Showing 75001 words to 78000 words out of 139085 words
Chapter 26 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt
kowa ya kama gaban shi, amma fa Hajia Turai ta zuba ido da kunne ta na jiran ta ji wani sabga da zai taso wanda zaisa ta had'u da amaryar Usman, Usman kam tunda ya shiga mota ya kifa kan shi yake jin zuciyar shi babu dad'i haka ma yanayin shi, wai me ya faru da shi da har ya aikata wannan abun kunyar? Gashi ya ja bala'in da yafi k'arfin na shi ta ci mutumcin shi son ran ta, Me ya sa ya yi haka to? Me ya sa baiyi bincike ba ko ya duba al'amarin? Amma kuma ya na tunawa da Haseenah sai zuciyar shi ta yi sakayau da ita, domin ya bata hak'uri ya sa ya k'arasa bakin titin da ke ofishin wajen masu siyar da waya, nan fa ya siya mata tsandareriyar waya ta ban hak'uri haka Bilal, dan ya jima ya na si ya siya mi shi dan ya dinga game, saida ya tsaya ya yi sallah azahar kafin ya wuce gidan, har madafa ya same ta ya bata wayar, ta yi murna sosai ta masa godiya, kallon ta ya yi yace "Ina Bilal?"
"Ya na falon maman shi, ba irin lallab'ar da ban masa ba ya fito ya k'i."
Fita ya yi ya na fad'in "Ina zuwa." Ganin ya sa ta bi bayan shi dan kar azo tambayar Bilal wani abu zaiyi, tare su ka shiga ya na kwance da alama ma bacci ya ke ji, zaune ya tashi yace "Abba sannu da zuwa."
Shafa kan shi ya yi ya na zama kusan shi yace "Yarima hutawa ake?"
"Um." Kawai ya fad'a yayin da Haseenah ta harare su ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "Hum! Yarima dai yarima, ku ba ku gaji sarauta ba amma ku lak'abawa yaro sunan yarima, haba dai." Ta k'arshe da yin k'wafa.
Ledar hannun shi ya mik'a mi shi yace "Duba ka ga tsarabar ka."
A hankali Bilal ya ciro kwalin ciki, ya na ganin waya ce ya yi sauri budewaya fito da ita sai shek'i take, dariya ya yi ya rumgume mahaifin na shi yace "Abba nagode, na ji dad'i sosai."
Rumgume shi ya yi cike da so da k'auna yace "Hakan na ke son ji dama."
Karb'ar wayar ya yi ya had'a mi shi da kan shi in da ya janyo mi shi mega (data) daga na shi ma'ajiyin sannan ya nuna mi shi yanda zaiyi ya dinga janyowa duk lokacin da ya ke so, nan fa suka zauna su na ta danne danne a wayar ya na nuna mi shi abubuwa da dama, Haseenah kam in ranta ya yi dubu tabbas ya b'ace, musamman da ya nunawa Bilal yanda zai iya janyo data amma ita saida ya amshi wayar ya jawo mata, haka ta gamo girkin ta kawo tare su ka ci da yaro kamar yanda suke ci a baya a faranti guda, har la'asar ya na gida tare da Bilal saida su ka yi sallah a masallaci kad'ai ya fita yace zaije gidan, dan da safe bai je ya gaishe su ba.
*Hajia Turai* ta na zuwa gida ta'aniya zazzaga bala'i, k'arshe dai shiryawa ta yi a motar ta taje gidansu Khadija, Khadija na falo sun gama girkin rana suna cin abinci ta zo gidan, nan fa ta tashi duk wani mai baccin rana a gidan ta na fad'a mu su wulak'ancin da Usman ya mata, Khadija da ta iya k'awar ta ta shiru ta yi saida ta kalle ta tace "Ke kuma sai magana na ke amma kin min banza, ko har yanzu ki na son mijin na ki?"
Tasan in ba ta bita sannu ba sai sunyi baran-baran, dan haka tace "Haba kema dai bari fad'in haka mana, ai ni tuni na yi wuri na aje shi tunda ya tab'a min ke k'awa ta, kwantar da hankali kinji tawa ki manta da lamarinsu kawai."
"Yawwa yanzu na ji magana, ai na d'aukar har yanzu ki na son komawa gidan shi." Ta fad'a ta na saka hannu cikin kwanon abincin, murmushi Khadija ta yi tace "Haba ina, ai sai a aljanna kuma idan da rabo mun had'u."
Saida ta cika baki da abinci tace "Shegiyar yunwa na damu na, amma wannan mijin na ki ya k'i bari na ci abinci ya aika min da yan sanda gida na, ke kinga bala'i da zafin shi ni da Usman a ofishin yan sanda."
