Showing 60001 words to 63000 words out of 95991 words

Chapter 21 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5402

gefan gado fina ta rike baki tana kallon Sumayya da mamaki
"Wai yanzu Sumy wannan ce kishiyar taki daman?"
"Ita ce" Sumayya ta faWa a san yaye
"Cab tabbas zaki ga takaici jibi yarinya sai iyayi kalli uban kuWin da ta fito dasu daga Wakin mijinta"
"Mijinta kuma" Sumy ta kuma faWa cikin sanyinta
"To mijinta mana Sumayya ke kina zaune anan bazar kin saki jiki kina zaune da kishiya lafiya waya gaya maki ana zama da kishiya nifa nan da kika ganni sanda zan auri Alhaji na shiga malamai nayi na rabasa da matarsa da yayansa ya kaWa ta can aka koma gida akaci gaba da cin tuwon dawa, na kama abina ram na rike yanzu in gaya maki daga ni sai Wana muke abinda ranmu yake so mota sai wacce naso nake hawa, yanzu ki duba misali ace yau Mustapha ya mutu mai zaki samu a dukiyar sa sai dai fa aWan tsakurar maki Wan kaWan, kizo muje inda za'a maidaki tauraruwa a idanun mijinki ya zama sai abinda kika ce shi za'ayi a gidan nan"
"Bazan bi malamai ba, inkai zunubin ina" raWa Lima tayi mata a kunne komai suka cewa Sumayya oho tadaiyi murmushi tai shuru tsawon lokaci kana ta ce
"Ina son Musty tabbas nima zan so na haihu da shi zanyi abinda kuka ce yau she zamuje wajan malam Win?"
"Basai munje dake ba can enugu ne wajan da nisa sosai indai zamuje kwana biyu muke yi, Mustapha zai barki kiyi tafiyar kwana?"
"Zai bari mana, zan masa karya zani Kaduna gidan yayar babanmu nasan zai amince, ban taSa ce masa zani wani waje ba ya hanani"
"Yawwa yar gari toki tanadi kuWi, Malam yana aiki kamar yankan wuka amma fa sai yaji dumus" Lina tafaWa tana dariya
"Banda matsala da kuWi Mustapha nasamin kuWi a acount Wina duk wata bana amfani dasu tarawa kawai nake yanzu zasumin rana" nana suka rabu akan jibi zasu tafi enugu, koda Al'Mustapha yadawo ta gaya masa baiyi musu ba sai fatan sauka lafiya da yayi mata, sanda yace zai sai mata ticket anan ne tace bata son zuwa a jirgi mota zata bi, washe gari ta kira yar uwar babansu tafala mata tafiya zatayi ne bikin kawarta a enugu tasan in Mustapha yasan ga inda zata bazai bari ba tace masa nan zata zo, koda wata magana ta taso tace nan ta zo, jiki na rawa Matar ta amsa mata da to sukayi sallama Sumy ta tura mata dubu hamsin, randa sukai alkawari ranar suka tafi gaba Wayansu ukun, Sumayyya tun tana tafiyar marmari harta fara galabaita sabida a enugun ma inda sukaje can wani kungurmin daji ne ba gida gaba ba gida baya, sai wata bukka saman tsauni haka su Sumayya suka hau tsaunin nan kafin suka rufe idanunsu lina na karanto masu wasu Walasimai wata guguwa ta Webe su, tai kamar zata buWe idanunta taji anan faWin
"Karki soma kada ki sake ki buWe mana idanunki anan, kina buWe su sun zama banaki ba mallakin aljani tsunju" ai kara damke idanunta tayi har zuwa sanda taji guguwar ta tsaya taji wata murya mai kamar ana busa usur tana masu magana, Feena ta zungureta ta buWe idanunta tai tozali da wani ramamman mutum dogo sosai ga rankwameman kai zaune saman fatar damisa" shekewa yayi da dariya yana kallon Sumayya
"Yarinya burinki ya gama cika tunda kika zo nan ungo wannan" yafaWa yana wullo mata wani kullin magani kulle cikin kyallan atamfa
"Kimasa lemu ki tabbatar kinsa garin maganin nan to daga ranar sai abinda kika cewa mijinki duk abinda kika ce masa shi zaiyi zai manta da kowa da komai sai ke, hakama kishiyarki kowa nata zai manta da ita sannan zamu kafe ta a gidan komai zakiyi mata bazata iya barin gidan ba, gaba Waya dukiyar Mustapha ta zama taki sai abinda kika ga dama kika ce yayi shi zai yi" ranta ne yayi wasai taji gaba Waya kamar an yaye mata damuwar dake ranta, saidai jikinta ne yayi sanyi sanda taga Malam na saduwa da Lina ta bayanta anan ne hankalinta yata shi taga lina bata ko damu ba, agabanta ya kuma biyan bukatarsa da Feena, jikinta ne ya hau Sari ganin malam na kallonta yana lashe baki
"Ki nutsu bazanyi komai dake ba, bama bukatar irinki akwai sauranki sai nan gaba kema zakiyi abinda suka yi juye mana kuWin jakarki" gaba Waya ta zazZzage masa kuWin cikin jakar suka fita da baya da baya"
"Lina mai naga kunayi da mutumin nan"
"Wannan ba huruminki bane Sumayya kiyi kallo kawai kuma karki sake ki bawa kowa labarin abinda kika gani mun aikata da boka, wannan wata bukatar ce daban" hotal suka kama suka kwana...
' [2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin*

