Showing 90001 words to 93000 words out of 139085 words

Chapter 31 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

mi shi jagora ya ganta kwance da k'arin ruwa a hannu, dan tunda ta yi sallah asuba zazzab'i ya sake rufe ta, hakan ya sa Naseer ya d'auko likita har gida aka dubata, sosai suka nuna mi shi b'acin rai da cewa ba za ta koma ba har sai Usman ya dawo hankalin shi, baiga laifin su ba kam dan ya sa dole wata rana zai neme ta, haka malam ya juya rai b'ace da kuma kunyar abin da ya aikata, tun a hanya yace Usman ya same shi gida za su yi magana, da "To Baba." Ya amsa.


*Ku na ganin zaije? Yanzu fa Haseenah ita kad'ai ce.*


Saida ya sake wanka ya shirya yace "Amarya ta zanje gida na dawo, amma ba zan jima ba kinji, ki kula da kan ki."


Kallon shi ta yi ta na k'ara rufe jikin ta da zanin gado tace "Gida kuma? Na d'auka d'azu ka ce min gida ka tafi, ya da wuri haka za ka koma."


Ya na gyara zaman hular sa yace "Eh wallahi Baba ne wai ya ke son gani na, amma na san ba zan jima ba ai zan dawo."


Shiru ta yi a zuciyar ta tace "To idan fa yanzu ma dawo da Khadija za su tafi? Dole na yi wani abu."


Shagwab'e fuska ta yi tace "Yanzu tafiya za ka yi ka barni a haka? Ba ka da matsala kenan tunda ka samu biyan buk'atar ka ko?" K'ok'arin saukowa ta fara daga kan gadon ta na fad'in "Shikenan ai ka tafi."


Matsowa ya yi kusan ta zai kamo hannun ta ta kubce ta shige ban d'aki, bakin k'ofar ya tsaya yace "Haba ke kuwa, kar ki yi hushi mana, kinfa san ba na son b'acin ran ki ko kad'an."


"Ahhhhhhh, wayyo Allah ciki na, marata." Fad'in Haseenah daga cikin ban d'aki, bai tsaya tunanin komai ba ya kutsa ciki ya same ta zaune dafe da ciki alamar fad'uwa ta yi, bai tsaya komai ba ya d'auko ta sai kan gado ya dire ta, kallon ta yake ciki da damuwa ya na rik'e da hannayen ta yace "Garin yaya ki ka fad'i haka? Haseenah karfa ki mana asarar kyautar nan da Allah ya bamu, kinfi kowa sanin lokacin da na d'auka ina fatan Allah ya sake bamu haihuwa, ina son na ga gidan nan ya cika da yara kuma ya zamana ke ce uwar su."


Yanda ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka ne yasa tace "Ka yi hak'uri dan Allah, ni ma santsi ne kawai ya kwashe ni, ban kula ba sai ji na yi na fad'i saboda rai na a b'ace yake."


Kallon ta ya yi yace "To me ya b'ata mi ki rai haka da har ki ke neman ja mana babbar asara."


Cikin turo baki tace "To ba kai ne ka ce zaka fita ka bar ni ba, ni kuma wallahi ba na so ka tafi, satin ka biyu fa baka gari, kasan dai dole munyi kewar ka mu na buk'atar ka a kusa da mu, shine kawai daga ka samu yanda ka ke so sai ka ce za ka fita."


Da rawar jiki yace "Ai dai fitar ce ba kya so ko? To na fasa, kin gani ma? Zan kira Baba na fad'a mi shi ya yi hak'uri zan je anjima, shikenan kinji dad'i?"


Dariya ta yi ganin ya cire hular shi da takalma ya fasa tafiyar, ko farfajiyar gida babu wanda ya lek'a a cikin su suna d'aki suna soyayyar su, hatta abinci sai dai ya kira Bilyamin ya siyo ya kawo mu su, haka dare ya yi amma Haseenah na jikin Usman, da ya yi maganar tafiya wajen Baba za ta fara shagwab'a wai zai barta ita kad'ai, haka ya k'arar da wunin na shi bai je kiran Baba ba kuma bai kira shi a waya ba.


