Showing 75001 words to 78000 words out of 95991 words

Chapter 26 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5401

na saki Aimanah saki Waya_ dafa bango Ammi tayi tana hailala da tasbihi ga ubangiji lalle mutum abin tsoro futowa tayi daga Wakin tana kalllon Ahmad,
"Muje Ahmad" bata tsaya ba tayi gaba abinta, Alhaji Kamal na tsaye jikin mota yaga futowar Ammi da Ahmad harma da Mustapha da Sumayya, har kasa Sumayya ta tsugunna ta gaida Abba daya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa
"Abba wai dama Aimanah bataje gida ba, tun jiya da yamma fa tabar gidan nan Mustapha ne ya bata takarda sabida ya kamata ta satar masa kuWi, ba yanda banyi da ita ba akan ta zauna mu basa hakuri ta kafe sai da ta tafi ko ina taje, Allah yasa tana lafiya" Sumayya ta faWa harda kukanta kamar gaske, kallon mamaki Ammi kewa Sumayya lalle mace shu'uma ce
"Assha Mustapha garin yaya haka ta faru banyi farin ciki da jin maganar nan ba"
"Abba ba wannan ba, bar waWannan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mutanan mu fara kiran yan uwa ko Aimanah taje kano" kusan duk wanda Ammi ta kira amsa Waya ce bata zo ba, haka ya kuma tasar hankalin Ammi sosai, hankali tashe suka baro Abuja suka juyo zuwa kano, Ammi kuka sosai take da tunanin inda zasuga Aimanah anan kano bincike sosai akayi har mutuware sai da Ammi da Ahmad suka rinka zuwa suna dubawa wai ko ta taho sukai hatsari ta mutu, wasa wasa tun ana Soye magana har magana ta fito sarari Aimanah ta Sata, hanakali tashe yayu da iyayan Aimanah suka duro kano, Mus'af kamar yayi hauka lokacin da labari yaje masa yana sauka a nageria Abuja daman ya sauka sawa yayi yan sanda suka kama Sumayya da Mustapha da zargin sun Satar da yarinya, anan sell na yan sanda yabarsu ya hau jirgi ya wuce kano, sai da Sumayya da Mustapha suka kwana biyu a cell sannan Mus'af yafaWa yasha faWa a wajan Daddy shiya tilas ta sa aka sake su suka koma gida Sumayya na daWa cin alwashi...
' [2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da biyar*


Hajiya Zainab zaune gaban gadon da Aimanah ke shimfiWe kamar gawa, Muhd na gefanta yana dannan waya yayinda Azinatu ke zaune itama kan gadon daga gefan Aimanah, gaba Waya sunyi shuru abin duniya duk ya dami Hajiya Zainab zuciyarta fal da zulumin kar yarinyar nan ta mutu
"Moha a fara binciken daga ina yarinyar nan ta fito, na tabbata zuwa yanzu iyayanta na cikin tashin hankali yau kwana shida fa kenan"
"Mom wannan fa daga gani irin yaran nan ne dake aiki a gidajan masu kuWi kilama sata tayi aka koreta daga inda take aikin" Azinatu ta faWa tana hararar Aimanah wacce bata san tanayi ba
"Wannan ce tai maki kama da masu aiki, ke dai kawai kin saba saikin ai bata mutum, ke bazaki canza hali bako, bar asibitin nan ki sani Wan adam ba abin wulakantawa bane kilama tafi ki gata" Azinatu hararar yayan nata tayi tareda kyauda kai gefe
"Moha bana son hayaniyar nan taku kuje gida dan Allah"
"Gaskiyya Mom anemo wacce zata kula da yarinyar nan ki koma gida yaufa kusan sati kenan rabonki da gida, ga ranar Anty Ramla inda tana nan da tini ita ke kula da yarinyar nan" Muhd kallon Azinatu yayi ya fice daga Wakin batare daya ce mata komai ba, da sauri ta mike tabi bayan Muhd tasan ba karamin aikinsa bane ya tafi ya barta anan, Hajiya Zainab mikewa tayi ta shiga bathroom tayi alwala ta tada sallah nan cikin Wakin, tana zaune saman dadduma tai nafila raka'a biyu ta soma jero addu'o'i har barci ya Wauke tana nan saman daddumar

SUMAYYA
Suna komawa gida daga stesion wanka kawai tayi ko magana da Mustapha batayi ba tai shirin tafiya enugu, gaba Waya ma ta manta da wata amarya dake kwance a asibiti ba lafiya, ta isa enugu lafiya ta zube gaban malam har kuka saida ta masa akan yataimaka mata kar asirinta ya tonu, wasu Walasimai yafara karantawa take wata tukunya ta bayyana a gabansa yacewa Sumayya leka kiga kanta tai kasa da shi tana leka cikin tukunyar Aimanah ce ta bayyana cikin tukunyar kwance kan gadon asibiti