Musty ke zagaya falon da gudu, yara da Aimanah na biye da shi suna dariya, kallo Waya zaka masu su matukar baka sha'awa Gwaggo Fulani na can karshan falon tana kallon ahalin dake cikin zallar nishaWi, dukan su ba wanda ya iya kama Mustapha, zilliya yake masu kamar a filin kwallo, sai da yagaji dan kansa kana ya zube kan kujera Aimanah da yaran gaba Waya suka faWa kansa suna faWin

"Yee mun kama Abbie mun kama abie"
"Abie ni coculate zaka bani" Islam tafaWa tana taSe fuska kamar zatayi kuka
"Abi mu kuma sweett muke so ko Aslam" Tasnim yafaWa yana kalllon Aslam

"Ba wanda zan bawa komai, sabida ba wanda ya iya kama ni"

"Harni?" Aimanah ta faWa tana taSe fuska kamar wata karamar yarinya

"Ni na'isa nace har ke, in ban baki sweet ba yaya zanyi da ita" yafaWi haka yana shafa mararta, bakinsa kan kunnanta yake mata raWa
"reina inajin kishi fa, kizo muje ki bani ruwa" yafaWa da wata irin murya da sauri ta Wago kai ta kalli cikin idanunsa waWanda suka tabbatar mata da abinda yafaWa

"Baby yara na nan fa?"
"Ni ba ruwana da wasu yara" yafaWa yana mikewa tsaye, kallonta yayi da runan nun idanunsa da suka fara canza launi, lumshe su yake a hankali yana buWe su akanta, bayansa tabi ganin ya nufi Wakinsa, yaran ma suka bi su, cak suka tsaya daga bakin kofar Wakin Mustyn sanda Mustapha ya shiga

"Amma, Abie ya shige bai bamu sweet Win ba, kuma kin hanamu shiga Wakin sa" haWa yaran tayi gaba Waya ta rungume su, dai dai nan Musty yafito da alawa da coculate yabawa kowa
"Mungode Abie Allah yakara arziki" yaran suka haWa baki suka faWa gaba Waya

"Amin maza ku wuce wajan Gwaggo ta Sare maku sweet Win" da gudu mazan suka tafi, Islam ta makale jikin Aimanah tana yamutsa fuska
"Ammi na wuce kije kinji bazan jima ba, Abie zan sa yayi barci ya huta yanzu zan zo wajanki" sakin Amman tata tayi ta tafi tana waigenta, Mustapha jawo Aimanah yayi suka faWa Wakin
"Baby ka fiye rigima fisabilillahi da tsakar ranar nan"
"Aimah bazaki gane ba" yafaWa sanda suka faWa gado, ta buWi baki zatai magana ya haWe bakinsa da nata yafara aika mata da zafafan sakonni masu wuyar karSa=ض?
@&?

