Showing 66001 words to 69000 words out of 95991 words

Chapter 23 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5403

Dr Win dake duba su ta kira a waya yazo suka shiga wajan su Aimanah tare....
'


[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da biyu*

Dr yakalli Aimanah cikeda damuwa yace "Garin yaya akayi sake haka har olsa maleria da typoid suka kama wannan yar karamar yarinyar da bata haura shekaru huWu ba" Aimanah ta share hawayen takaici tama kasa cewa komai ido kawai ta zubawa Dr Win
"Dr lalura ce kawai Allah ya saukar mata ayi duk abinda yadace yanzun" Maman Hanif tafaWawa Dr Win, Drip dr yasawa Islam yace a kula sosai da hannun bari yaje ya Wakko allurai da magunguna yadawo, Maman Hanif ta dafa kafaWun Aimana da hawayan fuskarta suka ki tsayawa
"Dan Allah kibar kuka Aimanah, komai na Allah yanada iyaka insha Allah komai zai wuce ku dawo normal rayuwarku mai daWi irin tada koma fiyeda haka" Aimana fashewa tayi da matsanancin kuka tana kallon Maman Hanif
"Nagama auran Mustapha addu'a nake yasakane ni na kama gabana maman Hanif aure ma gaba Waya bazan sake ba, aikina zanci gaba da yi na rungumi yarana shi kuma yaje su karata da Sumy ko kashe sa tayi ita ta jiyo"
"Daina faWar haka Aimanah ba rabuwa tsakaninki da Mustapha insha Allah" lamo Aimanah tayi ta zauna kamar wata karamar yarinya xuciyarta na mata wani irin zafi

Ammi

"Abba kuna waya da Mustapha kuwa?" Ammi dake haWawa Abba cofee ta tambayesa idanunta nakan abinda take haWawa
"Muna waya ko yauma munyi Wazu ina kasuwa ya kirani mun gaisa yace abubuwa ne suka masa yawa shiyasa bai shigo kano ba kwana biyu" kai Ammi ta gyaWa kawai bata kara cewa komai ba, sai can ta nisa kana ta ce
"Inaso naje Abujan naga yaran nan"
"A wanne dalili? bazaki je ba, daga nan har abuja kawai dan kiga yara"
"Alhaji ka..."
"Na gama magana Saudat bazaki ba, za'ayi hutun karshan shekara kinsan kuma nan suke hutun ko wanne shekara, kamar yau ne fa" shuru Ammi tayi bata sake ce masa komai ba taci gaba da abinda takeyi, haka kurum inta tina Aimanah sai gabanta yai wata irin faWuwa, hakan yasa ta yawaita kiran Aimanah a waya suna gaisawa kusan duk safiya saita kirata, tana tambayarta suna lafiya takan amsa mata da suna nan kalau hakan yasa hankalinta ya kwanta sai kawai take binsu da addu'a,

