Showing 18001 words to 21000 words out of 139085 words

Chapter 7 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

shi ya shiga ya yi shirin kwanciyar shi sannan ya d'auro alwala, raka'a biyu ya samu damar yi wani nauyayyen bacci ya sure shi akan sallayar, daga wannan bacci ne Allah ya karb'i abin shi.


Mutuwar nan ta girgiza mutane sosai, musamman Sadiya da ke kwance asibiti ba ta san me ake yi ba, Khadija ma yan uwan ta kad'ai take iya yarda da su, amma haka ko da lokaci ya tafi kowa ya manta, sai dai ciwon na nan a zuk'ata, dukansu mazan babu wanda bai da aikinyi mai kyau, hakan ya sa suke matuk'ar kula da k'anwar su, sosai suke shagwab'a ta, ga yarinya na girma amma gatan da take samu yasa kullum kamar yarinya.




Tun Khadija na da shekara sha biyar Ashir ya gwangwaje ta da moto, duk da sauran yan uwan kowa ya so ace shi ya siya mata, amma haka suka hak'ura tun da ya fisu zafin nama, wannan lokacin ne aka musu rabon gado, kowa ya tashi da na shi kason mai tsoka, na Khadija kuma tace a bawa Ashir da Mansur su ci gaba da juyawa dan sune suka fi sha'awar kasuwanci, mamansu ma dama ta na nata kasuwanci, dan haka ta ci gaba daga inda ta tsaya.


*Duk* wata ba'a daina abin da Alhaji Ahmad ya fara ba, ana yanka rago ayi sadaka, sannan akanyi waina ayi miya sai su aika inda mahaifinsu ke zama da yamma wajen abokanan shi, haka rayuwar ke tafiya har lokacin da Khadija ta ci jarabawarta kuma sakamako mai kyau, babbar walima yayyun ta suka shirya mata a bazata, kayan da suka shirya mata suka sata ta saka suka tafi da ita babban wajen cin abinci, k'awayenta da maza da dama ta samu wanda su ka yi karatu tare, ta ji dad'i sosai a ranar, anan ta yanka (πŸ˜‚bansan me zan kira cake da hausa ba, amma bara nace mu ku panke) saida ta bi duka yan uwanta biyar ta saka mu su a baki kafin k'awar ta *Kaltume* da *Salamatu*, haka aka gama shagali aka yi murna sosai aka watse.




*Komai na da mafari a rayuwa*, matar Ashir da Bashir da mama sun gama waina, sai dai babu mai kaiwa, Habib kad'ai ke gari kuma shi ma ya na wajen d'aurin auren abokin shi a wani k'auye *Dak'oro*, hakan ne ya tilasta mama cewa Khadija ta shirya sai ta kai a kan moton ta, shiryawa ta yi tare da Kaltume da su ke kusa da juna suka tafi, Kaltume ita ke rik'e da kwanukan abincin a baya, sun isa lafiya su ka kai abincin, cikin ladabi su ka gaishe da dattawan, da kansu su ka wanke babban faranti suka zuba mu su wainar sannan suka d'aure kwanukan su ka mu su sallama, kasancewar akwai rairai kafin su hau titi ya sa Kaltume ba ta hau ba ta na jiran Khadija ta fita daga rairain, cikin rashin sa'a wani tsoho ya taho zai shiga shagon d'inkin shi, tana murd'awa sai kuwa ta bige tsoho ya fad'i, dukan su suka fad'i k'asa da azama aka kawo mu su d'auki, duk da masuburbud'ar zafi (shagama inji salim, salansa inji mak'obtanmu) ta tab'a ba bai dame ta ba, tsohon mutane data bige shine a gabanta, kuka take ta na tambayar tsohon bai ji ciwo ba, duk da k'afar shi da ta buga yaji ta na masa ciwo haka ma gwiwar hannun shi daya fad'a samanta, amma sai ya nuna ba komai kawai ta tafi, cikin abokan mahaifin nata ne ya lura da hannun shi har jini ya d'an fara fitowa ta cikin riga, nan aka ce a kai shi likita Khadija tace ita ma za ta je, da k'yar suka lallab'a ta dan ta tafi gida, amma duk ta d'aga hankalinta sosai sai hawaye take, wani daga cikin dattawan ne yace "Kinga Khadija ki daina kuka, zai samu sauk'i, kinga ciwon ai kad'an ne, Allah ne ya aiko dole hakan ta faru, yanzu kije gida ki huta, zuwa gobe sai kije godanshi ki dubo shi ko, hakan ya yi?"


