Showing 18001 words to 21000 words out of 95991 words

Chapter 7 - AIMANA complete by MAMI YUSUF DABO.doc

06 Mar 2025

5379

gashi har kin iya kalaman soyayya"
"Mahh" Aimanah ta faWa cike da kunya, mikewa Aimanah tayi tabar wajan tana dariya, Mah tabi Aimanah da kallo tana mamaki, ada in wani yagaya mata Aimanah zata so wani bayan Mustapha zata karyata amma hukunci na ubangiji yau ga Aimanah nason wani mutum fiyeda son datayiwa Mustapha.

Mustapha sun sauka lafiya a nageria kai tsaye jirginsu a kano ya sauka daga airport texzi yasamu ta kawo su har gidansu wanda baida nisa sosai da airport, ba wanda yagawa dawowarsu hakan yasa kowa na gidan ya shiga murna da dawowar Mustapha banda Amarya da damuwa gaba Waya ta mamayeta har ?ar rama tayi na fargabar halin da zasu shiga itada Sumayya Murjana ba karamar Sarna tayi masu ba hatta aikin da tayiwa Alhaji Kamal saida tabi inda suka binne ta tone komai shima gaba Waya ya canza mata, yau tsaka sai ganin Sumayya tayi a Wakinta saida gabanta yafaWi ganin Sumayya
"Ke kuma yazaki shigo min nan basai ki wuce gidanki ba, ni basai naje mu gaisa ba"
"Mama Musty fa cewa yayi na zauna zai neme ni" dafe kai Amarya tayi tana faWin
"Shikenan na shiga uku tamu ta kare" Murjana dake zaune a gefe dariya tayi tareda saka eair pies a kunnanta tana faWin
"Kuna ruwa"
"Allah wadaranki Murja ubangiji ya kwashe maki albarka yasaki a masifar da kika samu"
"Mama wannan wacce irin addu'a ce? kefa uwa ce in kina mata irin wannan baki saiya wahalar da ita"
"To Sumayya wahala ta nawa kuma ai wahala yanzu ta fara itace fa ta tone duk abunda muka bunne"
"Duk da haka Mama, Murja ai yarinya ce yarinta ke Wawainiya da ita dan Allah ki daina mata addu'a irin haka" Mama bata sake cewa komai ba taja hannun Sumayya suka wuce cikin Wakinta.