Yanda Khadija ta santa tasan yanzu ma saita sake dawo da labarin baya, hakan ya sa Khadija cewa "Haba k'awa ta rabu da su kinji, ci abinci dai yanzu muje d'aki akwai hira."
Wata dariya ta yi "Hahahaha, haka na ke son ji k'awa ta, ki barsu kawai wallahi lokaci na zuwa da saiya dawo da k'afafun shi ya neme ki, wallahi saiya durk'usa har k'asa ya na neman afuwarki, ita kuma wannan tsinannar ko, haba, yo an fad'a mi shi mu na wasa ne, ai iskancin ma ba haka kawai mu ke yin shi ba, wallahi ko uban..."
Tabbas Khadija tasan cewa za ta yi uban shi dan ita ba damuwa bane gare ta, dan haka ta rufe mata baki tace "A'a k'awata, surukina ne fa, dattijon arzik'i ne babu ruwan shi."
"Hakane kuma, ai da ina so na mi ki misali da gyatumin shine."
Duk abin da suke fad'a mamar Khadija na gefe na saurarn su, dariya kawai take ba tare da sanin su ba, haka suka gama sun shiga d'aki nan ma kuma Salamatu ta zo wacce Khadija ta fad'a mata a waya tana gida, aifa d'akin Khadija kamar zai tsage saboda hargowar da suke yi, har k'arfe biyar na yamma suna gidan nan kafin suka tafi.
A wajen Usman kuma ko da ya je gida bayan sun gaisa da Hajia ta tambaye shi ya iyali, nan fa ya kora mata bayanin abin da ya faru daren jiya, Malam da shigowar shi kenan ya rabka salati ya na fad'in "Fodio, me na ke ji kana fad'a haka? Ka ce ta tafi gidan su sai ka neme ta? Me ka ke nufi da haka? Fodio ba ka ji kunyar fad'in maganar nan ba dan Allah?"
K'asa ya yi da kan shi baice k'ala ba, malam ne ya d'ora da "To tashi ka fita, kuma da anyi sallah isha'i ka zo ka d'auke ni k'afar ka k'afa ta muje mu dawo da ita, ni ba za ayi wannan haukan da ni ba kaji na fad'a ma ka."
A hankali ya mik'e ya saka takalmin shi zai wuce ta gaban malam ya kalle shi da kyau har ya fita, kallon Hajia ya yi yace "Anya kuwa yaron nan lafiyar shi k'alau?"
"Ni ma dai abin da na ke tunani kenan, ya na wasu abubuwa kamar ba'a hayyacin shi ba." Cewar Hajia da ke k'ok'arin d'auke tabarmar da ya tashi akai.
"Ai kuwa sai a d'auki mataki tun kafin abu ya yi nisa, amma in ba haka ba taya ma zai ce Khadija ta tafi gida saiya neme ta."
"Gaskiya kam."
K'arasa shiga d'aki malam ya yi ya na fad'in "Allah ya sawak'e."
Kamar yanda ya fad'a ana sallah isha'i ya dawo gidan ya d'auki malam, basu zame ko ina ba sai gidan su Dijeh wajen biko, karo na farko a rayuwar su da haka ta faru, sallama su ka yi tun farfajiyar gidan aka amsa, Ashir da kan shine ya mu su iso falon Mama, dan dama suna nan zaune dukan su, matansu ne suka fito tare da yara aka bar mazan tare da Mama sai Khadija da ke d'aki ta kan iya jiyo maganganun da suke.
*'Yata kawai ki koma*π
14/02/2020 Γ 16:55 - πππ: ππππππππππ
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
ππππππππππ
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*25*
Saida ya gama fad'in abin da ya faru kafin ya d'ora da "Wallahi Mama Khadija ta bani mamaki, wai ni Khadija zata kalla ta dinga fad'awa duk abin da ya zo bakin ta, saboda kawai na mata kishiya saita raina ni, ko kuma dan na mata magana akan abin da tayi bata kyauta bane, wannan abu ya b'ata min rai sosai, shine dalilin da ya sa nacr ta zo gida saina neme ta, banyi haka dan cin mutumcin ta ko cin zarafinku ba, sai dai nasan dole anan akwai wanda za su fad'a mata kuma ta saurare su, dan naga yanzu kishi ya rufe mata ido gaba d'aya."
Malam ne yace "Kai dallah rufewa mutane baki, koma menene ai sai kayi hak'uri, duniyar nan uban waye baisan halin mace ba akan kishi, ko kai kana ganin kamar uwarka ba ta da kishin ne, ita kan ta mahaifiyar ta ta da ka ke magana akai ai tasan zafin shi, kenan sai ka yi hak'uri ka d'auke kan ka dukansu na d'an lokaci ne za su yi, in banda rashin hankali irin na ka da can farko ta ma ka haka kafin zuwan amaryar?"