D'aga kai ta yi alamar eh, sai da ta hau moton Kaltume ma ta hau sannan tace "Ina ne gidan?"


"Gidan ya na nan yan banana wajen masallacin ladan."


Ta na shan majina ta wuce zuciyar ta ba dad'i ko kad'an, tun da suka je gida daf da magrib sun samu duk yan uwan ta sun dawo daga uzurirrikansu ban da Naseer dake karatu a *France*, yanda ta shigo tana kumboro baki ta na murzar ido ta cire gilashi ne ya sa Ashir zaburowa ya kamo hannun ta yana fad'in "Auta lafiya? Me ya same ki kike kuka?"


Zaunar da ita ya yi ya karb'i gilashin ya maida mata ya kalli Kaltume yace "Umma waya tab'a ta?"


Cikin taushin murya Kaltume tace "Wani tsoho ta bige, ita ma kuma ta fad'i, amma duk ta damu."


Bashir da Mansur a zabure suka matso Bashir na fad'in "Subhanallah, auta ba ki ji ciwo ba?"


Dukansu duba jikin ta suke ko sunga ciwo amma shiru, Mama na gefe tana kallonsu ta yi shiru, a hankali Khadija ta janye siket d'in ta ta nuna musu in da take jin zafi, wajen har ya yi bak'i ai sai suka zabura da ganin wannan d'an ciwo, da gudu Habeeb ya wuce d'akin shi ya d'auko maclean dan a shafa mata, tuni kuma Bashir da Ashir sun umarci matansu da su d'auko musu suma, sai ga abun wanke hak'ora har hud'u a gaban su, nan dai suka shafa mata akayita lallab'a ta har zuwa dare.


Kwance take a d'akin ta cikin bargo yayin da suk yan uwan ke kewaye da ita sai kanta dake kan k'afafun mama, d'aya hannunta na sak'ale cikin hannun Habeeb ya na shafawa, sai mama dake shafar kanta Ashir kuma na karanta mata wani littafi mai sunan *magana jari*, lumshe ido take sosai ta na so tayi bacci, janyo hannun ta tayi daga hannun Habeeb ta tusa shi ta k'asan gilashinta ta murza idon ta tana turo baki gaba, ganin ta rufe ido ya sa Ashir matsowa kusan fuskarta yace "Auta."


Bud'a ido ta yi ta kalle shi, cikin murya k'asa k'asa yace "Albishirinki."


"Goro." Ta fad'a ta lumshe ido, d'orawa ya yi da "Na biya mi ki kujerar hajj, tare da Mama za ku tafi wannan karan insha Allah."


Zunbur ta tashi zaune tace "Da gaske yah Ashir? Kai amma naji dad'i sosai, nagode."


Da k'arfi mama ta maida kanta akan cinyar ta tace "Dan Allah ki kwanta ki yi bacci ko muma mun samu mu rintsa."


Daddab'a ta ta ci gaba da yi har bacci ya d'auke ta, addu'a mama ta shafa mata Mansur ya cire mata gilashin ya aje mata gefenta kafin suka kashe mata wutar d'akin suka fita, har ga Allah wannan kulawar da suke nuna mata Mama tasan ta yi yawa, haka kuma matar Bashir da Ashir suna jin haushin hakan, saboda kai tsaye suna nuna musu farin cikinta yafi nasu, kulawar da suke nuna mata basa nuna musu kwatankwacin ta, shi ya sa mama ke fatan su rage ko dan kasancewar ta ya mace, dan ma ita d'in yarinya ce mai son aiki da kazar-kazar.




