Showing 48001 words to 51000 words out of 95991 words

Chapter 17 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5399

a jigawa gidansu Abbas akayi mata jere, sosai aka sha shagalin biki dinner kawai akayi Abbas ma ya halarta washe gari aka Waura aure Anty Hasana bata zo ba can a Qatar tayi taronta itada Dr shiyasa Daddy shine komai shiya Waura mata aure karfe biyu aka tafi da Amarya Daddy yace karsu sake su kwana suna kai Amarya su juyo, har Aimanah akaje jigawa bayan sun sha rigima da Mistapha yace bazataje ba ta ce sai taje rigima sosai sukayi har gaban Ammi goyan baya tabawa Aimanah ba yanda musty yayi yanaji yana gani haka aka tafi jigawa da Aimanah, hannu biyu Hajiya Hafsatu ta karSi su Mah abinci kala kala aka kawo masu saida sukayi sallar Insha suka baro jigawa Rumana nata kuka, har Abbas ya shigo tana zaune saman bed tana kuka...
' [2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da biyar*

Abbas ya tsaya a kanta yama rasa mai zaice mata can dai ya zauna kan gadon yasa hannu ya buWe mayafin data rufe fuskarta da shi, ido huWu sukayi da sauri Abbas ya Wauke ganinsa kana ahankali ya ce
"Kiyi shuru Rumy ki daina kukan nan yana tadan hankali" Ai kamar wanda yace cigaba da kuka ta kuma rushewa da kuka
"Kinga tashi kiyo alwala muyi sallah mu godewa Allah daya mana wannan ni'imar mu rokesa yabamu zaman lafiya da fahimtar juna mai Worewa da zuri'a Wayyi ba" bata masa musu ba ta mike tashiga ban Wakin dake cikin Wakin tayo alwala ta fito, yana tsaye kan daddumar daya shimfiWa binsa tayi sukai sallah raka'a biyu sosai yamasu addu'a kana ya fita zuwa kichin yadawo rike da plate da ya ajje a gabanta kallo Waya tayiwa plate Win ta kauda idanunta kaza ce dataji kayan haWi sai tururi take da tashin kamshi, lemu ya zuba a cup ya mika mata karSa tayi ba musu ta sha kaWan, ahankali yake bata zallar tsokar naman kazan tana taunawa kamar mai cin magani bata wani ci dayawa ba ta ce
"Na koshi" kallonta yayi da murmushi a fuskar sa
"Baza dai kici dayawa ba sabida tsoro ko" dariya tayi ta mike ta koma gefan bed ta zauna, tana kallonsa yagama kwashe komai yamaida kicin yadawo sanye da farar jallabiya ya kwanta Wan nesa da inda take kwance, baice mata kala ba haka itama batace masa ba, har barci yayi awon gaba da su, da asuba ita ta rigasa farkawa mamaki tayi ganinta a jikinsa ya zagaye ta da hannayansa ta shiga jikinsa sosai, hannunta tasa tana kokarin cire hannunsa daga jikinta taji yayi motsi, a kunnan ta yake magana a hankali
"Asuba tayi ne?" bata iya magana ba sai kanta data Waga alamar e, tashi yayi zaune kafin ya sakko kasa ya mika mata hannu ta Wora nata saman nashi ya mikar da ita, tare suka shiga bayi sukai alwala ya wuce masallaci ita kuma ta tada sallah anan Wakinta saman dadduma, Abbas bai dawo Wakin ba sai bayan bakwai na safe ya tarar Rumana harta koma barci nan saman daddumar Waukarta yayi ya maida ta kan gado, ta buWe idanunta dasuka soma canza kala ta kallesa kana tace masa
"Ina kwana"
"Kin tashi lafiya ya kwanan bakunta" dariya tayi haWeda runtse idanunta ganin ya cire jallabiyan jikinsa ya rage daga shi sai gajeran wando da farar singleti gadon yahawo yajawo ta jikinsa, bikinsa ya haWe da nata yana aika mata da wasu sakonni masu wuyar Wauka, safiyar wannan rana Abbas yamaida Rumana cikakkiyar mace, yasha kuka yakushi harda cizo, barci ne yayi gaba da ita, shi kuma ya mike ya shiga bayi ya tsarkake jikinsa yai wanka ya fita sai faman murmushi yake shi kaWai, sashin hajiya ya shiga har bedeoom Winta ya tarar bata Wakin ya shiga Wakin Babansa inda yake zaton tana can nan ma Wakin ba kowa, motsin daya jiyo a kicin yasa ya leka, Hajiyarsa ce tsaye tana aiki a kicin Win, babansa kuma na tsaye jikin gaban teble yana gyara attaruhu, dariyar dayayi yasa suka jiyo gaba Waya suna kallonsa baba ma dariyar yayi ya ce
