Showing 54001 words to 57000 words out of 95991 words

Chapter 19 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5400

da wayar a hannunsa, saida ya futa compound na gidan kana yabi kiran Ammi daya katse, Aimana batasan ya sukayi ba taga dai yadawo Wakin ya kwanta baice mata komai ba, sa da tabari yayi nisa a barci ta tashi tsakiyar gado ta zauna tana faman kukan shagwaSa
"Aimanah baza ki barni nayi barci ba ko?"
"Ba kaine ba kadaina min magana" tafaWa cikin kuka, dafe kansa yayi gamida zuba mata idanu kana ganin yanda take kukan kasan na zallar shagwaSa ne, matsowa yayi kusada ita yasata a jikinsa yana buga bayanta a hankali da hannunsa
"Is ok ya isa Reina kece rigimar ki tayi yawa a wannan halin da kike ciki kice wani zakiyi tafi"
"Naga a jirgi zanje kuma ai ba kwana zanyi ba randa naje ranar zan dawo bafa nisa legos zuwa Abuja"
"Hmmm" kawai yace ya kwantar da ita haWida sata a jikinsa yana share mata hawaye har sukai barci a haka, shiya rigata ta shi yauma yayi abinda zaiyi ya fice sai text messages dayai mata na fatan ta taahi lafiya ya kuma sanar da ita ta shirya zasubi jirgin karfe biyu zuwa Abuja, murna tayi sosai sanda taga sakon cikin lokaci kankani ta gama komai, Aimana maca ce mai tsabta da iya girki ga uwa uba iya ado da kwalliya, ko kafin Musty yadawo tagama komai harta shirya cikin doguwar riga yar dubai tayi matukar kyau, sanda yadawo wanka yayi suka ci abinci ya fita masallaci yai sallah itama tayi nan cikin gidanta yana dawowa suka wuce airport yariga da yasaba indai zaiyi tafiya nan cikin airport Win yake varin motarsa inya dawo ya Wauki abarsa, lafiya suka sauka Abuja duk Woki da son ganin Rumana da Aimanah take haWiye sa tayi dan tunda suka sauka a Airport na Abuja Mustapha ke cika yana batsewa, wani haWaWWan hotal Mustapha ya kama masu can suka sauka a recepsion ya karSi key na Wakin ya wuce dan tun a office Winsa ya gama komai ta online shiyasa key kawai suka basa anriga da an gaya masa number Wakin, suna shiga Wakin Musty tafara rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai singlate da gajeran wando ya haye gado yana faWin wash
"Amma yaya inace hospital Win zamuje" kanzil baice mata ba saima gyara kwanciya da yayi yana kallon agogo, ba yanda taso itama kwanciyar tayi nesa da shi ta cure waje guda a haka barci yayi gaba da ita, Kiraye kirayan sallar la'asar ya farkar da Mustapha daga barcin da yayi yaga yanda Aimanah ta cure waje Waya, da sauri ya gyara mata kwanciya ya lulluSa mata blanket ya wuce bathroom yai wanka da alwala ya wuce masallacin dake nan cikin hotal Win, harya dawo rike da babbar leda a hannunsa bata tashiba shima bai tashetan ba sai wayarsa daya Wauka yana dannawa, biyar da kwata Aimanah ta farka taga gari yafara duhu addu'ar tashi daga barci tafara kana ta tashi zaune
"Sannu kin tashi" gira kawai ta Waga masa ta mike ta shiga bayi tayi wanka da alwala, futowa tayi tana raba idanu
"Yanzu kayan nan zan maida wai" da idanu ya nuna mata ledar dake ajje saman bedsite drowar buWewa tayi dogayan riguna ne guda biyu yan maroco ja da baka sai manyan hijabai guda biyu, jar tasaka ta Waura karamin mayafin rigar a kanta ta saka hijab Win tai sallah, kafin ta idar taga yagama shiryawa cikin bakaken suit sak yafito a kalarsa ta ma'aikacin banki>?-?tana azkhair ya zauna gefanta ya ajje likab a gabanta, dariya taso kwace mata amma sai ta shanye ta, ta shafa fatiha tana kallon sa shida likabin gabanta
"Kisa muje hospital Win"
"Inajin yunwa, kuma Allah bazan saka abin nan ba, ban taSa sawa ba dan haka bazan koya yau ba"
"Aimanah ki taimaki zuciyata ki sakaya min kyakkyawar fuskar nan taki"
"Mustapha kar muyi haka dakai duka akan Abbas ne kake wannan abun, Abas Rumana yake aure, na tabbata a yanzu babu wani sauran abinda yayi saura tsakani na da shi, kai nakeso kaine abokin rayuwar da Allah ya zaSa min koda baka raye nan duniya bana jin zai iya auran wani kisa a ranka ni taka ce har abada na roke ka ka rage kishin nan naka akan Abbas"
Jikinsa ne yai sanyi da maganganun Aimanah hakan yasa yai shuru tareda komawa gefe ya kira a waya aka kawo masu abinci, basu sami fita ba sai bayan da sukai sallar mangari ba sannan suka fita zuwa hospital Win da Rumana take
"Baby a ina kasami mota?"