Sumayya basu shigo Abuja ba sai dare hakan yasa bata sami damar aiwatar da aikinta ba ta bari sai washe gari, ai kuwa washe gari sai dare kana Mustapha yadawo yariga da yafaWa mata, tun yamma ta gama haWa komai har lemun daya sha maganin da malam yabata ta jere komai bisa danning jiran dawowarsa kawai take, bai shigo gidanba sai bayan sallar insha yana shigowa Wakin yara yafara shiga ya duba su kamar yanda ya saba, cake ya basu sunata murna sannan ya fito Aimanah na zaune a falon tana aiki a systam Winta, ya tsaya Wan nesa da ita kaWan

"Sannu da dawowa Baby"
"Sannu fa, ya kike ya gida da yara?"
"Alhamdulillah gida lafiya" gaba yayi ya shiga Wakinsa yai wanka ya shurya cikin jallabiya marun kana ya shiga Wakin Sumayya dake kwance tana chat dasu lina,
"Sannu da zuwa"
"Yawwa"
"Muje ko abinci na danning" jerawa sukai zuwa wajan damning area Win yana cin abincin a hankali yana satar kallon Aimanah dake can nesa da su ta dukufa tana danna systam da alama aiki take mai mihimmanci, murmushi Sumayya tayi sanda taga yakai cup Win lemu bakinsa, nan take yaji kansa ya wani sara masa, yai lu zai faWi, Sumayya ta tallafo sa kamar wani mai jin barci ta gaban Aimanah suka zo suka wuce Sumayya na rike da shi, maimakon ta kaisa Wakinsa saita shiga da shi Wakinta ta kwantar da shi kan gadonta tana murmushi ganin yanda yai lamo kamar mara lafiya,

Rawa tayi tai juyi ganin aikin ta yayi kamar yanda malam ya shaida mata, tana kallon yanda yake barci, malam ya tabbatar mata Wannan barcin idan yayi sa to yana farkawa zai manta da kowa, komai sai tace yayi sannan zaiyin, aiko hakance ta faru da asuba ya farka sai dai ji yayi jikinsa ya masa nauyi ya kasa ta shi, sai da Sumayya ta ce
"Kaje kayi sallah" kana yasami kwarin gwiwar mikewa yai alwala yatafi masallaci, ko acan wani iri yarinka ji Allah Allah yake a idar da sallar ya dawo gida yaga Sumayya

A ranar gwaggo fulani tasami labarin rasuwar babbar yarta tafiya ba shiri lokacin Mustapha na barci Wakin Sumayya, ta kira wayarsa yafi a kirga bata shiga haka yasa tai Kncking na kofar Sumayya, lekowa Sumayya tayi tana kallon Aimanah a wulakance
"Barka da safiya Sumy, dan Allah ki faWawa Baby Anma Gwaggo rasuwa zata wuce kano"
"Barci yake kuma yace kada a tashe sa" Sumayya nagama faWar haka ta maida kofarta ta rufe tabar Aimanh baki buWe, jiyowa tayi tana kallon gwaggo daketa rusar kuka Salman na lallashinta
"Salman zaka iya tuki zuwa kano?" Aimanah tafaWa a sanyaye
"Bazan iya ba Anty bana cikin nutsuwa"
"Shiryawa gwaggo kayanta, saina kaiku tasha" Aimanah da kanta takai su Tasha ta biya masu mota shata ta Waukar masu sukai ciniki ta biya kuWin motar, gefe sukayi da Salman ta basa Atm card Winta
"Salman karike wannan a hannunka dan Allah duk wata harka ta kuWi inta taso ayi amfani da kuWin ciki suna da yawa nasan zasu isa komai daga anyi bakwai ka dawo sabida makarantarka Gwaggo kuma ta zauna in mukazo kano nida Baby sai muje mu tawo da ita zuwa sannan ta gama amsar gaisuwa, motar har Wanbatta zata kaiku na biyasa kuWin sa"
"To Anty Mun gode Allah yasaka da alkhairi" Salman yafaWa yana share hawaye
"Kadaina kuka Salman ka lallashi gwaggo Allah ya mata rahama ya raya abinda tabari"
"Amin" yafaWa tana kallonsa ya shiga motar suka tafi tana Wagawa gwaggo hannu, sai da taga futarsu daga tashan kana ta shiga tata motar taja itama ta tafi gida,