"Kamin dariya mana, fisabilillahi da girmana da shekaru na akawo ni kicin asani gyara attaruhu wai lalle sai anyiwa surukata girki harda ni" Abbas dariya yayi sosai harda rike ciki yana kallon hajiyarsa data sha mur, ya karasa gaban Babansa ya karSi wukar hannunsa
"Abbas fita ka koma Waki kayi barcinka barsa Allah dashi za'ayi girkin nan,"
"Hajiya da dai kun barshi basai ayo order ba da safan nan ki wahalar min da Baba" hajiya batace komai ba taci gaba da abinda take, Haka Babanma Abbas ya gaida su ya fita yana dariya, sanda ya koma Wakin Rumana na zaune kan gado farkawarta kenan daga barci gaba Waya jikinta ciwo yake mata musamman ma kasanta wani raWaWin azaba take ji ko motsi ta kasa, kallo Waya ya mata ya shiga bathroom ya haWa ruwa mai Wumi yadawo cak yaWauketa daga gadon bai direta ko ina ba sai cikin ruwan daya haWa, wata karar azaba ta saki tana kokarin fitowa daga cikin ruwan
"A'a Hubbi daure ki zauna zaki daina jin zafin yi hakuri kinji" yafaWa a tausashe kamar mai shirin mata kuka
"A'a Kalbie bazan iya ba zafi nakeji wayyo Allah Anty zan mutu" hannunsa duka biyun yasa ya riketa ganin tana kokarin futowa daga cikin ruwan, bai saketa ba saida ya tabbatar ruwan ya yi sanyi kana ya fito da ita daga ruwan yace
"Yi wanka" juyawa yayi ya fita daga bathroom Win ya koma Waki ya zauna haWe da yin tagumi, ya zubawa kofar bathroom Win idanun yana jiyo zubar ruwan datake wanka,
kulawa ta musamman Abbas ke bawa Rumana satinsu Waya a jigawa suka koma Abuja, saiga Rumana a gidan Abbas gidan daya gama tsara yanda zaiyi rayuwa da Aimana, gaba Waya ya manta da Aimanah yanda yakejin Rumana yanzu bazaice ta wuce Aimanah a zuciyarsa ba amma kam sosai yakejinta a zuciya musamman yanda take da biyayya bata taSa masa musu ba iya tsawon zamansu, tana da tsafta batada son jiki ga iya girki da kwalliya.

Aimanah na kwance kan gado, yau gaba Waya batajin daWi zazzaSi take ji, Mustapha ya shigo Wakin yatarar da ita kwance
"reina har yanzu baki tashi daga kwanciyar nan ba" ido kawai ta zuba masa ta kasa ce masa komai, hannu yasa ya taSa jikinta yaji zafi zau
"reina bakida lafiya kizo na kaiki asibiti"
"Baby nifa lafiyata kalau, ina dai jin yunwa jikina kuma ba kwari bazan iya dafawa ba"
"Mai zaki ci to"
"Dambun shinkafa mai zogale da gyaWa"
"Yanzu reina ina zan sami dambu dan Allah yanzu da ranar nan" turo baki tayi gaba kana ta juya masa baya ranta Sace, dafe kai yayi shima baice mata komai ba yafita daga Wakin, kai tsaye gidan Ammi ya shiga yayi sa'a dawowarta gidan kenan daga makaranta gaisawa sukayi yai tsaye ya kasa ce mata komai, shi kunyarta ma yakeji jiya haka Aimanah tasa ta mata awara yau kuma gashi tazo da mata maganar wai dambu
"Yadai babban Mutum kazo kamin tsaye anan" shafa kansa yayi kana ya ce
"Ammi reina ce da rigima wai dambu zata ci ni narasa wannan cin nata" mirmushi Ammi tayi kana ta ce
"Badamuwa zan bawa Surayya ta kawo mata" Mustapha ya juya ya fita bayan yayi mata godiya sanda ya koma gida yatarar Aimanah har tayi barci, bai tasheta ya zauna gefanta yana kallon yanda take barci ta wani taSe fuska kamar mai shirin kuka ta cuno baki gaba, sumbatar kumatunta yayi ya fita daga Wakin, Sumayya ta gama shaka ganin yanda yaketa zuruftu wajan Aimanah amma bata ce komai ba zura masa idanu kawai tayi, Aimanah sosai taci dambun nan, yau kuma gaba Waya sai taji nan duniya ba abinda takeson jin kamshi sama da turaran Mustapha Wakinsa ta shiga ta rinka shan shana kayan sa harta gaji ta kira wayarsa
