Showing 12001 words to 15000 words out of 95991 words

Chapter 5 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5378

saura minti goma baki dawo gida ba"

"Ina gidan Ana fa Mah ce tagayamin na sauka acan inna dawo" Aimanah ta faWi haka tana turo baki gaba, tanajin sanda ya yi ajjiyar zuciya sannan ya ce

"Mai yasa baki gayamin ba kinsa sai zarya nake daga nan zuwa bakin titi"

"Yi hakuri Yaya mantawa nayi, yanzuma zamu tawo gida" tafaWi haka ganin su Mahh sun fito daga Wakin Ana gaba Wayansu fuskarsu ba annuri, sosai idanun Ammi sukayi ja alamun taci kuka ta koshi,katse kiran tayi ganin su Ammi sun nufi kofa, gaba Waya sukayiwa Ana sallama ko wanne ya shiga motarsa yaja, Aimanah tana tsaye jikin motar Mahh tana kallon inda Mah da Ana suke tsaye da alamar wata maganar suke tattaunawa sun jima suna magana kafin sukayi sallama, suka shiga mota zuwa gida.


*Gidan Mustapha*

Jiki sanyaye Mustapha yake haWa kayansu a trolly, yau karfe bakwai nadare jirginsu zai tashi zuwa India shida Sumayya, wacce yanzu take gefansa tana kwance tana aikin nata na danna waya, shi kuma yana haWa masu kaya nasa da nata,Wagowa tayi ta kallesa akayi katari da shima ita yake kallo da sauri yai kasa da kansa, hakanan yarasa dalili baya iya haWa idanu da Sumayya wani tsoronta yakeji sosai, dariya Sumayya tayi sai kuma can tayi shiru tana kallon sama tunani take a zuciyarta, na yazatayi duk ranar da asirin da akayiwa Mustapha ya karye, tasan makomarta saki ne, tunda shidai daman ba sonta yake ba itace ke sonsa har Amarya ta shiga ta fita ta samo kansa akayi aure, a baya Mustapha ko kallo bata ishesa ba, ta tina zuwanta na farko garin kano wajan mahaifiyarta.