SUMAYYA
Cigaba tayi da jin daWinta a gidan Mustapha nan da nan tai kiba ta zama katuwa masha Allah, Mustapha ko albashi ya Wauka gaba Waya yake Webo su yazo ya juyewa Sumayya su tayi abinda ranta ke so, wani dankareran gini ta sa Mustapha yafara a kano can Wan bare, gida ne na alfarma wanda taciwa buru daga an kammala ginin kano zata dawo taci gaba da zama, gidanta ya zama gidan mata kawayanta take tarawa na makaranta azo aci abinda rai keso wasuma har suyi guzuri banza ta faWi, gidan ne gaba Waya ya hautsine da hayaniya yayin da wasu ke can gefe an kunna kiWa ana casu da alama wani shagalin suke, Hajiya Hanne ta kalli Amarya tana fari da idanu take faWin
"Anya kuwa kin gane kwatamcan gidan nan da yarinyar ta maki?"
"Haba na gane mana inaga wannan kwanar zamu sha" Amarya ta faWa tana nunawa Hanne dake tuka motar kwanar da zasu yi, motoci birjik a kofar gidan da Amarya take tunanin shine na yarta Sumayya kamar yanda Murjana ta masu kwatance, kai tsaye scurity yabasu damar wucewa ganinsu gwagaggun wayayyun mata har wani risina masu yake yana kwasar gaisuwa ganin da ya masu jibga jifga da su daga gani nera ta zauna, Amarya saida gabanta yafaWi ganin Sumayya cikin mata tana tikar rawa, zuciyarta tai wani tsalle kamar zata fasa kirjinta ta fito, saurin karasawa tayi ta katse kiWan ganin yanda gaba Waya basu san an shigo ba hankalinsu nakan rawar da suke anata rungume rungume, leena ta kalli Amarya tana yamutsa fuska
"Yada haka ne hajiya zaki zo ki rage mana jin daWinmu"
"Ke! mamana ce" Sumayya ta katse lina da sauri tana karasowa gaban mama ta ruko hannunta ta mata mazauni nan kan kujera, Hajiya Hanne wani kallo tabi Leena da shi tana latsar leSe, Mama na ankare da ita hakan yasa ta Sata fuska sosai ta hau sumayya da faWan ta tara mata a gida anata rawa maye hakan kamar a kauye,
"Mama kawaye na ne fa na school murna suke tayani na cikar wani buri nawa"
"To su bamu wari" mikewa sukai yayin da Hanne ke magana da lina ta idanu dan ta lura itama yar hannu ce, gidan tsit yayi daga Sumayya mama sai ko Hanne
"Naji gidan yayi shuru kuma ina kishiyar taki da yaran nata naji ance ta haifi yan uku ko?" Sumayya gyara zama tayi tana kallon Maman nata ta fara bata labarin abinda tayiwa Aimanah
"Da kyau Sumayya gado ba karambani ba, ko ke fa har kin wanke min zuciyata da bakin takaicin danake ciki na waccan yarinyar Murja, naji daWin wannan lamari, amma a ina wannan bokan yake da kin kaimu munje mun gansa kan wasu bukatu namu"
"Mama bafa boka bane malam ne"
"Duk kanwar ja ce Sumayya yaushe zaki rakamu"
"Mama sai dai gobe yau yamma tayi kuma kinga akwai j
nisa idam muka tafi yanzu ba lalle muje yau bama"
"Yau da goben ai duk Waya ne Sumy Allah ya nuna mana" Hanne kallon Amarya tayi
"Nan zaki zauna ne ko tare zamu koma hotal"
"Ki koma kawai ni ina nan goben dai ki fito da wuri sai mu wuce saura kuma ki nemi wata idan kikai haka ban yafe ba" dariya Hanne tayi ta fita batace komai ba, Hanne na fita ta hau dube dube kamar mai neman abu, ji tayi an rungumeta ta baya ana shafarta jiyowa tayi sukai ido huWu da Leena dake wani karairaya tana juya idanu
"Hotal zamuje ko kinada gidan da zamu je"
"Muje gidana mijina baya nan yara ma duka sun tafi tare garinsu"
"Yawwa naji daWin hakan" A motar hanne suka tafi daman Lina batazo da mota ba tare sukazo a motar feenah, finar kuma ta wuce,
"Mama wai har yanzu kina tareda matar nan baki koma katsina ba, mama kibar harkar nan kiyi aure kawai"
"Aure a wannan lamarin Sumayya nadai kusa barin harkar nan zan tuba ga Allah na koma gaban iyaye na na kama kasuwanci ni yanzu maza basa gabana ko sha'awa ma basa bani, wai wanna yarinyar mai tsayayyun idanuwa ina kika samota"
"Wa kenan?" Sumayya ta faWa tana dariya, Amarya kwatanta mata ita ta hau yi nan take Sumayya ta gano Lina Mama ke nufi
"Ki bita a hankali, na fuskance ta yar maWigo ce"
"Mama" Sumayya ta faWa hannunta saman kirjinta alamar tashin hankali
"Tabbas gaskiyya na faWa maki yanzu haka bana Webe shakkun suna tare da Hanne dan naga sunyi magana da idanunsu basu zaci na gansu ba," gumi ne yafara zubowa Sumayya tana gogewa da hannunta wani iri take ji a zuciyarta nan take tsoron Lina ya shige ta dan ita kam matsoraciya ce musamman akan irin wannan harkar, tun adaran taWau aniyar zata ja baya da lina tabbas, Amarya anan gidan ta kwana washe gari sassafe suka Wau hanyar enugu.

