Showing 69001 words to 72000 words out of 95991 words

Chapter 24 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5384

abinda kikewa kishiyarki yayi yawa tunda kin riga kin farraka tsakaninta da mijinki ki barta mana ta huta gara ma kisa ya rubuta mata takardar saki ta bar maki gidanki ki huta"
"Gane min hanya dai Faty da sanda muka tallata mata abin nan kamar ta kirki sai da muka sha fama ta amince mukaje enugu amma yanzu harta zarta mu wajan mugunta"
"Sumy dan Allah ki maido da yarinyar nan wajan nan canfa ba daWi kinsan yanda wajan nan yake ga yara" ca Win da kawayan Sumy sukai mata shiyasa ta sa Aimanah ta dawo Wakinta itada yaranta, Lina har Waki tabi Aimanah ta taya ta gyara Wakin

"Ammi karfe biyu na rana ta shigo Abuja, Abas yaje ya Wakkota, Rumana tana ganin Ammi da Abbas tasha jinin jikinta musamman irin kallo da taga Ammin na mata ko zama batayi ba tafar aikawa Rumana faWa Ammi ba baya ba wajan faWa da musamman inka Sata mata rai, Rumana jikinta yayi sanyi da faWan da Ammi ta mata sai sannan taga wautarta shekarunsu huWu da aure sanan ta haihu yanzu kuma ga wata kyautar daga Allah cikin kan kanin lokaci amma tana neman bin hudubar sheWan ta butulce ma Allah, tana kuka sosai tabawa Ammi hakuri sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nnan ta nemi Abbas daya yafe mata, da kyar ta lallashi Ammi ta zauna taci abinci ta umarci Abbas daya kaita gidan Aimanah su gaisa ba zama zatayi ba jirgin karfe huWu zata bi ta koma kano,
Aimanah na tsaye tana mooping anan falo aka turo kofa aka shigo, tsallan murna tayi tana Wane Ammi gaba Waya yaran sukayo kanta suna ihun ganin Ammi, Ammi zama tayi kan kujera tana kafe Aimanah da idanu ko gaisuwar da Aimanah take mata bata amsa ba saima tambayya data aikawa Aimanah
"Aimanah lafiyarki kalau kuwa naga kunyi rama gaba Wayanku keda yaran?" murmushin yake tayi batace komai ba tai kasa da idanunta hawaye na zubo mata ta buWi baki zata gayawa Ammi halin da suke ciki amma ta kasa bakinta ya mata nauyi maimakon ta faWi abinda ke cikin zuciyarta sai taji bakinta ya furta saSanin abinda ke zuciyarta ahankali ta ce
"Ammi muna lafiya kalau, munyi fama da zazzaSi ne gaba Wayanmu musamman Islam" Ammi dake rungume da Islam tana shafa kanta ta ce
"Gidan shuru Sumayya bata nan? daman nasan Mustapha yanzu yana office jiya ya kirani mun gaisa ya gaya min abubuwa suka masa yawa shiyasa kwana biyu bakuje kano ba" Kai kurum Aimanah ta Waga zuciyarta fal zulumi da tunani yanda zatayi da Ammi tun jiya da yamma Mustapha da Sumayya suka fita basu dawo ba sumayya ta kulle store suma Maman Hanif ke aiko masu da abinci, mikewa tayi ta shiga Wakinta jiki na rawa ta kira Maman Hanif ta gaya mata Ammi tazo,
"Gani nan zuwa" maman hanif tace Aimanah ta fito falo wajan Ammi da suke magana da yaran, Maman Hanif ta shigo da katon hijab Winta fuskarta da murmushi suka gaisa da Ammi, Ammin na tambayarta yara
"Maman Aslam baki kawo wa Ammi abinci ba"
"Nama manta gaba Waya Wokin ganinta ya mantar dani ana kawowa bako abinci da ruwa"
"Bari to nashiga kicin Win na Wora mata ko macaroni ne"