"Munyi magana da yah Mansur shiya saka aka kawo min"
"Mutanan landon ana can"
"Suna can kam Wazu mukai magana da Mus'ab ma zai wuce Rasha acan zaiyi P h d" taSe baki Aimanah tayi kana ta ce
"Shikenan gida yazama sai Mah da Ma'aruf kowa yasa gabansa yabar kasar"
"Wanda yasami dama ya dama Aimanah wannan kasar tamu sai dai addu'a kawai nima nafara tunanin komawa jordan can inda nafara aiki"
"Amma badai dani ba"
"Da Sumy" yafaWa yana hararata sunata hira har suka karasa hospital Win
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da takwas*

Cikeda tausayawa Aimanah takewa Rumana sannu, tana rike da hannunta
"Hajiya ina wuni" Aimanah tafaWa tana kallon Hajiyar Abbas data fito daga bathroom, hajiyar Abbas ta rike baki cikeda mamaki fuskarta da murmushi
"Wa idanuna ke gani kamar Aimanah mutanan legos, yar uwarki ta taso ki ko?"
"Nice Hajiya yamai jikin"
"Jiki da sauki gobe ma zasu sallame mu mu koma gida" Aimanah kan tayi magana aka turo kofa aka shigo Abbas nw shida Mustapha sai Ammi a bayansu
"Lah Ammi daman kina nan"
"A'a yanzu nazo Abbas ne ya Wakko ni a airport ashe kunzo" Musty can gefe yasamu ya zauna saman farar kujera yana kallon Aimanah
"Yaya Abbas ina wuni ya mai jikin"
"Da sauki" Abbas yafaWa idanunsa na kasa, Aimanah sun jima a hospital Win har tara saura, Mustapha yabawa Abbas hannu sukayi musabaha tareda fatan sauka lafiya, Aimanah tabi bayan Muatapha daya fita bayan tayi sallama da su Rumana,

Aimanah da Mustapha kwanansu biyu a Abuja kana suka wuce kano inda aka fara bikin Surayya da Mas'ud, Aimanah bata wani sake sosai a bikin ba duk da dama ba wani shagali aka sha ba to ango yana india wajan karatu can za'a tura masa amaryarsa bayan an Waura aure, satin su Aimanah biyu a kano suka koma Abuja,

Rumana sosai take samun kula ta musamman wajan Abbas, Hajiyar Abbas tunu ta koma jigawa vayan taga Rumana ta warware, sauri sauri Rumana ta shiga wanka ganin lokacin dawowar Abbas yayi akuwa tana bathroom ta jiyo karar tsayawar motocinsa, kafin ta fito harya shigo Wakin sanye ta fito da tawul Waure a kugunta yayinda hannunta ke rike da Waya tana tsane gashin kanta
"Wellcome sir" tafaWa tana tsugunnawa a gabansa ta fara cire masa takalmin kafarsa duka biyun ta cire ta ajje su mazauninsu kana ta dawo ta fara rage masa kayan jikinsa, janta yayi sukayi baya suka faWa saman gado suna dariya
"Mar'atul saliha albushirinki"
"Goro" tafaWa da sauri
"Gobe sassafe zaki sama sabuwar Waliba a jami'ar abuja" makale shi tayi sosai tana ihun murna
"Hayatie da gaske dan Allah wayyo ni ina kasami takardu na"
"Jaheed ya turomin da komai"
"Naji daWi sosai Hayatie nayi farin ciki yanda kake faranta min kaima Allah ya faranta maka fiye da haka"
"Amin yafaWa yana sumbatar ta" daga nan salo ya canza suka lula duniyar masoya>?-?

