Showing 9001 words to 12000 words out of 95991 words

Chapter 4 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5409

Aimanah ba bazan so abinda Wan uwa na ke so ba koda Yaya Musty baya raye bazan iya auran Aimanah ba, bare yana raye wani abu ne ya gifta yasa ba'ayi auran suba, har yanzu ina addu'a Allah ya warware kullin da akayi Yah Musty yadawo hankalinsa ayi auransa da Aimanah"

"Ammi niki nema min auran Aimanah zan aure ta" Shaheed yafaWi haka hankalinsa kwance, Ammi da Ahamad tare sukayi dariya kafin Ahamad yace

"Ina kaga an taSa haka Aimanah ta girmeka nesa ba kusa ba kai ba sa'an auranta bane yaushe ka gama scoundry ita ko datake fenal year a jami'a"

"Yah Ahamad ai ba haramun bane basai mu tafi malesia tare ba nifa dama can ina yin Yaya Aimanah kawai dai matsalar banida aikinyi" Ammi dariya ta kuma yi tareda shafa kan Shaheed tana murmushi.


*Aimanah*

Agajiye ta tashi daga barci sauri sauri ta shiga bathroom tayi wanka cream kawai ta murza a jikinta ta fesa turare kan doguwar abayar data saka ta fito, kamar yanda tayi zato hakan ce ta tabbata gaba Waya mutanan gidan na bisa danning ana breakfast wajan Daddy ta soma zuwa hannunta tasa ta rungomo Daddy ta baya ta kwantar da kanta saman kafaWarsa tana kallon fuskarsa tace

"Goodmorning Dad"
"Morning my lovely Douther ya kike hope kin tashi lafiya"
"Lafiya kalau na tashi Dad" wajan Daddy ta bari ta nufi Mahh dake cin abincinta kai bazaka kace tana kallon suba saboda gaba Waya hankalinta yana kan abincin datake ci
"Kinga basai kin zo ba sarki son jiki ni karki zo ki wani makal?aleni kamar wata mage, ja kujera kici abinci malama" Aimanah ta Sata fuska ta tsaya inda take tana kallon Yah Ma'aruf dake mata dariya
"Kaga Yaya kadaina min dariya"
"Ni kuma Allah ma yasa abinci na nake ci bana kallonki" Ma'aruf yafaWi haka ganin irin kallon da Mus'af ke aika masa shiyasa yai saurin waskewa, Mus'af mikewa yayi daga kujerar dayake kai yazo inda Aimanah ke tsaye ya haWa ta da jikinsa kaWan ya ruko hannunta har gaban teble yaja mata kujera ta zauna ya zuba mata fankaso cikin plate kana ya zuba mata miyar agushi data sha wadataccan naman rago a bowl ya mika mata gabanta "Maza cinye min wannan na ajjeki a makaranta"

"Yah wannan fa yamin yawa" tafaWa ranta Sace tana cuno baki gaba
"Ok karki cinye baki shirya siyan mota a wannan watan ba kenan" da sauri Aimanah tafara cin abincin tana dariya
"Na shirya fa yaya Dan Allah camry nakeso"
"Bakida damuwa nagama haWa kuWina cash Mahh kawai nakeso ta amince banida damuwa da Daddy yardar Mah nasan itace tasa"
"Haka mukayi dakai" Daddy yafaWa yana dariya,Ma'aruf yace
"Daddy kowa fa yasani agidan nan Mah itace batason mu huta" dariya a kayi gaba Waya banda Mas'ud daya kasa cin abincin gabansa yayi shiru kamar mara lafiya...
'
07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na Shida

Wanan shafin gaba Wayan sa sadaukarwa ne ga masoyan wannan book Win musamman ?an zauran Mami Yusuf Daboo>?p?


