinda yafaWa,
"Wai da gaske kai nayi farin ciki muna da babban bako,


"Aimanah bar yaran nan da Abbansu mu shiga kicin, koma dai jeki kawai ki shirya, kiyi gayu sosai babban waje zamu"
"Allah Anty kice na kure wankana" Aimanah tafaWa cikeda Woki, Anty tawuce kicin tana dariya yayin da Aimanah ta shige Wakin su Zaheed nan komai nata yake anan ta sauka tunda tazo, gefan gado ta zauna tareda kira a wayarta
"Mah bakiyi kewa ta ba?"
"Kefa Aimanah kin fiya rigima kewa kuma kamar wata karamar yarinya nan da watani ma aure zan maki ki tafi gidan mijinki " Mah tafaWi haka tana dariya

"Shikenan Mah bazan dawo ba anan zanyita zama tunda bakwa nemana, kuma ni bazanyi aure ba"

"Muna nemanki mana amma yaya zamuyi tunda Yayanku ya rike ki, kilama kinzo Abuja kenan, jiyan nan Daddy ke cewa yakamata ki dawo Monday zaku koma school nan da kwana takwas"
"Mom nadawo Abuja fa da zama kika ce?"
"Au SuSul da baka ne, inake ina Abuja wannan garin sai su Zaheed"

"Mom gobe zan dawo, garin nan ya isheni ba inda nake fita fa daga gida sai gida inkinga mun fita to shoping mukaje"

"A'a karki tawo gobe, kijira sai friday muna Kaduna nida Daddynku gidan ba kowa sai Alhamis zamu koma gida"
"Mom mai ake a Kaduna?"
"Daddy yazo samina shine muka tawo tare"

"Wow Mom kuna lokaci fa keda Daddy yanzu nan da Kaduna saida kika biyosa?"
"Ki kiyaye ni Baby, kyalesa zanyi yatafi shi kaWai yammatan zamanin nan su kallemin shi, ina bazanyi wannan saken ba, abaya ba'amin kishiya ba yanzu ba zan bada wannan damar ba" dariya Aimanah tayi tareda kashe wayar tana dariya sosai, yanda Mahh da Daddy suke wani abin kamar sabbin aure=??da sauri tamike ta shige bathroom tana faWin "Ainamah yi wanka ki shirya kafin Anty Ummi tazo tasaki a gaba tana mita" ilai kuwa tana fitowa daga wanka saiga Anty Ummi ta shigo
"Nashiga aljannah ni Sa'adatu daman wai baki gama shiryawa ba to maza ana jiranmu" closet ta buWe tazarowa Aimanah wata doguwar riga ta atamfa data sha stonework sai walwali take
"Saka wannan inkin gama shiryawa ki sameni a falo ina jiraki"
Aimanah a nutse tagama shiryawa ta ta feshe jikinta da kalolin turare masu sanyin kamshi ta kafa Waurin Wan kwali kalar na yammatan wannan zamanin sosai tayi kyau, wayarta ta Wauke ta kashe solpie tana murmushi
"Mustapha" tafaWa a hankali tunawa da tayi ko wanne lokaci in tayi kwalliya irin haka takanyi hoto ta tura masa yayita yabawa.

Jiki a sanyaye ta fito falon, Anty Ummi ta tarar tsaye gaban danning tagama haWa abubuwa saman babban plate, "Kai tawan Masha Allah kyau iya kyau, karSi wannan kaiwa su Yayanki falon baki, yayi bako leena bata nan taje kasuwa" Aimanah bata kawo komai a ranta ba ta Wauki plate Win ta wuce, bakinta Wauke da sallama tashiga falon kanta a kasa ta ajje farantin hannunta kan babban teble Win dake tsakiyar Wakin ta juya zata fita ta jiyo muryar Yaya Mansur nacewa
"Ke baki iya gaisuwa ba" da sauri ta jiyo ta kalli yayan nata ta tsugunna har kasa tana gaida bakon wanda bata Wago taga ko waye ba, taji dai muryasa kamar tasan muryar amma bata wani damu dataga wane ba ta fita, taWan soma tafiya taji muryar Ya Mansur na kiranta ta tsaya cak batare data jiyo ba