"A'a Maman Hanif bazan ci komai ba adai kawo min lemu da ruwa amma na koshi da abincin nan naci gidan Rumana" maman Hanif ta shiga kicin mintina kaWan ta fito hannunta Wauke da plate mai Wauke da goran ruwa dana lemu, lumshe idanu Aimanah tayi tana jin wani sanyi a zuciyarta
"Ammi gashi, kinga Aimanah duk ta rame jinya tayi sosai har kwana biyu mukayi a hospital Musty ya hana a sanar maku kada hankalinku yata shi" Ammi na murmushi ta ce
"Allah ya kara lafiya" har sannan idanunta nakan Aimanah kamar mai irga kashin wuyan ta, mamaki matuka take na ramar da Aimanah tayi tabbas yazama dole ta bincika mai ya saka Aimanah haka wannan rama ko kusa ko alama bata yarda Aimanah jinya tayi ba, tadaifi zaton akwai abinda Aimanah da Maman Hanif suke Soye mata, bata wani jima can ba sanin Abas na waje yana jiranta yasa ta mike
"Zan tafi Aimanah idan abokiyat zamanki tazo ki gaidata da mai gidan" har bakin get Aimanah ta mata rakiya
"Aimanah ga Abbas can ki fito ku gaisa" Aimanah nasa kafarta a bakin kofa taji kamar wacce aka saka mata shoking na nepa da sauri tayi baya har tana shirin faWuwa
"Subhanallah sannu bi ahankali Aimanah" Ammi tafaWa cikin kulawa
"Ammi ki gaida gida bazan iya zuwa mu gaisa da Abbas ba" da sauri ta juya zuwa ciki sabida har sannan bataji jikinta ya koma dai dai ba, saman kujera ta zauna jikinta na rawa sosai ji take ana sake Waure mata jiki wata kara ta saki bata sake sanin inda kanta yake ba....
' [2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da uku*

Sumayya dake tsugunne gaban malam, baya tayi zata faWi ganin Aimanah ta bayyana a gabanta gata nan muraran kwance kan kujera kamar mai rai kamar mara numfashi, ga Maman Hanif nan a gefanta tana faman mata fifita,
"Ran Malam yadaWe ban gane ba, kar dai kace min ta mutu?" Sumayya ta tambaya hankali tashe
"Hhhhhhhhhhhhh, bata mutu ba, saura kiris saura kiris aikinki ya tarwatse yau, wacece wannan?" malam yafaWa yana nuna mata wani kasko dake gabansa Ammi ce ta bayyana zaune cikin jirgi,
"Su ru ka ta ce" Sumayya ta faWa a rarrabe, Ammi gyara zamanta tayi cikin jirgin tareda Wago da hannunta ta fara tasbihi, wani feshin wuta ne yata shi daya kusa kama fuskar Sumayya data kurawa Ammi idanu
"Zata Sata mana aiki wannan matar tanada karfin ibada bata inda zamu ci galaba a kanta, tabar gidanki da kudurin binciko abinda yasa kishiyarki da yaranta rama ko mai zai iya tarwatsewa aduk randa ta sake shigowa gidanki"
"Malam ayi wani abin dan Alah, bana so na rasa wannan damar so nake na rayu a haka har karshan numfashi na"
"Wiiiiihuuuuuuuhuuuuuu, zamuyi zamuyi zamuyiiiiiiii" yafaWa da wani irin ihun dayasa Sumayya yin baya sosai da shi
"Nasa Aljani dundurusu yayi komai, zaki biya mu kuWin aikin mu sannan aljani Wan jani zai biya bukatarsa da ke," zaro idanu Sumayya tayi tsoro yasake mamaye zuciyarta aljani kuma yanzu aljani ne zai biya bukatarsa da ita, bata gama tunanin ba taji kamar ana shafarta bata sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa tayi ta ganta kwance a Wakinta, wani tsalle ta buga tareda sakin ihu, dai dai nan Aimanah ta saki wani numfashi Maman Hanif ta ce
"Alhamdulillah Allah mun gode maka, sannu Aimanah"