Mustapha kai tsaye Wakin Ammi ya shige yayi sa'a kuwa tana gida lokacin tana tsaye jikin firij zata Wakko ruwa taji an rungumeta ta baya bata zaci Al Mustapha bane duk zatonta Shaheed ne tasan shine mai mata haka
"Shaheed Allah ya nuna min randa zaka girma ka daina min wannan rungumar" jin ansake kankameta ba'ayi magana ba ga wani kamshin turare na daban da takeji yasa tasan ba Shaheed bane
"Hmm Amadu sakeni karka saka na faWi"
"Ammi kin manta dani, Allah yasa ma baki cire ni a jerin yaranki ba" Ammi goran ruwan hannunta ta saki ya faWi a kasa tai saurin janye hannunsa daga jikinta ta juyo tana kallon Mustapha
"Mai babban suna saida kabaro kasar nan kadawo ko?"
"Ammi na gama fa, bakiyi farin ciki da dawowata ba ko? nasani nasan za'ayi haka duba da tarin laifukan dana aikata"
"Nayi farin ciki sosai Yayansu na kuma godewa Allah daya dawomin dakai lafiya, ina matar taka?" Sata fuska Mustapha yayi ya juya zai fita Ammi ta rike hannunsa
"Ammi ba matata bace sakinta zanyi"
"Karka soma Mustapha ban amince kasaki Sumayya ba kaci gaba da zama da ita sannan ka zage wajan addu'o'i da Azkhar"
"Ammi bazan iya zama da ita ba, Ammi Aimanah tagama school ko?"
"Mubar maganar Aimanah jekayi wanka kazo kaci abinci mayi magana daga baya" Mustapha jiki sanyaye ya fita daga gidan zuwa gidansa, gidan yayi kura sosai, dole yadawo gidansu Wakin Ahmad yai wanka ya shirya, yasa Surayya itada Shaheed su gyara masa gidan, kafin ya gama wankan Ammi ta haWa masa abinci ya zauna taci abincin sosai saboda yayi kewar abincin gida nageria sosai, yana gama cin abincin yayi hamdala yana kallon Ammi
"Ammi muyi maganan Aimanah so nake naje na ganta na wanke kaina"
"Mustapha" Ammi ta kira sunansa tana kallonsa "Kayi hakuri bazan munafunce ka ba, Aimanah tasami wani auranta ma kwanaki suka rage" da sauri ya mike tsaye yana kallon Ammi yakasa cewa komai yai tsaye kan Ammi baki buWe so yake yayi magana amma yakasa saboda wani abu daya tokare masa a makoshi, yakoma ya zauna saman kujera ya kifa kansa saman teble, wani irin bugu zuciyarsa keyi harta Ammi dake zaune kusa da shi tanajin bugun zuciyarsa jin shiru tsawon mintina Mustapha bai motsa yasa Ammi ta Wora hannunta a kansa, Wagowa yayi ya kalli Ammi idanunsa sunyi ja sosai kamar garwashi Ammi hankalinta ya tashi sosai tasani daman tasan za'arina wai ansaci zanin mahaukaciya tasan tsananin son da Al'mustapha kewa Aimanah,
"Al Mustapha kayi hakuri kaWau abin nan a matsayin kaddara sannan kasa a ranka dama can Aimanah ba matarka bace"
"Ammi kaddara kaddara fa kika ce, sai in tsaya ina nan a raye a aduniya ina numfashi wani can wawa ya aure Aimanah,Allah kar yasa naga wannan rana, da wani ya auri Aimanah ina raye gara na mutu nabar duniya, Ammi wannan kaddarar tamin nauyi bazan iya Wauka ba, Ammi gayamin wacce addu'a akeyi mala'ikan mutuwa yazo ya Wauki ran mutum" Ammi ta mike tsaye tareda kama hannun Mustapha ganin yanda jikinsa ya fara rawa, kalaman dake futowa daga bakinsa kaWai sun tabbatar mata da Mustapha baya hayyacinsa, bedroom Winta ta kaisa ta zaunar dashi gefan gadonta ta ce
"Mustapha kwanta ka kaji barci inka tashi zakaji sauki a zuciyarka"
"Ammi barci bazai iya Waukata a wannan yanayin ba vani aron makullin motarki naje wajan Aimanah"
"Mustapha bazan bari ka fita a wannan yanayin ba ka kwanta nace" bazai iya masu da Ammi ba hakan yasa ya kwantar da kansa saman filon Ammi
"Kayita hasbunallahu wan'?wani'imal wakil zuciyarka zatayi sanyi" yajima yana kwancan yana ambaton hasbunallahu har yaji salama a zuciyarsa Ammi tana can Kicin ya lallaSa ya fice daga gidan.

......Aimanah a shirye ta fito daga Wakinta gidan shiru ba kowa, kowa ya wuce wajan aikinsa ita kaWai ya rage a gidan itama yau dan bazata fita da wuri ba, tana fitowa compount taga shigowar motar Ammi fasa karasawa wajan motar tata tayi ta nufi motar Ammi, motar Ammi tinted ce na waje baya ganin na ciki amma na ciki yana iya ganin na waje, buWe murfin motar Aimanah tayi cikeda Wokin ganin Ammi kasancewar sun jima basu haWu ba
"Ammi Wellcome" Da sauri Aimanah tayi baya tareda dafe kirjinta, tsaye tayi tana kallon Musty dake jingine jikin mota yana aika mata da zazzafan kallon love wanda ya kusa tarwatsa zuciyarta, tabbas yasani bata jure irin wannan kallo ko acan baya bare hanzu, juyawa tayi zata bar wajan da sauri yakira sunan ta
"Aimaah" cak ta tsaya ta kasa tafiya na ?an sakanni can kuma yaci gaba da tafiya da sauri ta nufi motarta, tasa makulli zata buWe motan Al'Mustapha ya Wora hannunsa saman nata ya zare car key Win daga jikin mirfin motar ya zirasa a aljuhunsa ya harWe hannayansa a kirji yana kafe Aimanah da lumsassun idanunsa masu kama dana maijin barci.....
'
*Saura kiris adaina fitar da Littafin Aimanah za'a daina posting Winsa a ko wanne group sai Aimanah fans group da Aimanah comment section idan har kinsan kinason cigaba da karanta Aimanah maza yi save Win wannan lambar 07039793439 kiyi magana ta whatssapp zatayi adding naki a group Win da zaki karanta hankalinki kwance batare da ko sisinki ba*
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048:

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo>?p?