Sumayya Habibu haifaffiyar garin katsina ce, itace ?a Waya tilo wajan mahaifinta Malam Habibu, Naja mahaifiyar Sumayya ta auri Habibu tun auren saurayi da budurwa suna matukar son juna Malam Habib alkacin da sukayi aure Wan kasuwa ne a jahar Katsina lokacin kasuwa na damawa da shi yanada arzikinsa, Amarya na nuna masa so da kauna sosai musamman daya sakar mata tana wadaka da kuWi son ranta daga ita sai ?arta ba ruwanra da dangin miji na kusa dana nesa, lokaci Waya Malam Habibu ya samu karayar arziki sakamakon kayansa da costom suka kama, aka shiga aka fita amma basu saki kayan ba, rayuwa ta soma canzawa a gidan Malam Habibu, kullum Amarya tana cikin mita da tsangwamar Habibu daga karshe ma tace bazata iya zaman talauci ba ya saketa tayi gaba tasami mai kuWi ta aura, badan yaso ba dole yasaki Naja duk da tsannin son dayake mata, lokacin Sumayya na ajin farko na sakandire, suka dawo gidan iyayan Amarya waWanda suma ba karfin ne dasu ba, rayuwarta take son ranta abinda taga dama take ba wanda ya isa yai mata magana Amarya tariga ta raina iyayanta bata wani Waukar maganarsu, shekara Waya da rabuwa da Habibu ta haWu da Alhaji Kamal ba Sata lokaci akayi bikinsu, daga farko Sumayya a wajan iyayan Amarya take zaune harta kammala scoundry, daga baya ta dawo wajan Amarya taci gaba da karatu, bata wani maida hankali akan karatun ba hakan yasa take yawan maimaita aji, daga karshe ma ta watsar da karatun, wata rana tana tsaka da shara a gidan taji gida ya karaWe da ihun murnar dawowar Babban Wan Alhaji Kamal Mustapha wanda kallo Waya datayi masa ta kamu da so ajje tsintsiyar hannunta tayi tanabin Mustapha da kallo ganin yanda yake rungume kannansa maza da mata har Murjana ya haWa duka ya rungume, sosai yamasu tsaraba ko alawa bai bawa Sumayya ba wacce ko kallo bata ishesa ba, baya kasar lokacin da Abbansa ya auri Amarya ama yanada labarinta da irin rashin mutumcin datake zubawa duka Anty Halima na gaya masa komai Halima itace babbar yayarsu Wiya ga Momy uwar gidan Alhaji kamal, shiyasa baya shiga sabgar Amarya yanadai gaidata duk safiya, yauma kamar kullum bayan ya gama gaida Ammi ya shiga ya gaida Momy sannan ya shiga Wakin Amarya, daga tsaye a bakin kofa kamar yanda yasaba ya tsaya yana gaida ta, ko kaWan bata wani sakar masa fuska hakan yasa yana gama gaidata yasaki labulan Wakin yayi gaba zuwa Wakin Alhaji Kamal, a can Wakin Amarya bayan sakin labulan Mustapha, Sumayya ta kalli mahaifiyarya tayi kasa da ki ta ce
"Mama gayan nan yana burgeni, amma shi na lura bana gabansa ko gaidasa fa nayi da kyar yake amsawa"
"Hmm" Amarya taja ajjiyar zuciya kana ta ce "Sumayya nima nayi maki sha'awar auran Mustapha, inada buruka akansa saidai ke gani nake kamar bazaki iya aikin ba"
"Mama Allah inason sa kuma zan iya yin komai indai zan auri Mustapha" Sumayya ta faWi haka tana haWa hannayanta alamar roko=?O?daga lokacin Amarya tafara masu garin maganin data Wakko daga jaka "yace dole sai an zubawa Mustapha wannan a ruwa ko lemu yasha"
"Mama wannan ba wani abin damuwa bane, wani sa'in yana bani indafa masa indomie zan haWa masa da lemu"
"Yawwa ?ar gari ina yinki Murja kanki yana ja" a ranar kuwa saiga Mustapha ya shigo gidan yana matukar jin yunwa Wakin Momy ya shiga yana neman Surayya ta dafa masa Indimie lokacin Sumayya bata nan taje gidan Anty Halima, Wakin Amarya ya shiga ya kira murjana yace ta dafa masa indomie ta kawo masa Wakinsa, Sumayya ce ta tayata suka dafa Indomie Win harda lemun Genger daya sha garin magani takai masa har Waki godiya yayi mata sosai sanda ta nuna masa lemun Genger tana gaya masa ita ta haWa masa, daga lokacin daya sha lemun nan gaba Waya ya birkice kan Sumayya har takai anyi auransu, daga nan suka Wora da masa banke bankan maganin asiri a abincinsa da abun shansa.

Sumayya taja ajjiyar zuciya hakanan taji jikinta yayi mugun sanyi, batasan ma Mustapha yafita daga Wakin ba saida taga yadawo Wakin da jaka a hannunsa yana kallon time shida saura minti huWu

"Sumayya taso mu tafi ga Mas'ud can yazo shi zai kaimu airport" batace masa komai ba ta zari mayafinta tabi bayansa, kofar motar yabuWe mata ta shiga shi kuma ya shiga gaba, Mas'ud yaja motar mai gadi ya buWe masu get suka fita, har sun Wan gota gidan Ammi Mas'ud yaja yai parking yana kallon Mustapha "Kayiwa Ammi sallama kuwa"? kai kurum Mustapha yaWaga alamar A'a, Mas'ud yafita daga motar ya zagayo ya buWewa Mustapha murfin mota yaja hannunsa ya fito da shi, Mas'ud ya kalli Sumayya ya ce "Sorry Madam bari Musty yayiwa Ammi sallama bazai bar kasar nan ba basa albarkar Ammi" bai jira amsarta ba yaja hannun Musty suka shige gidan, Ammi tana karatun kur'ani taga shigowar su Mas'ud kallo Waya tayiwa Mustapha ta Wauke kanta a gabanta suka tsugunna Mas'ud ya ce
"Ammi ga Mustapha na kawo maki kisa masa albarka zai tafi india"
"To Mustapha Allah yataimaka ya tsare hanya yabada abinda akaje nema"
"Ameen" Mas'ud yace yana kallon Mustapha da yayi shiru yakasa cewa komai yama lura jikinsa sai karkarwa yake, hannunsa yaja zasu fita har sunje bakin kofa Mustapha ya cire hannunsa daga na Mas'ud yadawo wajan Ammi rungumeta yayi na ?an sakonni kana ya sumbaci kuncinta baice komai ba yafita, Ammi ta shafi wajan da Mustapha ya sumbata tana murmushi ta sumbaci hannun data shafi wajan "Allah ya kuSuto min dakai Musty" tafaWa tana share hawayan dasuka zubo mata, Mas'ud suna zaune a recepsion jefi jefi suna Wan taSa hira da Musty har sanda aka fara kiran mutane su shiga jirgi, Mustapha ya rungume Mas'ud hawaye na zuba daga idanunsa "Aboki zan tafi kamin addu'a ko yaushe ina jin kirjina yanamin zafi kamar ana huramin wuta a ciki"
"Kana cikin addu'o'ina Musty Allah ya tsare kamaida hankali kan cost Win nan kasan ka kammala shi zaka sami karin girma a bank Winku kilama a canza maka wajan aiki ga wannan" Mas'ud yafaWa yana mika masa littafin Hislum muslim "Kayawaita karantawa a ko yaushe musamman zikirin safiya da maraice"
"Insha Allah" Mustapha yafaWa bayan ya karSi littafin, Mas'ud yana tsaye bai bar wajan ba saida yaga tashin jirginsu.