Murmushi Mama ta yi tace "Alhaji ka k'yale shi haka, to idan yace ya saka mu su ido suyi yanda su ka dama suna fakewa bayan kishi, ai kuwa kullum da tsiyar da za su b'ullu da ita a gidan, hakan zaisa ba za'a zauna lafiya ba, ni banga laifin shi ba dan hakan shine daidai, ka na ji ko." Mama ta fad'a ta na kallon shi cike da kulawa, kallonta ya yi take kuma ya sunkuyar da kan shi k'asa, d'orawa ta yi da "Ka yi hak'uri dan Allah akan abin da ya faru, insha Allahu zan ja mata kunne hakan ba zai sake faruwa ba, abinka ne da d'an yau ka haife shi baka haifi halinshi ba, babu irin tausar zuciyar da ban mata ba, amma ba ta ji ba ko kad'an, amma ka yi hak'uri kaji, insha Allah za ta kiyaye a gaba."
Kallon malam ta yi tace "Bara na kira mu ku ita sai ku tafi ko." Cike da dattako malam yace "Shikenan Hajia mun gode sosai da karamci, Allah ya bar zumunci."
Mama na wucewa d'akin Khadija dake ta cika ta na batsewa Usman ya d'ago kai a hankali ya kalli su Ashir da duk su ka hakimce su na kallon shi, d'auke kan shi ya yi dan gani yake kamar za su rufe shi da duka, dan ko basu fad'a ba kasan ba haka su ka so ba, musamman Naseer da Habeeb da bakin su ke ta motsiπ, a d'aki kam tuburewa Khadija ta yi wai babu in da za ta je, saida Mama ta fara nuna b'acin ran ta kad'ai ta fito ta na kumburo baki, wajen yan uwan ta ta tsaya ta ja birki ta na kallon su, Naseer ne yace "Ki yi hak'uri kinji auta, Hajia tace ba ta yarda mu ce komai ba."
Kallon Usman ta yi da shima yake kallon ta, har ga Allah kafin ta fito ya ji ya na son ya koma tare da matar shi, amma ya na ganin ta yanzu sai ya ji kamar yace ta yi zamanta ko kuma ya rufe ta da duka, haka kawai ya ji ranshi ya b'ace ko da ya ganta, amma sai ya dake ya mayar da hankalin shi kan Mama da tace "Maza ki bawa mijin ki hak'uri yanzun nan, sannan ki mi shi alk'awarin hakan ba za ta sake faruwa ba, in kuma ki ka sake to fad'an ni da ke ne ba da shi ba."
Kamar za ta yi kuka ta kalli Mama tace "Mama, wai ni ce ma zan ba shi hak'uri? Har fa mari na ya yi mama, kuma dama duk na ji abin da ka fad'a ina d'aki." Ta fad'a ta na mayar da hankalinta kanshi, ci gaba ta yi da cewa "Bansan me ya sa za ku yi tunanin na lalata abincin yarinyar nan ba, domin Allah ku dube ni da kyau ku dubi Haseenah, ace na rasa ta yanda zanyi na yi maganinta akan kishi saita hanyar zuba gishiri a abincin ta, haba dai kuma, wannan ai abune da hankali ba zai d'auka ba, kenan ma ta gagare ni?"
"Khadija." Mama ta fad'a cikin tsawa, shiru ta yi ta kalli Mama, cikin b'acin rai tace "Rashin kunyar da ya fad'a mana ki na masa ita ce za ki nuna mana sanfurin da ki ke ma sa?"
A hankali ta durk'usa duka gwiwoyinta biyu tace "Ki yi hak'uri Mama."
"Ba ni za ki bawa hak'uri ba, mijin ki ne gashi nan."
Saida ta had'e hawayen ta kad'ai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri." Yanda ta turo baki ne ya sa Mama cewa "Anya kuwa Khadija ke ce? Ke ce Khadija auta ta da na sani."
Kallon maman ta tayi ta sake kallon Usman ta saisaita murya tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, insha Allah ba zan sake ba."
Da k'yar ya iya k'arfin halin k'ak'aro mata murmushi yace "Ba komai ai ya wuce, ni ma ki yi hak'uri abisa marin ki da na yi, kuskure ne da b'acin rai."
'Anzo wajen." Cewar Naseer, d'agowa ya yi daga jinginar da ya yi a bayan kujera yace "D'an uwa Usman dan Allah a dinga kiyayewa, shi duka a fuska ya na da had'ari sosai, mari kan iya jayo makanta, mari ya kan iya sanadin rasa ji, mari zai iya sakawa haure ya fita, mari kan saka kai ya yi ciwo, dama wasu matsaloli da dama, ka ga sai a dinga sanin me za ayi idan rai ya b'ace."