"Malama koma ciki bakonki ne, ki tsaya ki saurare sa da kyau kiji da abinda yazo, duk da mun riga da mungama magana, shi zaki aura nagaji da wannan halin naki"
"Yaya kafa.." "Kimin shiru malama ba kanki fa aka fara soyayya ba'ayi aure ba ni tawa masoyiyar ma mutuwa tayi haka na hakura na auri wata wuce ki shuge ki bani guri kuma kika masa hauka na rugurguzaki wallahi"
"Yaya nifa bazan iya..."
"Zaki wuce ciki ko saina zaneki" Yaya Mansur yafaWi haka yana nannaWe hannun rigarsa, da sauri Aimanah ta shige falon ranta Sace, Yaya Mansur yayi murmushi yasa kai ya wuce

Abas yabi Aimanah da kallo wacce ta zauna saman kujera bata ko Wago ta kallesa ba
"Amincin Allah ya tabbata a gareki tauraruwa ta" kallo Waya Aimanah ta masa bata sake kallon saba tayi kasa da kanta tana goge hawaye, har Abas yagama maganganun dazaiyi bata kula saba tana kallo yafice bayan yayi mata sallama, Abas mutum mai naci da kafiya akan abinda yake sone hakan ne yasa bai gajiya ba wajan zuwa gidan yaya Mansur, haka kullum yakan turo mata messages na barka da safiya, haka da dare ma zai mata messages na zafafan kalaman soyayya, tun Aimanah na share sa bata Waka kiran wayarsa harta soma Waga kiran koda bazata ce masa komai ba, suna a wannan yanayin Aimanah ta koma kano haka yamaida kano wajan zuwansa duk da bashida kowa acan, daga karshe har mahaifiyarsa Hajiya Hafsat saida ya taso Hajiyarsa tazo har gida ranar Allah yasa mutanan gidan suna nan Aimanah bataje school ba haka Mah bata fita aiki ba ranar aikin dare ne da ita, Ainamah na zaune a falo tana kallo jefi jefi tana danna wayarta matar tayi sallama ta shigo, Ainamah ta amsa sallamar cikin girmamawa ta gaida matar kana ta mike ta kira Mah, Mah mace wayayya dason mutane ta gaida matar duk da kuwa bata santa ba, sai bayam sun gaisa ne hajiya Hafsatu ke cewa Mah
"Sunana Hafsatu mahaifiyar Abas dake son Aimanah"
"Kai madallah sannu da zuwa ya gida ina Abas Win ko ya koma Abuja?"
"Yan nan yanzuma tare muke dashi ya tisani a gaba da mitar nazo naga Aimanah nace taso shi" Aimanah tayi kasa da kanta tana murmushi jin abinda hajiyar ke cewa, mikewa tayi zata bar wajan Mah tace
"Ki shigo dashi" batace komai ba tayi hanyar fita daga falon, ta duba compound na gidan bata ga motarsa ba kamar yanda yasaba shigowa da ita ciki duk sanda yazo, wajan mai gadinsu ta karasa cikin girmamawa ta gaidasa kana tace
"Baba matar data shigo yanzu batare suke da wani ba?"
"E! tare suke da Abas yana waje can yafaka motarsa bai shigo ba yadai zo nan mun gaisa" buWe kofa tayi ta fita,

Yana tsaye jikin motarsa ya zubowa kofar gidan idanu, tunda ta fito yake kalonta ita ko idanunta a kasa harta karasa inda yake tsaye jikin motar sa nesa dashi kaWan ta tsaya ahankali kamar batason yin magana tace
"Ina yini ya hanya?" ta haWe kalaman wajan Waya batareda ta jira yabata amsa ba, wani daWi ne yakume zuciyar Abas yau Waya Aimanah ta kulasa harta gaida sa tana tambayar sa hanya
"Lafiya kalau Hayatie yakike ya school?"
"Lafiya! Mah tace kashigo"
"To muje" yafaWi haka yana nuna mata hanya
"kayi gaba na bika a baya"
"Naki wayon saidai mu jera" murnushi tayi suka jera zuwa ciki.

