Showing 51001 words to 54000 words out of 95991 words

Chapter 18 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5388

zaki da cin mutumci shiya biyo baya, yau harta kwanta barci ta tina da Alhaji Jamilu da sauri ta cire lambarsa daga black list data saka sa bugun farko yaWaga jiki na rawa ya ce
"Murja nayi kewarki kwana dayawa sau uku ina zuwa kofar gidanku nayita zama amma bana ganin gilmawarki yanzu ina zamu haWu?"
"Alhaji kana sona zaka aure ni?"
"So! sosaima kuwa nake sonki Murja, aure kuma ko yanzu kika ce na fito zanzo ga iyayanki" Numfashi Murja ta sauke kana ta ce
"Ok kazo wajan mahaifina kuyi magana"
"Nayi matukar farin ciki Murja Allah yabamu zaman lafiya amma dai kinsan sai kinyi istibira'i ko"
"Na riga da nayi free"
"Ok ki gayawa Abba gobe zanzo mu gana"
"Allah ya kaimu" tafaWa kana ta kashe wayar ta,

"Aimana yanzu in kika bini yaya zanyi da Sumayya?"
"Ni mai yayi ruwana da wata aba Sumayya ni mafita ta kawai nake nema, inka tafi kabarni yaya zanyi, ina zanji kamshinka nidai Allah binka zanyi" tafaWa tana dire kafafu irin na shagwaSaSSun yara, dariya yayi yana kallon yanda take kamar wata karamar yarinya, rigima da shagwaSar Aimanah suna kara narkar da shi a kogin sonta
"Ok dariya ma kake min ko, nidai a zubar da cikin nan tunda ai shine yajamin nakeson kamshin turaranka"
"A'a reina kar ayiwa boy Wina sharri fisabilillahi kwalba nawa ta turarena na ajje maki amma sai kice ke ba shiba na jikina kike so kawai dai nagano wayon so ake ayita zama a jikina"
"Allah ba haka bane" tafaWa tana faWawa kan gado haWe da fashewa da kuka, zama yayi kusada ita ya Wagota ya haWata da jikinsa yana kallon fuskarta kana yasa hannu yana goge mata hawaye
"Kinga zaki Sata min kyakkyawar fuskar nan taki nifa wasa nake maki, tashi ki haWa kayanki jirgin yamma zamubi motarki da kayan nayi magana da Anty Halima driver Winsu zai tafi da su can legos inya kai sai ya biyo jirgi yadawo" tsalle tayi ta Wane Musty tana ihun murna
"Nikam Aimah zanga randa zaki girma" hara ta masa irinta masoya batace komai ba taci gaba da abinda take, fita yayi zuwa kasa wajan Sumayya

Tana tsaye a Wakin nata rike da waya suna magana da Amarya, shigowar Mustapha Wakin yasa ta katse kiran tayi zuru tana kallonsa, zama yayi gefan gado ya nuna mata kusada shi ya ce
"Sumy zoki zauna muyi magana" ba musu ta zauna inda yace Win, jimm yayi na Wan lokaci har saida ta Wago kanta ta kallesa taga shima ita yake kallo kasa tayi da kanta tana murmushi
"Sumy kiyi hakuri da abinda zan faWa ki fahimceni please"
"Ina jinka" tafaWa tana wasa da zoban hannunta
"Zan tafi da Aimanah legos" da sauri ta Wago ta kallesa sai kuma tayi kasa da kanta hawaye masu Wimi suka biyo kuncinta
"Shi yasa nace ki fahimceni Aimanah nada juna biyu, tunda ta sami cikin nan take son kamshin turare na, na ajje mata su dayawa amma sai tace na jikina take so yau ranar komawata legos ta tubure saita bini na rasa yanda zanyi da ita shiyasa nazo na roki kimin alfarma natafi da ita"
"In naki yin alfarma fa?"
"Dole ta zauna ai bazan shiga hakkin ki ba"
"Hakki kuma na nawa Musty, ca nake nan kasai mata motar sama da miliyan talatin ni kuma kasaimin wacce bata kai miliyan goma ba"
"Sumy kibar maganar motar nan, kyauta ce na mata tun tuni na kudurce a zuciyata zan mata wannan kyautar tun kafin ki shigo rayuwarmu, Sumy bazan Soye maki ba kin rigada kin sani Aimanah itace jini da tsokata itace bugun numfashi na karki soma kwata??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta kanki da ita ina matukar iya bakin kokari na na kamanta adalci a tsakanin ku shiyasa kema na sai maki mota" tabe baki tayi ta tashi zata fita a Wakin sai da takai bakin kofa sannan ta juyo ta kallesa
"Na amince ku sauka lafiya" fita tayi daga Wakin ta faWa Wakinta ta fashe da kuka, tabbas ayau basai gobe ba zata barwa Mustapha gidan sa bazata zauna kishi ya kasheta ba, to in kuma nabar gidan yasakeni ina zan zauna gidan mahaifina ba daWi Mama tabar gidansu Mustapha ina zan kama tabbas dole na zauna a Wakin mijina in yaso na nemi mafita kawai, ko Mama zanyiwa magana mu koma wajan tsito a farraka tsakaninsu kai ai kuma komai daWewa asiri zai karye ga zunibi ga ba biyan bikata, ita kaWai take ta zancan zuci har barci yayi gaba da ita tanata barci Mustapha suka tafi bata sani ba saida ta tashi a barci taga massages na Mustapha yana sanar mata sun wuce yazo suyi sallama ya tarar tana barci in sun sauka zai kirata a waya

