Showing 78001 words to 81000 words out of 95991 words

Chapter 27 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5382

ya saiwa Aimanah waya Infinix hot 50 pro, da sabon layin da yayi regester da kansa, lokacin daya dawo gaba Waya suna zauna a danning ana cin abincin dare
"Mom shine ba'a jira ni ba"
"Ina kuwa zamu jira ka Yasar, ka sani dai dokar Mom ce in lokacin cin abinci yayi ba a jiran wanda baya nan inya dawo ya ci shi kaWai"
"Ok naji, Ummu zubamin abinci kamar wanda zaki iya cinyewa" Dariya Aimanah tayi ta soma zuba masa abincin cikin sanyi jiki,
"Yawwa barshi haka ina zan kai wannan abincin in da ina cinye kamar wannan aida tuni nafi haka kiba, Mom dafa sai dai a kara girman kofar shugowa"
"Yasar ka barni naci abincina karna kware kai wai dole in kana waje sai kasa mutum dariya"
"Mom nafison kullum na rinka ganin fuskarku wasai ba damuwa" Mom dai batace masa kanzil ba harta gama cin abin cinta tsawon mintina suna nan zaune a wajan, Aimanah ita ta fara mikewa zata bar wajan, Yasar ya jawo ledar daya ajje kasan kujera ya mikewa Aimanah
"Ummu ga wayarki kamar yanda na faWa maki, ki buWe ta ki saita komai zamuyi waya cikin dare" hannu Aimanah tasa ta karSa tareda masa godiya,mikewa Mom tayi
"Mom gashi"
"Na gani Aimanah Allah yasa albarka"
"Ya Moh kaga yabani waya a tayani godiya"
"Dai dai Allah yasanya alkhairi
"Anty Ramla kinga" Aimanah ta faWa tana mika mata ledar, Antyn ce ta zaro wayar daga kwalinta ta buWe ita tasa mata screen gard Win da wayar tazo da shi, tasa sim ta kunna wayar kana tace taje ta sata a caji, Aimanah ta karSa ta juya zata bar wajan Azinatu taja tsaki tareda bangaje ta tabar wajan, Aimanah murmushi tayi kawai ta wuce Wakin Mom, Aimanah cikin barci taji wayar na kara, cikin magagi ta Waga kiran
"Ummu bakiyi barci ba" taji muryar Yasar ta doki kun nan ta, cikin magagin barci ta ce
"Barcin fa nake" dariya sosai Yasar yayi
"A barcin kike magana kenan? wastsake dan magana zamuyi dake ta fahimta"
"Yasar barci nake ji sosai mubar maganar sai da safe"
"Bazan iya ba Ummu, Kaunarki ta shige ni sosai tsoro nake kar nayi jinkiri wani ya rigani samun fili a zuciyarki"
"Filin zuciyata babu kowa a ciki Yasar sa Yasar, ba yanzu ba banan kusaba bance bazan kuma bawa wani fili a zuciyata ba amma dai ba yanzu ba" Wif ta katse kiran tareda saka wayar a jirgi ta maida kai ta kwanta, Ahankali ta furta
"MUSTY" share hawaye tayu tareda runtse idanunta hawaye naci gaba da fita,
Yasar naushin fulon daya ke kai yayi da karfi yana faWin
"Ya Allah" haWe da sakin numfashi, Moha gyara kwanciya yayi tareda buga tsaki
"Ka takuramin fa Yasar kazo kana waya murya kasa kasa kamar munafiki, yanzu kuma ka fara kai naushi," filon sa ya Wauka ya sauka daga gadon ya koma saman doguwar kujera yasa fulon ya kwanta yana mita
"Gara nayi nesa da kai kafin ka kai min duka" Yasar dariya kawai yayi baice komai ba shima ya mike ya shiga bathroom ya Wauro alwala yazo ya tada sallar nafila, bayan ya gama jero nafilfili daya saba yi duk dare yai addu'a, sannan ya mike ya sake kawo wata raka'a biyun yai addu'ar istikhara na neman zaSin Allah" yasake addu'o'i ya kalli agogo yaga huWu da kwata hakan yasa ya fita zuwa masallaci, can ya zauna yana karatun kur'ani har akayi sallar asuba yadawo gida shida Moha wanda yabisa masallacin bayan anyi kiran sallar asuba, yana ganin Muhd ya shiga Wakin Mom su gaisa shi kuma ya wuce zai kwanta yana cewa Moha