"Baby nidai kamshinka nakeson ji kadawo gida"
"Nadawo kuma ni bana ma kusa munje gwarzo nida Mas'ud"
"Baby kasan yanda nakeso naji kamshinka kuwa dan Allah kadawo"
"Ok gamu nan a hanya zanzo yanzu" shuru tayi nan barci ya kuma yin gaba da ita, sai farkawa tayi taga Mustapha a kusa da ita, jikinsa ta shige tana jin kamshin turaransa
"Baby ki yarda muje hospital na rantse bakida lafiya, abincin da kike ci yayi yawa ga yawan barci yau zaki iya kirga sau nawa kikai barci" tabuWe baki zatai magana amai yazo mata hannu tasa ta danne bakinta da gudu ta shiga bathroom na cikin falon ta fara kwarara amai kamar zata amayar da yan hanjinta, sosai ta galabaita, Mustapha na tsaye gefanta sai sannu yake mata, taimaka mata yayi tai brush suka fito yana rike da ita, zubewa tayi saman tiles tana juyi rikeda cikinta
"Wayyo Yayanmu zan mutu, wayyo cikina" gaba Waya hankalin Musty yatashi
"Baby kinga abinda nake gaya maki ko, zo muje hospital a...kafin ya rufe bakinsa wani aman ya kuma zuwar mata, wayarsa ya Wauka ya kira Ammi yagaya mata Aimanah ba lafiya, kayan jikin Aimanah data Sata ya cire mata ya taimaka mata tai wanka Ammi da Momy suka shigo lokacin Aimanah na kwance kan doguwar kujera tana murkusu su
"Mustapha mai kake jira baka ga yanda take ba akaita hospital" Ammi tafaWa hankali tashe ganin idanun Aimanah sun canza kala
"Ammi taki yarda cewa take na barta ta mutu a Wakinta"
"To biye mata zakayi" Momy tafaWa
"Wakko mata hijab" Momy tasa mata ta ruko ta suka fita, hankali tashe Mustapha ke tuki jefi jefi yana juyowa yana kallon Aimanah daketa kukan wayyo cikinta kirjinta kanta duk ta tashi hankalinsa har suka karasa Waya daga cikin hospital Win dake zoo road, nan da nan likitoci sukayi kanta aka Waura mata drip sannan nurse ta Webi jininta zuwa lap, bayan mintuna aka dawo masu da sakamakon Aimanah na Wauke da cikin sati biyar
"Sati biyar" Mustapha ya maimaita yana dariya, Ammi tai kasa da kanta tana murmushi Momy na faWin
"Alhamdulillah masha Allah, Allah abin godiya ubangiji ya raba lafiya"
"Amin" Mustapha yafaWa a fili, Ammi ta Wago ta kallesa
"Bakada kunya Musty a fili kake amsawa da Amin"
"Ammi taya zanki amsawa addu'a fa mai kyau Momy tayi"
"Zoka ajjeni a gida tunda ga Momy nan mai zanyi anan" ta fita bayan tayiwa Aimanah sannu, Momy tabi bayanta suna magana, Mustapha ya matso kusa da gadon da Aimanah ke kwance ya sumbaci cikinta, murmushi tayi tana kallonsa
"Daman wai duk cin nan Babynmu ne yaja"
"Baby na ce dai taja, nifa mace nakeson haifa"
"Ni kuma boy nakeso nasa masa sunan Daddyn daya haifa min mata ta" taSe baki Aimanah tayi tace
"Allah ya kiyaye ni mace zan haifa Saudat" dariya yayi yana kallonta
"Zan maida Ammi gida maizan siyo maki a hanya"
"Apple" tafaWa tana kautar da kai gefe, dawowar Momy Wakin yasa ya fita yana murmushi

Murjana gaba Waya abin duniya ya isheta tun jiya dataje chemist suka mata test suka tabbatar mata tana Wauke da juna biyu tayi kuka sosai daran jiya ita kaWai a Waki tayi nadamar da bata taSa irinta ba, yau kwanan amarya uku bata gari tayita kiran wayarta bata ma shiga bare ta Wauka hakanne yasa yanzu Murjana ta shiga wajan Sumayya, Sumayya da damuwa take cin ranta tana ganin Murjana ta fashe da kuka
"Murja ina cikin damuwa a gidan nan, son Mustapha zai kashe ni gaba Waya bana gabansa, kina gani kwanaki fa mota ya saiwa Aimanah benz ni kuma ya sai min da toyota, komai zaiyi sai nata yafi nawa haka ake hakane adalci Murja?"

