Showing 30001 words to 33000 words out of 139085 words

Chapter 11 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

sunan gini, ta wani fannin kuma dije na zuwa makarantar ta hankali kwance.


Lokavin dacikin ta ya isa haihuwa ne wata tafiya ta taso mi shi zuwa DubaΓ―, shine karo na farko da zai fara zuwa, hakan ya sa a ranar Khadija ta wuni ta na kukan ba zai tafi ba, rarrashin duniya ya yi amma ta toshe kunne ta k'i fahimtar shi, a k'arshe dai dole ya yanke shawarar kaita gida ta zauna tare da su mama har ya dawo, ita kuma bud'ar bakin ta cewa ta yi "Aiko sai dai ka tarar na haihu wallahi, dan ba zan jira ka ni."


Dariya ya yi yace "Ba za ki haihu ba insha Allah har sai na dawo."


Haka ya kaita gida ya aje shi kuma ya wuce, tun a mota Murtala ya lura yanayin abokin shi ya canza sosai, cike da kulawa yace "Aboki na lafiya dai? Ya na ga ka yi wani iri ne?"


A hankali ya kalleshi ido sunyi jawur kamar zaiyi kuka yace "Khadija, ita na ke tausayi, sai ta haihu kafin na dawo, ba na jin za ta wuce sati ba ta haihu ba, dan duk alamu sun nuna haka, kwana hud'u ko bacci ba ta iya yi saboda ciwon baya da mara, mtss." Ya k'arashe da d'an guntun tsaki.


Murtala ne yace "To ya za ayi sai hak'uri? Kuma gashi ba ka fad'a mata gaskiyar magana ba cewa tafiyar nan za ta iya d'aukar ka wata d'aya ko fiye da haka."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sati d'aya ma na fad'a mata amma ta damu sosai, ina ga na fad'a mata wata d'aya zanyi? Shi ya sa ma na riga na barwa Hajia komai su kula idan ta haihu, kuma na gode Allah da na iya fad'awa yan uwan ta adadin lokacin da zan iya yi."


"Hakan ma da ka yi ya yi daidai, kaga za su dinga kwantar mata da hankali."


A haka su ka isa kuma su ka rabu suma cike da kewar juna, a daren wannan ranar Khadija nak'uda ta taso mata, da su ka tafi asibi har sai da gari ya waye rana ta yi fatsal-fatsal kafin ta haihu, duk abin da ake Usman na da labari, lokacin da Husseina ta bawa Khadija waya ya mata magana da ta kasa, wata k'ara tare da kuka had'i da salati da ta yi sai da ya ji kamar ya bud'a ido ya ganshi gabanta, a k'arshe dai *bayan wuya* sai dad'i, ta haihu lafiya haka ma yaro, lokacin wani mugun bacci ne ke d'ibar Khadija amma sai Usman yace Hajia ta bata waya su yi magana, daga kwance ta karb'i wayar ta d'ora a kunne, shiru ta yi sai shine yace "Barka baiwar Allah, daga k'arshe dai Gashi kin haifo min yaro, Khadija ina cikin farin ciki sosai, godiya ko dukiya ba za su iya biyan ki ba, amma ina so ki fad'a min duk abin da ki ke so? Ni kuma zan baki shi a matsayin tukuicin wannan kyautar."


Cikin muryar jin bacci tace "Ina hushi da kai kafin minti ashirin da su ka gabata, saboda ka k'i zama tare da ni a lokacin da na ke buk'atar ta, da ka k'ara kwana d'aya tak da na haihu a gaban idon ka, amma bayan minti ashirin da ya wuce, lokacin da na d'ora ido na akan yaron ka, sai na ji komai ya yaye a zuciya ta, dan haka ka d'auka yaron nan shine tukuicinka gare ni."


Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi hak'uri Khadija, haka Allah ya so, kuma duk da kin ce ba jya buk'atar komai, amma akwai wani abu da zan ba ki, kinsan me ye?"


Cikin lumshe ido tace "A'a."


"Khadija, nine ya cancanci na yi wa yaron nan hud'uba, kuma gashi bana nan, dan haka babu wanda yafi cancanta sai ke, na d'ora mi ki wannan nauyin a kan ki, idan kin ma sa hud'uba sai ki rad'a masa sunan da ki ka ga ya dace kuma ki ke so."


"Da gaske ka yarda na saka mi shi suna da kai na?" Ta tambaya da fara'a.


"Sosai ma, wannan hukuncin na jima da yanke shi ai, ba kawai dan bana nan bane."


Shiru ta yi kamar mai bacci kafin tace " *Abban Bilal*., hakan ya yi?"