Murjana tsaye tana kallon Alhaji Jamil dake zazzaga masifa kamar ba shi ba tun iya tsawon zamanta a gidan bata taSa ganin yana masifa irin haka ba, bata taSa zaton yanada zafi ba sai yau da Uwar gidanta ta taSo sa
"Dan Allah Abban Jannat kayi hakuri kuskure ne Maman Jannat ta riga tayi kuma tun farko da laifinka tunda kai kabata damar yin komai"
"Ke yarinya shiga hankalinki karki sake shiga maganar mata da miji"
"Rahila ki kiyaye ni ba ruwanki da yarinyar nan ke yanzu bakiji kunya ba, yaushe rabonki da zama ki kula da yaranki mai zaki iya faWa na halin yaranki tunda yarinyar nan ta shigo gidan nan gaba Waya kulawar yaran ta dawo kanta ko yaushe tana hidimarsu ke kuma kin maida kai wajan yawon koyarwar ki da tara mata da kike masu sarin kaya, to daga yau na soke karna sake ganin kafar ko wacce mata a gidana idan na kuma gani wallahi saina masifar saSa maki" yana gama faWar haka yasa kai ya koma sashin sa
"Kinyi nasara ki karawa bokanki kuWi yau Abban Jannat yamin abinda bai taSa yimin ba, zanyi maganinki ni nafiki tantiranci banbancinmu Waya ni ban taSa bin maza ba balle nayi cikin shegen da agarin cire sa na rasa mahaifa" Murjana da sauri ta Wago ta kalli kishiyar tata nan take kuka yazo mata najin abinda ta faWa da gudu ta wuce sashin mijinsu ta faWa gado ta fashe da kukan nadama, ina matar nan taji wannan labarin datake bunnewa bayan daga yayunta maza ba wanda yasani sai Alhaji Jamil kawai da ta faWawa jikin Murjana yai sanyi taji a ranta Alhaji Jamil shiya gayawa matar sa maganar, Alhaji Jamil daya fito daga wanka ya kalli Murjana dake matsanancin kuka tuwul Win hannunsa ya ajje ya zauna kusada ita ya Wago ta ya haWa ta da jikinsa
"Murja maiya faru maiya saki kukan nan?"
"Zaka ce haka mana tunda ka kwashe sirrina ka gayawa matarka sirrin dakasan ina matukar Soye sa"
"Maina gaya mata ni ban taSa gaya mata komai ba ki yarda dani yaushe ma na zauna da ita da har zan gaya mata wata magana"
"Zakace bakai ka gaya mata anciremin mahaifa ba sannadin aborsion"
"Zan iya rantse maki da Allah bani na gaya mata ba, amma zo muje ki ji gaskiyya daga bakinta" hannunta ya ruko suka je har Sangaran Maman jannart, Alhaji Jamil ya kalli maman Jannart kallon da Murjana ta kasa gano kona mene, shin naso ne ko kuma na gargaWi
"Ki faWi tsakaninki da Allah Rahila nina faWa maki wannan maganar" dariyar shakiyanci Rahila tayi tana kallon cikin idanun Mijin nasu ta ce
"Alhaji so kake na karyata kaina a gaban yarinya nace karya nayi, nan nan kazo kana faWamin kawai zaka auri murja ne sabida hutawa aiba haihuwa take ba mahaifarma an cire ta sakamakon cikin shegen da tayi aka zubar har kace na saki raina Murja zuwa zatayi ta tayani rainon ?a'?a na tunda ita batada mahaifar da zata Wauki cikima bare harta haihu kai nawa ne daga ni sai yarana harka manta ranar kenan?" Murja kuma rushewa tayi da kuka ta fice, Sangaranta ta koma ta ci gaba da kuka, Alhaji Jamil kasa motsi yayi daga inda yake zaune yana kallon Rahila da har sannan dariya take kamar wacce tasami matsalar kwakwalwa
"Rahila ni kika yiwa sharri? yau she mukayi haka dake?"