Yasan ba lallai Mama ta yi shiru ba, dan haka ya na fad'a ya tashi ya bar falon ya nufi b'angaren shi, da murmushi Usman ya bishi ya kalli sauran yace "In Allah ya yarda ma ba za ta sake faruwa ba, wannan ma tsautsayi ne."
"Allah ya kiyaye gaba." Cewar Ashir, haka suka tashi su ka koma gida, saida ya ajeta gida kafin ya wuce ya kai malam, Bilal ya yi farin cikin ganin mahaifiyar shi, Haseenah kam ba ta ji dad'i ba ko kad'an, sai dai tasan nan ba da jimawa ba za ta koma tunda yanzu sai yanda ta yi da Usman.
A matsayin kwanan Khadija ne yau ta shirya ta kuma je har d'akin shi kamar yanda ta saba, tabbas ya kwana d'akin, amma da kwanan shi da rashin kwanan duk d'aya, dan kuwa baya ya juya mata ko uhum ba ta ji daga bakin shi ba har ya yi bacci, amma ita ba ta yi baccin ba sai nafila da ta kwana ta na yi ta na kaiwa Allah kukanta, har asuba tana nan kafin ya tafi masallaci ita kuma tayi sallah, bayan ta kammala ta shiga madafa ta d'ora girki.
Usman kuma na dawowa daga masallaci d'akin Haseenah ya nufa su ka gaisa, daga nan ya fad'a mata gobe fa zai yi tafiyar nan ta shirya in tana zuwa, amma bayan tunani da tayi sai taga za'a zargeta idan suka tafi tare, dan haka ta marairaice tace "Um,um gaskiya ni na fasa tafiyar ma, ka ga kai kasuwancin ka ne zai kai ka, bai kamata muje tare ba kuma na hana ka sabgar gaban ka, kawai kaje Allah ya tsare mana kai, ranar da na haihu sai mu tafi tare da yaronmu mushak'ata."
Saida ya rumgume ta yace "Gaskiya ban ji dad'i ba, Haseenah ba zan iya farin ciki ba ki na nesa da ni, me ya sa ba za ki je ba? Zan iya yin wata d'aya fa ko sati uku ban dawo ba, ki na ganin zan iya rik'e kai na bayan na saba da ke a d'an lokacin nan."
Cike da gatsali tace "To ba ga aunty Khadija ba, ku je tare mana, ni kuma sai mu zauna abunmu ni da yarona Bilal, ko ya ka ce?"
Tunda ta ambaci sunan ya ji kamar ta jefe shi da mashi akan tsohon ciwon shi, b'ata rai ya yi yace "Ya ina magana da ke za ki kawo min maganar matar can? Gaskiya ba na so kar ki sake."
Saida ta shafi fuskar shi tace "To shikenan yi hak'uri ba zan sake ba."
"To yanzu fad'a min za ki je ne?" Ya fad'a ya na k'ara cukuikuyeta, ba alamar wasa tace "Gaskiya ba zan je ba, kawai ka tafi kai kad'ai."
"Shikenan, amma taya zan barki ki zauna tare da matar can? Na ga fa ba wani sakin jiki ki ke da ita ba."
Shiru ta yi ta na tunanin abinyi ita ma, da sauri yace "Ko na kira Hajia ta turo mi ki Aziza? Tunda kinga dama ita ce ke zuwa nan idan zanyi tafiya."
Wani murmushi ta yi da bai kai ciki ba tace "To shikenan ba damuwa, hakan ma ya yi ai."
Da haka ya fito ya shiga d'akin shi ya yi wanka ya shirya ya fito kan teburi, saida Haseenah ta fito kafin su ka fara cin abincin, tabbas daga yanda ya ke cin abincin za ka san ya masa dad'i, amma da zaran ya had'a ido da wacce ta dafa abincin saiya d'aure fuska, haka su ka gama ya tashi ya fita su ka bishi da addu'a, Khadija da ta bi bayan shi har wajen mota sannan ya juyo ya kalle ta yace "Ya dai malama ki ke bina haka?"
Murmushi ta yi tace "Abban Bilal hushi ka ke dani har yanzu akan abin da ya faru?"
Wani d'auke kai ya yi yace "Mtsss, ba komai kawai, kawai dai ki na ba ni mamaki ne."
A hankali ta janyo hannun shi ta na shafawa, in da shi kuma ya ke jin kamar hannun wuta ne da ita, cikin taushin muryar da tasan ta na tasiri akan mijin ta ta fara magana "Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, insha Allah ba zan sake b'ata ma ka rai ba, ka ji? Ka yafe min, kasan hankali na ba ya kwanciya idan ina ganin ka haka."
Saida ya raba hannunshi da na ta yace "Shikenan ba komai, Allah ya sa haka."
Juyawa ya yi zai shiga mota tace "Shikenan kuma ba komai za ka tafi."
"Kamar me fa?"
Cikin yanayin jan hankali tace "Ba