*Allah ka k'ara mana k'oshin lafiya, sis Alawiyya Allah ya baki lafiya.*
12/01/2020 Γ  22:18 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘






_SAMIRA HAROUNA_




*Littatafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._




*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›




```Fatan alkairi masoya```




_Bismillahir rahamanir rahim_




*10*






Washe gari da safe Khadija ta shirya su ka tafi tare da Habeeb ya kai ta gidan tsohon da ta bige, sai da aka mu su kwatance su ka isa gidan, a k'ofar gidan Habeeb ya tsaya ita ta wuce ciki ta na rabka sallama tun daga soro, kasancewar safiya ce kusan matasan gidan ba su riga sun tafi harkokinsu ba, dan wasu ma su na cin d'umamen tuwo ta same su, izini aka mata ta shiga ciki, gaba d'aya ta had'e tace "Ina kwanan ku."


"Lafiya k'alau." Aka amsa mata, d'orawa ta yi da "Antashi lafiya."


"Lafiya lau mu ka tashi."


"Ya mai jiki?" Ta fad'a ta na d'an kallon tsohuwar, da fara'a tsohuwar tace "Mai jiki da dama."


Da mamaki tsohuwar ta kalleta a nutse tace "Sannu ko yan mata?"


"Sannu Mama." Ta fad'a da murmushin ta, tsohuwar ce tace " Sai dai kuma ban shaida ki, gashi na ji har ki na tambayar jikin malam ko?"


Da k'ayataccen murmushi tace "Eh mama, na zo duba jikin su ne, ba za ku shaida ni ba dama, ni ce hatsarin nan ya faru tare da ita."


"Ayyah! Sannu ko, mai jiki ai da sauk'i, yanzu ma haka fitowa ya yi zai fita shago, babban yaron na shi ne ya hana shi yace ya koma ya kwanta, ya na ciki, muje na rakaki ki gan shi."


Ledar hannunta ta sake mayar da ita d'aya hannun saboda nauyin ta kafin ta wuce, ta cire takalmi za ta shiga kenan Usman shi kuma ya fito, saida jikinsu ya had'e da sauri ta ja baya, sai dai kuma ta na ja da baya ta kai wa tsohuwar karo, da azama ta sake matsawa ta na fad'in "Yi hak'uri, yi hak'uri dan Allah."


Wani banzan kallo Usman ya mata ya rab'ata ya wuce ya saka takalmin shi, Khadija kam ajiyar zuciya ta saune ta k'arasa shiga ciki, zaune ta yi kusan katifar da tsohon ke zaune ta aje ledar hannun ta, da murmushi tace "Baba ya jiki?"


Shima da murmushin yace "Jiki da sauk'i 'yata, ya na ki jikin? Ince dai ba ki ji ciwo ba ko?"


"A'a Baba, ban ji ciwo ba."


"To Allah ya k'ara kiyayewa, Allah ya kare mu daga sharrin k'arfe."


"Amee Baba, kuma dan Allah ka yi hak'uri, laifi na ne abin da ya faru."


"Ah haba haba, 'yata ba laifin ki bane, Allah ne ya aiko ai, sai dai Allah ya k'ara kiyayewa, kuma ku dinga kula ku na tafiya a hankali."


"Insha Allah Baba, nagode, ni zan wuce."


Tsohuwar ce tace "Sai tafiya y'ar nan, ko ruwa baki sha ba."


Da fara'a tace "Ba komai mama, ai daga na ke, kuma tare da yaya na mu ke, ya na sauri zai fita aikin shi na tsayar da shi."


"Kuma gaskiya hakane kam karki tsayar da shi."