Tunda malam ya ga shiru ya tabbatar da zargin shi na cewa akwai abin da ke damun Fodio, ganin har dare ya yi anyi shirin bacci ya sa malam samun Hajia a d'aki har ta fara bacci ya tashe ta, saida ta wartsake yace "Bacci fa bai kama ki ba, tashi ya kamata ki yi mu duk'ufa da addu'a, dan shakka babu Fodio ba kan shi d'aya ba."


Saida ta k'ara murza ido tace "Malam, ban gane ba, me ya ke faruwa da Fodio kuma?"


"Shiga gaba." Ya bata amsa kai tsaye kafin ya d'ora da "Na yi mamakin da ku ka kasa fad'a min gaskiyar abin da ya faru a gidan shi, kun fad'a min ta karb'i makulli da k'arfi, amma ba ku fad'a min ta karb'a bane saboda za ta kai Bilal asibiti, yaron da aka barwa Haseenah ya wahala saboda babu mahaifiyar shi nan, sannan shi kuma Fodio bai fad'a min ya daki Khadija ba, ke ma kuma ba ki fad'a min ba."


"Duka malam?" Ta fad'a da dafe k'irji, d'orawa ta yi da "Wallahi ban sani ba ni ma, bai fad'a min ba ko alama."


Gyara tsayuwa ya yi yace "Har da duka, kinga yanda ya kumburawa yarinyar nan fuska da kin tausaya mata, tun jiya ta na kwance babu lafiya har zuwa safiyar nan da na je gidan ana k'ara mata ruwa, wannan abun kunya da me ya yi kama? Kinga yanda ran 'yan uwanta ya b'ace su na cewa ba za ta koma ba si in ya zo ya nemi ta koma tare da alk'awarin ba zai sake tab'a lafiyar jikin ta ba, kuma ni banga laifin su ba ko kad'an dan su na da gaskiya."


Shiru Hajia ta kasa magana saida malam ya sake cewa "Na fahimci yarinyar nan ta na biyar shi da sharri, ba kuma alkairi bane ya kawota gidan nan, dan haka k'arya take tace za ta cutar da ahalina wallahi, ko da boka take yawo ni nan zanyi maganin ta, Allah ya fi k'arfin ta wallahi."


Kallon Hajia ya yi da zufa ta rufe ta yace "Ke ma ki taya d'an ki da addu'a."


Fita ya yi daga d'akin ita kuma ta k'ara gudun masuburbud'ar sanyin dake d'akin, ta jima bacci bai sake d'aukar ta ba ta na tunani akan abin da malam d'in ya fad'a, anya kuwa Haseenah za ta iya yin haka? Yarinyar da a zahirance ita ake cutawa, taya za ace kuma ta cutar da wani? Kai da kamar wuya gaskiya.




*Da kamar wuyar zata kassara ku.*
21/02/2020 Γ  19:15 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘




_SAMIRA HAROUNA_




*Litattafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


```Fatan alkairi masoya```




_Bismillahir rahamanir rahim_




*29*






Sai k'arfe *10:25* suka tashi daga bacci, Usman ne ya fara shiga wanka da tunanin ya gaggauta shiryawa dan ya fiya kiran malam, ya sakarwa kan sa ruwa kenan Haseenah ta shigo ban d'akin, bahon wanka ta cika da ruwa ta had'a sabulu a ciki ta cire d'aurin k'irjin ta, da k'arfi ta jashi su ka famtsama cikin bahon su biyu, dama abin da take so kenan, shi ya sa ma ta yi anfani da damar wajen b'ata lokaci suna wanka da 'yar shiriritarsu irin ta amare, sun d'auki lokaci kafin su ka fito haka nan ma wajen shiryawa saida su ka jima, suna fitowa falo cikin shiri ya kalle ta yace "Mummyn beby yau ma ba ki dafa mana komai ba fa, ya za mu yi kenan?"


Zaune ta yi akan kujera tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki masarrafar telebijin (remonte) ta kunna tace "To ai ina ganin ba sai na yi girki ba, tunda kaga amarci mu ke ci, ko ba haka ba?"


Zaune ya yi kusan ta ya na fad'in "Kuma fa da gaskiyar ki, dan mafiya yawancin lokuta idan na dawo daga tafiya sai dai muje cin abinci kawai."


Cike da izza ta na karkad'a k'afa ta kalle shi tace "Oho, kenan aka ake yi, amma shine ni ba za ka iya d'auka ta ba muje?"


Waya ya ciro daga aljihu yace "Yanzu dai bara na fara kiran Bilayamin ya kawo mana na karin kumallo, anjima da dare sai muje mu ci ko, hakan ya mi ki?"


"Ba damuwa." Ta fad'a cike da k'asaita, ta na ji ya bawa Bilyamin sallahun abin da suke buk'ata su ci, bayan d'an lokaci Bilyamin ya iso da abincin, ya na karb'owa kai tsaye kan teburi ya nufa da shi ya d'auki faranti ya zuba ya kalle ta daga in da ta ke zaune yace "Madame ki taso abinci na jiran ki."


Tashi ta yi cikin tako d'aya bayan d'aya ta isa, zaune ta yi akan cinyar shi ya dinga saka mata abincin a baki, saida su ka gama ya tashi zai fita tace "Babban mutum ni fa gida na ke so ka aje ni, idan za ka shigo da dare sai ka biya mu taho tare."


"Gida kuma?" Ya tambaya da mamaki, "Eh, gida." Jim ya d'anyi dan gaskiya a tsarin shi ba'a mi shi haka ko kad'an, ace sai yanzu ne kawai za ta fad'a masa ta na so ta fita kuma yanzu yanzu saboda raini, had'e fuska ya d'anyi yace "Ki yi hak'uri mana Mummyn beby, ki bari har gobe sai kije."


Yamutsa fuska ta yi tace "Gaskiya yanzu na shirya tafiya, in kuma ka hana ni wallahi kuka zan kwana ina yi a gidan nan." Ta na gama fad'a ta mik'e ta nufi hanyar falon ta, ganin fa da gaske ranta zai b'ace ya sa ya yi saurin rik'o ta ya had'a da jikin shi yace "Shikenan to naji, ran gimbiya ya huce, je ki d'auko hijabin ki sai mu tafi."


Cikin farin ciki tace "Da gaske kake?" Cike da tabbatarwa yace "Sosai ma, ai ba na da wani abu da ya fi min ke mahimmanci, zanyi hidimar ki kafin na yi tawa, ki yi sauri ki je."


Cikin d'an lokaci ta d'auko hijabi da jaka da takalma duk kala d'aya suka tafi, ba jimawa ya sauke ta gida tare da bata kud'i kafin su ka yi sallama, mahaifiyar ta kad'ai ce a gidan a farfajiyar gida zaune, bayan sun gaisa sosai suka fara tab'a hira, anan ne mahaifiyar ta tambaye ta ko ta na anfani da magungunan ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh, ina sha Mama, amma fa akwai matsala."


"Matsala kuma? Tame?"