"Yawwa" Aimanah tace a sanyaye, gaba Wayansu tsorata sukayi sanda sukaga Sumayya da rabonta da gidan tun jiya fitowa tayi daga Wakinta, cikeda mamaki Maman Hanif ke kallon Sumayya ita dai tana nan falon tun sanda Aimanah ta suma bata bar falon ba bare ta ce anan Sumayya ta shigo amma abin mamaki sai gata daga Wakinta, mintina kaWan kuma sai ga shigowar motar Mustapha
"Sannu maman Aslam ya kike jin jikin"
"Da sauki sai dai kaina ji nake kamar ba nawa ba"
"Sannu shima zai daina kici gaba da ambaton Allah" sallama Maman Hanif taiwa Aimanah ta fita, Aimanah ma Wakinta ta shiga sai dai ko zama batayi ba sai ga Sumayya a Wakin, tsaye tayi jikin kofa tana girgiza jiki
"Kizo ki wankewa Mijina mota" haka kawai tafaWa ta fita daga Wakin, jikin Aimanah yana rawa tabi bayan ta sabida wani tsananin tsoronta da ta ji ya kara shigarta fiye dana da, motar tayi datti sosai jikin tayar motar futu futu da jar kasar da alama motar wajan gari akaje da ita, tanayi tana haki ga sanyin ruwa haka ta gama abinda bata taSa yi ba, tanayi tana goge hawayen takaici, Sumayya na gefe ta kafa kujera tana kallon Aimanah tana mata dariya da wake waken habaici,
Aimanah data koma dakinta kuka ta sha sosai daran ranar batai barci ba raya daran tayi da nafiloli tana kuka tana gayawa Allah halin datake ciki, washe gari sarai ta tashi zuciyarta fes har wani nishaWi take ji, kasancewar da azumin nafila ranar ta ta shi, abincin da Maman Hanif ta aiko masu da shi gaba Waya taba yaran suka cinye duka matukar tausayin yaran take zuwa yanzu yaci ace suna aji suna Waukar darasi amma ga yanda rayuwa tayi da su hakan yasa ta bada kaimi wajan addu'ar Allah yafitar da ita daga wannan hali datake ciki, wayar hannunta ma Sumayya ta karSe ta a gabanta ta bugata da kasa sabida kawai ta ganta suna waya da maman hanif.

GIDAN MURJA
Alhaji Jamil da yaransa uku Jannart Labiba da Ansar zaune bisa danning, yayinda Murjana keta zuruftu daga kicin zuwa danning area Win sai da ta gama ajje komai kana ta zauna, kallon yaran tayi da murmushi a fuskarta ta ce
"Baza kumin sannu ba" lokaci Waya suka haWa baki suna faWin
"Momy sannu da aiki" dariya tayi tana kallon Alhajin daya ke Sata fuska kamar wani karamin yaro
"Kaifa Man wani bin in kana abu sai kace Ansar" ta faWa da murya kasa kasa,
"Inajin yunwa sosai, yau banci abinci a kasuwa ba" da sauri taja plate ta soma zuba masa abincin farar shinkafa ce sai farar doya da miya, sai haWin salad gabansa ta ajje plate tana faWin
"Bisimillah" kansa ya Wora saman kafaWarta murya kasa kasa ya ce
"Nifa ke zaki bani"
"Yara na nan fa" itama ta faWa a hankali
"Ki basu nasu su wuce wajan mamansu suci acan"
"Kasandai ba sakewa zasuyi a can ba ga nanny bata nan kawai dai ka daure kici da kanka" mikewa yayi zai bar wajan tasa hannu ta ruko sa
"Jannart zubawa kowa abinci a plate kuci" ga lemu nan kowa ya Wau wanda yake so amma Ansar kar abasa mai sanyi" taSe fuska Ansar yayi kamar zaiyi kuka murja taja kumatunsa tana murmushi ta Wauki plate Win data zubawa Alhaji abinci suka zauna can falo ahankali take basa abinci a baki yanata zuba mata shagwaSa kamar wani karamin yaro, saida ta tabbatar ya ishe sa sannan taci kaWan, ta koma wajan yaran data soma jiyo hayaniyar su
"To yaya ne, zaku fara faWan ko?"