Mah ta ajje cokalin hannunta tana kallo Mas'ud da damuwa ta bayyana karara a fuskar sa, sosai tabada hankalinta wajansa, musamman ganin yanda tai magana baiji ba hakan yatashi hankalinta sanin halin Mas'ud mutum ne mai faran faran kusan duk cikin yaran yafisu fara'a da surutu ga kirki da son mutane, ba kasafai ta fiya ganinsa a irin wannan yanayin ba, da Mus'af ne sam batada damuwa dashi saboda shi halinsa ne ciccin magani da miskilancin rashin magana da kin mutane,
"Ma'aruf taSamin na kusa dakai koya kurum ce ne ina magana baiji ba" Ma'aruf yasa hannu yataSa Mas'ud, Mas'ud jin an taSa sa yasa ya tsorata yaWago a firgice, tsam Maah tamike daga inda take ta karasa ta tsaya a kansa cikin kulawa tasoma taSa jikinsa taji ko zazzaSi ne ajikinsa tasan rago ne shi, idan zazzaSi yakamasa baya masa ta daWi, jikin taji sanyi kalau ba alamar zafi,alamun kalau yake damuwa ce kawai
"Sarkin maka lafiyarka kalau kuwa?"
"Mah ba kalau ba" Mas'ud yabata amsa batareda yaWago ya kalleta ba
"Taso mu shuga ciki muyi magana"
"Maganar bata sirri bace Mah ayita nan kusan ta shafi kowa dake nan akan Mustapha ne?" Mah takoma wajanta ta zauna tana kallon Mas'ud tace
"Kai nake sauraro sarkin maka" murmushi yayi ba karamin daWi yakeji ba idan Mah ta kirasa da sunan nan, "Mah Mustapha na cikin masifa! jiya nakirasa..."kaf ya kwashe yanda sukayi da Mustapha ya gayawa Mah, gaba Waya Mah hankalinta yatashi tarinka ambatan "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu har masaifar takai haka na shiga uku ni Aisha" Mah wayarta ta Wauka ta wuce Wakinta, prop bayanta yabi, sam ko kaWan Alhaji Faruok Mai naira baya kaunar ganin gudaliyar matarsa cikin matsala, Mah wayar Ammi takira Ammi na ganin kiran ta Waga da sauri dan tana cikin damuwa takira wayar yayar tata yafi a kirga amma saita jita a kashe

"Mah ina cikin masifa abubuwa sun run caSe yaya zanyi?"
"Kiyi hakuri Saudat bansan abin yakai haka ba kwanan nan kinsan haWuwa tayi mana wuya sanda zaki tashi a aiki ni kuma sannan zan tafi nawa, jiya nake cewa inna koma aikin safe nan gidanki zan wuto inna tashi,yanzu kuma Mas'ud yagayamin abinda yatashi hankalina"
"Ki bari Maaa wallahi yaron nan yana cikin jarabawa Allah ya fiddasa daga wannan masifar da haushin sa nakeji yanzu kuwa tausayin sa nake ji"
"Ba komai Ammi komai zai wuce yazama tarihi insha Allah yanzu mu haWu gida anjima zanyiwa su Yaya Muntari magana, mu haWe gidan Ana zan kira Alhaji usaini ma, sannan karki kuskura ki gayawa Hasana komai kin santa da masifa yanzu ta baro Qatar tazo tayi ta bala'i da mutane"
"Bazan gaya mata ba jiyama munyi waya tana tambayata Mustaphan nace mata baya nageria ya koma jordan,wallahi Maaah nakasa aikata komai a makarantar nan jiya na gayawa yara zamuyi test yau amma nakasa shiga class"
"Yi hakuri daure kiyi komai yanda kika saba khairan insha Allah" Maah data gama waya ta kalli prop dake zaune gefan gadonta yayi lamo kamar wani karamin yaro
"Lafiya na ganka a wannan yanayin prop"
"Lafiya kalau kawai banji daWin labarin nan danaji daga bakin Mas'ud ba," "Mata masifa ne! ni daman tun farko matar nan ta Alhaji Kamal batamin ba kawai dan ya nace ne na gaya masa yaki ji, dayabi tani bazai aure ta ba"
"Ya za'ayi prop haka Allah ya tsara matar sace kaga harda ?a a tsakani ai dole ayi aure, ni da cewa nayi zan aiki Mas'ud wajan yaya liman can kauye koda abinda za'ayiwa Mustapha"
"E kiyi hakan jiya ma gwaggo ta kirani bikin jikarta nan da sati biyu"
"Allah yakaimu, Aimanah naji tana maganar zuwa kauye sai tayi shirin zuwa biki nikam banajin zanje, satin ne bikin Raudah".