"Sam bamuyi haka da kai ba, nayi ne danna Sata maka kuma ba'a wajanka naji wannan labarin ba a duniya na jiyo" numfashi Jamil ya sauke sannan yasami kwarin gwiwar barin Wakin ya koma nasa ya gyara jikinsa sannan ya shiga Sangaran Murjana barci take da alama tana kukan barci Sarawo ya yi gaba da ita, sumbatarta yayi kana yasa kai yafita daga gidan zuwa kasuwa, Murjana fushi ta Wauka sosai da Alhaji ranar ko girki batayi ba kamar yanda tasaba takan bawa driver na gidan yakai masa kasuwa, Alhaji Jamil ma ganin time na kawo abinci ya wuce ba'a kawo ba yasa ya kira ta a waya lokacin futowarta kenan daga wanka tana ganin kiran harya katse bata Waga ba sabida ta shaka da yawa da abinda ya mata tagama sawa a zyciyarta inya dawo zata nemi ya sawwake mata ta kama gabanta tayi nisa da gari can tayi wani auran inda baza a san maita aikata a baya ba, zuciyarta ce ta kuma rauni hawaye ta soma sharewa tana sake nadamar abinda ta aikata a baya taci gaba da istigifari da jin tsananin tsanar mahaifiyarta Amarya da Salim da kuma ruWi da kuruwar sheWan da tabi yanzu gashi ta kaita kogin nadama, shikenan ita batada rabon ganin Wanta shikenan ita da haihuwa sai dai ta gani anayi, Jannart ce ta shigo tana gudu waya kange a kunnan ta
"Momy ga Abba yace na kawo maki waya zakuyi magana"
"Bar nan Jannart fita bana son ganinki bazan amshi wayar ba bazan amsa ba Win" tafaWa tareda fashewa da kuka
"Abba Momy taki karSar wayar kuka ma take yi" Jannart ta faWa tana tsaye daga inda take, Alhaji Jamil katse kiran yayi ko Jannart bata gaya masa ba yariga yaji kukan nata hakan yasa ya mike yabaro kasuwar zuwa gida, Jannart kasa futa tayi jiki sanyaye ta karaso kusa da Murjana ta tsugunna
"Momy mai aka maki kike kuka kiyi hakuri ki shuru mom"
"Jannart fita! ki fita kafin na saSa maki" Jannart yarinya yar shekara goma yarinya mai hankali da nutsuwa komai nata a nutse take yi cikin sanyi ta ce
"Mom vazan iya fita na barki kina kuka ba, muma fa kin hanamu kuka kina mana duk abinda muke so mom ta yaya zan futa na barki kina kuka" Murja Wagowa tayi ta kalli yarinya ta ruko hannunta taci gaba da kukanta, a haka Alhaji Jamil ya shigo yasame su ya kalli Jannart yabata umarnin ta fita ta futa kuwa tana waigan Momy Winsu
"Murja wai baki daina kukan nan ba har yanzu dan Allah kibar kuka haka"
"Bazan bari ba, nace bazan daina ba, ka sakeni Jamil kasake ni naje na auri wani wanda baisan sirrina ba bare ya gayawa matarsa sirrina, nayi nadama nai nadamar auranka da nayi"
"Ni kuma banyi nadama ba bazan kuma taSa nadamar auranki da nai ba, a yanzu ko anan gaba kowa da kaddararsa Murja ni ban taSa gayawa Rahila magana makamancin haka ba ke maca ce kinsan tuggu da kissa irin taku ta mata, tabbas ita rahila ta maki sabida tana bakin cikin zaman lafiyar da muke da ke, kima Wauka ana faWa mata na yarda na faWa Win duk da nasan ban faWa ba amma na karSi laifin indai zuciyarki zata yi fari kiyi hakuri, bana son Sacin ranki sarauniyata haka my zumata yi murmushi mana" Murjana Soye fuskarta tayi a kirjin Alhaji Jamil tana murmushin kamar yanda ya umarce ta
"Ko kefa masoyiya idan irin haka ta faru tsakaninki da Maman Jannart ki nuna mata bakiji hau shi ba ki kuma daina kuka a gabanta zata raina ki" kai kurum Murjana ta Waga batace masa komai ba, kasuwar da bai koma ba kenan ya zauna faranta mata daga nan suka lula duniyar maji daWi=ض?
@&?