Tashi ta yi ta fito ta musu sallama, tun ranar kuma Khadija ba ta sake samun damar dawowa gidan ba saboda shirye shiryen tafiyar su k'asa mai tsarki, haka lokacin tafiya ya yi kuma su ka tafi sama tare da mama da matar Ashir da ta Bashir, dan dama an had'a su da mama ne saboda dukansu zuwan su ne na farko, masha Allah sun je lafiya kuma sun dawo lafiya, dukansu sun canza musamman Khadija da dama Allah ya hallice ta da kyanta, inda ta k'awata haurunan ta da hak'oran makka guda biyu, saida su ka yi sati su na karb'ar bak'i da huta gajiya, sai dai har lokacin nan Khadija na tunanin tsohon da ta buge, tunanin ta kawai ita ce silar kwantawar shi, dan haka ta shirya da dare tare da ware kayan tsaraba dan ta kai mu su, sanye take cikin bak'ar doguwar riga har k'asa mai walkiya da kwalliya, takalma sai d'an kwalin da ta mi shi sassauk'an aji a saman kan ta, farin gilashin ta mai kewaye da bak'ar kala ya dace da fuskar ta da kuma rigar, farin man leb'e ne kawai ta shafa, yau kuma Naseer ne ya shirya zai kai ta wanda ya zo hutu, har k'ofar gidan ya dire ta shi kuma ya fito ya tsaya bakin motar, ta na zura kai cikin soron sai duhu, wayarta ta fara k'ok'arin fitowa da ita daga cikin k'aramar jakarta sai kawai ta ji ta zube a k'asa, πŸ˜‚ "Ahhhhhh."


K'arar da ta saki kenan lokacin da Usman ya yi gaba da ita ta fad'i zaune a k'asa, wayarta da ledar hannun ta da kuma gilashi duka sun kama gabansu, da sauri Usman ya kunna wutar ta shi wayar dan ganin wacece, " *mai gilashi*." Abinda ya fad'a kenan, sai dai mamaki ne ya lullub'e shi ganin Khadija nata lalubar inda gilashinta ya ke, tambayar da ta zo mi shi ita ce "Ba ta gani ne? Ko kuma har yanzu duhun take gani?"


Ya na kallon ta har ta kai hannunta kan gilashin ta, da saurita d'auka ta mak'ala a ido, tarau taga Usman zik'au a gabanta da hasken fitila, da sauri ta mik'e tsaye ta na tattare kayan da su ka zube, shi kam sai ya ji ta ma ba shi haushi, guntun tsaki ya yi ya wuce ta cikin b'acin rai ya fice daga gidan yana fad'in "Idan dai ki ka ci gaba da anfani da gilashi haka kawai, wallahi kin kusa zama makauniya, in banda hauka har cikin dare ma sai kinyi fama da gilashi, kuma yanzu haka ma na masu larurar ido ne take sakawa."


Ya na fitowa ya ga Naseer tsaye, gaisawa su ka yi cikin sanin juna, dan da Usman da Ashir sunyi aji d'aya a makarantar boko, hakan ya sa su ka zama abokai sai dai ba abota irin sosai d'in nan ba, ita ma data shiga ciki k'anan Usman da suke uba d'aya ne ya mata iso har d'akin babansu, bai gusa daga wajen ba ya na kallon fuskarta da murmushin ta ya na jin kamar yace ya na son ta, har ta taso ta fito ya rakota k'ofar gida, kallon juna su ka yi ita da Usman da suke ta hira da Naseer, sallama su ka yi Naseer ya shiga mota ita kuma ta juya ta kalli *Mannir* tace "To sai anjima ko."


"Sai anjima, sai yaushe kuma?"


D'an wasa ta yi da idon ta tace "Kowane lokaci ma za ka iya gani na."


"Shikenan to, sai anjima."


Bud'a k'ofar motar ta yi za ta shiga sai kuma ta ga Usman sai wani kallo ya ke mata kamar irin ya na jin haushin ta, dan haka ta rufe k'ofar ta zagayo wajen shi ta kalle shi cikin taushin murya da nutsuwa tace "Na ga kamar haushi na ka ke ji saboda abin da ya faru, dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min, duk da nasan laifi na ne, amma kuma Allah ne ya aiko, ka gafarce ni idan na b'ata ma ka rai."