Rayuwa mai daWi da kwanciyar hankali Aimanah keyi a legos tayi kiba ta kara yin fresh, kullum suna tareda Musty daga yadawo daga office baya kuma fita ko ina yana gida tare da Aimanah kulawa ta misamman yake bata yana, duk friday yake zuwa kano yayiwa Sumayya kwana biyu ya koma legos,

Aimanah ta tsaye a kicin tana soya irish Mustapha ya shigo kicin, rungumeta yayi ya zagaye ta da hannunsa Waya Wayan kuma yana shafa cikinta
Reina yakamata ki rinka samun hutu fa tun asuba kina nan kina fama nace zan samo maki mai aiki kinki yarda"
"Allah ya kiyaye baby inban kula da kai wazanyiwa ni bana bukatar wata mai aiki kawai ta kwace min kai" dariya Musty yayi haWi da kwantar da kansa a bayanta yana lumshe idanuwansa
"Reina zuciyata taki ce ke Waya ko bake a duniyar nan bana jin zan so wata bayan ke, ina sonki ina kaunarki! zuciya da ruhi duka na begenki hmmm reina baki yayi kaWan ya iya bayyana kalar son danake maki ki kalli cikin idaniya su kaWai sun isa su bayyana maki kalar so da kaunar danake maki, ko yaushe in ina tare dake ji nake kamar nan duniya gaba Waya babu sauran kowa daga ni sai ke Aimah I love you"
"Love you tuch baby" tafaWa tareda sumbatar hannunsa,
"Kawo na karasa kije ki huta bari zan haWo komai"
"A'a baby kabarni na karasa ladana"
"Nima ki bari na sami ladan, kije kawai bana son musu Aimah" hannunta tasa ta kunna famfon sink ta wanke hannunta ta fita, tana zuwa wanka ta faWa ta shirya cikin farin wando dogo da karamar riga black colour ta Waure gashinta waje Waya bata saka hula ba ta fito falo tana danna wayarta, ya gama haWa komai yana zaune a danning area yana amsa waya, kujerar kusa da tasa taja ta zauna tana kallon yanda yake dariya da alama ko da wa yake waya wayar na masa daWi
"Aboki bazaka gane bane abar maganar nan sai anyi bikinku da Surry zaka bani labari" tana jin haka ta gano da yaya Mas'ud yake waya, bataji mai yaya Mas'ud Win yace ba taji Musty na faWin
"Kaga gimbiyya na kusa bazaka cinye mata sauran lokacinta ba in na shigo kano ma karasa maganar amma dai nace ka zaSi India kasar nada daWin zama" bai jira abinda Mas'ud zai ce ba ya katse kiran, yaja plate yana zuba mata soyayyan irish ya mika mata gabanta tea ya haWa mata yasa tea spoon cikin mug Win ya ce
"Ha na baki a baki"
"Zan iya jira ka bani kuwa nifa yunwa nakeji sosai" Sata fuska yayi yana mata hararan masoya
"Nidai saina baki Allah" yafaWa a shagwaSe haWi da Sata fuska
"To naji gashi na buWe bakin" Irish Win ya Wiba ya zuba mata a baki ta soma ci a hankali, saida ya tabbatar ta koshi kana ya kyaleta