"Agaida min Mom sai nayi barcin safe zan zo mu gaisa kafin ku wuce kano"
"Ai dama ka zo kun gaisa Win a mota zamu tafi karfe bakwai zamu fita kaga sai kayi barcin sosai" juyowa Yasar yayi suka shiga Wakin tareda Muhd, Mom na bathroom Aimanah na zaune saman dadduma tana azkhair, sallamar da sukayi ta amsa ta Wago kai ta kallesu
"Yaya Moha barka da safiya anta shi lafiya"
"Lafiya kalau Aysha ya kika tashi"
"Aysha kuma yaya Aimanah dai, wannan babban sunane sunan mamata"
"Ummu ina kwana tunda ni baza'a gaida ni ba" Yasar yafaWa yana zama Wan nesa da ita kaWan,
"Ni na isa na ki gaida yayana, barka da tashi ya gajiyar hanya"
"Gajiya tabi lafiya Ummu," yaWan matsa kusa da ita ka Wan yana magana kasa kasa yayin da kan Aimanah ke cikin kafafuwanta fuskarta Wauke da murmushi har Mom ta fito daga bayi kallo Waya taiwa Yasar Win ta fita daga Wakin tana jin tausayin Wan nata yanda so yai masa mummunan kamu, a kicin ta tarar da Anty Ramla nata kokarin haWa abin kari dan ganin sun fita da wuri
"Sannu Ramla, Allah ya maki albarka yabaki yaran da zasu faranta maki fiye da yanda kike min Ramla"
"Amin Mom" Ramla ta faWa tana murmushi, kafin bakwai sun gama shiryawa zaman break kawai akai shima a gurguje akai dan ganin an fita da wuri, Ramla ta fito da jakar kayan Aimanah suka fita compound inda Moha ke cikin mota yana jiran fitowarsu, ahankali yake takowa har zuwa inda su Aimanah ke tsaye itada Mom
"Mom yanzu da ban fito ba tafiya zakuyi" Mom mota ta shiga bakinta Wauke da addu'ar abin hawa bata tankawa Yasar ba,
"Ummu dan Allah ki rike min alkawari insha Allah gobe zan zo kano muyi magana ta gaske"
"Sai kazo amma zaka iya auran bazawara mai ?a?a uku" zaro idanu Yasar yayi yana kallon Aimanah cikeda mamaki
"Wai dan Allah da gaske, nayi farin ciki daya kasance munada yara zan aureki a haka zan kuma haWa da yaranmu na rike ina maku fatan sauka lafiya"
"MOM Allah ya tsare hanya" yafaWa sanda ya leka kansa cikin motar"
"Yasar kana Sata mana lokaci fa, ance kazo a tafi da kai kace ba yau ba amma ka tsare mu da zance"
"Lafafa min Ya Moha a sauka lafiya" yafaWa yana rufe murfin motar yaja baya yana kallon Moha yaja motar suka fita daga gidan, gwauron numfashi yaja ya jima nan tsaye a wajan kana ya koma ciki ya koma barci, Tafiyar awanni biyar da wani abu yakawo su Aimanah garin kano ita ke nunawa Moha hanya bayan sun shigo kano har suka karasa gidansu dake gadon kaya,


SUMAYYA
Murmushi take ta dokawa sanda Dr ya basu sakamako tanada ciki na wata huWu wanda ita batayi zato ko tsammani ba
"Mustapha kaga kyautar da Allah ya mana" Musty baice komai ba, saima kallo dayabi Sumayya da shi ita da Dr suka gama maganganunsu suka taho gida bakin Sumayya yaki rufuwa sabifa murna, suna shiga gida Sumayya taga Lina da feenah a zaune cikin falon, turus tayi taja ta tsaya bakin kofa kamar bazata shigo ba sai kuma dai ta shigo ciki tana binsu da kallo
"Lafiya naganku yanzu ba sanarwa zaku zo"