"Mu muka sakata wannan dogon barcin muna jiran kizo muji mai kike so a mata"
"Malam amata duk abinda yadace nidai so nake Mustapha yazama nawa ni kaWai"
"Hhhhhjj shikenan zamuyi, zamu tashe ta daga dogon barcin da take aljani zai shafe tunaninta bazata iya tuna ita wace ba sai nan da wata uku sannan ta zama ba matar mijinki ba zata dawo hankalinta,muddin tana hankalinta asirin jikin Mustapha zai karye, Mijinki kuma mun rigada mun gama komai a kansa kije sai yanda kikayi da shi yanda kika dama haka zai sha ko kara kika ajje kika ce karya tsallaka bazai tsallaka ba"
"Yawwa malam nagode,"
"Ba'a mana godiya kije, wannan tukunyar zansa aljani yanzu ya Wauke ku keda tukunyar ya maida ku gida ki ajjeta waje mai kyau inhar ta sake fashewa to bani da abinda zan maki kuma ki kula sosai sannan in kina son magana da ni ki leka tukunyar nan ki kirani zan bayyana, rufe idonki" da sauri Sumayya ta rufe idanunta jikinta na karkarwar tsoro, tsawon lokaci idanunta na a rufe can taji kamar wacce aka ajje kan wani abu ta buWe idonta tana buWewa taganta zauna kan gadonta, zabura tayi har tana buge Mustapha dake barcin safe

MURJA
Kuka sosai take sanda taga Mama kwance a gadon asibiti ko zama bata iya yi, Alhaji Jameel shi yayi komai aka mata hoto wanda ya nuna lakarta ta rigada ta tsinke ba ita ba sake iya zama sai dai kwanciya, Amarya tayi kuka tai nadamar abinda ta aikata da bin son zuciyarta da tayi, Alhaji Jamil yadamu sosai ya rinka tambayar Dr Win ba yanda za'ayi ko zama a samu tarinka yi suka ce basuda kwarewa a wannan harkar sai dai zasu turasu kano asibitin kashi dake dala, a motar asibitin aka kawo Amarya asibitin kashi anan kano, bayan hotunan da sukai mata suka ce zasu mata aikin da zata iya zama amma itada sake taka kasa har abada, sanda aka gayawa Murja kuWin aikin hankalinta yatashi naira miliyan huWu da rabi, Alhaji Jamil shiya biya kuWin yai komai aka mata aiki, alhamdulillah aiki yayi kyau sosai tana iya zama amma sai an taimaka mata sai dai bata iya tashi da kanta komai a inda take zaune take hakan yasa aka saka mata ledar fitsari, sanda aka sallamesu rasa inda zasuyi da Amarya Murja tayi, Amarya ma kuka tayi sosai na nadama yau sai gashi ta tina da iyayanta dake katsina can Murja da Amarya suka tafi a motar da Alhaji Jamil yasamo masu a tasha ya biya kwana Waya yabawa Murja ta dawo sabida jibi zasuyi tafiya,
Dakyar da lallashi iyayan Amarya suka karSeta dan har rantsuwa sai da Babanta yayi baza ta zauna masa a gida ba sai da Murja ta nemo wani wan baban yayi masa magana kana aka bata Wakin da zata zauna, Murja ta kira Sumayya tana kuka ta gaya mata halin da mama ke ciki, hankalin Sumayya yatashi hakan yasa tabi jirgi zuwa Katsinan itada Murja suka shiga suka fita suka samo wata tsohuwa da za'ana biyanta zata kula da Maman tasu dan mahaifiyarta rantsuwa tayi da abinda zai kasheta bazata taSa Amarya ba, washe gari Murja da Sumayya suka baro katsina, kafin wani lokaci Amarya baya ya rarake yayi wani zurfi sai wari da yake fitarwa ko Wakin ba kowa ke iya shiga ba duk da kuwa tsohuwar na matukar kula da Maman, Sumayya ita ta koma aka samu nurse Win dake zuwa tana wanke wajan kullum, daya warke kuka sai wasu tsutsotsi yan mitsi mitsi da suke futowa daga gabanta cukus ba kyan gani Amarya ta rame ta kanjame duk da kuwa su Murja na matukar kula da ita suna ajje mata komai na amfani

AIMANA
Sai da tai sati guda bata ko motsi sai yau data cika sati guda sannan ta buWe idanunta, lokacin Mom na Wakin da sauri ta mike ta kira Dr ta cikin telephone Win dake cikin Wakin nan da nan sai ga Dr da Nurse a tare, Dr yakarasa gaban gadon da Aimanah ke kwance wacce keta dube dube
"Sannu yaya jikin?"