Cikin sanyin jiki tace "Mama wannan layun da aka aje na duba su ban gansu ba, kuma gashi har yanzu ana tsorata ni a cikin dare."


Da al'ajabi dattijuwar tace "Toh! Amma abun da mamaki, to ina suke? Kuma kin tabbatar an aje su in da ki ka duba?"


"Wallahi Mama wajen ne, su aunty Mariya fa da kan su su ka aje su, amma da na duba babu komai a wajen."


"Toh." Ta fad'a ta na girgiza kai kafin tace "Lallai wannan abu ya wuce duk in da ake tunanin shi, amma bari Baban ku ya shigo sai na fad'a mi shi komai."


Sosai ta ji dad'in wannan wunin da ta yi a gida, gashi ana ta bata kulawa a matsayin ta na mai k'aramin ciki, sai abin da take so ake bata ta ci, har mahaifin ta ya zo aka fad'a mi shi abin da ke faruwa, a cewar shi ta kwantar da hankalin ta zai sake karb'o mata wasu, sannan ta ci gaba da addu'a komai zai wuce.


A b'angaren Khadija kam ganin jikin ya k'i kyau ya sa Mama cewa "Khadija."


"Umm." Ta fad'a ta na d'an gyara kwanciyar ta, "Khadija ba ki da ciki kuwa?"


Murmushi ta yi tace "Ciki Mama? A'a, ba na da komai wallahi, kawai dai zazzab'in wahala ne."


"To Allah ya tabbatar da alkairi." Cewar Mama, Bilal ne ya shigo da sallama ya na cire jakar makarantar shi, kusan maman shi ya je ya sumbace ta da fad'in "Mummy ya jiki? Kinji sauk'i?"


"Na ji sauk'i yarima, har kun taso?" Saida ya fara cire rigar shi yace "Eh Mummy, kawu Ashir yace na mi ki sannu da jiki ba zai shigo ba ya na sauri."


Mama ce ta katse shi da cewa "Kai d'auki tarkacan kayanka ka wuce da su d'akin ka, kar ka kuskura ka min tsirara a tsakiyar falo."


Matsowa ya yi kusan ta ya yi tsaye yace "K'arasa cire min kayan ma in ki na son samun lada."


Rufe fuska ta yi tace "Kai b'ace min da gani kaji ko."


Fad'awa ya yi jikin ta ya sumbaci kumcinta ya na fad'in "Ina son ki Hajia ta."


Rumgume shi ta yi ita ma tace "Ni kuma ba na son ka yau, dan nasan akwai abin da ka ke so waje na."


Kallon ta ya yi yace "Me ki ka dafa yau?" Hararan shi ta yi tace "Uhum, nifa na san za'a rina dama, ina ka fito ci ina zaka ci, to wake na dafa."


Dariya Khadija ta yi tace "Mama ta na so ta sake kumbura ma ka ciki ne."


Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Kema kin zama aunty amarya muguwa?"


Daruya suka saka sai Mama ce tace "Ai ni mugunta ta ma sai tafi ta ta, dan kuwa idan ka gama ci ba ruwa zan baka kasha ba, sai dai na ba ka kwanan nan fura ka kora da ita."


D'aukar kayan shi ya yi ya nufi d'aki ya na fad'in "Kuma idan na mutu ke ce za ki fara zubar da hawaye."


"To ba dole ba, na rasa miji na uban 'ya'ya na, idan kai ma na rasa ka ai zan shiga cakwakiya."


Usman ya je gida bayan ya aje Haseenah, Hajia kad'ai ya samu dan rana ta take sosai zaiyi wuya ka samu namiji gida a wannan lokacin, bayan sun gaisa ne Hajia tace "Amma me ya hana ka zuwa tun jiya da aka kira ka?"


Cikin rashin gaskiya yace "Wallahi Hajia wani d'an aiki ne ya taso min, kuma yarinyar nan ba ta ji dad'i ba, saida ma na kai ta asibiti aka rubuto mana magani."


_Daga cikin bala'in da asiri ke iya jawa mutum akwai k'arya, zai iya k'arya dan ya kare kan sa ko kuma wanda ya ke so, akwai rashin kunya ga wanda baya hayyacin shi, abune mai sauk'i miji ya tub'ewa mata kayan ta ya mata wulak'anci a gaban 'ya'yansu, kad'an ne daga aiki sihiri daina ganin girman wanda ka ke ganin girman shi, akwai wasa da addini wanda za ka ga wani ya na sakaci da shi, illolin fa dayawa yan uwa, fatan mu Allah ya k'ara tsarkake mana zuk'atanmu._