Da farin cikin jin sunan da ta sakawa yaron ya sa yace "Masha Allah, Bilal, sunan da ke birge ni, sunan da ya nake da burin sakawa yaro na shi, hakan fa ya na nuna k'arfin soyayyar da ke tsakanin mu ne."


Jin bcci na son surarta ya sa tace "Ka gafarce ni Abban Bilal, bacci na ke ji sosai a ido na, za mu yi magana anjima."


"Ayyah sannu momyn Bilal, zan barki haka to, amma anjima za mu yi magana, kin yarda?"


Cikin hamma tace "Na yi alk'awari."


Da haka su ka yi sallama, kamar yanda ya bar komai hannun Hajia haka ta dage sosai ta yi takamata, dan mawasu lokutan maman Khadija da yan biyar ba sa tsayawa komai da an nemi abu za su siyo su kawo, haka dai aka yi shagalin biki babu uban yaro, a lokacin Khadija ta fara damuwa da rashin dawowar Usman, da k'yar yan uwanta da mama suke kwantar mata da hankali, tun suna waya ya na cewa zai zo aiki ne ya rik'e shi har ya kai ya rasa me zai ce mata, sai kawai zuciyar shi ta bashi ya daina kiranta, ita kuma idan ta kira jar ya d'aga sai an kwana biyu, wannan dubarar ce ta jefa Khadija a wani hali na daban, da ta kwashe kwanaki ta na kira bai d'aga ba, damuwar ta ta nunku sosai, mama kuma sai take cewa tayi hak'uri mana da yanda Allah ya hukunta mata, hakan ya sa Khadija tunanin ko Usman ya mutu ne dai, kawai sai ta yanki jiki ta fad'i, sai da ta kwana asibiti, a ranr Usman bai shirya tahowa ba amma dole ya taho, dan cewa ya yi neman kud'i ba zai ja mi shi rasa matar shi ba wacce ya ke da yak'inin ba zai samu kamar ta ba a wannn k'arnin, sai lokacin kad'ai Khadija ta samu sauk'i ta kuma huce.




*Allah ka k'ara mana lafiya mai anfani.*
20/01/2020 Γ  12:38 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘






_SAMIRA HAROUNA_




*Littatafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._




*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


πŸ’•πŸ’•πŸ’• *My Heenat, My BK, My Meelat*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