Mas'ud ya gyara zaman sa ya fuskanci Ammi dake cika tana batsewa jin abinda yakawo Mas'ud Win wajanta, harya gama maganar dayake bata katse sa ba har saida yakai aya
"Mas'ud kafita a idona ina ganin mutumcinka inda nasan abinda yakawo ka kenan da bazan tsaya na saurareka ba"
"Ammi dan Allah kiyi hakuri kinga kuwa yanda Mustapha ya koma, ko ke kika gansa zaki tausaya masa, dan Allah ki masa addu'a kirage fushin nan da kike dashi, fushin ki ma kawai zai iya saka sa a wata masifar da tafi wannan, ki masa addu'a na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba Amarya da Sumayya ba haka suka bar Mustapha ba, ni zuwa nayi muyi magana dake musan mai zamuyi akan lamarin Mustapha, wancan satin fa bakiga yanda yazo office Wina ba a birkice wai Sumayya ta aikesa ya siyo mata abinci, Mustapha fa Mistaphan da yarinyar nan bata ishe sa kallo ba ace itace yanzu ta aike sa siyan abinci ai daga ji Ammi kinsan akwai wata a kasa"
"To Mas'ud maizan maku yanzi?"
"Yawwa Ammi haka nakeso ki faWa yanzu dai daga farko yakamata mu fara masa abinda zai karya wanan sihirin da aka masa"
"Taya kasan sihiri ne ajikin Mustapha bayan sihiri ma fa harda hali" murmushi Mas'ud yayi kana yace
"Ammi ki yarda dani nafi kowa sanin Mustapha nasan halinsa wallahi mace tayi kaWan ta hana sa zuwa gareki kema kin sani kinsan soyayyar da biyayyar sayake maki, ki duba yanda duk ya birki ce yakoma kamar ba mutum ba, cemin fa yayi yana son ganin ki inya Wakko hanya zai zo gidan nan gaba Waya saiya manta hanya"
"Naji Mas'ud zan haWa masa maganin karya sihiri jibi kazo ka karSar masa"
"Yawwa Malama Ammi" mirmushi kawai Ammi tayi sukayi sallama Mas'ud ya shiga Wakin Umma sukayi sallama, wajan fitowara daga gidan ne ya haWu da Murjana zata shigo gidan itama, ko kallon inda take baiyi ba balle ya amsa gaisuwar datayi masa, Murjana tafaWa Wakin Amarya bako sallama tafara magana

"Mai wannan gayan na gidansu Aimanah yazo yi gidan nan?"
"Murjana kenan ni ina zan san maiya zo yi banma san ya zo ba, kin faWo min Waki ba sallama"
"Amarya nifa wallahi badan badan ba da sai nace nima a kama min shi ya shigo hannu nayi wuf dashi kawai gayan yana birgeni, harfa gaida sa nayi yaki amsawa" Murjana tafaWi haka tana zumSuro baki irin na shagwaSaSSun yara
"Murja ba ba irin wannan nakeso ki aura ba mai nasama yaci balle yaba nakasa, kijira akwai tanadin danake maki wanda zakiyi farin ciki da hakan"
"A'a nida gaskiyya Amarya banason wani ni Mas'ud nakeso, kuma dole ki san yanda zakiyi na aure shi ko na tone asirin da muka binne a makabarta...
'

07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na Biyar

"Murjana mai nake ji kina faWa? akul Winki wallahi duk randa kikayi wannan gangancin saina matukar saSa maki sannan kisa a ranki bazaki auri Mas'ud Win ba Salim zaki aura Wan kawata matar minista ana kai ki inda zaki huta kina cusa kanki cikin wahala mai za'ayi da Mas'ud har maye kuda balle romansa"

"Amarya salim kuma ni bana son sa bazan aure saba kin san maganar dayake min ne Wan iska ne fa"

"Ke wai Murjana sai yaushe zaki waye? yar soyayyar nan dayake nuna maki ce iskanci? maye a ciki danya rike hannunki ya sumbata ai soyayyace"

"Ni! ni!! ni!!! bana sonsa wallahi abani wanda nakeso ko nayi ba dai dai ba" Murjana tafaWi haka tana buga kafa irin na shagwaSaSSun yara ta wuce Wakin Amarya tana cigaba da faWar maganganu, Amarya tabita da idanu harta shige Wakin, tashi Amarya tayi daga wajan ta danna wayarta tasoma magana kasa kasa.

