Showing 87001 words to 90000 words out of 95991 words

Chapter 30 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5383

ajjiyarta ta fito jiki sanyaye, karaf idanunta cikin na Mustapha daya kafe kofar da idanu yana dakon futowarta, sassanyar ajjiyar xuciya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya ja, kallonsa ya maida can gefe sanda yaga ta zauna kasan carfet kusa da kafafun Ana ta fara matsa mata a hankali yanda zataji daWi ba zafi ba
"Ummu Aimanah" Ana ta kira sunanta, Aimanah ta Waga kai ta kalli Ana
"Abaya ina alfahari da auranku, dan Allah ina rokon kumin alfarma ku sasanta kanku ku maida auranku naci gaba da alfahari da auranku har zuwa sanda kasa zata rufe idanuna" Mustapha gyara zama yayi jin Ana ta tsokano inda ke masa kai kakayi
"Ana ita zaki gayawa ita ce ta kafe data bani dama da tuni ba wannan maganar ake ba, sai kuma Ammi data ce karna sake taji wata magana kan Aimanah wai anbar auran zumunchi a family" Ana har Wan zabura tayi jin abinda Mustapha yace Ammi ta ce
"kaico! yanzu Saudatun ce ta faWi haka, Assha zamani ya lalace nikan zan alfahari ace ko bayan raina anata auran zumunci a ahali na, zata zo ta same ni ne zan matukar saSa mata"
"A'a fa Ana karki Sallo min ruwa, Ammi tazo tana jin haushi ko tace na haWata da ke"
"Haba yaro ta manya zan mata sam bazaka fito a maganar ba" Ana ta faWa tana Wan tari
"Ana jikinki zafi"
"Kayya Ummu Aimanah yau sati guda kenan ina fama da zazzaSin nan ba wanda na gayawa azo a taru a kaina wannan Wan yazo a kaini ayita kafa min karfe"
"Ana ki ce dai allura kawai kike tsoro"
"Allurar me kuma Allah na tuba" Ana tafaWa tana kafe Tasnim da idanu
"Shi dai wannan inaga da kurma za'ayi sai kuma Allah yasa akayo sa mai magana" dariya Aimanah da Mustapha harda Gwaggo sukayi, wayar Aimanah tayi kara murmushi bayyane a fuskarta tai pickin call
"Da gaske harka karaso, minti biyu gani nan fitowa" mikewa tayi ta koma Wakin Ana tana murmushi, da gayya ta shafa humrar data san Mustapha na matukar so ta sakala mayafi a kafaWa ta fito ta na tafiya datasan dole taja hankalin Mustapha ta kalli Gawaggo Fulani
"Alhaji Sadam ne yazo zan fita," Gwaggo kasa cewa komai tayi ganin irin kallon da Mustapha ke wa Aimanah,
Aimanah ta fara tafiya tana gafda fita daga falon Mustapha ya kira sunanta hankali ta she
"Karki sake ki fita a gidan nan da wannan turaran"
"Saina fitan kai ka isa ka hanani abinda nayi niyya" bata tsaya jin abinda zai ce ba ta fice daga falon, afusace ya mike zai bi bayanta Ana ta hana sa haka ya zauna kan kujera yanata sauke numfashi kamar wanda yai tseran gudu, zuciyarsa sai bugawa take da karfi da karfi hawaye suka zubo daga idanunsa ya share da hannunsa, inama Ana ta barsa ya fita yau da anyi kare jini biri jini ji yake zai iya yin komai inda anbarsa ya fita, kansa ya Wora saman kujera yana shashekar kuka, imagen kawai yake yanda Aimanah da Sadam suke a wajen
"Barka da zuwa Alhajina" Aimanah ta faWa sanda ta karasa wajan Alhaji Sadam wanda ke tsaye jikin motar sa
"Barka dai amaryata, ina yarana na"
"Suna ciki basu san kazo ba da tuni sun fito"
"Gaskiyya Aimanah na gaji da zaryan nan ki amince manya su shiga maganarmu a tsaida mana rana ko hankalina ya kwanta, zuciyata kullum cikin zulumi take kada wani yazo yai min shigar sauri, kada kuma baban yara yadawo"
"Bakada damuwa Alhaji na, na riga na amince maka ka turo kawai a tsaida mana rana, amma dai ka sani ina aiki ina zuwa makaranta"
"Bakida damuwa Amaryata, wannan duk ba damuwa bace nidai fatana da burina shine ki amince kuma kin amince Win ina godiya"

