Showing 27001 words to 30000 words out of 139085 words
Chapter 10 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt
zuciyar shi, Khadija kuma kuka na rad'ad'i da zafin da take ji da ya zama sabon abu a wajen ta, da taimakon shi ya taimaka mata ta gyara kan ta ta tsarkake jikinta, har bacci ya fara d'aukar ta tajiya k'wak'ume ta kamar zai mayar da ita ciki, haka bacci ya rideta amma banda Usman da ya kwana ya na kallon fuskarta ya na shek'a mata sawar albarka da tunanin yanda rayuwarshi ta canza sanadiyarta cikin k'ank'anin lokaci, har aka kira sallah idon shi biyu, sai da ya yi alwala sannan ya zo ya tashe ta a hankali, masallaci ya nufa ita ta yi sallahnta a gida, tun akan sallaya ta kwanta saboda zafin da har yanzu take ji a k'asan ta da kuma bacci, ko da ya same ta bai tashe ta sai da ya tabbatar ya had'a mata ruwan shayi da soyayyen k'wai, tashin ta ya yi da kan shi ya mata wanka duk da ta cije akan bata so amma bai barta ba, haka ya saka mata kaya suka karya, yinin ranar babu inda ya je duk da yaran mak'wabta na shigowa, ya na zaune ya na kallon matar shi na kai da kawo ya na jin dad'i da sabon abu a game da ita.
*Muje da sauri fan's*, sati biyu kad'ai da auren su, amma shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanin su sosai, a cikin k'ank'anin lokaci suka saba da junan su, dan sosai Usman ke sakin jiki da Khadija ya na janta a jikinshi, *sabo tirken wawa*, sai gashi ita kanta Khadija ta saba da shi sosai ta yanda ba ta kl cin abinci in ba tare da shi ba, dan ji take kamar ya zamar mata yan uwan ta biyar, cikin wannan rayuwar farin ciki Usman ya shirya tafiya *zinder*, matuk'a Khadija taji ba dad'i, tunanin ta ya za ta yi rayuwa a gidan ita kad'ai babu shi, ya yi k'ok'ari sosai ya kwantar mata da hankali, amma hakan bai mata ba har sai da tace ya d'auko Aziza ya kawota nan, ya ji dad'in tunanin ta sosai, kuma haka akayi kam, a ranar da zai tafi a ranar aka kawo Aziza da kayan ta, haka ya tafi suka rabu cike da kewar juna.
Ta ji dad'in zaman ta tare da Aziza duk da yarinya ce, ita ke kula da duk d'awainiyar ta, haka ma yan uwan Usman d'in na yawon kawo mata ziyara, haka ma jefi jefi yan yan uwan ta su kan lek'o dan su ga halin da take ciki, a haka har aka kwashe *kwana goma sha biyu*, a kwana na sha uku Usman yace ya na nan tafe, duk da ba ta san ainahin abin da ta ke ji a ran ta ba a game da shi, amma haka ta ji farin ciki ya mamaye ta sosai, a ranar Kaltume ta zo gidan, kuma Kaltume yarinya ce da Allah ya bawa basirar sanin kan tsiyar maza😂, idan ta fad'i wata magana sai ka d'auka babbar mace ce, haka ta samu ta had'awa Khadija wani had'add'en lemun kayan marmari sannan ta zuba mata madara a ciki da *garin raihan*, wuni ta yi ta na shan shi bayan tasha lalle da kitso na tarban miji, bayan nan kuma da kan ta ta taimaka mata suka canza zaman duka kayan d'akin, kuma duk su na aikin ne ta na k'ara fad'a mata irin shiri da kwalliyar da za ta yi, duk Khadija na sauraren ta har ta gama, girki ta d'ora su ka ci kafin ta tafi gida.
Kasancewar shigowar rana zaiyi ya sa tun k'arfe *d'aya* na rana Khadija ta kammala girki ta aje in da ya dace, dama tun da safe Hajia ta aiko Mannir ya d'auki Aziza, hakan ya bata damar sakewa sosai ta yi aikin ta, wanka ta yi ta jima ta na shafawa ta na zanawa da dangwalawa, k'ananan kaya ta saka riga da siket na kanti masu kyau da suka dace da ita, turaren tsintsiya ta kunna sannan ta turara na wuta mai dad'in k'amshi, sai kuma na ruwa (airfreshner) shi ma mai k'amshin lemon tsami ta fesa, ko ina ya d'au harama mai gidan kawai ake jira, k'arfe *uku* cip-cip ta na zaune ta ji sallama, shaida muryar ya sa ta ja dogon numfashi lokacin da ta tuna hud'ubar Kaltume, mik'ewa ta yi ta fice da gudu ta yaye laluben, ba ta tsaya tunanin komai ba ta fad'a jikin shi ta rumgume shi k'yam, cikin farin ciki take fad'in "Sannu da zuwa miji na, sannu da dawowa, na yi farin ciki da dawowar ka gare ni."