"Hmmm Anty Sumayya kenan ke ki godewa ma Allah da wannan Win ma, kefa kika kawo kanki kika raba masoya Allah yayi kuma da rabon zama a tsakani komai ya rushe daman ai zaki ga abinda yafi haka yayi maki da kauna ma da bai sake ki ba, nifa masifar danake ciki tafi wacce kike ciki cikine dani fa harna tsawon wata uku ban sani ba" karaf maganar a kunnan Mustapha wanda ya shigo basu sani ba, hankali tashe yayi kan Murja da duka bugunta yake ta ko'ina da kafarsa
"Murja mu zaki wulakanta ki tozarta mu kibar mana abin faWa gayamin wane ya maki ciki ki gayamin cikin waye a jikinki" ganin taki magana ya shake mata wuya, idanunta suka firfito waje Sumayya ganin idanun Murja sun canza launi hankalinta ya tashi ta fice daga wajan da gudu ta nufi can cikin gidansu Mustapha, Murjana da taji azabar shaka ta ce
"Na na na Salim ne, salim ne yamin" haWata yayi da bango ya Wauke fuskarta da marin da azabarsa tasa saida taga wuta
"Waye salim Wan waye ina ne gidansu zaki magana ko saina zubar maki da hakora" hankali tashe Ammi da yaya Ahmad suka shigo da kyar yah Ahmad ya iya SanSare hannun Mustapha daga jikin murjana
"Mustapha bakada hankali ne mai Murja ta maka har haka dazaka mata irin wannan dukan na fitar hankali"
"Ammi ci ci cikene fa Murja, Murja ta cucemu ta Sata mana suna" Musty fashewa yayi da kuka kamar wata mace yabar Ammi da Ahmad ba buWaWWan baki, afusace Amarya da dawowarta kenan daga yawonta taga shugowar Sumayya hankali ta she kamar bazata shigo gidan Sumayyan ba sai kuma ta biyo baya taji maike faruwa, ganin Murja zaune kasan tiles tana numfashi ya kuma fusata ta ta karasa gaban Murjan tana tambayarta mai aka mata
"Mama Murja fa cike ne da ita" Sumayya dake can gefe rakaSe ta faWa tana kallon maman tasu
"Dan tana da ciki shine mai, a wannan zamanin ai ciki ba wata damuwa bace asibitocin da ake zubad da ciki ai yawa ne da su a garin nan" wasuma watan nin au nawa da aure ko Satan wata matansu basu taSa yi ba shine sabida hassada yata na Wauke da ciki zaku tara mata mutane, Ammi juyawa tayi tabar gidan ta koma sashinta,
"Amarya kinsan mai kike faWa kuwa yarki ce fa keda cikin shege" Ahmad yafaWa cikeda mamakin maganganun amarya
"Sai me Ahmad, abin kunya ai ba a kanta aka fara ba" Mustapha juyawa yayi ya haye samansa, Ahmad ya fice, Amarya ta ruko Murja suka fita suma, Sumayya kuka ta zauna tayi sosai na bakin cikin abinda yasami yar uwarta, labarin cikin nan dayaje kun nan Alhaji kamal har suma sai da yayi sabida tashin hankali, Murja tarinka kuka kamar ranta zai fita, tun tana basu Mustapha hauci har tadawo tana basu tausayi Alhaji Kamal sanda ya dawo hayya cinsa kasa magana yayi sai hawaye kawai dake bin kuncinsa tsawon lokaci Murja na gabansa tana kuka saida ya Waga kai ya kalleta kawai, Mustapha dake zaune a wajan tareda Ahmad, Musty yabata umarnin ta fita a Wakin, fita tayi tana waiwayowa tana kallon baban nata