"Boka tsito mai dogon zamani barka da dare" da wata iriyar murya kamar bata mutane ba yasoma magana wacce ke futowa da wani ihu

"Barka dai doguwa mai dogon zunubi maike tafe dake a wannan daran?"

"Tsito yarinyar nan Murjanatu keson bani matsala a kan yaron nan Mas'ud kadai san maganar"

"Mai dogon zunubi ki bar wannan maganar komai namu zai iya lalacewa in muka shiga shirgin yaron nan a tsaye yake kan addu'a da azkhair gashi mayan karatun kur'ani na duba ta ko'ina naga bazamu sami riba akan yaron nan ba, ita kuma Murjana yau zanyi aiki a kanta zata manta da duk wani sirrinki data sani zamu rike zuciyarta sai yanda kikayi da ita, daga karshe gobe kizo anan zaki kwana kin dai san aikin basai na maki bayani ba"

Hmmm Amarya taja Numfashi kafin tace "Tsito na gane amma ina cikin jini hakan bazaiyu ba sai nayi tsarki"

"Yawwa hakan yayi daman ina neman jinin al'adar mace wadda tai haihuwa biyu bata sake ba zanyiwa wani Wan majalissa aiki, kizo goben da wurwuri"

Jiki a sanyaye ta amsa masa da "To" ta ajje wayarta tana mita "Gaskiyya boka kana takuramin kai kullum cikin jaraba kai aba ba wani girman kirki ba".

*MUSTAPHA*

A hanakali yake cakalar abincin da sam ba daWi ci kawai yake saboda yana tsoron masifar Sumayya wacce ke zaune fegansa ita hankali kwance take cin abincin bata da wata damuwa, wayar Mustapha datayi kara ita taja hankalinsu gaba Waya, yakai hannu zai Wauki wayar Sumayya tariga sa Wauka, "Aboki" Sumayya ta faWa tana tsare Mustapha da idanuwa, mika masa wayar tayi
"gashi wannan sarkin nacin ne Mas'ud Waga kiran kuma kasa a hansfree," haka yayi kamar yanda tace Win
"Barka da dare Amini na fatan ka wuni lafiya yau gaba Waya banji kaba"

"Aboki abubuwa ba sauki aikin office ya rikeni ban samu shigowa wajan kaba kamar yanda nace, kasan inata shirye shiryan tafiya india cost Win nan na wata uku a satin nan nakeson tafiya"

"Yayi kyau ashe da ban kira ka ba sai lokacin tafiyar yayi sannan zaka faWa? ka gayawa Ammi?" kwarewa Mustapha yayi sakamakon Ammi dayaji an ambata gabansa yai wani irin faWuwa

"Wace Ammi?" Mustapha ya ambaci hakan hankalinsa kwance, Mas'ud saurin jingina yayi da fuskar gadonsa take wasu hawaye masu Wimi suka zubo masa yasoma sharewa kamar bazaice komai ba sai kuma yamagantu

"Mustapha Ammi ce baka sani ba? ashe nima baka sanni ba?"

"Freind ka yarda dani na rantse ban santa ba nakasa tuna inda nasan sunan a kasan zuciyata inaji kamar na santa" Mas'ud katse kiran yayi ya kifa kansa saman cinyarsa yafashe da kukan tausayin Wan uwan nasa "Yazama dole a kaina insha Allah saina fito dake daga wannan mummunan duhun daka faWa"

Sumayya daWi ne ya mamaye zuciyarta jin aikin da boka tsito yayi masu jiya, aiki yayi sun sa yamasu aikin da gaba Waya Mustapha zai manta da mahaifiyarsa su mallake dukiyar sa gaba Waya itada Amarya, zuciyar ta fal daWi ta wuce Wakinta ta kira Amarya tana faWa mata yanda Mustapha sukayi da Mas'ud, Amarya tayi farin ciki sosai daman ta riga da ta yadda da aikin tsito daga ka faWa ne bukata zata biya, har rawa rayi tai juyi a cikin Wakinta, Murjana na mata dariya, tsakar gida ta fito tayi ko sa'a Ammi ta fito daga Wakin Momy uwar gidansu, Amarya ta fashe da dariyar keta tayi tsalle tai juyi ta fara yar waka "Daka haifi gwammana gwara ka haifi matar gwamna saini Amarya surikar Mustapha yau ya gwangwaje ni da kujerar hajji, ?a mace kyautar Allah wata ta haifi maza ta haifawa wasu ita da banza Waya suke a wajan Wanta"