Ajiyar zuciya Usman ya sauke ya d'an juya ya kalli *Kabir* k'annan shi da ya d'auko shi daga gidan mota, karb'ar jakar hannun shi ya yi yace "Nagode ko, ka gaishe da su Hajia sai na shigo."
Baki bud'e ta d'ago a hankali dan ganin waye, ta na ganin Kabir ta sake saurin sunne kan ta cikin k'irjin shi ta cakumo rigar shi ta rufe fuska da ita, dariya su ka mata Kabir yace "Matar yaya wai ba dai sati biyu da ya yi baya nan ne ya saki wannan farin cikin ba kamar ya yi shekara?"
Ita kam kunya ce ta sake rufeta ta kuma tusa kan ta cikin k'irjin shi dan ba za ta iya d'agowa su had'a ido ba, murmushi Usman ya yi ya na shafa bayanta yace "Dallah malam ka wuce ka yi abin da na saka ka, sai ka takura min yar..."
Shirun da ya yi ya sa Khadija d'agowa ta kalle shi, had'a goshinsu ya yi wuri d'aya yace "Yar yarinya ta na ke nufi."
Cikin dariya Kabir yace "To sai anjiman ku amare, sai ka shigo d'in, amma ni banga alamar za ta barka ka fito ba."
"Saboda me?" Cewar Usman ya na kallonshi, shafa kan shi ya yi yace "Ai na ga ta yi kewarka ne sosai."
Wannan maganar ce ta sa Khadija juyawa da k'arfi za ta koma d'aki Usman ya fizgota ta fad'a kan shi, dariya su ka saka Usman ya juyo ya kalli Kabir yace "Kai wai za ka fice min ko sai na raka ka ne?"
Sosa k'eya ya yi yace "To ai ba ka ban tsaraba ta bane, ko ka manta yanda mu ka yi da kai kafin ka tafi?"
Sakin Khadija ya yi ya aje jakunkunan hannun shi ya tunkari Kabir ya na fad'in "Ina zuwa, bara ka gani d'an hancin uwa kai."
Maimakon ya fita daga gidan sai ya daka da gudu ya yi hanyar ban d'aki ya na dariya ya na fad'in "Amma fa sai da na fad'a maka banda mai a moto na, kace idan mu ka zo za ka ban kud'i na saka, ka bani kawai sai na tafiya ta na barku ku soyewar ku."
Dawowa ya yi ya kama hannun Khadija ya sunkuya zai d'auki jakunkunan ta tu saurin karb'a ta na fad'in "Bara na shigar ma ka da su."
Kabir ne ya sake fad'in "Dan Allah ka fito ka sallame ni kafin ka shiga d'akin nan, dan bansan me zai faru ba idan ka shiga."
Juyowa ya yi ya kanne shi Khadija kuma k'arasa shiga ta yi saboda kunya, suna shiga Usman ya tsaya ya na k'arewa d'akin kallo, komai a d'akin kalar kayan d'akin ta ne ma'ana fari da maron, sai telebijin da k'aramin teburin tsakar d'aki ne kad'ai bak'ak'e, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace "Duk wannan shirin na zuwa na ne?"
Cike da kunya tace "Eh mana, sati biyu ba ka gidan ka, ya na da kyau ka tarar da sabon abu dama."
Hannunshi ta kama tace "Muje ka cire wannan kayan ka yi wanka, idan ka fito sai ka zo ka ci abinci."
"Na ci abinci ko ki ba ni abinci?" Ya fad'a ya na tsare ta da ido, murmushi ta yi ta kalle shi tace "Duk yanda ka ke so ai girman ka ne, ka cancanci fiye da haka ma."
Wani basaraken murmushi ya yi ya nufi d'aki yace "Godiya na ke Nana Khadija."
Zasu shiga d'akin Kabir ya d'aga murya daga waje yace "Kai fa na ke jira, wallahi yah Fodio kar ka manta da ni anan waje ka shiga harkar gaban ka, kasan dai nima matar ce da ni ko."
Shima d'ago muryar ya yi yace "Naji me mata, amma aljihunka ba ka da kud'in da zaka saka mai a moto, to waye zai ciyar maka da matar kenan, ko dai hak'uri take ci?"
K'arasa shiga d'akin su ka yi, k'amshin da ya daki hancin shi ne yasa shi lumshe ido, a hankali ya bud'a ido ya sauke akan gadon da shi ma zanin da aka shinfid'a sama fari da maron ne, kallon ta ya yi yace "Khadija kin wahalar min da kan ki dayawa fa."