_Alkhairin Allah ya lullub'e min ku, ina k'aunar ku._😘




```Fatan alkairi masoya```


*MOMYN DADY, KI JI DAD'IN KI WANNAN PAGE TA KI CE KYAUTA.* πŸ˜‰


_Bismillahir rahamanir rahim_




*13*




Kullum taresu ke idan dare ya yi har ba ya son rabuwa da iyalin shi, kuma bai sake wani tafiya ba har sai da ta yi arba'in, sabon gidan da ya gina mu su matsakaici daidai da rayuwar su suka tare, haka suke rainon Bilal cikin kulawa da so da k'auna, ta b'angare d'aya kuma ta na ci gaba da zuwa makarantar ta, kasancewar babu nisa da gidan su da makarantar ya sa take aje Bilal nan kafinta wuce, idan ta sauko ta biyo ta d'auko shi, a haka dai har ta kammala karatunta lafiya, haka ma Usman ya na k'ara samun hab'aka a kasuwancin shi, a lokacin da ya ke tunanin nemawa Khadija aikin karatun da ta yi, sai kawai ta shawarce shi kan ta na son fara kasuwanci, ta na so Ashir ya fara kawo mata kwanuka da karap (jug) da sauran kayan anfanin mata ta na siyarwa, ya ji dad'in haka kuma yace nauyi ne a kan shi ya mata hakan, Ashir ya nema su ka yi magana sannan ya fara bashi *million d'aya* dan a fara da ita, cikin ikon ubangiji kuma sai Allah ya sawa kasuwar albarka, duk da komai bashi ne, amma dai ana samu sosai, lokaci na tafiya kamar walk'iya in da abubuwa ke faruwa, ta na taimakon danginshi da danginta da ita kan ta ma da kasuwancinta, in da Aziza kuma ta zama kamar ba k'anwar Usman ba, dan ya zama Khadija ita ce komai na ta, har tafi son zama gidan nan akan gidan su, a lokacin kuma Khadija su na ta sake zuba ido akan samun wata haihuwar amma shiru, abu d'aya shine kasuwancin ta ya na d'aukar hankalin ta sosai.


*Shekarar Bilal takwas* sai kasuwar ma ta durk'ushe, sakamakon wata mata da ta shigo rayuwar ta da sunan kasuwanci, da farko sai da ta sa Khadija ta yarda da ita ta hanyar yi mata ciniki na milyoyin kud'i sau ba adadi, sun saba sosai ta na bata kaya za ta biyata kud'i a take, daga k'arshe sai ta nemi ta bata kayan milyoyin kud'i, ba fargaba Khadija ta kwashe duka kud'in ta ta bayar aka siyo mata kaya, wannan karan matar cakin (check) kud'i ta bata da nufin ta je banki ta cira, sai da ta d'auki kayan sannan Khadija taje cirar kud'i, cakin k'arya ne na bogi, hakan ne ya jefa Khadija matsala har aka mata taro ana neman mik'a ta hannun kwalawa🀣, sai da Usman da Ashir su ka zo kad'ai aka samu matsalar ta mutu anan su ka dawo gida, ba girgiza ko damuwa a tare da ita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Ta ci kad'an wallahi, ita da Allah, ya na sama ya na gani, dan haka na barta da shi."


Usman ya si bata wasu kud'in amma tace kawai ta hak'ura da kasuwanci, tun da dama ta na yawan samun irin wannan matsalar, wannan karan dai ne abun ya girmama, tunda ba ta rasa ci da sha ba da duk abun buk'ata, dan haka ta hak'ura tun da akwai wanda ba sa son ta da arzik'i, ya nuna mata wannan ba shine maslaha ba amma ta rufe ido tace ba ta so, dole ya rabu da ita kawai ba dan ya so ba, a lokacin ta rage hada hada da jama'a Aziza kuma ta k'ara girma an zama yan mata, lokacin ne ta fara sakawa rayuwar su ido saboda yanda ta ga d'an uwan ta na rawar k'afa akan Khadija da d'an ta Bilal, in dai har yayi tafiya ya dawo to na tsawon kwana biyu ko uku Khadija ba ta girki in ka cire ranar da zai dawo, saboda Usman na da buk'ata sosai, idan ya dawo sai ya yi kwana uku bai lek'a waje ba idan ba masallaci ba, hakan ne ya sa yace ba ita ba shiga madafa sai dai in ruwan zafi za ta d'ora mu su na wanka, a cikin kwanakin da zaiyi kusan kullum sai sun fita cin abinci ko shan ice crime ko ya mu su siyayya ko kuma sada zumunta gidan yan uwan shi da yan uwan ta, yayin da su ke jin dad'in rayuwar su sai Aziza ta fara zargin akwai wani abu a k'asa, yanda ya ke komai dai matar shi da d'an shi abun na bata mamaki, musamman idan Kaltume ta zo ta ga sun shige d'aki ana ta dariya da ba ta yan k'unshe k'unshe, sai kawai tace sun mallake shi ne, (d'an adam butulu), a hankali sai ta fara fad'awa yan uwan ta su Hassana, su kuma ba tunanin komai su ka yarda, dan suma sun fahimci hakan, musamman idan ya zo daga tafiya ba ya fita wani lokacin gidan su ma sai ya kwana ya hantse baije ba, su kuma iyayen da yake su na da hankali sai suke ganin wata buk'atar ce ta sa haka, a hankali sai suka fara canza mata fuska, ko alheri ta musu sai su k'i karb'a, ana haka wata rana k'anwar shi *Rabi'a* ta zo neman jari wajen shi za ta fad'ad'a kasuwancin ta, rashin sa'ar da ta yi Usman kwanan shi biyu da dawowa, sai yace mata ba ya da kud'i yanzu, amma ta yi hak'uri ta dawo nan da kwana uku, ita kam a ganinta wannan k'aton gidan da suka sake ta kalli Khadija ta ganta mulmul cikin rantsetsen leshe, sai taga ai k'arya ne ma ace babu kud'i a gidan nan (🀣🀣🀣), sai kawai ta tashi rai b'ace ta na gunguni, Khadija ce ta dawo da ita ta zauna ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko kud'in da yan uwan ta ke bata ta mik'a mata, sai da ta kalle ta sama da k'asa ta kalli Usman tace "Dama akwai kud'in kawai tsoron bani ka ke saboda ba ta yarda ba, to ki bar shi nagode."