&? *First Class Writer Asso*&?
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha biyu*


.....Aimanah kasa jure kallon nan tayi hakan yasa tayi kasa da idanunta gabanta na cigaba da dukan uku uku
"Aimaah nasani ni mai laifi ne a wajanki, kiyi hakuri ki yafe min bada sanina hakan ta faru ba"
"Kamin shiru ka kyaleni Al'Mustapha ka bar nan wajan bana sonka bana kaunar ganinka" Aimanah tafaWa tana rushewa da kuka
"Aimaah please stop craying kukanki kin sani yana taSan zuciya kiyi shiru muyi magana ta fahimta"
"Na fahimceka? wazan fahimta? kai can a baya mai yasa katafi ka barni da ciwo a zuci sai yanzu kadawo kace na fahimceka, Musty nariga nawuce level Winka kaje can ka zauna tareda masoyiyarka wacce ka guji kowa sabida ita"
"Aimah komai zan faWa maki bazaki gane ba ki bani dama a karo na biyu a zuciyarki"
"Zuciyata a yanzu babu kai Abas ne aciki shine mai mulkin zuciyata dan Allah indai zancan soyayya ne yakawo ka kabar nan"
"Bazan bari ba Aimah yazama dole ki tsaya muyi magana, ashe daman har akwai wani da zuciyarki zata so bayan ni?"
"Kasa a zuciyarka ban taSa soyayya da kai ba, lokacin dana so ka bansan za?i da Wacin so ba, kasani a yanzu bana sonka! bana sonka!! bana sonka!!! nafaWa bana kaunarka" taci gaba da kuka tareda kwasa da gudu ta shige falo ta rufo kofa, da sauri yabi bayanta kafin yakai harta sakawa kofar key da karfi yake buka kofar yana faWin Aimah Aimah please ki buWemin kofa"
"Bazan buWe ba kafita kabar mana gida mugu macuci mayaudari azzalumi"
Aimanah ta dafe kirjinta datake ji yana wani irin bugawa da sauri sauri "Mai yasa kadawo yanzu? mai yasa zaka shigo rayuwata a yanzu, Abas kazo ka Wauke ni nadaina ganinsa" haka tayita surutai bayan ta kulle kofar tana jiyo sa yana rokonta amma takasa cewa komai kuka take sosai na tausayin kanta.