Abbas Home

Kuka take kasa kasa, yayin da Abbas ke rungume da Usaina yana jijjigata dan itama kukan take tsan yarawa, Hassan ne kwance cikin net Winsa yana wasa, kallo Waya yayiwa Rumana dake kuka ya Wauke kansa duk da kuwa har cikin zuciyarsa yake jin kukan, da kyar yasamu usaina ta daina kukan tai barci net Winta ya buWe yasata yana mata addu'ar kwanciya barci, sake kallon Rumana yayi data karo sautin kukan nata ya matso kusa da ita
"Yi shuru to naji za'a zubar da cikin amma nima zaki bani dama na kara aure na auro mai sona wacce bazata gaji ba wajan haifa min ya'ya"
"Nima ai ba gajiyawa nayi ba, kawai ina tausayin su twince ne duka duka watansu shida fa kuma ace ina Wauke da cikin wata uku ai da tausayi yaya za'ayi da su?"
"Amma ca nake a gabanki Dr yace ba damuwa indai za'a basu kulawa kuma za'abi dokoki a kiyaye su zasu kasance cikin koshin lafiya"
"Amma Hayatie duka nono na shekara Waya fa zasu sha kenan"
"To maye a ciki, Allah kawai ya raya su"
"Nidai wallahi bazan yarda ba yazama dole a zubar da cikin nan ko kana so ko baka so ni saina Sarar da shi" mikewa Abbas yayi yafita daga Wakin ransa Sace, wayar Ammi ya kira bayan sun gaisa ya Wanyi shuru kamar bazaice komai ba har sai da yaji Ammi na faWin
"Hello Abbas kana kan layi?"
"Ina nan Ammi, daman wata yar matsala ce ta taso Rumana ce batada lafiya, jiya munje hospital likita ya tabbatar mana tana Wauke da cikin wata uku, tun safe yau take ta kuka wai sai an zubar da cikin, na lallasheta taki ganewa yanzu tace ko ban yarda ba wallahi ita saita zubar da shi, Ammi inason haihuwa ni kaWai iyaye na suka haifa zanyi farin ciki idan naga nima na tara iyali da yawa"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ita Rumanar zata aikata wannan babban zunubin ina fatan kana gidan?" bata jira amsar saba taci gaba da maganarta "idan kana ciki ka zauna ko nan da can karka motsa ka saka mata idanu sosai ni kuma ka bani awanni uku zan shigo abujan bari nasa Ahmad yasai min ticket Allah yasa akwai jirgin da zai zo nan yanzu zan taho insha Allah ka kula sosai"
"Insha Allah Ammi amma dan Allah karki faWawa Anty kinsan yanzu taji labarin nan hankalinta zai ta shi ta Wagawa kowa hankali" Ammi dariya tayi kana ta ce
"Hasana kenan kaima kasan wannan halin nata, bazan gaya mata ba kaima kai shuru da maganar dan Allah ko hajiyarka karka faWawa"
"Insha Allah Ammi sai kinzo" juyawa yayi ya koma ciki yayin da ita kuma Ammi ta wuce sashin Alhaji Kamal wanda akai katari yana gidan bai futa kasuwa ba, bai mata musu ba sanda ta faWi abinda ke faruwa nan take yasa aka sai mata ticket na tafiya Abuja

AIMANAH
Islam taji sauki sosai ta murmure, bayan tasha allurai da magunguna yau Aimanah tun safe take aikin bauta sai Worawa da saukewa take na kawayan Sumayya da suka cika gidan ko wacce kuma da kalar abinda zata ce ayi mata, Lina duk wani motsin Aimanah idanunta na kai har zuwa yanzu da Aimanah ta kawo masu soyayyar taliyar data gama yanzu
"Kai nifa bazanci taliyar nan ba, inaga ko indomie za'a dafa min" feenah ta faWi haka tana kallon Aimanah wacce sam bata iya ko yi masu musu duk abinda suka ce aiwatarwa kawai take
"Ba wani indomie da zata dafa maki in bazaki ci wannan ba ki bar shi" Lina tafaWa a zafafe, feena wani kallo ta mata ta Wauke kai tana murmushi
"Ke Aimanah jeki ki huta kuma ki Webi yanda zai isheki keda yaran" juyuwa Aimanah tayi ta koma kicin Win
"Gaskiyya kawarmu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login