Ta na fad'ata mik'e ta bar gidan, Usman kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Waya saki? Keta tambaya ko ni? Yanzu gashi kin ja k'aramar yarinya za ta fad'a mana magana."


Murmushi ta yi baiwar Allah ta b'oye abin da ke ran ta tace "Allah huci zuciyar ka, ba na fatan ganin b'acin ran ka a lokacin da ka ke cikin yanayin farin ciki."


Tun fa daga ranar su ka sake kafawa Khadija k'ahon zuk'a, sai dai ba su tab'a yarda sun bari iyayen su sun sani ba, dan sun san iyayen su yan a mutun Khadija, za su iya b'ata mu su fiye da tunani Saboda ita, amma kullum buri da addu'ar su Allah ya kawo wata gidan wacce za ta fanso d'an uwan su daga sharrin Khadija, babban abun haushi shine lokaci da su ka had'u da Usman gida su ka saka Kabir da ke bi mi shi a cikin maza ya mi shi magana ya k'ara aure, murmushi ya yi ya kalle shi yace "Me ya sa zan k'ara aure?"


Shi dai Kabir ya fad'a ne ba da wata manufa ba, dan shi ba ya manta alkairi kuma ya na k'aunar Khadija, cewa ya yi "Ko ba komai ai ka k'ara saboda ka samu zuri'a dayawa."


Cikin bacin rai Usman yace "Wallahi, da ace wani ne ba kai ba ya fad'i wannan maganar, da sai na fad'a maka kalmar da har ka mutu ba ka manta ba, kai ba dan ma butulu bane har Khadija ce za ka yi fatan a k'arawa kishiya? To jini da kyau, kar ka sake min wannan maganar, sannan duk wani mai wannan banzan tunanin a gidan nan ma ya daina, dan za mu iya samun matsala da mutum."


Hussei na ce tace "Yanzu yah Fodio saboda an ma ka maganar aure shine ka ke wannan kumburin? Na ga dai da ba'a aure ai da ba ka aure ta ba, kuma k'ara aure sunna ce ta *ma'aiki*, bugu da k'ari za ka k'ara samun ya'yan da za su gaje ka."


Murya kasa k'asa yanda ba zaiji ba Rabi'a tace "To ba sai ta ba shi damar yin hakan ba, shi fa a d'aure ya ke ba ya da katab'us sai yanda ta yi da shi."


Duk da ba duka Usman ya ji ba, amma dai ya ji kalmar k'arshe ta sai yanda ta yi da shi, cikinjin zafi ya juyo ya kife ta da mari, zai k'ara mata wani marin Hajia ta d'aga mi shi hannu, huci ya dinga yi kafin yace "Wallahi dukanku butulu, kun manta alkairi kuma kun manta hallaci, Khadija bata cancanci wannan daga gare ku ba, ko ba komai ita uwar d'ana ce, ita da Bilal sun fiye min komai a duniyar nan, ita kad'ai ta bani farin cikin da ku ma da ke yan uwana ba ku ba ni shi ba kafin zuwan ta rayuwa ta, dan haka in dai har ku na son zama da ni to dole harshenku ya san me zai dinga fad'a akan mata ta."


Ya na fita Hajia ma ta mu su fad'a sosai tare da tuna mu su baya, daga ranar kuma ba su sake yarda sun b'ata Khadija ba a gaban iyayen su bare kuma Usman, amma abin takaicin shine k'iyayyar da su ke ma Khadija sai ta shafi har Bilal, dan yanda su ke ganin Bilal na wahalar da mahaifin shi, yaro ya zama saurayi amma kamar k'aramin yaro, ba ma in sun had'u da shi gidansu Hajia, ya kan zo da kayan ciye ciye ma su tsada da kyau da dad'i, duk abincin da za'a mi shi tayi ba zai ci ba, haka mahaifin su malam Ali zai dinga biyewa yaron ya na siyo mi shi duk abin da ya ke son ci, to fa ana hakane har Allah ya had'a Usman da Haseenah, lokacin ya na yawan zuwa wajen wani shago da ke can wajen filin kokawa saboda wasu kaya da ya ke kawowa mai shagon, a nan ya had'u da Haseenah wacce a lokacin ta samu exam (brève) d'in ta ta na zaune gida, baban ta ne ya tilasta mata komawa makarntar islamiyya dan ta k'ara samun ilimin addini, a lokacin har nik'abi take sakawa da dogon hijab, wannan nutsuwa da hankalin na tane su ka sa Usman jin kamar ya samu wata Khadija, fatan shi shine ta zama kamar yanda ya ke tunani, bayan ya yi tambaya a kan ta an fad'a mi shi yarinyar kirki ce daga gidan mutanen k'warai, sai kawai ya gabatar da kan shi a matsayin yana son auren ta, duk da bai cika magana akan matar shi ba, amma ya fad'a mata ya na da mata d'aya da yaro d'aya, kuma ya na matuk'ar son su, a lokacin da su ka fara soyayya Usman na bata lokaci wajen waya da Haseenah har dare, sannan duk abin da ta yi ya kan yaba hakan kamar d'abi'ar shi ce, amma a tunanin Haseenah matar shi ba ta da kulawa ne shi ya sa har za ta yarda ya na waya da ita tsawon dare ko ya na gari, abin da kuma ba ta sani ba shine duk lokacin da ya ke wayar da ita to ba ya gida, Khadija kuma ba ta damuwa saboda ta san in baya gida yana tare da su Murtala, ta na ba shi lokaci sosai da ya ke jin dad'in rayuwar shi shima kamar yanda ya ke wuni tare da ita da safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login