Aimanah wanka ta Wauro alwala bayan ta shirya cikin doguwar rigar barci ta zura babban hijab Winta na sallah ta kabbara sallah, raka'a biyu tayi ta idar ta fara addu'ar istikara, ta gama tsab ta Wora da wasu addu'o'in ta gama ta kwanta a gado, agogo ta kallah taga karfe 10:45pm murmushi tayi ta kira lambar Abas, bugun farko ya amsa kiran kamar daman zaman jiran kiran yake
"Nayi fushi masoyi shine yau gaba Waya baka kirani ba ba tex Win daka saba yimin"
"Allahu akubar!" Abas yafaWa yana tsalle shi Waya a Waki "Sake faWa Hayatie da gaske kike dan Allah daga bakinki wannan maganar ta futo?"
"Daga bakina ta fito ba wasa, Kalbie nariga da amince da soyayyarka tun safe nake jira ka kirani nayi maka wannan albishir Win sai kuma kaki kira" Aimanah tafaWi haka tana turo baki gaba kamar tana gabansa
"Oh Sorry hayatie Moh ne ya hanani kira wai nabari ki kirani da kanki"
"Au ai ban sani ba da nima bazan kira ba saina ja ajina" tana gama faWar haka bata jira yayi magana ba ta katse kiran, tana kallon kiransa taki Wagawa addu'ar kwanciya barci tayi ta juyawa wayarta baya wacce tana jin kira nata shigowa daga wannan ya katse wancan yashigo....
'
07039793439
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Takwas*

Abas ya kasa zaune ya kasa tsaye ganin abin yake kamar a mafarki,daina kiranta yayi ganin taki Waga kiran ya kira Joshua cikin barci Joshua yaWaga kiran Abas bai saurari abinda Joshua ke cewa ba ya ce "Zan sami jirgin da zai tashi zuwa kano yanzu?"

"Sir kano yanzu? dare yayi ba jirgin zuwa kano yanzu sai bakwai na safe"

"Asaimin tiket shida kazo ka kaini airport"

"Ok Sir" messages ne yashigo wayarsa hannunsa na rawa ya buWe tex Win
_Kalbie ka kwanta kayi barcin, bazan Waga kiranka ba sai safiya, fi Amanillah_ yaji daWin tex Win nan sosai ya karanta sa ba adadi kwanciya yayi kan gadon kafafunsa a kasa, Idanunsa na kallon P o p Win Wakin, ya lankwasa hannayansa ya Wora kansa akai, wani irin bugawa Numfashinsa keyi, da sauri ya Wauki wayarsa ya dannawa Hajiyarsa kira, Hajiya wacce ke kwance jikin mijinta gabanta har faWuwa yayi jin ring na waya ahankali ta mike zata bar jikin mujinta, hannu yasa yadawo da ita jikinsa ya rungumeta yasa Waya hannun ya Wakko mata wayar,
"Abas" Hajiya tafaWa hankalinta tashe ta Waga wayar "Hajiya Aimanah ta amince dani yanzun nan ta kirani"
"Abas shine zaka kirani da daran nan da nayi barci fa"
"Hajiya bani da wanda zan raba farin cikin nan da shi kin sani sai ke, da inada kanwa ko kani tabbas su zan kira a daran nan" tausayin Abas ya rufe ta ta kakalo murmushi tareda kokarin Soye halinda take ciki ta ce
"Nayi farin ciki Abas Allah yasa albarka ka turomin lambar ta zan kirata da safe, amma kadaina kirana a irin wannan lokacin kasan dai lokacin Abbanka ne" dariya Abas yayi ya katse kiran, tareda sake kiran lambar Aimanah, Aimanah wacce barci ya fara Waukarta firgigit ta farka jin karar wayarta
"Wo Abas" Aimanah ta faWa tana lumshe idanu, ta maida kanta ta kwanta karar shigowar tex bayan kiran ya katse yasa ta Wauki wayar tasan ba tantama Abas ne _Hayatie ki Wagamin kira inaso naji muryarki nayi barci mai daWi Inba haka ba zan tawo kano yanzu_
"Hmmm Abas" tafaWa ta kashe wayar gaba Waya ta maida kanta ta kwanta.

