Showing 3001 words to 6000 words out of 139085 words

Chapter 2 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

kalle shi ba tace "Shikenan ba damuwa, insha Allah zan fad'a ma sa."


D'an gyara zama ya yi alamar zai tashi yace "Mama babu wata matsala ko wani abun da ku ke buk'ata?"


"Ah, Fodio kai ne za ka bar gidan nan da wata matsala? Ai sai dai in ba ka raye, Alhamdulillah wallahi babu komai, Allah dai ya yi albarka, Allah ya sa ka gama da duniya lafiya."


Sai da ya durk'usa k'asa ya amsa da "Ameen Ameen Mama, nagode sosai da addu'ar ki gare ni, ni zan wuce sai anjima idan na dawo."


"To Allah ya yarda, Allah ya tsare, ka gaishe min da waccen mutumin."


Dariya ya yi yace "Watak'ila fa gobe ku gan shi gidan nan, dan mahaifiyar shi ta tafi d'auko shi."


Cikin wasa irin ta kaka da jika tace "Ka ce mi shi ma kar ya kuskura ya zo in har ya san ba zai taho da k'atuwar bak'ar leda ba."


"Zai zo da ita Mama, ai kin san shi da k'ok'arin cefanai."


"Ko dai k'ok'arin jefawa a ciki ba."


Da wannan wasan ya bar gidan zuciyar shi sakayau da ita kamar kullum, dan har abada babu abin da ke dagula mi shi lissafi, b'angaren mace, Allah ya wadata shi da mata kamar Khadija, babu abin da ya nema a gurin ta ya rasa, haka ma iyaye, Allah ya bashi iyayen da su ke son abin da ya ke so, sannan su ke nusar da shi tare da kora shi da addu'a a kullum, hakan na sa shi farin ciki , kuma shima ya na k'ok'ari sosai wajen sauke hakk'ok'in duka b'angarorin, haka ne m'a sanadiyar da ta sa kullum ci gaba ya ke gani babu komawa baya ko rashin nasara, dan Allah ba ya kunyatar ko tab'ar da wanda ya kiyaye hakk'ok'in wannan mutanen a duniya.


Khadija ma a gidan su farin ciki ta ke kamar ba ta farin ciki a gidan ta, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon samun kan ta da ta yi a tsakiyar mahaifiyar ta da kuma d'an ta, sai sauran matan yayyun ta da kuma 'ya'yan su, bayan sun ci abincin rana yan uwan ta maza su uku su ka shigo gidan, anan ta tara su kuma ta fad'a mu su auren da mijin ta zaiyi, ta gaggauta fad'a mu su hakane saboda ta san sune za su iya bata shawara mai kyau wacce ta dace, kuma kamar yanda ta yi tsammani hakane ya faru, sosai su ka kwantar mata da hankali tare ja mata kunne da nasihohi ma su shiga rai, tare da kafa mata misali da matar babban yayan ta wanda da zai k'ara aure ta tashi hankalin kowa, a k'arshe dai sai da ta bar gidan, yanzu gashi nan sai amaryar ke rayuwar ta a b'angaren na su, abin da ba ta son ganin shi ke faruwa a bayan idon ta kuma ba yanda za ta yi, ga yayan ta ma su na hannun uban su sai yaga dama ya ke barin su su je wajen uwar, saboda hure mu su kunne da ta ke, hakan ya k'ara saka jikin Khadija yin sanyi, kuma ta yi niyyar yin aiki da shawarwarin da su ka bata, a haka ita ma ta yi yammacin ta tare da maman ta abar k'aunar ta, zuwa *5:30* na yamma kuma Bilal ya d'auki kayan shi su ka wuce tare da maman shi a motar ta.


Su na isa gida Bilal ya wuce da yan kayan shi d'akin shi tare da canza na jikin shi, ita ma kaya ta sauya ta wuce madafa dan sarrafa abin da za su ci da dare, tare da Bilal su ka shiga ya na kama mata duk aikin da ta ke yi, sai da aka gama sallah magrib ta gama lokacin Bilal ya wuce masallacin da ke had'e da gidan su, ta na gama ajewa a mazaunin cin abinci ta yi wanka ta shirya cikin riga da zane wanda su ka d'auke jikin ta sosai, kasancewar babu wata tazara mai tsayi tsakanin sallah magrib da isha'i ya sa ta yi sallahn ta, ta na kammalawa ta fito falon ya yi daidai da shigowar Bilal daga masallaci tare da baban shi.


Ta na ganin shi ta tashi tsaye ta turo baki tace "Sai yanzu za ka dawo min gida? Ina ka shige haka?"


Kallon Bilal ya yi yace "Yau salon gaisuwar maman ka kenan? To ka fad'a mata ba zan amsa ba."