"Da in zamu zo sanarwa muke ai, Sumayya abinda kika yi kinyi adalci kenan ki ce na tura maki vidio ashe ke da manufa kikai haka, to burinki ya cika mijin Lina yamata saki uku yanda ya saketa ya rabata da yaranta wallahi kema yau sai mijinki ya sake ki kila ma ke har sai an haWa maki da duka, yau zamu nuna maki mu yan asalin hau ne, sai kinga hau yau yasin" Feenah ta faWa tanayin gaba zuwa Wakin Sumayya, Lina tabi bayanta da sauri Sumayya ma ta rufa masu baya, Kayan Wakin suka fara watsi da shi harda kayan sawarta, Sumayya ta shako wuyan Lina ta shake duk yanda Feenah taso ta kwaceta ta kasa hakan yasa ta janyo karfan labule ta bugawa Sumayya zafin azabar daya ziyarci idanunta yasa ta hankaWa Feenah tayi baya sai gata ta faWa kan tukunyar tsafin Sumayya, wani bakin hayaki ne yatashi ya dunkule waje Waya yai sama ya saki kara da rugugi kamar na hadari, Feena da Lina da gudu suka fice daga Wakin dayake futar da tiriri
"Wayyo Allah na shiga uku ni Sumayya shikenan asiri ya tonu shikenan komai ya karye wayyo ni rayuwata, Feenah kun cuce ni nayi dana sanin saninku a rayuwata kun ruguza min komai" ta zube kan gwiwoyinta tana fashewa da kuka
Mustapha kamar wanda aka tasa daga barci haka ya mike firgigit daga kan gadon dayake kwance ya fito yana sake tina mummunan mafarki da yayi, tun da yafito daga Waki yake kwaWawa Aimanah kira
"Reina! Aimahh!! Aimah!!! wai ina kika shiga ne, Aslam Tasnim Islam Gwaggo Fulani ku fito mana dan Allah kuna ji ina kwaWa maku kira" turus yaja ya tsaya lokacin daya buWe kofar Wakin Aimanah da yayi kura sosai alamar anjima ba'a amfani da Wakin, da hanzari ya karasa Wakin yara ya buWe nan ma kamar na Aimanah ya haWa uwar kura harma tafi ta Wakin Aimanah, hankalinsa ne ya kuma tashi tuna mafarkin da yayi na wulakancin daya rinka yiwa Aimanah da yaranta bama abinda yafi Waga masa hankali kamar wai a mafarkin da yayi wai ya saki Aimanah" hankaWa kofar Wakin Sumayya yayi ya shiga, Sumayya idanunsa kawai ta kalla tagano tabbas asirinta fa ya riga ya tonu hakan yasa ta fara ja da baya ta haWa hannuwa waje Waya alamar roko
"Dan Allah kayi hakuri Mustapha son zuciya ne da bin ruWin kawaye yasa na aikata komai, na tuba na bika bazan sake yin asiri ba dan Allah kaje ka dawo da Aimanah zamu zauna lafiya ba faWa ba gaba wallahi ni zan rinka mata komai zan zama kamar baiwarta nidai fatana kawai ka zauna dani" dafe kansa yayi da yaji yana matukar sara masa ya rike kan da hannunsa yana ambaton Allah
"Wai Sumy mai kike faWa haka, kina nufin ba mafarki nayi ba, abubuwan da duk nagani a zahiri ne da gaske na saki Aimah na saki reina wai" Mustapha yafaWa hankali tashe yana matsowa kusa da Sumayya yayinda ita kuma take yin baya harta dangana da bango
"Ka gafarce ni Mustapha aikin asiri ne" wata shaka Mustapha ya kaiwa wuyan Sumayya yana ihu da faWin
"No wallahi no kar ya ne ni na saki Aimanah ina bazaiyu ba" shake wuyan yayi kamar zai kasheta idanunta suka firfito waje
"Sumayya na sake ki na sake ki na sake ki saki uku" yafaWa yana yin wurgi da ita ta faWa gefe tai suman wucin gadi, a guje kamar ta SaSSe ya fita daga Wakin yaje ya Wau wayarsa ya na dannawa Ammi kira

AIMANA
Tsabar kagauta da Wokin ganin ahalinta da gudu ta fita daga motar ko gama tsayawa motar W batayi ba, da gudu Ammi wacce ke gidan tun safe ta fito tazo ta rungume Aimanah suka fashe da kuka tare
"Sannu Aimanah sannu munyi kewarki munyi kuka na rashin ganinki da tunanin halinda kike ciki"