Abas yau kwanansu uku kenan cikin jeji sun fafata da ?an ta adda sosai an kashe wasu dayawa a cikinsu yayin da wasu suka ji mugayan raunika, Abas yana cikin waWanda sukayi rauni sosai a hannunsa hakan yasa suna dawowa bareck aka yi asibiti da su, ya kira wayar Aimanah tafi a kirga amma bata shiga hakan ba karamin tada masa hankali yayi ba, ko raunin hannunsa bai Waka masa hankali ba kamar rashin shigar wayan Aimanah, Anty Ummi ya kira ita ta tura masa lambar Mas'ud shima yinin ranar yanata kiran lambar tana shiga amma ba'ayi pickin ba, kallon matashin sojan dake tsaye kusa da shi yayi ya ce
"Joseph Wakko mota ta a gida ka kaini kano"
"Amma oga kano yanzu dare yayi kafin mu isa sha biyun dare zatayi fa"
"Umarni na baka ba cewa nayi ka bani shawara ba" Abas hanunsa nannaWe da bandeji ya shiga mota Josepha kejan motar sai Hilux guda Waya mai cikeda sojoji da zasu masa rakiya zuwa kano, kamar yanda Joseph yafaWa kuwa basu shiga kano ba sai sha biyu da minti ashirin da biyar na dare, hotal suka kama Abas yana Waki Waya tareda Joseph dake kula fa shi, Daran ranar idon Abas baiga barci ba, hankalinsa a tashe yake da tuna nin mai ya sami wayar Aimanah, kafin bakwai na safe yagama shiri yata shi Joseph dake barci ya na gaya masa yata shi zasu fita
"Sir zan iya yin wanka?"
"Kasan zakayi wankan ka kwanta kanata barci, tashi mu tafi bana da lokaci inmun dawo ka yi wankan kafin mu wuce jigawa" Joseph haka ya tashi suka wuce, karfe takwas na safe a kofar gidansu Aimanah tayiwa Abas, mai gadi yasa yayi masa sallama da Aimanah, lokacin Aimanah fitowarta kenan daga Wakin barcinta sakon Baba Sunusi ya isketa tana da bako a waje, daga farko cewa tayi bazata fita ba a zatonta Al'Mustapha ne sai da Baba sunusi ya ce mata Abas ne, cikeda Woki ta shiga Wakin Mah tafaWa mata Abas na waje yana kiranta
"Aimanah da safan nan, karki fita ki cewa Mus'af ya shigo da shi falon baki" Aimanah tafaWawa Mus'af ya fita ya shigo da shi, Aimanah Kicin ta shiga tana gayawa Haule mai aikinsu a dafa mata shayi yai kayan kamshi a soya plantein da irish ra fice zuwa falon baki, Joseph ta hanga tsaye a kofar Wakin ta karasa, Joseph ya kame tareda sara mata
"Good morning Madam"
"Morning ya kake ya aiki" bata jira amsar saba tayi wuf ta shige Wakin sabida ta Wokantu taga Masoyinta abincin ruhinta, cak taja ta tsaya tana kafe sa da idanunta wanda shima itan yake kallo da sauri ta karasa kusa da shi ta Wora hannunta saman hannunsa mai ciwo idanunta na zubar da kwallah ta ce
"Kalbie maiya sami hannunka?"
"Ina wayarki?" mirmushi tayi tai saurin tashi ta koma saman kujera ra zauna tana sake kafe sa da kallo, ita gaba Waya ma ta manta da wata waya tun shekaran jiya data kashe wayan saboda masifar nacin kiran da Al'Mustapha keyi mata
"Ki bani amsata Hayatie" Aimanah turo baki tayi gaba tareda kauda kanta daga kallonsa
"Ni nafara tambayanka fa Kalbie maiya sami hannunka?"
"Harbi ne ba wani babban ciwo ba"
"Wayata ta sami matsala ta Wauke gaba Waya, Yah Mansur yace zai turomin da wata" shiru Abas yayi yana kallonta yanayin yanda tayi magana kawai jikinsa yabasa ba gaskiyya ta faWa masa ba hakan yasa ya ce
"Mus'af baya nan ne, inhar wayarki lalacewa tayi nasan bazai taSa bari yinin ranar ta wuce batare da ya canza maki ba"
"To karya nayi kenan?" Aimanah tafaWa da damuwa a fuskarta ganin ya ramfo ta,
"Ni na isa na ce Hayatie tayi karya kawai ban karSi maganar bane"
"Kaci abinci?" Aimanah ta waske da masa tambaya
"Banci ba banama jin yunwar idanuna kawai so suke suga Sarauniyata mai mulkin zuciyata" mikewa Aimanah tayi tana faWin
"Ina zuwa" ta fice daga Wakin yabita da kallon yana jin wani yanayi na daban na shigar sa, saurin rintse idanunsa yayi tareda kwantar da kansa saman saman kujeran, zuciyarsa na bugawa da matsanancin soyayyar Aimanah.

Kicin Aimanah ta koma ta taya Haule suka gama shirya komai ta sa Haule takaiwa Abas ita kuma ta koma ciki wajan Mahh, Abas godiya ya yiwa Haule ya umarce ta data Wibarwa Joseph ta bashi ya koma mota yayi breakfast, kusan mintina goma sha sannan ta koma Wakin har sannan baici komai ba daga cikin tarin abubuwan da aka ajje masa, kwansa kwance saman kujera ta shiga Wakin, buWe idanunsa yayi ya kalleta sau Waya ya maida idanunsa ya rufe,
"Kalbie baka ci ba wai?"
"Bazan iya ciba ko zaki bani a baki, hannun dama na keda ciwo" Gaban teble taje ta haWa masa shayi mai kauri a Mug ta zuba irish da plantein a plate ta koma kusa da shi ahankali take basa yana karSa sai wani narke mata yake kamar wani karamin yaro, baici dayawa ba ya ce
"Hayatie am full" hararan shi tayi ta Sata fuska
"Umm uhmm Kalbie baka koshi ba jibi fa kaWan kaci"
"Allah na koshi Hayatie rabon dana ci abinci da yawa irin haka tun kafin na haWu da ke, daga sanda kika shigo zuciyata na kasa sakewa naci abinci da yawa kullum far gaba nake da tsoron kar wani yazo yamin kwace bazan iya wani sakewa naci abinci sosai ba sai randa aka mikamin ke gidana, daga ranar inaga abinci sai kin rinka kwacewa" sosai Aimanah tayi dariya kafin ta ce
"Naji to yanzu shanye wannan tea Win" tafaWi haka tana Wora masa Mug Win a kan laSSansa baki ya buWe tana basa a hankali harya shanye gaba Waya, sun jima suna hira kamar bazasu rabuba kafin yatafi bayan yaje sun gaisa da Mah.