Aimanah na vaje a falon tayi Wai Wai tana fidda numfashi yayinda Al'Mustapha ke zaune kusa da ita yana yanka kata Apple
"wash" Aimanah tafaWa cikeda raki
"Sannu reina sannu kinji"
"Baby na gaji da cikin nan gani nake ma kamar mutuwa zanyi" Aimanah ta karasa faWa tana kuka, ya buWi baki zaiyi magana wayarsa tayi kara alamar kira ya shigo, Ammi ce hakan yasa ya Waga cike da ladabi
"Mustapha zan saSa maka fa yaushe kadaina jin magana ta" Musty dafa kansa yayi a zuciyarsa yana faWin wayyo ni
"Ammi kiyi hakuri Aimanah tayi nauyi da yawa idan ta tawo kano a haka zata wahala"
"Ni kuma nace ka kawo min ita yau zuwa gobe nabaka ka wucw wannan wa'adin zan saSa maka" Ammi nagama faWar haka ta katse kiran
"Kamaida ni kanon in mutuwa ma zanyi na mutu cikin Ahali na"
"Aimanh ba yanzu ba insha Allah sai kinga auran twince Winmu da jikokinsu" murmushin yake tayi tana jin mararta na kullewa, yayin da abinda ke cikinta yayi wani irin motsi
"Ya Allah" Aimanah ta furta a hankali
"Sannu" kawai yake aika mata, a washe garin ranar Mustapha ya maida Aimanah kano suna sauka Ammi taji labari tazo ta wuce da Aimanah gidanta tanata ma Mustapha masifa ganin yanda kafafunta suka kumbura, a daran ranar ta kaita hospital suka dubata sosai haWeda mata hoton ciki inda suka sake tabbatar yan biyu ne a cikin Aimanah kamar yanda a asibitin da take awo a can legos suma suka faWa, cikin wata takwas harda sati biyu, Mustapha kwanan sa biyu ya koma legos shida Sumayya cikeda kewar Aimanah,
Rayuwa mai daWi da kulawa Aimanah keyi a gidan Ammi sai abinda takeso take ci kullum sukam futa da dare suyi zagaye su dawo, Mustapha tunda yatafi sai da yayi kwana goma bai zo kano ba, yau yakasa jurewa ba shiri ya biyo jirgin karfe tara na dare, lokacin daya zo sai Aimanah ita kaWai a Wakin Ammi, Ammin bata nan tana wajan Abba, da sallama ya shigo bedeoom Win Ammin, Aimanah da barci yafara Wibanta ta buWe idaninta a hankali da sauri ta tashi zaune tana mistsika idanunta
"Baby" tafaWa da muryar barci
"Bakiyi barci ba? ina Ammi?"
"Yanzu ta shiga wajan Abba tace bazata jima ba taje basa tea" dariya Musty yayikan ya ce "Taje basa tea kawai dai ta tafi kula da mijinta ke kuma ta rabaki da naki mijin"
"Oh Baby"
"Gaskiyya fa nafaWa" dariya tayi, ya zauna kusa da ita ya ruko hannunta
"Nayi missing naki sosai reina" yafaWa yana sumbatar hannun nata, dai dai nan Ammi ta shigo Wakin da mamaki take kallon sa ta haWe rai
"Kai kuma maiya kawo ka da wannan daran?"