"Saudah wai maye haka kamar wata karamar yarinya kin wani rungumeta kuna kuka" Mah tafaWa sanda ta fito compound Win
"Barni nayi kuka Yaya Aysha baki san yanda naji ba barni na koka zuciyata ta sami salama" Mah amsar baki tayi ta masu jagora zuwa ciki kasancewar lokacin sallah yayi ko zama basuyi ba akai alwala Moha yabi Ma'aruf zuwa masallaci matan kuma sukai sallah nan cikin gidan Wakin Mah, sai da akai sallah sannan kuma aka shiga gaisawa duk a zaton Mom Ammi itace mahaifiyar Aimanah shiyasa kusan ita tarinka bawa hakuri kan abinda yafaru, Ammi wayarta ce tayi kara alamar kira na shigowa sai da gabanta yafaWi ganin Mustapha ne ke kira, tayi mamaki matuka dan rabon data ga kira irin haka tana tunanin tun kan rabuwarsa da Aimanah hakan yasa ta fita daga falon
"Hello Ammi ki yafemin dan Allah ina Matata da yarana"
"Masha Allah, Allah abin godiya Mustapha kaine da gaske"
"Ammi da gaske nine ina matata da yarana"
"Aimanah gata nan cikin gida yanzu suka zo daga abuja yara kuma suna school sai shida na yamma Shaheed zaije ya Wakko su"
"Ammi kano zan tawo nariga da na datse duka igiyoyin aure na da Sumayya na mata saki uku kafin nazo nan nasan ke ba ganin girman zunubin nan data aikata zakiyi ba, da zuciyarki ta musulumci saiki ce na barta da tun abaya kin barni na sahale mata da duk haka bata faru ba"
"Assha Mustapha saki irin haka ba daWi fa banso kayi uku lokaci guda ba"
"Ammi bazan iya sake zama da mishirika ba, gaba inaga kashe ni zatayi"
"Allah ya kyauta Mustapha, yanzu dai muna tareda baki zan koma ciki sai kazo" sallama sukayi Musty ya koma Wakin Sumayya da har sannan take tsugunne kan kafafunta tana kuka, jawota yayi har compound ya watsota waje ya maida kofa ya rufe, mikewa Sumayya tayi Allah yasa da mayafi a jikinta har jakarta na kafaWarta futa tayi ta tai tafiya mai nisa sannan ta sami inda tasai takalmi kai tsaye tashar mota ta nufa ta hau motar zuwa katsina, cikin motar kuka take sosai tana daWa cin alwashin duk yanda zatayi sai ta koma gidan Mustapha ko zatayi yawo tsirara

Abbas zaune a falo fuskarsa cunkushe da damuwa tsawon watanni a haka yake, Rumana ta kasa gane kansa ita dai zata iya cewa tun bayan Satan Aimanah Abbas ya koma haka duk iya kokarinta nason ganin ta goge masa wannan damuwar data bayyana karara a fuskarsa ta kasa, wayar Rumana dake ajje kusa da shi ce tayi kara ya kalli sreen na wayar ganin Ammi ke kira ya mikewa Rumana wayar ya mike zai bar wajan ihun murnar da yaji tayi yasa shi juyowa a fusace zai mata faWan abinda tayi, tsallan data yi ta rungumesa ya hana shi magana
"Honey Yaya Aimanah yau ta dawo gida Allah alhamdulillah" wata nauyayyar ajjiyar zuciya yayi wacce tasa har Rumana sai da ta kalllesa kallo irin na tuhuma, fuskarsa ta kalla take taga ba wannan kuncin sai wani zallar farin ciki da ya mamaye fuskarsa
"Abbas daman wannan damuwar danake gani a fuskarka tsawon lokaci duk akan Satan Aimanah ne, kana nufin har yanzu akwai son Aimanah a ranka ashe farin ciki kayi da Yayanmu ya sake ta" a razane Abbas yaWago yana kallon Rumana da tsawon rayuwar auransu bata taSa kiran zallar sunan sa ba sai yau
"Rumy maine haka kuma ni muka..."
"Kimin shuru bakada abinda zaka faWa min" Rumana da gudu ta faWa Waki Abbas ya rufa mata baya yana kiran sunanta....