Ita ma Bilal ta kalla tace "To ka fad'awa Abban ka ya juya ya koma in da ya fito, dan ba ya da muhalli a gidan nan yau."


Dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka tambayar min ita kaji, wai dama ana korar mutum da gidan sa?"


Da shu'umin murmushi a fuskar ta tace "Ka fad'a ma sa sau nawa aka yi, idan kuma bai tab'a gani ba to yau zai faru a kan shi."


Bilal da ya saki baki ya na kallon su dukan su ne ya matso kusan maman shi ya rik'e hannun ta yace "Momy dan Allah ni dai muje ki zuba min abinci na ci yunwa na ke ji."


Dafa kanshi ta yi tace "Muje ka ji yaro na, kai da gidan ku."


Sun juya za su wuce ta ji ya rik'o hannun ta, juyowa ta yi su ka kalli juna, murmushi ta masa tace "Ina so na rumgume ka, zuciya ta bugawa ta ke da k'arfi."


Jan hannun ta ya yi su ka nufi d'akin shi, Bilal na ganin haka ya k'arasa shi kad'ai ya zuba abincin ya fara ci, dan ba zai iya jiran su ba, su na shiga d'aki su ka k'wak'wume juna kamar sun shekara ba su had'u ba, sumbatar ta ya ke tare da fad'in "Na yi kewar ki sosai, wuni d'aya ba mu had'u ba alhalin ina cikin garin nan, gaskiya ba zan k'ara nesanta kai na da ke ba."


Da k'yar dai su ka rabu ta taimaka mi shi ta cire ma sa kayan ta mi shi wanka kafin su ka fito, zaune ya yi ta zuba mu su abinci a faranti d'aya, amma saboda sabo har Bilal sai da ya sa hannu a na su abincin ya sake ci, cikin farin ciki da k'aunar juna su ka kammala, Bilal ya wuce d'akin shi ya na kallo, su kuma su na nan falo.




*Wannan ita ce rayuwar farin cikin da su ke ciki.*


Bayan mahaifin Usman ya zo mahaifiyar shi ta fad'a mi shi komai, kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Masha Allah, wannan ai abun farin ciki ne, dan girma ne zai k'aru, fatan alkairi kawai za mu ma sa, zuwa safe kuma idan ya zo sai muji yanda za ayi."




*Allah ka bani lafiya mai anfani.*
27/12/2019 Γ  20:31 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘






_SAMIRA HAROUNA_




*Littatafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._




*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›




```Fatan alkairi masoya```




_Bismillahir rahamanir rahim_




*3*








Kasancewar maza ne su ka shiga al'amarin, sai akayi komai cikin sauk'i da sauri aka gama, kuma cikin k'ank'anin lokaci aka saka *wata biyu* mai zuwa, dan haka kowane b'angare ya fara shirye shiryen da su ka dace da shi a bikin, amma b'angaren Khadija hankalin ta kwance ya ke, dan dama tun farko mace ce mai kama jikin ta da tsare gida, hakan ne ya sa ba ta buk'atar d'aga hankalin ta wajen gyaran jikin ta ko wata kwaskwarima, kayan d'aki ne kawai ta ke buk'atar canzawa, shi ma kuma a nutse ta ke so ta yi komai, tunda kud'i ba su ne matsalar ba.


Wajen amarya ma yan uwan ta ne ke tsaye kan kula da gyaran jikin ta, dan mahaifiyar ta dattijuwa ce kuma babu ruwan ta, ita ma kuma ba zaune ta ke ba ta na d'an k'ok'arin ta wajen ganin ta gyara kan ta da kan ta.




*Duk* abin da aka sa ka ma rana to k'ararre ne, sai gashi kamar k'yabtawar ido har an ciye *wata d'aya* da sati d'aya, hakan ne ya sa biki ya rage saura sati uku, kuma har yanzu uwar gida ba ta tab'a ganin amarya ba, amarya kuma ta ga uwar gida amma a hoto ba'a zahiri ba, shirye shirye ya kankama sosai, sai dai kuma Khadija ta d'an fuskanci wani k'alubale a wajen dangin mijin ta, kasantuwar ta mace mai fara'a da kyauta da kirki ya sa yan uwan ta da yan uwan Usman su ke son yawan kawo mata ziyara, amma tun da aka saka ranar auren shi har yanzu ba ta ga k'eyar kowa ba, ba ma kamar k'anwar shi *Aziza* wacce har kwana ta ke a gidan.


Yau dai sunyi sallama da Usman za ta je wajen bikin k'awar ta *Halisa* da ta haihu, kuma tace za ta fara biyawa ta gidan su ta gaishe da mama, tsaf ta shirya cikin kayan da ta fi son sakawa, leshi (less) ne aka gwangwaza mata d'inki mai kyau riga da siket, sai takalmanta ma su tsini da mayafin da ya dace da kayan, ta na shigar motar ta ba ta zame ko ina ba sai gidan su Usman, cikin sa'a sai ta samu k'anwar Usman d'in da ke bi mi shi wacce da Usman ya had'awa Khadija kayan fad'ar kishiyar ta ya kai mata yace ta kai wa Khadija, ba dan ba zai iya ba sai dan ya na so ya bata mamaki, ita kuma ganin kayan sunyi yawa ya sa ta taho da su nan d'in dan ta nunawa mahaifiyar su.


Da isar Khadija a soro taja birki ta tsaya saboda jin muryar aunty *Hassana* na fad'in "To domin Allah Hajia yanzu wannan kayan da mata ne za ki ce ba su yi yawa ba? Ko fa lefen amarya da aka kai wallahi bai kai wannan kayan ba, haba dai, kayan fad'ar kishiya har akwati goma, kuma kowace cike da kaya, gaskiya ni ba zan kai su haka ba."


Tshohuwar ce tace "To ya za ki yi da su? Ragewa za ki yi? Ko kuma me za ki yi?"


Ai kuwa sai muryar Aziza a kunnen Khadija ta na fad'in "To dama ina zai had'a lefen ta dana amarya, kin manta ta gabar goshin ce? Ai ina tabbatar mi ki a yanda na san yah Usee (sunan da su ke kiran shi da shi kenan) ya na tsoron matar nan, wallahi da za ta ce ya fasa auren nan, to ko musu babu zai fasa shi."


Tsaki tsohuwar ta yi tace "Kullum ina fad'a mu ku ku dinga kyautatawa mutum zato, abin da ba ku da hujja da yak'ini a kan shi, amma ku na hukunta yarinya da shi, wannan fa bai dace ba."


Hassana ce tace "Hajia ba kya son laifin Khadija ne kawai, amma duk wanda ya san rayuwar su wallahi ya san da magana a k'asa."


Aziza ce tace "Ku ai duk labari ne ku ke ji, ni da na mayar da gidan fa kamar gidan mu, kar ki so ki ga wani abun haushin idan ya na yi wallahi, su kad'ai a cikin gida sai shegen yaron nan da ba komai ya ke ci ba sai abin da ya ga d..."


Ba ta k'arasa ba tsohuwar nan ta kwashe ta da mari, hararan ta ta yi tace "Dan rashin mutumci d'an yayan na ki za ki sheganta? Kuma a gaba na, dama gulma da d'aukar rahoto ne ke kai ki gidan na su? To kinyi na k'arshe, mutuniyar banza kawai."


Tashi tsaye ta kalli Hassana tace "Ke kuma ki tabbatar kin kai wannan kayan in da aka aike ki da su." shigewa ta yi d'aki ta barsu nan, Khadija kam k'walla ne su ka cika idon ta, juyawa kawai ta yi ta fita ta d'auki hanyar ta zuwa in da za ta je, Hassana kuma tattara kayan ta yi ta rufe akwatinan kafin ta samu yaro aka mayar da su a motar da ta kawo su, Aziza kuma ta ci gaba da kumburar baki.




Ko da Hassana ta je gidan babu kowa, dan haka ma ta kira Usman d'in dan ta fad'a mi shi, a cewar zai aiko da yaro da makullin falon Khadija ta bud'e ta saka kayan, bayan nan kuma sai da ya mata fad'a wai ba ta kawo a kan lokaci ba har ta fita, hakan ya sake tunzurata ita ma, dan ganin ta ke kawai ba ya k'aunar b'acin ran matar shi bai kuma damu da b'acin ran su ba, haka ta jira yaron shi ya zo ya kawo mata aka bud'e aka jera akwati nan kafin ta bar gidan.




⏩⏩⏩⏩⏩⏩




*Yamma* ta yi sosai *Hassenah* ta kammala girkin ta ta na jiran isowar yayar ta, kallon maman ta ta yi cikin b'acin rai tace "Wallahi aunty *Mariya* ta cika b'ata lokaci, sai da na fad'a mata akwai in da zanje ta yi sauri fa."


Dattijuwar da ke cike da kamala da sanyin jiki wanda da alama hallitar ta ce haka tace "Watak'ila wani abun ne mai mahimmanci ya tsayar da ita, amma ki k'ara hak'uri."


Tsaki Haseenah taja cikin b'acin rai, amma ba ta dire tsakin har k'arshe ba Mariya ta shigo a hargitse da sallama, mahaifiyar kad'ai ta amsa sai kafeta da ido da Haseenah ta yi, ita kam goyon da ke bayan ta ta kwance ta aje kan tabarmar da ke shinfid'e ta na gaishe da maman na su, cikin rashin kunya Haseenah tace "Dan Allah aunty Mariya me ye haka? Na fad'a mi ki fa za mu fita tare da su *Zeinab*, amma shine ki ka b'ata mana lokaci haka."


Cikin d'aga murya tace "Ke dallah can, ke in da kinsan me ya tsaidani ma ko magana kya yi."


"To me ya tsaida ke d'in?"


Sai da ta aje jakar ta da bak'ar ledar hannun ta ta gyara zama da kyau tace "Kishiyar ki na had'u da ita wajen bikin."


Cikin harara ta kalle ta tace "Ke aunty Mariya, ke kuma ina ki ka san kishiya ta da har ki ka gan ta wajen biki? Ko ni fa ban tab'a ganin ta a zahiri ba, bare kuma ke."


Tsaki Mariya ta yi tace "Aikin banza, to tunda na ce mi ki na ganta ba sai ki tambaye ni ya akayi mu ka had'u ba."


"To na ji, ya akayi ku ka had'u."




*Tofa, kinga irin wannan sune yan haddasa bala'i.*
29/12/2019 Γ  13:46 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘






_SAMIRA HAROUNA_




*Littatafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._




*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›