Ainamah shirye cikin shirinta na tafiya makaranta tayi sallama a Wakin Mah ta nemi izinin shiga maa tayi mata izini sannan ta shiga, sallama tayiwa Maaa da Daddy ta fito, ta tarar har Yah Mus'af yafitar da motarsa wajen gidan, a can tasame sa ta shiga yatashi motar suka soma tafiya, Aimanah wayarta take dannawa Yah Mus'af yakira sunanta ganin yanda ya kira sunan nata ya tabbatar mata da magana zai mata mai mahimmanci hakan yasa ta saka wayarta cikin hand bag Winta ta Wago tana kallonsa

"Aimanah bani aron hankalinki" sake nutsuwa tayi tana cigaba da kallon sa shi kuma hankalinsa na bisa titi "Aimanah Abas yana matukar sonki, naga ke kuma hankalinki baya kansa, nakasa gane inda kika nufa, inma har yanzu Mustapha ne a ranki to kiyi gaggawar shire sa sabida ko yau Mustapha yadawo hayyacinsa yazo bazan taSa amincewa da auranku ba saboda wahala zaki sha zama da irin mutane su Amarya ba abu bane mai sauki indai akace maki abu akwai asiri ka nisanci abin nan duk tsananin son da kakewa abin, koda kin auri Mustapha bazasu taSa bari kiji daWin gidan auranki ba, haka yasa yanke hukuncin Abas zaki aura, akwai freind Wina da muke aiki dashi a asibiti shima ya nuna yana sanki na taka masa burki saboda naga shi Wan tsalle tsalle ne yau kajisa anan gobe acan, kirike Abas sosai yana matuwar sanki zan iya rantse maki da Allah yafi Mustapha sanki, mahaifiyarsa na sonki in har kika aure sa insha Allah bakida matsala a gidansa, sai dai binciken danayi antabbatar min shi Win soja ne,zaki iya auran soja?" ya karasa faWa da murmushi yana kallota

"Zan iya auransa tunda har kana sonsa nima zan so sa insha Allah duk abinda kake so nima inaso"

"Au zama ki so sa wai har yanzu baki sonsa cab sannunki"

"Yah Mus'af duk bazaku gane ba, baku san irin son da zuciyata takewa Mustapha ba, har a Wazu da safe gani nake kamar ko wanne lokaci zai iya zuwa gareni, amma daga sanda Yah Mas'ud yafaWi maganar nan nasan Musty yariga da yamin nisa koda ayau zai dawo gareni bazan iya auran saba, inna dawo daga school zan kira Abas zan faWa masa na amince dashi yaturo iyayansa"

"A'a karki saurin cewa yaturo iyayansa ku fara fahimtar juna tukun kisan halinsa yasan naki"

"Nariga da na yarda da binciken ka tunda har ka amince dashi nasan halayansa masu kyau ne, bazaka taSa zaSan abinda kasan yanada matsala ba"

"Hakane my kanwa zan saka maki credit a wayanki ki kirasa, amasa zafafan kalamai wanda zai sa ya manta hanyar kano"

Dariya Aimanah tayi saboda tina lokacin da tafara soyayya da Mustapha Yah Mus'af ke faWa mata zafafan kalaman da take tura masa duk safiya"To naji zan faWa masa amma ka sake faWan wasu ba irin na Mustapha ba"

"Hhhhhh yarinya nemo da kanki ni zan maki zaman aure ne, nifa zamanki kawai nake a kasar nan daga randa aka Waura maki aure zan wuce Rasha na cigaba da karatu" Aimanah hawaye tafara sharewa, dariya yayi mata yana tuna mata randa ya tafi A B U zariya yanda ta rinka kuka shima yana tayata, sunata hira har suka karasa ya ajjeta a B U K shi kuma yadawo zuwa Asibitin Aminu kano inda yake aiki.



*ABAS*

Kwance yake a Waki zuciyarsa fal damuwa gaba Waya bayajin daWin kwanciyar, agogo ya kalla yaga biyar saura minti biyar 04:55 pm dafe kansa yayi dayaji yasara masa, hannunsa na dafe a kansa yamike yanjin jiri kamar zai faWi, labulan window yaWaga ya kara gudun A c yakoma gefan gado ya zauna yana tina kalaman mahaifiyarsa
"Abas kayi hakuri da yarinyar nan naga kamar ba kaine a agabanta ba kamar tanada wanda takeso a zuciyarta"

"Hajiya bafa kowa a zuciyarta yanzu, kawai wani can banza ne yadasa mata tabo a zuciya wanda yasa takejin haushin maza take ganin kamar duk halinmu Waya"

"Bazadai ka hakura ba kenan?"