Ammi murmushi tayi harta soma tafiya zuwa Wakinta sai kuma ta tsaya ta maida martani dan tasan kai tsaye Amarya da ita take

"Amarya ki fita sabgata zan matukar saSa maki a gidan nan, nafa sani nariga nasan komai aikin asirin, na riga na bar maki shi ke da yarki na godewa Allah dayasa ba shi kaWai na haifa ba bare abin yadaman"

"Saude ni kike gayawa na ma Wanki asiri inace nan nan yazo har Wakina yace yanason ?ata Sumayya daman sai da nace masa bazan basaba yanace saboda nasan kun riga kun tsane ni a gidan nan" Amarya tafaWi tareda fashewa da kuka, Alhaji Kamal da yaji kukan Amarya fitowa yayi daga Wakinsa

"Ya isa nace ya isa wai mayake damun kune da daran nan zaku tayarwa da mutane hankali, ke Saudat na fuskanci tunda akayi auran nan kin tashi hankalinki kin tisa naja'atu a gaba kamar ita tace Mustapha zoka auri yata" Momy tai saurin kallon mijin nasu cikeda mamakin sauyawarsa a jiyan nan mafa sunyi magana akan auran Mustapha da Sumayya har yace yana tausayin Ammi ganin yanda Wanta ya juya mata baya ko gidan ya shigo shi da Sumayya basa shiga inda Amni take Wakin Amarya kawai zasu shiga su gama abinda zasuyi har subar gidan baya ko kallon Wakin Ammi

"Alhaji laifin Ammi ka gani ai kuwa idan ba'a tausayawa Ammi ba ba'a ga laifinta ba, inace jiyan nan..."

"Ya isheki haka Asiya daman ai na lura kun takurawa Naja a gidan nan da da take faWar kun haWe mata kai bana yarda yanzu naga zahiri, ke Amarya shige Wakinki barni da matan nan zanyi maganinsu a kanki zan iya aika ko wacce gidan su" Momy mamaki yakashe ta ta dafe baki>??kawai tana kallon Amarya, Ammi batace komai ba ta karasa Wakinta, Amarya ma komawa Wakinta tayi tana jinjinawa aikin Boka tsito dan jiyan har Alhaji Kamal tace a haWa duka a Winke bakinsa akan auran nan yadaina ganin laifinta, saura Momy ma zatayi maganinta itama.

Ammi zama tayi saman kujera tana goge hawayan dayake fitowa daga idanunta Saheed Wanta na uku daya ji komai saboda yana falon Ammin yana kallon kwallo, kashe kallon yayi yadawo kusa da mahaifiyarsa yana goge mata hawayan dayake zubowa daga idanunta, tsabar takaici takasa magana wani abu ya tokare mata a kahon zuci, shigowar Ahmad Wanta na biyu wanda suke matukar kama shida Mustapha ganinsa yasa tafashe da kuka, da sauri ya karaso inda take ya zauna a kasa ya kifa kansa saman kafafunta ji yake kamar shima ya fashe da kukan yanzu Surayya takirasa ta gaya masa abinda Abba yayi a gidan, Shaheed ya Wora kansa saman kafaWar Ammi yana tayata kuka, jin kukan da Saheed yake yasa ta katse nata kukan tasoma ajjiyar zuciya a jere a jere, idanunta ta rufe

"Shaheed yi shiru daina kukan nan bakai yakamata kayi kuka ba ni ce zanyi kuka an cuce ni, ana kuma ganin laifi na, ni Alhaji ke gayawa magana duk hakurin danayi bai gani ba, gobe zan bar gidan nan ku maza ne ba mata bazan iya zaman hakuri ba, Ahmad kayi aure kabar cikin gidan nan kafin wata masifar ta ritsa da kai zanso ka auri Aimanah hakan zai faranta raina, Shaheed zan tattara kuWaWe na nasama maka makaranta a malesia ko thailand katafi can kayi nisa da gidan nan kaima"

"Ammi munyi maganar nan dake tun kwanaki bazan iya auran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login