"Baby nima tsaya na baka" zama ya gyara ta ciyar dashi cikeda kauna, har wajan mota ta masa rakiya tanata masa shagwaSa harya kusa makara yatafi tana Waga masa hannu, sai da get man ya rufe get san nan ta koma ciki, gyara ko ina tayi ta sannan ta shiga kicin ta tarar ya wanke kayan da sukai amfani da shi, ta wanke plate da Mug Win da sukai amfani dasu ta wuce bedroom ta kwanta, bata tashi ba sai azahar sallah tayi tai wanka ta zauna suna chat da Rumana datake bata labarin rayuwar da suke itada Abbas tana mata godiya bisa zaSin data mata, ganin biyu da rabi har tayi yasa ta mata sallama ta wuce kicin, wake ta Wora a electry kana ta Wora shinkafa kan gas ta Webo kayan miya ta wanke ta saka hand clove ta gyara kayan miyan ta cire dattinsu ta sake wanke su sosai da gashiri kana ta markaWa su a blandar kafin la'asar ta gama haWa lafiyaryar shinkafa da wake da miyar dake ta tashin kamshi ta yanka salad tumatir cucumber da albasa har green pepe ta zuba haWaWWiyar kula ta kawo su dannin area ta ajje, salla taje tayi bayan ta idar azkhar na maraice tayi ta Wau wayarta ta kira Mustapha, bugun farko yai pickin call Win
"Barka da aiki Rayuwata"
"Barka dai habibiya"
"Baby inajin yunwa fa baka dawo ba har yanzu" shafa kansa yayi yana murmushi yayinda kujerar dayake kai ke juyawa da shi, sai wani kumshe idanu yake da gani wayar na masa daWi
"Beb kici kawai, ayyuka sun rikeni Aliyu baya nan ya haWamin aikin office Winsa da nawa gaba Waya ni nake yi inaga sai mangari ba zan da wo"
"To abincin fa? haka zakayita zama bakayi lonch ba gaskiyya bazan laminta ba, sai yunwa ta kama min kai,"
" zan.." A'a Baby karka gayamin zaka ci abincin waje, Allah bazan yarda ba, ko nazo na kawo maka nan"
"A'a bari na turo driven mu na office ya karSar min ki bawa Joseph in yazo sai ya basa" dariya Aimanah tayi tana mamakin kishin Mustapha
"And kisa hijab kuma basai kin masa magana ba zan masa waya"
"Baby"
"Uhmm bebyn baby yane" .
"I love you" kissing wayar tayi kana ta katse kiran, tayi kamar yanda ya ce, bai dawo gidan ba kuwa sai gabda sallar insha, wanka kurum yayi ya fita masallaci dake nan kusada gidan, wajan takwas da rabi ya shigo gidan ya tarar tana zaune a danning area, can ya isketa yana mata sannu, soyayyar taliyar da tayi wadda taji kayan lambu ta zuba masu a plate suna ci a hankali suna hira jefi jefi

A kano tuni aka Waura auran Murjana da Alhaji Jamil ta tare a gidansa da yake tare da matarsa anan tarauni , sam bata sami matsala da matar saba mace ce yar ba ruwana aikinta kawai tasa a gaba sai dai ta kula tana yawan tara mata a sashinta datayiwa Alhaji Jamil magana yace ai tana business ne shiyasa, ganin bata shiga sabgarta itama saita kama kanta kusan ma ba zaman kasar suke da ba kullum suna tafe itada Alhaji Jameel data zamo masa jela.