Take Hajia ta fahimci k'arya ya fad'a, amma saboda kunya ta dake tsakanin uwa d'an fari sai kawai ta share tace"Allah ya sawak'e, gashi kuma yanzu malam d'in har ya fita, sai dai in za ka same shi can shagon."


Cikin sunne kai yace "Ba damuwa sai na je can d'in ai."


Ba tare da ta kalle shi ba tace "To ya maganar Nura, ya fad'a min sunyi magana da Khadija kuma tace ka amince, amma a bari sai ka dawo, gashi kuma ka zo ba ka ce komai ba."


"Eh Hajia, ya na ina ne Nuran?"


"Ya na shago mana."


"Shikenan zan kira idan na fita saiya same ni ko can shagon Murtala ne."


Cikin had'e tafukan hannayenta tace "Hakan ma ya yi."


Kallon ta ya yi yace"Hajia me zai hana ku je ku d'auko Bilal?"


Sai lokacin ta kalle shi tace "Ban gane na je ba? Kai me zai hana ka tafiya? Kuma ma ka na nufin ba za ka je ka dawo da mahaifiyar shi ba kenan?"


Cikin b'acin ran an ambaci sunan Khadija yace "Hajia ni babu in da zanje, ita ta tafi saboda ta na so, dan haka taje can ta k'arata, ni yaro na ne kawai matsala ta."


Karo na farko a rayuwa da Hajia ta iya d'agawa Fodio murya, cikin jin haushi tace "To ba zan je ba, ranar da ka shirya ganin d'an na ka sai kaje ka d'auko shi da kan ka."


Kallon ta ya yi shima, amma saboda ran shi a b'ace ya ke da maganar Khadija sai kawai ya mik'e cikin kumburo baki yace "Ni zan wuce, sai anjima."


Da kallo kawai ta bi shi har ya fita daga gidan, girgiza kai ta yi ta na mamakin wannan canjin daga Fodio, mik'ewa ta yi ta shiga d'aki ta na fad'in "Ai kuwa da alama gaskiya malam ya fad'a, amma koma menene zan wa tubkar hanci."


Daga nan wajen malam ya zame, k'ofar shagon ya samu malam zaune akan bacci shi da wani suna hira, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su kafin malam ya sallami waccen, mayar da kallon sa ya yi kan Usman da ke durk'ushe yace "Fodio sai yanzu ka zo kiran nawa? To nagode."


"Wallahi Baba..." D'aga mi shi hannu ya yi alamar ba ya son ji kafin ya d'ora da "Jiya na je gidan su Khadija, kuma naji duk abin da ya faru, Fodio ka bani mamaki sosai da na ji ance wai ka d'aga hannu ka daki Khadija, wannan abun kunyar har yaushe da irin shi, duka! Kai a matsayin ka na mai hankali da ilimi, a shekarun ku na k'uruciya haka ba ta faru ba sai yanzu da girma ya fara riskar ku, wanda ya kamata ace yanzu ne soyayya take da tausayin juna, amma ace ka dake ta akan abin da ma k'arya ake mata da sharri, kawai rud'in zuciyar ka ne ka biyewa da kuma wata banzar hud'uba da wasu sakarkari suka ma ka, kasan me ya sa ta karb'i makullin motar? To saboda ta kai yaron ka asibiti ne, yaron da ya wuni da yunwa alhalin ya na gidan uban shi wanda ke wadace da kayan abinci sama da na shekara d'aya, amma wai akan hakane har ka d'orawa baiwar Allah laifi har ka iya dukan ta, ni ko a gani na ko taka Haseenah ta yi ta mayar da gabanta gabas ta yanka ta da wuk'a za ka iya mata uzuri, uzurin kuwa shine za ka duba dalilin da ya sa ta yi haka tunda ita uwa ce, amma ba komai, ka je gidan ka gani yanda ka lalata mata fuska da rashin hankalin ka, tace ba za ta dawo ba kuma na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login