Ammi cikin barci taji wayarta na kara alamar kira, buWe idanunta tayi ta janyo wayar bata tsaya duba ko waye ba ta Waga kiran
"Ammi barci kike ki tashi mu raya daran nan kinsan matsalar da muke ciki"
"To Mah nagode" Mah bata sake magana ba ta ajje wayar kan daddumar data ke kai taci gaba da jan carbinta Istingifari tayi guda Wari ra Wora da salatin annabi kana ta fara jero addu'a wacce gaba Waya kan Mustapha Allah ya fitar dashi daga halin dayake ciki, acan gidan Ammi ma alwalan tayi ta tada salllah haka mahaifiyarsu Ana itama sosai ta raya daran da sallah haWeda addu'o'i, Aimanah washe gari bayan tayi sallar asuba barci ta koma bata tashi ba sai bakwai da rabi, cikin mintuna da basufi talatin ba tayi wanka, yau kasancewar garin antashi da sanyi yasa ta sanya riga ja da bakin wando ta Wora doguwar rigar sanyi wacce tazo mata har gwiwarta tasa hula da karamin hijab daya sakko ya rufe kirjinta, da sauri ta fito ganin har takwas ta gota al'adar gidance karfe takwas ake zaman breakfast, kamar jiya yau ma kowa ya rigata zuwa wajan banda Daddy da jiya ya tafi legos sai Mah da taga bata fito ba, gaba Waya tayi masu jam'i da ina kwananku, tare suka amsa tamaida hankali wajan cin abincin saboda yau da yunwa ta tashi, Yah Mus'af na lura da ita na yanda yau ta zage tana cin abinci sosai abinda suka daWe basu gani ba tun sanda ta shiga kuncin rabuwa da Mustapha, wayarta ta kunna kamar jira ake kira ya shigo, dafe kai tayi ganin Abas ne mai kiran, kamar bazata Waga ba sai kuma ta Waga batace komai ba