Ammi ta kalli Al'Mustapha dake lulluSe cikin bargo sai rawar sanyi yake ta ce
"Dan Allah Mai babban suna katashi kasha tea Win nan, sai lallashinka nake kamar wani karamin yaro, rabon da kaci wani abu fa tun jiya da safe"
"Ammi kimin addu'a mutuwa zanyi Aimanah ta guje ni ta manta dani bata son gani na"
"Al'Mustapha ka kiyaye ni kai wanne irin mutum ne mai taurin kai da rashin magana, sau nawa na gaya maka ka futar da Aimanah a ranka kananun mutane kake so mu zama" Mustapha ya lumshe idanunsa tareda buWe su akan fuskar Ammi ya ruko hannunta ya Wora a kirjinsa
"Ammi taSa kiji yanda zuciyata take bugawa na tabbata son Aimanah shi zaiyi ajalina" Ammi ta zauna gefan gado ta runtse idanunta tareda saurin Wauke hannunta daga kirjin Mustapha tai shiru, Ahmad dake tsaye a Wakin shima zaman yayi kusada Mustapha yana kallon sa cikeda rausayawa.

Amarya gaba Waya abin duniya yadame ta ganin yau kwana biyu kenan Sumayya na gidan Mustapha baice masu komai ba, kullum cikin zulumi take da fargabar karya kawo masu takardar saki
"Mama ina kika sakamin wayata ne?" Murjana ke faWa tana tsaye kan Amarya
"Ban sani ba shegiya ?ar banza"
"Amarya ki daina zagina karna rama wata rana kiji haushi, ni ki bani wayata Mas'ud ne bazan daina waya da shi sabida shi zuciyata ke so kuma shi zan aura, shi yayi min alkawarin indai na tone komai zai aure ni"
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Murjana daman sabida Mas'ud kika tona mana asiri" Amarya ta shaki wuyan Murjana tana kokarin kasheta da sauri Sumayya ta shiga tsakanin su ta SanSare Murjana da ga jikin Amarya da kyar wacce tuni ta fara fitar da numfashi
"Allah ya isa tsakani na da ke, ubangiji ya kwashe maki albarka kuma yanda kikai sanadin asirinmu ya tonu kema bazaki taSa samun masa'ud Win ba ko zanyi yawo tsirara bazan taSa bari ki auri wannan munafikin ba"
"Karki bari mana badai shiga bokaye bane nima zanbi mu zuba ni dake sai na sake tarwatsa komai, saina faWawa Abba har zuwa kike wajan boka kina kwana da shi mazinaciya" Murjana tafaWi tana haki, Sumayya hannu tasa ta Wauke fuskar Murjana da mari
"Bakida hankali Murja uwar tamu kike kira mazinaciya a gidan ubanki tayi zina"
"Gidan ubanki dai karki sake zagina dan wallahi zab iya ramawa" fuu Murja taja mayafinta dake ajje kan hannun kujera ta fice daga gidan gaba Waya, Amarya ma mayafin nata ta Wauka ta fice daga gidan aka bar Sumayya ita Waya a Wakin, karan farko kenan da Sumayya taji Wakin yayi mata kunci ta fito tsakar gida kawai ta tsinci kanta da shiga Wakin Ammi, tabi Wakin da kallo karan farko kenan data taSa shigowa sashin Ammi, babban falo ne tangameme daya sha manyan royal cheir daga can gefe kuma babban danning ne sai wasu set na kujerun acan gefen dama na Wakin kofofi biyu ne manne a bangon Wakin daga kudu alamar Wakuna ne sai Waya kofa daga Sangaran yamma nan ma da alama Waki ne, sau biyu tana sallama sai ana uku taga an buWe Waya daga cikin kofofi biyun dake jere da juna, Ammi ce ta fito da murmushi a fuskarta ta ce
"Sumayya sannu da zuwa kin biyo mijinki ko?" Sumayya ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi ta tsugunna har kasa ta gaida Ammi
"Tashi tashi Sumayya zona shiga dake yana Wakin Ahmad bayajin daWi shiyasa ma bance ki koma gidanki ba" Wakin data fito suka koma ciki inda ta hangi Mustapha kwance yana barci
"Kinga ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login