MURJANA Rayuwa ta mata daWi tana zaune gidanta cikin kwanciyar hankali da salama soyayya sosai suke sha da Alhaji Jamil ga yara da yanzu suka zama nata tuni Allah yayiwa Rahila rasuwa wajan datake zama tana bara anan mota ta taka mata kai ta rasu, Murjana jin yaran take kamar ita ta haife su komai yi masu take tsakaninta da Allah tana matukar son yaran musamman ganin yanda suka maida ita tamkar itace ta kawo su duniya, ji take da su sosai karma Ansar yaji labari wanda take matukar tausayawa danshi gaba Waya mantawa ma yake da Mamansa gara manyan lokaci bayan kokaci suna zancanta itama tana yawan gaya masu idan sunyi sallah suyiwa Mama Addu'a Allah yamata rahama, Jannart data fi sauran yaran wayo ita basai ance bama ko karatun kur'ani tayi takance Allah yakai ladan kabarin Mamanta,
Kauna soyayya kulawa ta musamman su Alhaji Jamil kewa Murjana wacce yake matukar girmamawa ganin irin rukon da takewa yaransa na tsakani da Allah ga danginsa datake kyautata masu wani abinma baisan anyi ba sai dai a masa waya ana masa godiya Murjana ta masu wani abun shi yasa ya sakar mata komai kusan tare ma suke komai na business Winsa tasan komai, idan tafiya ta kama sa da ita suke tafiya ta zame masa jela ko ina suna tare, subar yara tare da Innah da Nanny Winsu
Jannart tsalle take itada Ansar suna murna wannan karan dasu za'ayi tafiya ummara Alhaji Jamil ya shirya masu zasu tafi duka gidan gaba Waya yaran har nanny Winsu da kanwar babar Alhaji Jamil wacce take zaune da su anan gidan, suna tafe a mota Alhaji Jamil na tuki sun nufi airport acan zasu haWu da driver Win da zai juyo da motarsu,
Murjana juyowa tayi sanda motar su ta tsaya a moto park na cikin airport tana zare idanu ganin wanda idonta ya gani, da sauri ta Wauke ganinta ga Salim wanda ta kula da shima ya ganta, tana fitowa a motar yana karasowa wajan, Alhaji Jamil ya haWe rai ganin Salim kusa da Murjana
"Barka da yamma Alhaji Jamil" Salim yafaWa yana mikawa Alhajin hannu
"Barka dai! ya kake ya kwana biyu?" Alhaji Jamil yafaWa baina baina fuskarsa ba yabo ba fallasa
"Murja na jima sosai ina son ganinki, na roke ki yafiya kan abinda yafaru a baya rayuwa ta koya min darasi da yawa, wajan yawo ce yawace na Wakko ciwon H I V ga sanyi dana gamu da shi, uwa uba ma rashin haihuwa da ban samu ba har yanzu, ina yarona ko yarinya ta" yafaWi haka yana kallon Ansar wanda a zatonsa shine gudan jininsa
"Ashe har kana da bakin da zaka iya tsayawa dani kamin magana, harka tambayeni cikin dakace nasan yanda zanyi da shi, ciwo sai dai nace Allah ya karo wasu yanzu ka fara gani insha Allah bazaka gama da duniya lafiya ba, Wa kuma da kake tambaya baizo duniya ba" Murjana taja hannun Ansar suka bar wajan da sauri tana goge hawaye, Salim shima hawayan yake musamman daya ji Wan dayake saka rai yana da shi guda Waya ashe baima zo duniyar ba, ya jima tsaye a wajan yana tunanin rayuwa da yanda ta juya masa baya, kuWin da yake takama babansa nada shi yau duk babu, baban ma bai raye daman shine ke gaya masa gaskiyya Momy ta gamu da lalurar shanyewar Sarin jiki, komai nasu ya kare gidaje motocin da suke takama duk babu sai gidansu na kano da shi kawai suka tsira a ciki ma suke zaune yanzuma Abuja yaje jiya wajan abokin babansa yakai takardunsa na makaranta a sama masa aikinyi zaman haka ya ishe sa ko wadataccan abinci basa samu, a tasha jiya yahau mota yatafi abujan dan yanzu ba shida da kuWin jirgi, abokin dadynsa ne yanzuma ya biya masa kuWin jirgi yadawo a ciki rabonsa da hawa jirgi tun dady na raye, ya goge kwallar data zubo masa yasa kai yafita daga cikin airport Win yana jin karar tashin jirgi wanda yake zaton su Murjana da mijinta na ciki,
Murjana acikin jirgi tayi lamo jikin Alhaji Jamil tana share hawaye ganin Salim yau yatada mata da wani miki na zuciyarta data daWe da binne sa, kuka take ahankali tana share hawaye
"Kiyi shuru Honey dan Allah ki bar kukan nan"