"Da sauki ta faWa a hankali"
"Ya sunanki,kinsan wannan?" Dr ya tambayya yana nuna Hajiya Zainab
"Ban san sunana ba, itama ban santa ba"
"Yasalam" Nurse tace tana komawa gefe ta tsaya, Hajiya Zainab ta share hawaye tana zubawa Aimanah idanu
"Hajiya abinda muke gudu yafaru fa sai dai zamu Worata akan magani mu gani"
"Yanzu ina ne ke maki ciwo"
"Bako ina" Aimanah ta faWa a hankali
"Hajiya zamu sallame ku ku koma gida sai dai zakuna zuwa ganin likita duk sati, sannan ayi kokari a samo yan uwanta ina zaton in taga wani nata komai nata zai dawo dai dai"
"Insha Allah zamu bincika Dr" Hajiya Zainab ta kira Moha yazo ya Wauke su, Aimanah da idanu kawai take binsu, sosai Mom ke kula da Aimanah gefe guda tana binciken yan uwan Aimanah, wasa wasa Aimanah sai da ta shafe watanni biyu da wani abu tana cikin wannan halin,
Zaman Aimanah a gidan zama ne na gata sosai Mom da Muhd suke kula da ita, a wajan Azinatu kawai take samun damuwa, Aimanah shuru shuru ta koma bata cika son zama cikin mutane ba kusan ko yaushe tana Waki, cin abinci wanka sallah komai sai Mom tace tayi sannan take, yau gidan antashi sosai da murnar dawowar Wan Hajiya zainab tun safe Ramla dake aure a kaduna tazo, sai Worawa da saukewa ake
Hajiya Zainab haifaffiyar nan garin Abuja ce, mijinta tuni Allah ya masa rasuwa tana zaune gidanta itada yaranta guda huWu Muhd shine babba sai Yasar Ramla sai auta Azinatu, Ramla an mata aure tuni tana kaduna tareda mijinta Allah bai basu haihuwa ba, Muhd baiyi aure ba andai saka masa rana da yar kanwar babansa, Yasar shekarunsa bakwai kenan rabonsa da nageria yana zaune a madina inda yayi karatu tuni harya fara lacture a jami'atul madina, takurawar da Mom ta masa na rashin zuwa gida yasa zai kawo ziyara ya koma, sai da suka gama komai suka gyara gidan yanata tashin kamshi sannan Muhd ya zo suka tafi airport Wakko sa sabida jirgin da yasar ya biyo na gafda sauka, Ramla Azinatu su suka tafi ba yanda Mom batayi da Aimanah ba wacce suke kira da Aysha ba kan tabi su tace bazata ba hasalima komawa tayi Waki ta kwanta,
Yasar rungume Muhd da Ramla yayi yana kissin Winsu ta ko ina
"Nayi kewarku sosai, Yaya Moha ka kara girma, Anty Ramla tawa kin kara kiba" dariya duka sukayi banda Azinatu dake can gefe tana taSe baki, dariya Yasar yayi sanda ya hangi Azinatu
"Autar Mom sarkin rigima haka kika kara tsayi, amma dai taliya Mom ke baki ko"
"Kaifa daman bakinka baya shuru, wuce muje" Moha yafaWa yana rike da jakar kayan Yasar, tunda suka shiga mota bakin Yasar bai yi shuru ba sai surutu yake dan dama shi ba baya ba wajan magana, har suka karasa gida suna yi da Ramla Moha sam baya saka masu baki danshi mutum ne ba mai son magana ba,
"Our wellcome ustaz" Mom tafaWa sanda ta rungume Yasar, Sun batar ta kawai yake ta ko'ina yana rungume da ita
"Mom nayi kewa" yafaWa yana share hawaye
"Nima nayi kewar surutun nan naka, ince dai larabawa basu canza min kai ba"