*Gidan Abbas*

Ruma na kwance lamo kan kujera yayinda Abbas ke zaune kan carfet yana aiki a laptop Winsa, jefi jefi yake kallon ta ganin yanda take juyi kan kujera
"Rumy yane?" yafaWa yana barin danna laptop Win dayake
"Hayatie cikina ciwo wayyo ?a'?an cikina zasu zubo" da sauri ya mike ya karasa kusa da ita ya Wagota ya haWata da jikinsa
"Daman bakida lafiya baki gaya min ba mai yasa kika Soyemin"
"Yanzu ne fa, yanzu naji cikina na ciwon wayyo zan mutu" tafaWa tana juyi tareda wata mika, gaba Waya hankalinsa yata shi lambar nurse jamila dake cikin barreck Winsu yake kira amma bata shiga, da sauri ya mike ya Wauki Rumana cak ganin idanunta sun kakkafe, yafita da ita yana kwalawa jakop direver Winsa kira da sauri jakop ya karaso inda uban gidan nasa ke kiran sa
"Jakop maza Wakko mota muje hospital Rumy ba lafiya" yafaWi haka yana leka idanunta dayaga sun kafe waje Waya
"Jakop" yafaWa da karfi hankali tashe a bayan mota ya kwantar da ita yana tukin da hankasa, mahaukacin gudu yake bisa kwalta yanayi yana juyowa yana kallon Rumana dake kwance kamar gawa....
' [2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da bakwai*

*Wannan page Win gaba Wayansa sadaukarwa ne ga yan Aimanah real fans group 2 comment Winku na matakur sani nishaWi ina godiya da kulawa mutane na*

Hankali tashe likitoci suka karSi Rumana akai emargency da ita, tsananin tashin hankalin da Abbas ke ciki yasa ko gabansa baya iya gani, Jakop ya taimaka masa ya zauna a recepsion yadafa kansa yayinda shi Jakop Win ke zarya tsakanin inda Abbas yake da inda aka kwantar da Rumana
"Ina yan uwan Rumana Mahmud" da sauri Abbas ya mike tsaye yabi likitan zuwa office Winsa, kujera ya nunawa Abbas dake tsaye kikam a kansa, ba musu ya zauna zuciyarsa na dukan uku uku
"Sorry matarka tayi Sarin cikin wata biyu" a razane ya Wago idanunsa yana kallon likitan, hawaye suka zubo daga idanunsa shikenan sun rasa wannan cikin da suka kwallafa rai a kansa, ya Hajiya zataji idan taji wannan labarin mai tada hankali
"Kayi hakuri mahaifar Rumana nada rauni koda ta sake samun wani cikin banajin zai zauna sai dai zamu Worata kan magani sannan zata cigaba da zuwa ganin likita duk bayan sati biyu" Abbas kansa kawai ya Waga alamar yaji, Dr ya mika masa takarda ya ce
"Ga wannan asiyo waWan nan magungunan da allurai" karSa Abbas yayi ya fita, Jakop yabawa takardar shi kuma ya shiga Wakin da aka kai Rumana, tana kwance samSal saman gado kamar gawa ko motsi batayi a kallo Waya daya mata yaga ta rame sosai kamar wacce ta shekara tana cuta, hawayan idanunsa ya share ya sumbaci kuncinta ya fita daga Wakin, recepsion ya koma ya kira wayar hajiyarsa bugu Waya a na biyu ta Waga
"Soja mazan fama barka da yamma ya surukata"
"Hajiya" zuciyarsa ce tai wani irin rauni ya na shashshekar kuka ya ce
"Rumy tayi Sari"
"?ari! innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu tana ina?"
"Muna hospital"
"Kamata sannu zan biyo jirgi na tawo na kula da ita"
"Hajiya basai kinzo ba zan kula da komai"
"Malam Abbas kabari kawai nazo, kaga yanayin aikin ka yanzu ma ana iya kiranka batada kowa a Abuja wazai zauna da ita kabarni kawai nazo"
"Shikenan Hajiya Allah yakawo ki lafiya" Abbaa komawa Wakin yayi yaja kujera ya zauna kusada gadon hannunta na cikin nasa, motsi tafara yi kana ta buWe idanunta, lemar dataji a kasanta yasa ta kankame hannun Abbas dake cikin nata
"Hayatie maiya same ni mai ya sami cikina?"
"Ba abinda ya sameki Rumy kina lafiya, haka cikin ki ma yana lafiya"
"A'a Hayatie ka faWa min gaskiyya jini ne fa yake bina"
"Kinyi Sari ne" Abbas yafaWa a sanyaye
"Cikina ta zube wayyo Allah na"
"Kiyi hakuri Rumy kwana nawa ne zamu sami wani dan Allah karki saka damuwa a ranki Allah shiya bamu wannan lokacin da bamu zata ba ko tsammani, shi zai kuma bamu wani kilama ki mana tagwaye" yakarasa faWa yana murmushin karfin hali, Rumana maida kanta tayi ta kwantar haWeda runtse idanu hawaye na zubowa daga idanunta, Hajiyar Abbas a ranar tazo ita taci gaba da kulawa da Rumana.