' [2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da bakwai*

"Rumy maiye haka dan Allah ki tsaya ki fahimce ni mana, wallahi bako Wigon son Aimanah a zuciyata ina jinta kamar yar uwata wacce muka fito ciki Waya, wani Sangaran kuma ina mata kallon yayar matata"
"Haka zakace min mana zaka min daWin baki, inka Soye sirrin zuciyarka ai fuskarka ta fallasa asirin zuciyar" kusa da Rumanan ya karasa ya jawota jikinsa yana shinshinar wuyanta
"Ba wata mace a wannan xuciyar ta Abbas saike Rumy, kece dai ke kaWai zaki mulkin wannan zuciyar yanzu ko gaba har zuwa karshan rayuwata Abbas bashida wata mace bayanke bazance na maki alkawarin bazan maki kishiya sabida komai mukaddari ne amma dai ina da tabbacin bazan iya son wata macan bayan ke ba, kece komai nawa" Sosai kalaman Abbas sukai tasiri a xuciyar Rumana anan dai suka raya sunna daga rigima aka Sige da soyewa, tare sukai wanka yana shirin fita tace
"Yaushe to zanje kanon" dafe kansa yayi yana kallon cikin idanunta
"Ke dai kam Maman twince kin fiye rigima yanzu dai so kike mu kara wani faWan, ko inaga dai so kike mu koma scound round" yafaWa yana kashe mata ido Waya
"Nidai ba daWin bakin da zaka min wallahi sai naje kano naga Yaya Aimanah kuma tare zamuje da kai" zaro idanu yayi tareda haWe fuska
"Ke dan Allah yaushe rabon da ki ganni a kano inaga tun randa aka Waura mana aure da ke, bana jin nan kusa zan iya zuwa kano" yafaWa yana lumshe idanu tareda kwantar da kansa a fuskar gado, alamun damuwa suka bayyana karara a fuskarsa, Rumana kallon mijin nata tayi tana murmishi tareda kudurce wani abu a ranta hakan yasa ta zauna kusa da shi tasa hanunta cikin nasa tana mirzawa a hankali tsawon lokaci suna a haka kafin tayi magana
"A wannan karon fa sai kaje kano, mai kake tsoro a kanon badai karka fama mikin son Amanah bane to itama tana kano kuma a yanzu kanada damar da zaka mallaki Aimanah, Abbas nabaka dama idan har Yaya Aimanah ta amince da kai ka aure ta" buWe idanu Abbas yayi yana kallon Rumana daya soma tinanin ko kishi yaWan taSa mata kai ne,
"Ke!!! Rumana dawo hankalinki please"
"Ahankali na nake Abbas da gaske har cikin zuciyata gaskiyya nake faWa maka inma bazaka iya yakin ba ni zan zama sarkin yakin neman auran Aimanah gimbiyar Abbas" Rumanah tafaWa tana dariya
"Rumana abin nan bamai yiyuwa bane ki bar faWa dan Allah, Aimanah fa yayarki ce"
"Dan tana yayata aiba haramun bane addini bai halatta haka ba"
"Amma al'adarmu ma bata aminta da hakan ba"
"To addini ko al'ada wanne ka zaSa"
"Mubar maganar nan please tana samin ciwon kai, ki shirya zamubi jirgi zuwa kano, amma hotal zamu sauka"
"Ni bazan kwana hotal ba kamar wata.."Dan Allah bana son musu a wannan yana yin kiji abinda nace kawai" batace masa komai ba tabisa da kallon tausayi har ya fice daga Wakin

MUSTAPHA
Jirgin karfe huWu na yamma Mustapha yabi zuwa kano, Ahmad yaiwa waya suka haWu a airport na kanon shiya Wakko sa zuwa gida acikin mota suna tafe ba wanda kewa wani magana can dai Mustapha da shirun Ahmad ya damesa ya Wago ya kallesa suka haWa idanu, Ahmad kauda idanunsa yayi yana kallon kwalta batare daya ce komai ba
"Duk haushi na kuke ji ko?" Mustapha ya tambayi Ahmad yana kallon sa, Ahmad dake tuki da hannun daman shi yayinda Wayan hannun ke tallafe da kansa batare da ya kalli inda Mustapha yake ba yayi kamar baiji abinda ya ce ba can dai yamaida masa da
"Rayuwarka ce fa Yayanmu kayi duk yanda kaga dama kawai dai inajin haushin ka ne daka saki Aimanah inda ace iyayanmu basuda fahimta mai kake tunanin zai faru da tuni zumunchi ya Saci"
"Na rantse da Allah Ahmad ban saki Aimanah ba, hauka nayi da zan rabu da farin cikina" wani kallo Ahmad yaiwa Mustapha kafin ya furta
"Ga takarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login