Aimanah canji tagani daga Mustapha daya zama ko kallon inda take bayayi bare kuma yaran, kwanaki huWu kenan ko gaida sa tayi baya amsawa kullum yana Wakin Sumayya daga yadawo a office ya shiga bazai sake futowa ba sai safiya, ko abinci Sumayya bata bari yaci nan falo sai dai a Wakinta, tunda gwaggo ta tafi bataje aiki ba daman gwaggo take bari da yaran yanzu kuma bata nan, yau ta tarawa dawowar Mustapha haka yasa ta zauna nan falo tana jin tsayuwar motarsa ta fita compound Win da sauri dai dai zai shigo ita kuma zata fita, gefe tayi ganin yana kokarin ture ta, ta tsaya gefe
"Yaya Mustapha yaya zanyi da yaran nan inason zuwa wajan aiki fa"
"Kiyi duk yanda zakiyi da su, ke kada ma ki kara fita wannan aikin naki, and dan Allah ki rinka nesa dani banason ganinki" cak ta tsaya tana kallon Mustapha dake faWar maganar nan cikeda mamaki, Sumayya dake tsaye jikin kofarta dariya ta saki tana tafa hannuwa kamar wata sabon kamu, hannun Mustapha taja suka faWa Wakinta, Aimanah bata gama shan mamaki ba sai washe gari da Sumayya ta risketa a Wakinta lokacin ta idar da sallar asuba kenan tana azkhair na safiya,
"Mustapha yace ki wanke masa motar sa, sannan ya ce nagaya maki duk wani aikin gidan nan daga yau ke zaki rinka yi kama da gyara compound wanke motocin gidan nan bawa fulawowi ruwa dan na sallami mai kula da fulawoyin jiya" Aimanah a fusace ta mike tana kallon Sumayya sama da kasa
"Kije ki gaya masa bazanyi ba, ba aiki nazoyi gidan nan ba, ke Sumayya ki fita a idanuna miji ne kin janye sa nabar maki ki ji?a abinki ki sha amma ki sani kinyi tsararo wallahi kisa na maki bauta a cikin gidan aure na" Aimanah na gama faWar haka ta fice daga Wakin zuwa kichin ta Worawa yara abin break, wayam taga store Win babu komai, afusace ta fito ta banka kofar Wakin Sumayya ta shiga, Mustapha na zaune gefan gado yadafe kansa da'alama da abinda ke damunsa,

"Malama ina kika kai mana kayan abincin cikin store" Aimanah tafaWa tana kallon tsakiyar idanun Sumayya
"Shi yace na kwashe su ana masa Sarnar Abinci"
"Mustapha kai kafaWi haka?" Aimanah ta tambayesa tana kallon sa, kai kurum yaWaga alamar e
"Fine" Aimanah ta faWa tana ficewa daga Wakin, yaranta ta Wiba suka fita babban store ta je tayo siyayya sosai ta jibge su a babban kicin Win dake comopound nan take komai nata daga ta gama tasa key ta rufe ta koma Wakinta, Sumayya bayan Mustapha ya fita Waki ta koma tasa key ta kira lambar malam da fina ta bata bayan sun gaisa take masa bayani kan Aimanah
"Ranka yadaWe malam yarinyar nan fa sam bata tsorona in na bata umarni bata yi, Wazu fa kawai dan nace ta wanke mana motocin gidan nan baka ga yanda tayo kaina ba kamar zata dake ni"
"Sumayya yarinyar tanada hatsari banajin zan iya komai a kanta sabida a tsaye take kan ibada da azkhar amma zan duba inga ta inda zamu Sullo mata"
"Yawwa malam ka duba Win dan Allah nasan dai ai babu abinda ya gagare ka" shekewa da dariya malam kibauu yayi kana ya kashe wayar sa.

Murjana kuka sosai take tana kallon Amarya dake zaune da wata yaloluwar doguwar rigar barci da alama bata jima da tashi a barci ba
"Mama banajin daWin ganinki da nake a wannan gidan da aka maida tsaSon Allah ado a cikinsa, Mama dan Allah kizo muje ki bawa Abbanmu hakuri yamaidaki Wakinki, inma bazaki koma gidan ba ki koma katsina gaban iyayanki please mama, abinda yakamata ace mu mukeyi kina mana faWa shi kike yi mama" Mirja tafaWa cikin matsanancin kuka