"Kabarni nayi kuka dear, kana jifa wai ina Wansa Wansa fa kawai yake tunawa ni ta sanadinsa na rasa mahaifata na rasa ladan da ko wacce mace take samu wajan haihuwa da reno" Murjana ta faWa tana sake shigewa jikin Alhaji Jamil
"Kibar kukan dai nace, ki godewa Allah gasu Ansar nan inba wanda yasani ba waye zaice ba naki bane, lada kuma insha Allah zaki samu na renon marayun nan da kike bana son ganin hawayan nan adaina sa please" Murjana sosai ta maida hankali ga ibada a birnin makka ba wannan ne zuwanta umara na farko ba amma tana jin wannan ta daban misamma daya kasance ta zo a yanayi na damuwa, satinsu guda acan aka mata waya jikin Mama ya tsananta

SUMAYYA
Cikinta ya girma sosai shiyasa tai sanyi ta ajje komai saita haihu a wajan awo ta haWu da wata sabuwar kawa yanda taga mijinta na nan nan da matar yasa suka kulla alaka, dan ko yaushe zata zo awo shike kawo ta ya zauna ya jirata harta gama yana rike da jakarta, sosai Sumayya ta shiga jikin matar tasan duk wani sirrinta, matar tayiwa Sumayya alkawarin ta bari su haihu suyi arba'in zata raka ta wajan wani malami aiki yake kamar yankan wuka, Sumayya dukta kagu ta haihu suje ga cikar burinta rabon dataga Mustapha tun randa tazo kano sai dai duk wata Ammi tana saka sa ya turawa Sumayya dubu hamsin, Sumayya tunda ta baro Katsina sau Waya ta koma taga mamanta wacce ta rame ta kankance Wakin nata sai masifar wari da Woyi yake da kyar Sumayya ta iya kwana Waya a gidan ta juyo ko waiwayarta bata sake yi ba, Amarya tana ganin rayuwa ita kanta neman mutuwa take ta huta daga halin datake ciki kullum tana kwance ga jikinta daya saluSe namanta sai zakwanyewa yake tun mahaifiyarta bata kulata hardai ta hakura ta ke gyarata tareda mata addu'ar samun sauki, Amarya ta rinka nadamar abinda ta aikata tayita neman gafarar ubangiji har sannan tsutsotsin dake fita daga jikinta basu daina ba kullum ne sai sun fito bakyan gani, Murjana ita ke kulawa da ita tana masu aiken kuWi da kayan abinci duk wata takanzo ta ga mamanta wani bin tayita kuka, cikin Sumayya watansa bakwai Allah yaiwa Amarya rasuwa a wani dare na talata, mutane kin yiwa Amarya wanka suka yi kowa gudunta yake saboda wani wari datake gata ta koma abin tsoro, maza ma tsiraru ne suka kaita makwancinta na gaskiyya=?-?Ammi Momy Gwaggo Fulani da Aimanah har katsina suka je gaisuwa banda Mustapha da yake abuja sanda Ammi ta gaya masa mutuwar tace yaje yai gaisuwa cewa yayi aiki sun masa yawa bazai sami zuwa ba Allah yajikanta, Sumayya ana yin bakwai ta baro Murjana ta dawo kano a cewarta gidan ba daWi bazata iya zama ba

Prop Faruk Mai nera ya kalli falonsa dake cike da yayansa maza da matansu da yaransu, wani irin nishaWi yake ji yanaji ko a yau Allah yaWau rayuwarsa alhamdulillah, ya sake Wagowa yana kallon ?an jikokinsa dake ta tsalle tsallan su na yara suna wasa su Zayyad da Ziyad da suka zama manya sune kaWai a nitse saman kujera suna hira da Aimanah, Prof ya zubawa Aimanah idanu haka nan shi dai baisan Aimanah ta auri Alhaji Sadam son samunsa ta koma gidanta ta rungumi yaranta su gina sabuwar rayuwa, mikewa yayi ya wuce sashinsa yana yiwa yaran nasa sallamar sai da safe, yaune suka dawo daga saudiyya sabida bikin Ma'aruf da ya gabato yau saura sati guda kenan, sai da ya nutsu a falon sa dake sashinsa ya kira lambar Aimanah yace ta zo, a nutse Aimanah take takawa har zuwa sashin Daddy Win yana zaune kasan carfet yana danna wayarsa, sallamar datayi ya amsa ya Wago yana kallonta
"Aimanah zauna hira yau zamuyi ki bani labarin zawarawanki" dariya Aimanah tayi tareda rufe fuskarta da hannunta alamar taji kunya
"Alhaji Kamal ke gaya min kin fitar da wanda zaki aura har iyayansa sunje sunyi magana da shi"
"E!"