"Hajiya ayi min addu'a kawai Allah yazaSa alkhairi"

"Amin kagama magana nima inason yarinyar yanayinta yayi min batada hayaniya gata da kunya ba kalar yammatan wannan zamanin bace, duk da na lura gidansu akwai dadtako manyan mutane ne, sun bawa yaransu tarbiya"

"Hakane Hajiya nima abinda na gani kenan shiyasa na nace"

"Saika cigaba da nacin nidai na baka nan da sati guda indai yarinyar nan bata canza ba ka hakura kawai ga Nafisa nan ?ar kanwata kaje kawai ayi yar gida" shiru yayi bayan ya gama tina maganarsu da hajiyarsa, zafi yakeji sosai duk da sanyin A C daya mamaye Wakin shi gumi yake haka kurum yakejin faWuwar gaba yau tinda yatashi aduk sanda yatina da Aimanah sai gabansa ya faWi, bathroom yashiga yayo wanka yafito ya tsaya gaban madubi yana karewa kansa kallo yana neman abinda ya gaza a jikinsa da har Aimanah ta kasa karSar sa a matsayim masoyi, ba laifi shi Win kyakkyawa ne ajin farko irinsu ne ake kira da black beauty, baki ne shi wankan tarwaWa inji hausawa bakinsa mai kyau ne, yanada tsayi sosan sosai bashida kiba tsayin sa shiya shanye kibar sa, yanada doguwar fuska mai Wauke da Wan madaidaicin bakinsa, idanunsa ba farare bane launinsu ya Wan sirka da ja, kasancewar yanada matsalan ido, sumar kalar ta filani a kallo daya inka masa zakasan sun haWa jinsi da filani, shafa kwantancan gashi kansa yayi da yasha gyara, ya busa iska a bakinsa ya furzar da iska mai zafi yana jera ajjiyar zuciya, shiri yayi cikin kakin sojoji yai matukar masa kyau ya saka gilashi a idonsa wanda yake kara masa karfin gani, glass Win ba karamin kyau yayi masa ba, ya fito daga Wakinsa hannunsa na rike da hular sojoji, sojoji ne birjik a compound na gidan nasa sun kusa guda goma, da sauri wani yatawo garesa ganin ya nufi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? mota ya buWe masa murfin mota, ya kame waje Waya tareda sara masa, Abas yai murmushi yasa kafa ya rofe mirfin motar ya buWe murfin gaban motar ya shiga frot seat, sojan ya maida murfin motar ya rufe ya zagaya da sauri ya shiga drever seat yatada motan, saida suka hau babban titi kana yace
"Oga ina muka nufa?"

"Brecck" Abas yabasa amsa batareda ya kalli inda yake ba yaci gaba da magana "Joshua nasha gaya maka ka daina buWemin bayan mota nafison zama na anan amma bakaji"

"Sir wani iri nakeji idan kana kusa da ni ba girmanka bane zama anan kagi dacewa da bayan ni ina nan ina aikina" murmushi Abas yayi yamaida hankalinsa kan wayarsa sau uku yanayi kamar ya kira Aimanah saiya fasa, yanzuma har ya danna call kiran yafara tafiya yai saurin katsewa saboda yanda gabansa yai wani irin faWuwa, kansa ya kwantar saman seat ya lumshe idanunsa bai buWe ba har suka karasa bareck, yanajin gaisuwa da sojiji ke masa tun daga bakin get bai iya amsa masu sai dai kawai ya Waga kansa, jin an tsaya yasa ya buWe idanunsa, yana kallo Waya daga cikin sojojin dake tsaye a wajan ya buWe masa murfin mota ya fito, gaba Waya sojojin wajan suka kame lokaci Waya suka haWa baki wajan faWin "Wellcome sir" suma bai iya ce masu komai ba ya Waga kai kawai da sarsarfa ya shiga office Win Muhd Ahmad ?an batta ( *SOYAYYA DA ZUMUNTA*) ya iske yana nan aiki ma yake a laptop Winsa, zama yayi a kujera yai shiru yakasa cewa komai, Muhd ya Wago kai ya kalli Abas, dariya yayi sosai kana ya rufe laptop Winsa ya shiga rera waka "So yakama ni, kauna ta shiga ran wani bai shirya ba"

"Moh Dan Allah kabari bakasan yanda nakeji ba, zuciyata saura kiris ta buga" Moh dariya yaci gaba dayi sosai kana yace

"Mazaje kana bani dariya wai duk sone ya maida ka haka?"