"Barka da safiya abincin ruhi na"
"Hmmm Barka dai! ya kake" Aimanah mikewa tayi zata bar wajan ganin gaba Waya yayun nata sun zuba mata idanu suna kallonta musamman ma Mas'ud wanda yakasa jurewa sai da yabiyo ta har Wakinta lokacin ta gama wayada Abas
"Ke dawa kike waya?" Mas'ud ya watso mata tambaya yana tsareta da idanu
"Uhmmm ummm Abas ne"
"Waye Abas?"koma wane ki gaya masa an maki miji" da sauri ta Wago ta kallesa batace komai ba saboda maganar Mus'af da taji daga bayan yaya Mas'ud wanda bata sanma yana Wakin ba, yana tsaye jikin kofa ya Wora hannunsa Waya saman kofa Wayan kuma ya rike kugunsa dashi
"Yah Mas'ud waye yayi mata miji?"
"Kai mai kake anan?"
"Yaya ba wannan ba tambayya nayi"
"Ni nayi mata" Mas'ud yafaWa a zafafe, Mus'af yayi dariya har ya juya zai fita daga Wakin sai kuma ya dawo yana kallon Mas'ud ya ce
"Yaya nasani kana taya abokinka kishi ne, amma kasani yanzu ba Mustapha a zuciyar Aimanah, haka ba wanda zai mata dole anan dan haka ka zuba idanu kawai Aimanah ta sami mijin aure wanda yafi Mustapha" Mus'af yana gama faWa yasa kai ya fice daga Wakin Mas'ud yabi bayansa a zafafe, hayaniya suka fara yi wanda yasa Mahh ta fito daga Wakinta tana kallonsu
"Yau kuma yarinta za'amin a gidan nan" Mah tafaWa tana kallon yaran nata da basu san ta fito ba daga Wakinta,
"Mah ni yaron nan zai tsaya yana gayawa magana, na lura yaron nan shiyake so ya cusawa Aimanah soyayyar wani ba Mustapha"
"To Mas'ud ina Mustaphan yake yanzu zama zamuyi tayi da ita muna kallonta har Mustapha yadawo, ba wannan maganar kabar Aimanah ta so wanda zuciyarya ke so, koda Aimanah har yanzu Mustapha take so bazan yadda ba na kaita gidansa wanda bazata tsinci komai ba a gidan sai tarin wahala kishi da Sumayya ka zaSa mata, kana kallon halin da ake ciki amma kake kokarin kare soyayyar Mustapha karna sake jin hayaniya a tsakaninku kan wannan maganar, kai Mus'af bawa Mas'ud hakuri kuma karna sake jin sa'insa a tsakaninku koba akan wannan maganar ba" Mus'af yabawa Mas'ud hakuri yai gaba abinsa
"Kayi hakuri bawai na goyi bayan Mus'af bane kasan dalili na"
"Na fahimta" Mas'ud yafaWa yana mai wucewa Sangaran su ransa ba daWi tabbas da yana da dama saiya Waurawa Mustapha aure da Aimanah saboda yasan duk randa Musty yadawo Mustaphansa akwai matsala in Aimanah ta?i sa, Mah ta kalli Mus'af daya koma wajan daya tashi yaci gaba da cin abincin sa
"Karage zafin zuciyar nan taka Mus'af"
"Insha Allah zan rage" Mus'af yafaWi haka yana cigaba da cin abincinsa,
"Gobe ka shirya zaka kaini ?anbatta"
"Mah inada tiyata fa"
"Kullum tiyanta bata tashi sai anyi maganar zuwa ?auye, Mus'af bafa a raina asali"
"Mah bana gudun ?auye kawai banaso ne naje ayita kallona kamar sunga sabuwar halitta" Ma'aruf yayi dariya sosai wacce tasa har Mah dake tsaye saida ta dara ya ce "Mah Yaya fa bazai kaiki ba kibari ni zan kaiki gobe sunday bazan shiga kasuwa ba, inama Gwaggo Rakiyya zata birgeni data haWa auranka da Ummita"
"Allah ya isa tsakani na dakai" Mus'af yafaWa tareda ture plate Win abincin dake gabansa, Mah dariya take sosai, yanda Mus'af yawani zazzaro idanu shi yafi bata dariya
"Ai kuwa ka kawo shawara haka za'ayi bari Daddy yadawo" Mus'af cak ya tsaya daga tafiyar daya fara yi zai bar wajan Mahh dan Allah kar muyi haka dake karma maganar nan taje wajan Daddy shifa Waukar maganar zaiyi da gaske ina ni ina wata Ummita mai zanyi da kazamar yarinyar nan"
"Kai dai kake mata kallon kazama" Ma'aruf yafaWa yana cigaba da dariya
"A'a Yah Ma'aruf kodai kodai"
"Kodai mai karma ki karasa bar maganarki anan kafin na faWo maki sunan naki masoyin Amadu" Aimanah dariya tayi sosai kamar zata faWo kasa daga saman kujera "Kasan Allah banakin Yaya Amadu kawai banason kaunar sa ne da ace ina kaunarsa zan iya auransa maye a cikin zaman kauyan wani bin fa sun fimu kwanciyar hankali, kuma ma ai birninka aljihunka" Mah bata sake ce masu komai ba taci gaba da dariyar Mus'af wanda tini yabar wajan,wayar Aimanah ce tayi kara ta kalli screen na wayar tana murmushi ganin Abas ne.

Akwana atashi yau Aimanah da Abas sun kwashe watanni tare da Abas soyayya suke sosai kamat baza'a mutu ba=??kusan ko yaushe suna jone a waya duk karshan sati yana kano, tun Hajiyarsa na mita harta zuba masa idanu,

Yauma kamar ko yaushe suna tare ta masa rakiya zai wuce Jigawa, Aimana ta gyara tsawarta jikin motar Abas tana kallon yanda yake tsara mata kalamai wanda take jinsu kamar a film, ba shine saurayinta na farko ba amma yanzu kam zata iya cewa ba kowa a zuciyarta samada Abbas, lumshe idanu tayi tareda buWe su akan kyakyawar fuskar Abbas wanda yai kuri yana kallonta, "Abbas ina sonka sosai, zuciyata bugawa take akowanne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login