"Da kyau ke baki sha'awar ki koma gidan Mijinki ko shine baya son komawar?"
"Daddy bana so na koma har yanzu fa yana tareda matarsa inna koma ban rabu da matsala ba gara nayi wani auran inda hankali na zai kwanta"
"Gidan Alhaji Sadam ba inda hankalinki zai kwanta bane Aimanah, Alhaji Kamal yayi bincike akansa bazaki aure sa ba, idanma bazaki koma gidan Mustapha ba gara wannan yaron Yasar, nidai son samuna ki koma gidanki Aimanah hankalina zaifi kwanciya"
"Daddy kayi hakuri idan har Sumayya na gidan Mustapha bazan iya sake zama da shi ba"
"Mustapha ya saki Sumayya tun tuni tana zaune a gidamsa ne tana rainon cikinta, saki Uku Mustapha ya mata, dan Allah Aimanah ki amince a karo na biyu a sake Waura maku aure da Mustapha idan kika min wannan alfarmar zanyi farin ciki"
"Shikenan Abba na amince amma ba yanzu ba, a kara min lokaci na kammala karatun nan"
"Ki karasa a gidanki Aimanah, hankalina zai fi kwanciya bana jin daWi ina can ke kina nan, hankalina zaifi kwanciya idan kina gidan mijinki, a rinka mantawa da komai da ya wuce ki yafewa Mustapha ku koma kamar da koma fiye da da Win, kin sani duk abinda suka faru ba laifinsa bane kin rigada kin san komai" Aimanah kuka take sosai jin maganganun Daddy harya gama bata sake tanka masa ba har sai da yace ta tafi sannan ta mike kai tsaye Wakinta ta wuce taje ta sha kukanta na dolan da Daddy ke son mata a karo na biyu, duk da akasan zuciyarta tana kaunar Mustapha har yanzu amma bata sha'awar sake rayuwar aure da shi, sati na zagayowa aka fara gabatar da bikinsu Ma'aruf ba wasu event zasuyi ba kasancewar bikin ba amarya tana Abuja ranar Waurin aure Mah tayi yinin ta sai washe gari da akayi buWar kai a Waya daga cikin wajan biki dake garin kano,

ABBAS
Kansa ya kwantar kan teburin dake gabansa yai shuru yana tunani har baisan sanda Captein Uweer ya shigo ba sai da Captein yasa kafa ya taka kafar Abbas kana Abbas Win ya Wago a fusace kamar zai kai duka ganin Captein tsaye a kansa yasa yai guntun murmushi
"Kayi sa'a ban kawo maka duka ba nayi zaton Mejor Mahmud ne"
"Inda ka kawo min ma zan shanye kasani, kana nan kasa kanka a damuwa, abin nan da kake so ba haramun bane amma duk kabi ka damu kanka nafaWa maka kayiwa Aimanah magana kawai kila ma rabonka yasa ta fito daga gidan mijin" Abbas sauke gwauron numfashi yayi bakinsa na furzar da wata iska mai zafi
"Captein bazaka gane ba, Rumana tana da girma da kima a idanuna bazan iya mata kishiya ba amma tabbas zuciyata har yanzu tana son Aimanah kuma tana kwaWayin ganin mun kasance tare sai dai ta ina zan fara Aimanah da Rumana causin ne ta yaya zan haWa su na aura?".