"Ai wallahi ko kaWan Mom Wanki bai canza ba, tunda fa muka tawo yake surutu shida Ramla, surutu cai cai kamar yaci aku nifa harya samin ciwon kai, Dan Allah Mom kar a ce ya zauna a Wakina kamar yanda muke da, ga Wakin Ramla can ya sauka anan, bazan iya da surutun Yasar ba"
"Caii wai nine mai surutun, Mom inama Wakin Yah Moha Win yake tabbas can zan sauka yau kwanan hira zamuyi anjima ba'ayi hirar zumunchi ba"
"Mom ina Aysha ne, banga motsinta ba" Moha yafaWa yana kallon kofar Wakin Mom
"Tun bayan fitar ku ta kwanta barci, ke Azinatu taso ta, tazo aci abinci da ita"
"Mom wace Aysha ko anyi bikin Yaya Moha ne banda labari"
"Wata yarinya ce fa Mom ta kaWe ta wata uku kenan amma an rasa iyayanta take zaune anan" Azinatu ta faWa tana taSe baki, hararta Anty Ramla tayi kana ta shiga Wakin Mom inda Aimanah ke kwance
"Anty Ramla kun dawo?"
"Mundawo Ashanty Mom tace ki fito aci abinci ga Yasar ma yadawo" mikewa Aimanah tayi tana gyara zaman doguwar rigar dake jikinta tabi Ramla suka fito tare, da sauri Yasar ya kalli yarinyar da ta fito tareda Ramla zaro idanu yayi sanda idanunsu suka gauraya dana juna
"Kambu, Mom maza bani ruwan zam zam a jakata" da sauri Aimanah ta juya zata koma ciki, caraf yayi ya ruko hannunta ya zaunar da ita nan saman tiles yana zare idanu,
"Kai Wago ka kalle ni," yafaWa da karfi yana zare idanu, kai Aimanah ta fara Wagawa,
"Azinatu Ramla kubar falon nan" Yaseer yafaWa cikin bada umarni
"Wai Yasar ban gane ba mai kake wa yarinyar nan haka ne, maca ce fa kake kiranta da kai"
"Zauna Mom da aljani kuke tare, asiri ne a jikin yarinyar nan bani zam zam dan Allah" Sim sim Azinatu tayi ta fice daga gidan gaba Waya jin an ambaci aljani, Anty Ramla zama tayi tai tagumi tana kallon Aysha dake bubbuga kafa
"Bazaka Wago ka kalle ni ka gaya min waya turoka ba" nan ma kai Aimanah ta kuma Wagawa kanta na kasa
"Anty bani cup" ta tashi ta Wakko cup Win a kicin ta dawo ta basa, zam zam Win hannunsa ya fasa ya tsiyaye a cikin cup Win ahankali yafara karatu cikin ruwan, tsawon lokaci kana ya kalli Mom
"Mom rike min cup Win nan ki rike sosai, zan matse bakinta ki zuba mata ki rage min kaWan" Mom tayi yanda yace Win sauran daya rage ya cewa Ramla zoki shafa mata a jikinta, Ya soma karatun suratul bakara a hankali cikin kira'a mai daWin sauraro
"Wayyo wayyo ku daina zamu fita zamu fita, daman aiko mu akai turomu akai mu shiga jikinta mu Wauke mata tunaninta ta manta komai har zuwa sanda zatayi idda ta zama ba matar Mustapha ba, yau kwana huWu kenan data kammala daman muna shirin tafiya, kana kona mu kana konamu kabari zamu tafi"
"Zaku tafi kamar ya ku zauna, ina mijin nata yana ina"
"Yanzu haka yana wajan aikinsa"
"Mai sukai maku da zaku rana auran sunna"
"turomu akai kishiyarta ce ta turo mu"
"To ku fita kuma ku karya asirin da kukai masu, kuna jina"
"Munji zamuyi yanda kace"
"Nafa sanku bakuda alkawari, in bakuyi abinda nace ba zansa a kawo min ku nan kuna ji"
"Zamuyi komai yanzu ma" shuru Aimanah tayi tareda jero atishawa, can kuma ta buWe idanunta ta mike a guje zata fita, rike ta yayi gam yana kallonta