Murmushi kawai ta yi ba tace komai ba, zai fara cire kaya Khadija ta nufi wajen wata k'aramar jakar ta ta hannu ta d'auko ta fito, a tsakar gida ta samu Kabir ya na ta shawagi shi kad'ai, bud'a jakar ta yi ta ta ciro yan jikka jikka har guda biyar mik'akk'u ta mik'o mi shi tace "Gashi wai a baka."
Da mamaki ya kalli hannunta yace "Inji shi?"
"Eh." Ta fad'a da murmushi, jim ya d'anyi kafin ya karb'a, dan shi dai a iya saninshi Usman na k'ok'ari da su sosai wajen yi mu su buk'atunsu, amma kyauta irin haka dai ta shiga tsakanin shi da su gaskiya da wahala, saboda shi kan shi ma ai ba k'arfi bane da shi, da wannan mamaki yace "Ki masa godiya matar yaya, nagode sosai, ni na wuce."
"Amma ai da ka jira shi sai ku ci abinci ko."
Cike da zolaya yace "Me ki ka dafa ne? Kinsan ni fa ina son abu mai dad'i."
Dariya ta yi tace "To ka tafi tafi kawai, dan nasan abin da na dafa ba lallai ya birge ka ba."
"Da alama dai ba kya so na ci ne, to na hak'ura ma bana ci."
Jin motsin Usman ya sa ta dawo ciki, da sauri ta karb'i abun tsane ruwan hannun shi ta d'auki kwandon sabulu ta kai ban d'akin ta dawo ta cika bokiti da ruwa ta kai mi shi, kallonta ya yi yace "To na shiga na yi ne? Ko kuma madam ce ke da wannan alhakin?"
Dariya ta yi kawai ta kama hannun shi su ka nufi ban d'akin, shine ya fara shiga ita kuma ta tsaya baya tana tunanin ta mi shi wankan kamar yanda k'awar ta tace? Ko kuma dai ta bar shi ya yi da kan shi, wata zuciyar ce tace ma ta to ai mijin ki ne, ya sanki kin san shi, dan haka babu kunya a wannan fanni tsakanin ma'aurata, shiga kawai ta yi ta fara gurza shi soso da sabulu, haka su ka fito ta gama shirya shi cikin k'ananan kaya na kanti, sai dai la'asar ta matso ya sa shi yin alwala ya nufi masallaci ya fara sallah, ya na dawowa su ka ci abinci tare kamar yanda su ka saba, daga kan teburin ya kashe ta da wani kallo yace "Khadija."
"Na'am." Ta d'ago ta na kallon shi, cikin taushin murya da nuna buk'atar shi yace "Kinyi kewata kuwa?"
Da idon ta nan masu kama da na mai jin bacci ta kalle shi tace "Dan ba ka gan ka akan gado na bane ka fad'i haka?"
Sai da ya d'an lashe baki yace "Da gaske? Kenan kema yanzu haka ki na jin abin da na ke ji?"
Da gangan ta d'auki kofin (cup) lemun shinkafar da ta yi ta zuba a rigarta a tsakiyar maman ta tana kallon shi tace "Ya ma fi wanda ka ke ji."
Taso da ita ya yi tsaye ya d'aga kan shi ya na kallon ta ya soma cire mata mab'allan rigar ta har sai da ya rabata da ita, rigar nonon da ta kamata ya cire ita maya jefar kafin ya sa harshe ya na lashe jikinta in da lemun ya zuba... *gyara kimtsi*.
*Misalin* 05:54, su na kwance akan gado ya kalleta yace "Khadija, kin mayar da ni babban mutum, ina godiya ga Allah da ya k'addara had'uwa ta da ke a lokacin da babu wanda ya yi tsammanin faruwar wani abu tsakani na da ke, sannan ina godiya a gare ki da ki ka zama yarinya mai hak'uri da zab'in iyayen ta da kuma tawwakali da hukuncin ubangiji, ina kuma godewa Ashir da ya yi tunanin had'a ni da ke har yanzu mu ke kwance akan gado d'aya a matsayin mata da miji, sannan ba zan manta da k'ok'arin iyaye na a kai na wanda su ka jajirce har sai da su ka ga kin zama mallaki na, tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayen shi ba ya tab'ewa, ni shaida ne kuma na gani a zahiri, Khadija, zuwan nan da na yi na taho mi ki da tsaraba mai yawa, amma babbar tsarabar da na ke so na ga ta k'ayatar da ke ita ce *kyautar zuciya ta*."