"Momy Ansar ne fa wai sai ya sha lemu mai sanyi kuma kin hana abasa sabida yana mura"
"Naji ku wuce to Jannart ki tabbatar kin tayasu sunyi homework ke kinga munyi naki Wazu in kun gama ku kwanta barci zan shigo Wakin kowa yayi addu'a ku kuma kunna karatu a mp na Wakin ku kisa bakara" kai Jannart ta Waga alamar to har sun soma tafiya suka jiyo suna mata bye bye Ansar da gudu yadawo ya rungumeta ya sumbaci kuncinta ya ce
"Goodnight Mom" Murmushi Murjana tayi tana kallon yaron da yayi gaba da gudu, hawayan dake zuba a kuncinta taji ana share mata ko tantama batayi ba tasan Alhaji Jamil ne hakan yasa ta faWa jikinsa ta fashe da kuka
"Shikenan banda rabon ganin Wana a duniya shi kenan bazan sami soyayyar da yara ke wa uwarsu ba? shikenan bazan taSa haihuwa ba har abada? bazan sami Wan da zai kula dani ba bayan na tsufa, kaicona kaicona nayi nadama Allah na tuba ka yafemin, Allah kabani hakuri da juriyar cin wannan jarabawar da kamin ya Allah" sosai take kuka mai taSa zuciya, Alhaji Jamil ma hawaye ya share yana buga bayanta a hankali alamar lallashi
"Yi shuru Wife dan Allah ki daina kukan nan gasu Ansar nan insha Allah zasu maki dukkan wani abu da Wa kewa uwa" bata tsaya sauraron saba taci kukanta ta koshi yanata aikin lallashi, sai da tai shuru suka wuce Wakinsa har sunyi shirin kwanciya ya ce
"Mako guda ya rage fa tafiyarmu India"
"Bazani ba, ka tina yanda akayi a tafiyarmu indunusia irin tashin hankalin da akayi da matarka dan haka wannan karon ka tafi da ita ni ina nan zan kula da yara" wani kallo yamata kana ya ce
"Bazani da itan ba, dake naga damar tafiya kuma da ke zan tafi" jiki sanyaye Murjana ta kalli Alhaji daya kwanta ya juya mata baya agogo ta kalla taga tara saura minti biyar na dare
"Gaskiyya Abban Ansar ba haka ake ba, yanda na sani in anyi tafiya da wannan in wata tafiyar tazo da waccan za'a tafi sai dai in ita tace ta yafe a tafi da wata" afusace ya mike yaja hannun Murjana zuwa sashin Rahila, kofar ya buWe a fusace falon shuru ba kowa hakan yabasa damar buWe kofar bedroom Winta, abinda yagani ya masifar Waga masa hankali bama shi kaWai ba har Murjana wacce ta zaro idanu tana salati, salatin da Murjana tayi shiya dawo da Rahila da Hanne hayyacinsu da sauri suka ja bargo suka rufa, Rahila na zare idanu ganin Alhaji Jamil tsaye kamar wani sakago ya saki baki yana kallon su da kyar ya iya saita kansa ya ce
"Daman abinda kike aikatawa kenan shiyasa kike tara mata a gidana, kike kin bina wani waje ina can na saki baki ashe ke ga abinda kike aikatawa, kin cuci kanki Rahila keda Allah kin aikata babban zunubi Rahila kije dan kanki na sake ki saki uku bake ba yarana na haramta miki su har abada ki nesa da gidan nan ki nemi inda zaki" juyawa yayi ya fita yanajin sa wani saroro kamar iska zata Waga sa sama, kuka ya sha sosai daran ranar, Murjana ko Wakinsa bata koma ba Wakinta ta koma itama ta sha nata kukan takaicin wannan zamanin da mata suka lalace,
Rahila sanda Alhaji Jamil ya furta mata kalmar saki ba karamin tashin hankali ta shiga ba fiye dana ganinta da yayi kwance da wata hakan yasa ta fashe da kuka, shikenan ta kare mata ina zata iyayanta gaba Waya sun rusu da gidan Alhaji jamil ta dogara sai kuma aikin datake wanda bata wani tara abin arziki ba
"Ki daina kukan nan dama ma yabaki yanda zaki sakata ki wala kiyi harka yanda ranki ya ke so munada kungiya ta mata yan less zamu saka ki a ciki zaki samu kuWaWe sosai zaki fantama mota sai wacce ranki yakeso akwai alhazan birni zaki iya auran Waya daga ciki wanda shi ba mace bace a gabansa shima yanada tasa harkar a gabansa ma zaki iya yin duk abinda ranki yaso da mace bazai ce maki komai ba si dai kawai yayi aure ne dan kada a zargesa in anga yana zaune ba aure, gobe ne ma zamuyi taronmu na shekara a kaduna ki zo mu tafi gidana inada mata kala kala acan da suke zaune" Rahila mikewa tayi ta sitirta jikinta ko wanka ba wanda yayi haka suka bursuna kaya suka fita a gidan a motar Rahilan,
Amarya rai ta Sata ganin Hajiya Hanne data ce mata taje jigawa sai gobe zata dawo, amma sai gata yanzu da tsohon daran nan harda guzurin wata matar
"Daman wai ba jigawar kika tafi ba?"