"Kinga nutsu kina cikin aminci" Wani kuka ta saki tareda kokarin kwace rukon da yayi mata
"Musty ka sake ni barin gidan nan zanyi, kariga da ka yanke igiya Waya ta auranmu ka sake ni nasamu na fita daga wannan gidan na bala'i"
"Kinga buWe idanu ki kalle mu sosai nan ba gidan ki bane, Mom ta bike ki kusan wata uku kenan" da sauri ta buWe idanunta tana kallonsu Waya bayan Waya
"Ya sunanki" Moha ya tambaya a hankali
"Aimanah Farouk mai naira ni haifaffiyar kano c.........nan ta basu labarin ta da abinda ya fito da ita daga gida, Mom sosai ta tausaya mata anan take Aimanah ta bada lambar Ammi aka kirata a waya, Ammi dan Murna ji take kamar ta fasa wayar ta shigo ciki, cewa ma tayi gatanan zata biyo jirgi tazo Abujan, Mom ta hana ta tace su yakamata suzo gobe zasu biyo jirgin safe, Yasar mikewa yayi ya shiga Wakin Moha yayi wanka kana ya fito, kallon Aimanah yayi yana murmushi
"Sannu Ummu ya kike ji, kanki baya ciwo ko" kai ta girgiza alama e
"Ba da kai zaki min magana ba baki zaki buWe kimin magana Wago ki kalli idanuna naga wani abu" Wagowa tayi tana kallonsa da fararan idanuwanta, wani abu yaji ya tokare masa a kirji, ya lumshe idanu yana ambaton Allah a hankali, yana buWe idonsa sukai ido huWu da Mom murmushi mom tayi tana bin Yasar Win da kallo yanda ya kafe Aimanah da idanu, kallo Waya inkayi masa fuskarsa zata fallasa asirin zuciyarsa....
'

07039793439
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da shida*

"Kazo ka zauna kaci abinci sai kaje ka kwanta ka huta" Mom tafaWa tana kallon Yasar daya kafe Aimanah da kallo,shafa kansa yayi kana yaja kujera ya zauna,
"Ummu kinci abinci" Aimanah tayi murmushi batare data ce komai ba, Anty Ramla da Moha suka kalli juna suka fashe da dariya, Aimanah gaba Waya ta kasa sakewa idanun Yasar take ji a ko ina na jikinta, bata wani ci dayawa ba ta mike zuwa Waki
"Ummu ki tsaya na baki habbatus sauda ki turara, sannan ki maida hankali sosai wajan yin azkhar na safiya da maraice ki yawaita karanta kur'ani kina kuma yawan saurara a wayarki"
"Batada waya ai" Anty Ramla ta faWa tana kallon Yasar
"Bari inna fita anjima gaida gwaggo mariya zan taho mata da waya"
"Da wuri haka" Moha yafaWa yana dariya
"Kasanmu a lamarinmu ba Soye Soye, sak muke tafiya ba kwana kwana"
"Yanzu dai so kake kace kaga mata"
"Ta aure ma insha Allah" ya maidawa Anty Ramla martanin maganarta
"Tana dai da mijinta, kajira kaga yanda zata kaya" Mom tafaWa tana kai lomar abinci bakinta
"Mom tariga tayi idda fa, ba wata uku tai a gidan nan ba"
"Hakane tayi idda yau kwana biyu kenan datai wanka, amma dai kabi a sannu karka zurma
"Mom nafa riga na shiga irin sosai Win nan" yafaWa yana dariya, Barci Yasar yayi na awanni sai yamma yatashi ya sake wanka ya fita ya zaga su gaisa da yan uwa, sai bayan sallar insha yadawo a hanyarsa ta dawo wa ya tsaya babban shagon sai da wayoyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login