"Ammi naji kewar Aimanah ne kawai ba biyo jirgi na ganta" taSe baki tayi sannan ta juya ta fita daga Wakin, Musty bayanta yabi yasawa kofar key yana murmushi, gadon ya hawo sosai yasa aimanah a jikinsa yana sauke ajjiyar zuciya a jere kamar wanda yayi gudu, Aimanah ma lamo tayi a jikinsa tsawon lokaci suna rungume da juna ganin time na ja yasa ya cire jikinsa daga nata ya fita daga Wakin, Aimanah gyara kwanciyarta tayi tana jin kewar mijinta na shigarta, har tayi barci Ammi bata dawo Wakin ba, sai da safe ta ganta kwance kisada ita, Musty bai shigo gidan ba sai da ya tabbatar Ammi ta tafi makaranta sannan ya shigo sashin Momy ya shiga ya tarar bata nan itama, daWi yaji sosai hakan yasa ya shiga Wakin Ammi cikeda karsashin son kaWaicewa da Aimanah kofar sashin ya fara sakawa key bayan ya shiga haka yayiwa ta falo ma, Aimanah taso kin bashi haWin kai tana nuna masa rashin dacewar abin a Wakin Ammi, wasanni daya rinka mata yasa ta bada kai bori ya hau, sai dai suka nutsu kana kunya duk ta kama ta gani take kamar Ammi taga komai da kyar da taimakonsa ta gyara jikinta ya cire bedshet Win yasa a wash machine ya wanke ya shanya yana addu'ar Allah yasa ya bushe kafin Ammin tadawo, Aimanah kaWan kaWan tafara jin ciwon mara azatonta kaWaicewa da sukai da Musty yakawo haka take ganin gaba kaWan zata daina ji, maimakon ciwo yayi baya sai yayi gaba tun tana jurewa harta kasa ta kira lambar Ammi ta sanar mata abinda takeji, Ammi tace mata ta jirata gata nan tana hanya tama kusa shigowa anguwar, Musty na can gidansa yana barci, ko kafin Ammi ta karaso Aimanah tafara fita hayyacinta, tayi sa'a tare suka shigo gidan da Ya Ahmad hakan yasa tasa shi suka nufi hospital, wayar Musty Ammi ta kira tace ya Wakko masu kaya a Wakinta suna hospital ruWewa tasa basuma taho da komai ba ance haihuwa ce, Aimanah na zagaye cikin Asibitin taga shigowar Mustapha ya ruWe sosai, Aimanah tun tana iya zagayan harta gaji kar finta na neman karewa aka maidata Waki har sannan da likita ta dubata a 4 cm take, Musty na rike da hannun Aimanah duk yanda likitoci suka so yafita a Wakin ki yayi ganin ba wata a Wakin sai Aimanah kaWai yasa suka barsa, idanunsa kaWai zaka kalla kasan yanajin ciwon gaba Waya yadamu jiyake ina ma da dama da ya karSi leboor Win nan Aimanah ta huta, Tun safiya Aimanah take abu Waya har mangariba bata haihu ba, Musty sallah kawai ke fitar da shi daga Wakin har kuka ya yiwa Aimanah musamman yanzu data fara kuka tana neman yafiyar mutane tana faWin mutuwa zatai, Nurse Win dake zaune gefansu ya kalla
"Babu wani abu da za'a iya mata ne wai?" ya tambayeta cikeda damuwa
"Babu, zata iya haihuwa da kanta yanzu tana 8 cm nan da ko yaushe zata iya haihuwa" kukan jaririn da sukaji ya karaWe Wakin yasa Musty faWin
"Alhamdulillah Allah abin godiya" da sauri likita dake office Winta ta fito ta karaso bakin gadon tana yiwa Aimanah sannu
"Dr Waya ne yafaWo akwai wani a cikin kuma da alama mahaifarsu Waya ce, Nurse Musty ta kalla
"Matso ka rike wannan karkayi nisa" matsowa yayi ya karSi jaririn dake faman tsan yara kuka ya rike idanunsa nakan Aimanah dake kiran sunan Allah ya share hawayan idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya
"Sannu Aimah" bata ko iya Waga kai ta kallesa ba,
"Aimanah tsaya kar kiyi nishi" likitan ta faWa tana danna mata ciki a hankali, kamar cirar kaya haka Aimanah taji sanda ta sake jin kukan wani jaririn ciwo ya tsaya cak Murmushi Musty yayi sai sannan ya kalli yaran, da Nurse ta matso ta zata yanke masu cibiya, wani gadon tayi daban da yaran Musty yadawo gefan kan Aimanah yasa hannunta cikin nasa
"I love you Aimanah" murmushi tayi ta kauda kanta Dr na mata dariya
"Ranka yadaWe zamu kwarfe mata jini yakamata ka bamu waje"
"Baki da damuwa dani Dr kiyi komai ina nan yau nan zan kwana" Dr dariya tayi tana canza safar hannunta
"Wayyo" Aimanah tafaWa sanda taji hannun Dr a jikinta
"Aimanah mai nake ji kinji wani babyn fa" Dr Rubina ta faWa tana ciro hannunta daga jikin Aimanah
"Wani babyn kuma?" Aimanah da Musty suka faWa a tare, kai dr ta Waga tareda kokarin yiwa Aimanah scaning hoton baby ya bayyana, Musty Lumshe ido yayi yana jero hamdala ga ubangijin da yayi masa wannan baiwar yara uku rigis lokaci Waya kai masha Allah, Aimanah wani sabon ciwon taji yana taso mata, tafara cize baki tana mimmikewa
"Wasa farin girki" Dr Rubina tafaWa tana kallon Musty
"Dr yanzu wani leboor Win kuma zata sake?"