"Murja ki fita sabagata kin riga kin girma kinyi hankalin kanki ki zaSi rayuwar dazakiyi nima na zaSi tawa, ca nake nan nazo maki da zaSi na kika nuna ban isa ba kika zaSi wanda ranki yake so, kije ki zauna da shi, yanda bana zuwa inda kike nima dan Allah ki nesanta kanki dani, basu Saudatu kika maida iyayanki ba to kije na bar masu ke"
"Mama...Murja ki fita nace kafin na saSa maki" murja mikewa tayi ta futa tana kuka, motar Alhaji Jamil dake jiranta a kofar gidan ta buWe ta shiga ta zauna a mazauni gaba tana ci gaba da kukanta,
Ahankali Alhaji Jamil ke tuki har cikin ransa yake jin kukan da Murja keyi hakan yasa ya faka motarsa gefan hanya ya kashe ta yai shuru yana sauraron shashshekar kukan Murja
"Murjana dan Allah ki daina kukan nan, nasan dai akan mama taki amincewa ta koma gidan Abba ne, kiyi shuru kuka baya maganin damuwa kiyi addu'a itace maganin duk wata masifa" Kai kurum ta Waga alamar to kana ta Wago fuskarta tana share hawayanta da hijab Winta
"Haba ko kefa, jibi yanda kika Sata min kyakkyawar fuskar nan taki" Murmushi Murja tayi tana daWa jin son mijinta can kasan zuciyarta, Alhaji Jamil tukinsa yaci gaba jefi jefi yana kallon Murja, tausayi take basa sosai, ganin yanda batai dacan uwa ba, a zaman da yayi da ita ya fuskanci tanada saukin hali rashin dace da mahaifiyar kwarai da batayi ba shiya jefa ta ga rayuwar bariki wacce ta dalilinta har tayi rashin mahaifarta, yana matukar tausaya mata musamman ganin yanda take matukar kulawa da yaransa uku gaba Waya komai nasu itace tun sanda ya aureta kulawarsu gaba Waya ta dawo kanta musamman in suna kasar, daman Mamansu ba wani kulawa take da su ba aikin ta da kasuwancinta su kawai tasa a gaba nanny ke kula da su da ita suka saba sai bayan zuwan Murja suka san daWin uwa.

Abbas ya shafi cikin Rumana mai watanni biyar, yana murmushi
"Kana son cikin nan dayawa Hayatie"
"Sosai nake son sa, karo na farko ciki ya kai wata biyar a mahaifarki insha Allah wannan zai zo duniya"
"Allah yasa Hayatie, ni duk bansa rai ba kawai ji nake a kowanne lokaci zamu iya rasa sa kamar yanda muka rasa guda uku a baya"
"Ki daina faWar haka dan Allah masoyiya insha Allah zamu ga ?a?anmu harma da jikoki"
"Anya kuwa, kasan yanda nakeji kuwa ni kaWai nasan azabar da nake sha gani nake kamar mutuwa zanyi hayatie" Rumana ta faWa tana fashewa da kuka, gaba Waya hankalin Abbas yatashi ya rungumota jikinsa ahankali yana share mata hawaye
"Ki daina ambaton mutuwar nan Rumy ki daina bana so, in kika ci gaba wata rana zakisa zuciyata ta buga na rigaki barin duniyar, zuciyata zullo take aduk sanda kika ambaci mutuwa, muna tare ni dake zamu rayu tare zamu mutu tare Insha Allah rana Waya lokaci Waya zamu mutu amma ba yanzu ba" yafaWa yana sumbatar kumatunta.

Sumayya malam waya yayi mata akan tazo ga aikinta ya gama ta karSa, hakan yasa washe gari ta Wauki hanyar enugu, a jirgi taje shiyasa bata wani Sata lokaci ba tana zuwa tsaunin da malam yake tahau kamar yanda sukayi wancan zuwa wannan karan ma hakan tayi malam wata koshashshiyar mage ya wullo mata ta cafe
"Kishiyarki nada hatsari sosai, indai wani abu zamiyi mata bazai taSa kamata ba, sai dai na biyo mata ta bayan gidan, wannan magen da kike gani kisata a karkashin gadonki kar ki bata abinci ba ruwanki da ita, ga wannan" yasake wulla mata garin magani a cikin kwalba
"Ki jika shi ki sha, sanda zaki sha ki ambaci sunan kishiyar taki zata rinka jin tsoronki kuma duk umarnin da kika bata zata bi, hhhhhhh gida ya zama naki yarinya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login