*Musty Home*

"Baby danna min kafar nan sosai zugi takemin bakaji azaba ba" Mustapha dake matsa mata kafa kara himma yayi tareda aika mata sannu akai akai tausayi take basa sosai ganin yanda ta kumbura musamman kafafunta da suka tasa cikinta mai wata huWu inka kallesa zakace yakai watanni bakwai sabida girmansa, wayarta dake kusa da shi ce tayi kara alamar kira ya shigo hannu yasa ya Wauka ya mika mata cikeda Woki ta Waga ganin Rumana ce ke kiranta,
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Aimana ta faWa a razane tareda sakin wayar tata ta faWa kan cinyarta, a razane Musty ya Wago ya kalli Aimanah dake kokarin mikewa tsaye
"Ke maine wai nutsu Aimah"
"Baby Rumana ce a asibiti tayi Sari" tsaki yaja yana cigaba da abinda yake a fusace ya ce
"Shine kika ruWe haka, dan tayi Sari Allah zai basu wani ai" saroro tayi tana kallonsa cikeda mamaki
"Baby Rumana fa!"
"Rumana maizan mata fatan samun lafiya kawai zan mata" fusge kafarta tayi ta mike
"Nidai Abujan zan tafi naga lafiyar yar uwata"
"Kiga lafiyar yar uwarki ko ki gano masoyinki"
"Mustapha" Aimana ta faWa cikeda mamakin maganarsa, bai Wago ya kalleta ba saima danna wayarsa daya fara yi ganin bai kulata ba yasa taci gaba da magana
"Nidai wallahi sai naje na duba Rumana yaufa kwananta huWu a hospital ta kirani ta gayamin sannan kace bazani ba Allah sai naje naga yar uwata" kanzil baice mata ba saima tashi da yayi yabar mata gidan, bai dawo gidan ba sai batan sallar insha abinda bai taSa mata ba matsawar yana gari baya fita ko ina ko wani uzirin ne ya kamasa na fita tare suke zuwa ko ina ne, a Wakinsa ta kwanta ya shigo yana ganinta baice mata komai ba yai shirin barci ya kwanta can karshan gado nesa da ita sosai, ganin haka saita juya baya, washe gari kafin ta tashi yagama haWa break yaci nashi yabar mata nata nan saman danning ya wuce office
"Kam bala'i" Aimana ta faWa sanda taga abinda yayi agidan kicin ta wuce ta haWa abinda takeso taci ta ajje sauran, saida ta fuskanci lokacin dawowarsa yayi ta koma Waki ta kwanta lamo kamar mara lafiya, tana ganinsa ya shigo Wakin da sallama kasa kasa, suit Winsa ya cire ya Waura tawul ya wuce bathroom bai kalli ko inda take ba, yana fitowa daga wanka ya ganta zaune kan gado tana kuka kasa kasa ba karamin juriya yayi ba ganin bai kulata ba, jin kukan yake har cikin ransa, ta gefan idanunsa yake kallonta yayin da yayi kamar baisan tana yi ba, wayarta ta Wauka ta kiran layin Ammi
"Ammi Mustapha zai kashe ni daga nace zanje na duba Rumana shikenan yaWau fushi dani ya daina kulani ya daina cin abinci na yama daina kwana a Wakin danake" murmushin gefan baki yayi yana satar kallonta ganin yanda take haWa masa karya a gabansa ko kunyarsa bata ji
"Shi mai babban sunan yamaki haka, cab bari na kirasa naji dalilin da zaiwa yar Ammi haka kuma ki soma shiri gobe zaki gano yar uwarki" kwalo tayiwa Mustapha a zatonta baya ganinta, Musty yana ganin kiran Ammi yaki Wagawa saima barin Wakin dayayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login