"Da a lama" Awanni biyu suka shuWe ba alamar fitowar baby har an fara kokarin yiwa Aimanah cs sai kuka sukaji Aimanah ta sauke numfashi tana kallon babyn,
"Maca ce wannan" Dr Rubina ta faWa tana jijjiga babyn ganin kukanta baya fita sosai kamar na sauran yaran
"Nurse Fatima kai wannan babyn nursery wajan su Dr Auwal emargency bata da cikakiyar lafiya da alama tasha ruwan mahaifa, naWe yarinyar A tawul nurse Fatima tayi ta fita da sauri ita da Ammi suka nufi Sangaran yara na hospital Win, nan da nan Aimanah tai wanka ta shirya sai sannan Mah tazo hospital Win shima Ammi ce ta mata waya anyi haihuwa ta kawo ma mai jego abinci da tea, Wakin na musamman aka kai Aimanah da babyn ta guda biyu Wayar na sashin yara ana bata kulawa, Musty har sannan bai kalli yaran ba yana kusa da Aimanah yana dai kallo ana ta Waukan babyn wannan yaba wannan dan tuni yan uwa sun cika hospital Win kai baza kace dare bane musamman daya kasance haske gashin tar wai ko alluranka ce ta faWi zata iya ganinta kaWau kayar ka
"Yayanmu babyn nan da kai yake kama" Ma'aruf yafaWa sanda ya Wau babyn a hannusa duka biyun
"Ya Ahmad zokamin hoto da babyn nan a tura a group kowa yaga yau na girma"
"So kake ka tashi hankalin Anty Hasana da daran nan tasa dr neman jirgi" Ammi tafaWa tana dariya, Mah dai na gefe tana murmushi bata ce komai ba
"Mustapha yaWau yaran nan kuwa?" Mah ta tambaya tana kallon Mustaphan
"Mah basai na Wauke su ba tunda ga ku ai shikenan"
"Mu daban kai daban, maza Wauke su kamasu huWuba ka masu kuma addu'a" kallon Aimanah yayi
"Da alama dai ranka yadaWe fushi kake da babys Win nan sun wahalar da madam" Dr Rubina ta faWa tana kallon Mustaphan, dariya yayi
"Aimahh wanne suna za'a saka masu?"
"Daddy da Abba" yana kokarin karSar yaran Alhaji Kamal da prop Farouk suka shigo Wakin kana kallon fuskar su zaka hango zallar farin ciki, Musty fasa karSar yaran yayi ya koma inda yake ya zauna Alhaji kamal ya karaso gaban gadon da Aimanah ke kwance yana mata sannu, yayin da Prop ya wuce ya karSi yaran, fuskarsa da murmushi yake faWin
"Masha Allah bakin duniya, Sauda kalli yaran nan kamar Mustapha randa aka haifosa" dariya akayi gaba Waya, Alhaji kamal ya amshi guda Waya yana masa kiran sallah a kunne, Alhaji Farouk ma hakan yayi kamar yanda sunna take
"Prop sai kayiwa kanku takwara ai"
"To nidai na hannuna nasa masa Umar faroup" Prop ya ce
"Au haka ne bari wannan to na masa huWu ba da Muhammad Kamal" dariya aka kuma yi Dr Rubina dake haWa allura zatayiwa Aimanah tana kallon Family Win tana yaba haWin kansu.

"Baby wai wannan allurar ni za'ayiwa?" Aimanah ta tambayi musty rai Sace kamar zata yi kuka
"bake zata yiwa ni za'ama madadinki"
"A'a kadai faWawa madam gaskiyya ita zanwa duk kun hanata barci gara tayi barci ta huta gajiyar nan"
"Babban mutum ajjeni gida" Ammi tafaWa tana mikewa tsaye, da sauri Mah ta tashi
"Mai kike nufi wai na zauna anan Allah ya sauwaka"
"Ai kuwa zama ya kama ki yaya tunda Momy na wajan Babyn can, ke ki zauna tareda Aimanah ni kuma naje gida na kwanta na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login