```Fatan alkairi masoya```




πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ




_Bismillahir rahamanir rahim_




*4*




Saida ta kalli maman su wacce ta ke da yak'inin za ta tsawatar mu su kafin tace "Kawai dai a gurin bikin mu ka had'u, kuma masha Allah wallahi ba ki ganta ba, kyakyawa da ita, musamman gilashin idon ta ya k'ara mata masifar kyau, gaskiya ta birgeni sosai saboda da ganin ta akwai fara'a da kuma kama jiki."


Wani bak'in ciki ne ya tokare Haseenah a wuya, amma sai ta dake tace "Ni dai yanzu ki ban abin da ki ka rage wajen siyayyar."


Hannu tasa a jaka da nufin fito da kud'in, hakan kuma ya yi daidai da tashin maman su ta shiga cikin d'aki, dan haka Mariya ta gyara zama murya k'asa k'asa tace "Haseenah kinsan wacece kishiyar ki kuwa?"


Cikin yamutse fuska tace "Ni kuma ina zan sani."


Gyara zama ta sake yi tace "Hum! Haseenah, wallahi sai kin tashi tsaye tsayin daka, dan kishiyar ki ba ta wasa ba ce, wai kinsan su wanene k'awayen ta?"


Cike da jin haushi tace "To wai ni dan Allah ina zan sani, haba, ki yi magana yin za ki yi kawai."


Sai da ta bubbuga k'afar ta tace "Khadija kishiyar ki, su *Hajia Turai Dubai* da *Hajia Salamatou k'urori* da *Barira nagoma* da *Hajia Natali*, sune manyan k'awayen ta, shin kinsan ma wacece aminiyar ta?"


"Sai kin fad'a." Cewar Haseenah.


Sai da ta sauke numfashi tace " *Hajia Kaltume*, Kaltume mai kayan dad'i."


D'orawa ta yi da " Haseenah, wallahi sai kin tashi tsaye, kinga matan nan da na lissafa mi ki, gogagggun wayayyu ne, manyan mata ne ma su ji da kan su, duk kishiyoyin matan nan in fad'a mi ki ba su da daraja a wajen majazensu, kinga Kaltume mai maganin mata, to in fad'a mi ki in ba ki cika cikakkiyar mace ba ma ba ki siyan maganin ta, dan k'aramin magani a wajen Kaltume shine na *jikka hamsin* (jaka hamsin), duk wata mace da ta k'oshi kuma ta ke mulki a gidan mijin ta to Kaltume ce sirrin farin cikin ta, dan wani shegen gyaran jikin idan ta mi ki shi, to wallahi tun a daren farkon ki kin gama da mijin ki kenan, duk wata mace da za ta raba ki da shi, to sai dai fa in ta sihiri ne, amma d'and'anon ku ba ya tab'a zama d'aya a wajen shi."


Gaba d'aya jikin Haseenah ne ya yi sanyi da jin wannan al'amari, ganin haka ya sa Mariya cewa "Akwai mafita d'aya da ta rage mi ki."


"Wace iri?" Cewar Haseenah da saurin ta, d'orawa ta yi da "Nasan kishiyar ki a tsume take da had'in Kaltume, kuma tunda ita ce aminiyar ta kinga kenan ba za ki tab'a cin mata ba , amma abu d'aya shine, kema ki samo kud'ad'e a hannun Usee, sai kawai muje mu ga Kaltumen, sannan akwai wata ma da ke kawo min kayan mata, ita ma sai ta had'a mana da nata, koya ki ka gani?"


"Hakan ma ya yi, kuma kinga dama shi mutum ne mai kyauta, ba sai ka tambaye shi ba ya ke yi."


"Dan haka sai ki samo mana kud'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login