"Abba kayi hakuri mai faruwa ta riga ta faru kasa karka furta kalma mara daWi akanta idan bazaka saka mata albarka ba kayi shuru kar kace komai Abba" Mustapha yafaWi haka jiki a sanyaye
"Sakaci nane Mustapha laifin komai a kaina yake na Wauki kaddara"
"Baba bakada laifin komai kwaWayinta itada mahaifiyarta shiya jawo komai, ta gaya min duk abinda yafaru dama wanda yamata cikin, zan neme sa muyi magana inyaso inta haihu sai ayi maganar auransu da ita suje su raini yaron"
"Hakan yayi Allah ya sauketa lafiya"
"Amin" suka amsa gaba Waya, Amarya na zaune a Wakinta gaba Waya abin duniya ya dameta ko kaWan batai farin ciki da samun cikin nan na murja ba a wannan kadamin data hango wani Alhaji daya mato kan Murja Win sanda ya ga hotonta a wayarta yace da gaske yana sonta da aure Alhajin Wan siyasa ne, abokin mijin Hanne ne matar ta rasu yanada yara biyar, sosai tayiwa Murja sha'awar auransa musamman ganin yanada kuWi kuma abin hannunsa bai dame saba hannunsa a sake yake,
"Murja cikin nan na waye?"
"Ance min cikin watansa uku a lissafina ciki na Salim ne shine wanda mukai ma'amala watanni uku da suka wuce"
"Kiramin wayarsa muyi magana" kiran wayar tayi Salim ya Waga bayan sun gaisa da Amarya ta masa bayanin cikin dake jikin Murjana, wata dariya yayi ta shaki yai kana yai fito ya ce
"Mama mama kenan ciki kuma ki tambayeta in zamuyi harka bana bata kwaya tana sha, kwayar hana Waukar ciki ita kullum nake bata tadai nemi uban Wanta acan bariki badai ni ba" Amarya katse kiran tayi tana kallon Murja
"Kindai ji abinda yace ko"
"Naji daga farkon tarayyarmu inya bani kwayar ina ca amma daga baya sai nake kin sha sai na masa wayo na zubar"
"Yanzu ai kinga wayo, tashi zakiyi muje a zubar da cikin nan bazaki bar min abin kunya ba cikin kishiyoyi"
"Mama zubarwa kuma, dan Allah kibar min cikin nan inason abinda zan haifa na yarda ko katsina ne ki kaini na haihu acan"
"Bazan kaiki ba na rantse da Allah sai kinzo munje an zubar da cikin nan" Murja ba yanda ta iya tabi Amarya suka sami wani asibiti anan aka birge cikin Murja wanda garin haka mahaifarta tasami matsala tanaji tana gani aka cire mata mahaifa yazamo itada haihuwa har abada" kuka take sosai da kuma istigifari tana rokon Allah ya yafe mata zunubanta, sanda Alhaji Kamal yaji labarin anzubar da cikin Murja kuma amarya ce taja nan take ya rubuta mata takardar saki uku yabata yace tabar masa gida bashi ba ita, Murja kuma ya bata sati Waya tak ta fito da miji yamata aure ko tabar masa gidansa tabi Amarya, Amarya ko gizo batayi ba dan ita a nata haukan taimakonta yayi yanzu ne zata fantama ta more dasu Hajiya Hanne, kai tsaye ma gidan Hanne ta maida komai nata sashi guda Hanne ta bata aka fara haWa ta da mata suna holewa........=?0?
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da shida*

Murjana gaba Waya duniya tayi mata zafi ta rasa wanda zata kawo har gashi yau saura kwana biyu wa'adin da Abba yabata ya cika, har Salim ta kira kan maganar auran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login