"Moh waike mantawa kayi inace nan kazo kasani a gaba har kuka kamin akan Zuhura sai anyi magana kace tausayinta kakeji ashe taka soyayyar ce tazo harda su kuka akan mace ba gwara ni ba"

"Kaga mufar maganar naji karka ci gaba da kiramin Zuhra anan yanzu na tafi wajanta na manta dakai anan, wai har yanzu yarinyar nan bata canza ba, nifa kawai gani nake ka hakura da ita" kiran sallah akayi gaba Waya suka mike zuwa masallaci, Wabi'ar su ce komai suke aka kira sallah sukan ajje sa aje ayi sallah in andawo a Wora.

*AIMANA*
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMAOuujeP6dLtFTHo1Edxx



Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Bakwai*


Aimanah tana tashi daga makaranta kai tsaye gidan Ana ta wuce, Ana kakarta ce itace wacce ta haifi su Mahh, Ana yaranta biyar uku mata biyu maza Muntari shine babba sai Aisha mah kenan sai Saudat Ammi sai ?an biyu Anty Hasana wacce ke aure a Qatar sai Alhaji hussain, Ana da mijinta Alhaji Mahmud suma haifaffun garin Wanbatta ne kauyansu bashida nisa danasu Alhaji farouk mai naira mahaifin Aimanah.

Akofar gidan Anan adaidaita sahu ya ajjeta ta basa Wari biyar bata tsaya jiran yabata canji ba tayi gaba abinta, da sallama ta shiga gidan, Ana ta washe baki tana faWin "Ga Aimanah ga Aimanah yau agari" Aimanah ta yi murmushi kana ta tsugunna har kasa tana gaida Ana "Nayi fishi Aimanah fisabilillahi kwananki nawa rabonki da gidan nan"Ana tafaWi haka tana kyauda kai gefe

"Ana kiyi hakuri karatu ya rikeni bana samun zuwa ko ina daga gida sai makaranta, yanzuma Mah tace inbiyo tanan intazo saimu wuce tare"

"Allah yataimaka Ummu Aimanah, Aisha basu karaso ba Wazu wannan Wan yakirani yafaWan zasu zo gaba Waya ko lafiya" Aimana ba tace komai ba tamike ta shige falon Ana

"Wash" Aimanah tafaWa sanda ta zauna a Waya daga cikin kujerun dake tsakiyar falon Ana, danna wayarta take jefi jefi suna magana itada Ramla mai aikin Mah wacce ta shigo bayan ta shigo Wakin ta kawo mata abinci, tana nan zaune har su Mah sukazo kusan tare suka shigo, gaba Waya gaidasu tayi tana kallo suka shige can bedroom Win Ana, batasan mai suka tattauna ba amma dai tasan koma maine akan Mustapha ne, wanda yanzu takejin matukar tausayin sa, Yau gaba Waya ta nemi son Mustapha ta rasa wani tausayinsa takeji, duk cikin sallolinta azahar da la'asar datayi a makaranta gaba Waya addu'o'in da tayi rabi Mustapha tayiwa, sosai takejin matukar tausayin halin dayake ciki, haka wani gefe na zuciyanta na matukar tausayawa Abas ganin irin nacin dayake mata, kenan irin yanda takeji a zuciyarta game da Musty haka Abas yakeji akanta, tabbas batayiwa Abas adalci ba yazama dole ta kira yau basai gobe ba ta amince ta soyayyarsa, wayarta ce tayi kara saida gabanta yafaWi duk a zatonta Abas ne yau gaba Waya bai kirata ba tex Winma dayake yawan yi mata yau ko Waya baiyi mata ba, sanda ta kalli screen na wayar dariya tayi ganin Yah Mus'af ne "Hello yayana" Amainah tafaWi haka a shagwaSe bayan ta Waga kiran

"Ke ina kikaje?"ba karfe huWu zaku tashi ba yau? yanzu har shida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login