"Amma dai aiba addini ne yai hani ba ko? kuma Rumana ko jiya munyi maganar nan da ita tace min da wannan halin da kake ciki gara mata ka auri Aimanah inhar zaka kasance cikin farin ciki, ina tausayin yarinyar nan tana cikin watan haihuwarta amma kana saka ta a damuwa"
"Ina matukar kokari Uweer zuciyata ce ta kasa jurewa harta fallasa sirrin dake cikinta tabbas ina son Aimanah" Abbas yafaWa yana maida kansa saman tebur ya kwantar, wayarsa datayi kara alamar kiran waya ya shigo murmushi yayi koda baiga wake kira ba ring Win kaWai ya tabbatar masa da wace
"Barka da yamma rayuwata"
"Wayyo Abbas leboor nake zan mutu"
"Subhanallah ina Tina bata gidan ta taimaka maki ku tafi hospital gani nan"
"Bata nan taje kasuwa katawo karna mutu Abbas" da gudu Abbas ya fice daga office Win nasa tuki yake hankali tashe ya karasa gidan yana shiga Rumana ta santalo jariri, shiya taimaka mata ta gyara jikinta da baby kana suka tafi hospital a duba ta, Ammi ya kira ya faWa mata haihuwar lokacin suna wajan buWar kan amarya na bikin Ma'aruf gaba Waya family murna ta daWu Aimanah da Gwaggo Fulani da yamma suka Wauki hanyar Abuja,
Driver Abbas ya tura yaje ya Wakko su daga airport, Aimanah sanda taga jaririn jitayi kamar ta sace sa ta gudu yana matukar kama sosai da Abbas,
Abbas tunda yaga Aimanah a gidansa ya kasa sakewa ko ina tayi yana binta da idanu har dai ya fice daga gidan yabasu waje, Aimanah ita ke kula da gidan tunda sukaje Rumana na Waki Gwaggo Fulani tasata jego irin nada, Aimanah na tsaye a kicin tana haWawa Rumana abinci zata mika mata motsi taji a kofa ta juyo da sauri gabanta ne yai wata irin faWuwa ganin Abbas tsaye jikin kofa yanayin yanda yai tsaiwar saida yasa gabanta ya faWi take lokutan baya suka shiga dawo mata a kwanyarta, diri ricewa tayi tama kasa yin abinda yakawo ta kicin Win
"Mai kike jira har yanzu baki aure ba?" Abbas ya jefo mata tambayar da batada amsarta, jiyowa tayi zata bar kicin Win ya tare kofar da hannu wansa
"Abban Twince ka matsa min na fita"
"Ba inda zaki sai kin bani amsar tambayar danayi maki"
"Bazan amsa ba Win," Aimanah ta faWa a fusace murya raunane kamar zatayi kuka
"Ni kike jira ko?" Abbas yafaWa yana nuna kansa da Wan yatsa
"Abbas kayi hauka ne?"
"Aimanah daman tun tuni ni ai mahaukaci ne, hauka nake haukan sonki na riga na haukace a sonki" Aimanah hankaWa Abbas tayi gefe ta juya a fusace ta shiga Wakin Rumanah ta faWa gado ta fashe da kuka
"Lafiya maizan gani haka uwar Wakina" Gwaggo Fulani ta faWa tana zama kusa da Aimanah, Rumana murmushi tayi ta mike ta fita, a falo ta tarar da Abbas zaune a Waya daga cikin kujerun falo ya dafe kansa
"Mai yasa zaka mata magana anan, ai kamata yayi kaje can kano ka sameta kuyi maganar acan" Rumana ta faWa sanda ta zauna kusada Abbas, hannu tasa ta janye hannunsa daya dafe kansa da shi, yaWago idanunsa da suka canza launi sukai ja ya kalli Rumana sai kawai ya rungume ta yana sauke numfashi, Rumana bayansa take bugawa a hankali tana magana kasa kasa
"Karka sawa ranka damuwa masoyi a wannan karan Aimanah ta muce da yardar Allah"
"Rumy ni fa banc..."
"Karka ce komai koma maine Rumana tana bayanka" Rumana ta katse sa mikewa tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login