"Naje daga can ma nasamo mana wannan"
"Ko dai kikaje wajanta ba, waton ni kin barni a nan kika ajje ni kin hanani holewa da kowa kince ni taki ce ke kuma kina bin wasu, nan haka da mukaje habuja gidan Sumayya daga ganin wata sai da kika bita kika kwana da ita, to gaskiyya nima fita zan na hole yanda raina ke so"
"zaki iya yin hakan ai" Hanne tafaWa tareda jan hannun Rahila sukai sama, saroro amarya tabisu da kallon mamaki can kuma tayi kwafa ta koma Wakinta,

Lumshe ido yayi tareda buWesu lokaci Waya ya saki murmushi, ya buWe kofofin hancinsa yana jin kamshin kasar sa da ya kwashe shekaru biyar cif baya cikinta ahankali kamar baya so ya ce
"Nayi kewarki kasata, ina son kasata" zama yayi zaman jiran jirgin da zai kaisa tashi nan da minti arba'in da biyar zuwa kano
"Yaya Aimah" yafaWa a hankali sake kallon agogon da ke Waure a tsintsiyar hannunsa yayi still dai yanada saura mintina arba'in da uku kafin tashin jirgin da zai kaisa kano, mikewa yayi ya saSa jakarsa a baya ya gyara zaman sun glass Win dake idanunsa ya fito zuwa waje inda masu texzii suke,
"Barka da safiya Baba" Shaheed yafaWa sanda yakarasa gaban wani tsoho mai texzii
"Barka dai Wana an sauka lafiya, ina zan ajje ka" faWa masa sunan unguwar da Mustapha da Aimanah ke zaune yayi kana bayan ya shiga gaban motar mutumin har ya fara tafiya Shaheed ya ce
"Baba zamu iya zuwa nan da minti talatin mu dawo airport jirgin kano zanbi na karasa gida"
"Zamu iya duk da akwai yar tazara amma inba daWewa zakiyi ba a wajan har ma dawo bari na kara gudun motar" kwantar da kansa yayi saman seat na motar kamar wani mai barci, haka kawai yaji gabansa na faWuwa yayinda suka kusa zuwa unguwar ya buWe idanunsa da suka soma canza kala
"Yaya Aimah" yafaWa a hankali,
"Munzo ranka ya daWe" Baice komai ba ya buWe murfin motar ya fita yana kallon tangameman gidan dayake zaton nan ne inda yazo, jakar sa ya ajje a bayan motar yana kallon mutumin mai tasi ya ce
"Baba bari na shiga bazan jima ba yanzu zan fito gidan yayata ne gaisawa kawai zamuyi"
"Afito lafiya" sa kai yayi zai shiga get man ya tare basa kofa
"Daga ina"
"Daga gidan uwarka, dalla gyara ka bani waje na shige kasan koni waye a gidan nan zaka tare min hanya," hannu yasa ya wurgasa can gefe ya shiga ciki yana huci
Aimanah na rike da Islam wacce ke kukan yunwa yau yini biyu kenan basu saka komai a bakinsu ba, bata san ya akai ba Maman Hanif jiya da yau duka bata shigo ba gashi ita kuma ba waya a hannunta, sallamar da taji yasata Wago da sauri ta kalli wanda ke shigowa
"Shaheed" ta faWa a hankali yayinda idanunta ke kawo ruwan hawaye, da sauri ya karaso ya tsaya a kanta can kuma ya zube kan kafafunsa yana kallo Yayar tasa ba ko kiftawa
"Yaya Aimah kece kece kuwa lafiyarki kalau cuta kika yi da kikai wannan ramar ina Yah Musty"
"Shaheed abinci, yaran nan yunwa suke ji rabonsu da abinci tun jiya da safe" bai tsaya tambayar ba'asi ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login