Juyawa ta yi ta shiga motar, shi kuma juyawa ya yi ya na jan wani tsakin, bin Mannir ya yi da harara yace "Sai ka rufe bakin to sakarai, har da wani sai yaushe za ta dawo, to uwar me za ta maka idan ta dawo?"


Bai jira me zaice ba ya wuce sabgar gaban shi, tun daga ranar kuma Khadija ba ta sake komawa gidan ba, dan lokuta da dama ta kan ji ta na so taje saboda tsohuwar da tsohon masu kirki da kuma saka mata albarka, amma idan ta tuna Usman sai ta share kawai, a cewar ta wannan ba shi da kirki ko kad'an, gashi da d'acin rai da zuciya, alhalin Usman kuma ba ma mazauni bane, baya cikakken sati a gida bai tafi sabgar gabanshi ba, musamman ma da iyayen ke yawan mi shi magana akan ya yi aure, shi ya sa ba ya son zaman gidan dan duk motsin shi sai suce da ya na da aure da anyi kaza, aure ba shine gabanshi ba, ya na so ya taka wani mataki kafin ya yi aure, shi ya sa ma shekarun shi *talatin da d'aya* ba sa damunshi, k'annan shi mata yan biyu da suke bi mi shi tuni suka hayayyafa a gidajensu, sannan d'aya k'anan shi da suke uwa d'aya ma yayi aurenshi shekara biyu data wuce, k'annan shi mata kuma hudu ne a gidan mazajensu, duk iskancin da suke mi shi ko a jikinshi kam, neman sisi da kwabo yasa a gaba.




*Bayan wata bakwai* Khadija har ta fara karatunta na jami'a (lycΓ©e) hankali kwance, ta yi sababbi k'awaye sosai a ciki ne ta had'u da *Barira nagoma* wacce unguwarsu ke kusa da gidansu Usman, duk da Khadija ce ta bige tsohon amma ta manta da abin da ya faru, ranar kawai sun taso daga boko da yamma ta kawo Barira gida akan moton ta, layinda ta shiga dan ya sadata da titi ne ya kawota k'ofar gidan, har zata wuce sai kuma tace bara ta tsaya ta shiga, har ta shiga soron sai kuma ta ji ba ta so ta samu wannan mai d'aure fuskar, da k'arfi ta juya dan ta koma wajen moton ta sai kawai wata yarinya k'arama data shigo da gudu su ka ci karo, fad'uwa yarinyar ta yi ta fashe da kuka saboda buguwa da kanta ya yi da bango, yanda ta tsala kukan ne ya sa Khadija yin saurin durk'usawa ta rumgumo yarinyar ta na lallab'a ta, gidan kuma akwai mutane har da Hassana ma ta zo, kuma d'iyar tace aka bige, da sauri su ka fito soron dan gani me ke faruwa, har da Usman wanda zuwan shi kenan daga *zinder* ko d'aki bai shiga ba, lafiya lafiya? Kowa ke tambaya, Khadija kam tsaresu ta yi da ido sai da Usman ya daka mata tsawa yace "Wai ba tambayar ki ake ba? Me ki ka mata?"


Tsaye ta mik'e lokacin da Hassana ta d'auke yarinyar daga jikin Khadija, kallon tsohuwar ta yi tace "Dan Allah ku yi hak'uri, wallahi ban lura da ita bane, kuma ta shigo ta na gudu."


Hassana ce tace "Ba komai haba, ai yaran kenan, bare ma *Fadila* da bata tafiya sai gudu."


Usman ne yace "Baiwar Allah, in dai har za ki ci gaba da saka wannan gilashin, to fa ki sani wallahi kullum ki na cikin karo da mutane ki na ji musu ciwo, me zai hana ki cire shi ki aje ko kuma ki dinga hutawa? Shi fa gilashi ba dan sakawa kullum bane, yawan anfani da shi ya na b'ata ido, wanda su ka san abun ma za ki ga akwai lokacin da kad'ai suke anfani da shi, amma ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login