Tashi ta yi daga kxance ta na kallon shi tace "Ka na nufin ka mallaka min zuciyar ka gaba d'aya?"
Sai da ya jinjina kai alamar tabbatarwa kafin yace "Hakane, kin cancanci fiye da wannan ma, dan da akwai abin da ya fi zuciya ta mahimmaci a gare ni, to da shi zan ba ki, dan a gaskiya ba zan iya ba ki rayuwa ta ba."
Da sauri ta kalle shi tace "Ka na nufin ba zaka iya sadaukar da kan ka ba wa ni?"
Da fuskar tausayi yace "A gaskiya ba zan iya ba."
Cikin rashin jin dad'i tace "Kenan akwai wata da ka ke so?"
"Akwai mana." Ya fadada murmushi, sai lokacin ta rarumo gilashin ta ta saka ta kalle shi da kyau, ganin idonta sun kawo ruwa ya sa ya saki dariya ya rumgume ta yace "Ina da wacce na ke so mana, ga ta a gaba na, Nana Khadija *baiwar Allah*, Khadija ke ce na ke so, ba zan iya sadaukar da rayuwa ta ba wa ke saboda da ke kad'ai na ke so na yi rayuwa, ina so na na k'are rayuwa ta tare da ke cikin farin ciki."
D'agowa ta yi daga jikinshi ta kai mi shi duka a k'irji ta na fad'in "Har ka tsorata ni."
Dariya ya yk yace "Hakan na nufin nima na samu shiga kenan a cikin wannan tattausar zuciyar?"
Sai da ta rumgume shi tace "Sosai ma, kai ne farko da ka fara shigar ta, kuma insha Allah kai ne za ka zama na k'arshe, saboda ka na shiga na rufe ta na kuma jefa makullin a cikin tekun maliya."
Sumbatar ta ya fara yi daga nan dai aka sake juyewa ni kuma na sake juyowa na fito😎,haka su ka dinga gudanar da rayuwar su abar sha'awa, sun manta da yanda ma aka yi su ka had'u, soyayyar su suke barjewa kawai, zan iya cewa daga cikin biyayyar da Usman ya wa iyayensa akan auren Khadija ce ta sa k'ofofin arzik'i su ka fara bud'e masa ta ko ina, ga kuma addu'a da kullum ya ke samu daga matar shi da iyaye da yan uwa akan k'ok'arin da ya ke da kowa, sosai ya ke samun ci gaba ta fannin kasuwancin da ya saka a gaba, duk da su na d'an samun k'arancin lokacin juna hakan bai hana Khadija taya shi murnar samun ci gaban ba, dan ta lura mutum ne mai son samun na kan shi ba ya kuma buk'atar taimakon kowa, dan ita kan ta yawan kyautar da take wa yan uwan shi da iyayen shi lokuta da dama ya na nuna rashin jin dad'in shi, musamman idan Kabir ko Mannir ko Nura da ke k'arami su ka zo ya ga ta d'auki kud'i masu yawa ta basu wasu lokuta ma har da sabulan wanka da turaruka, sai yai ta fad'a wai ta lalata su har Kabir da ke da aure, ita kam tausayin shi take ganin koyarwa ce ya ke sai wata a baka, duk da ya na fad'a ba ta daina ba saboda a ganinta ita ta na da halin da za ta yi mu su tun da yan uwan mijin ta ne, sannan duk wata ita ma yan uwan ta su kan turo mata kud'i daga cikin ribar da ake samu na kud'in ta da suke juya mata, haka dai har lokacin hutunta ya k'are ta ci gaba da zuwa makarantar ta cikin kwanciyar hankali, duk da mijinta ba mazauni bane, amma ta na gamsuwa da kulawar da ya ke nuna mata.
*Wata biyu* da komawa makaranta Khadija ta kwanta rashin lafiyar da ta jijjigata sosai, dan sai da ta kwana hud'u asibiti ba ta cikin hayyacin ta, ta galabaita da mugun zazzab'i da ciwon kai, ga kuma ciwon ciki da ya murd'ata dole ta yi amai, allura kam tasha ta har ba adadi, haka K'arin ruwa har sai da hannayenta su ka kumbura saboda sukar da ya sha, duk da jikin ya yi dama amma sai da ta cika sati d'aya a asibiti kafin aka sallame ta, cikin ikon Allah kuma sai jiki ya yi kyau sosai, tun daga ranar kuma Khadija ba za tace ga ranar da ta sake kwantawa rashin lafiya ba, sai dai kawai abin da ba'a rasa ba irin su ciwon k'ugu, ciwon baya da d'aurewar mara, kullum Usman godiya ya ke wa Allah da Khadija da ta zama silar sauyawar rayuwar shi, bai tab'a tsammanin auren shi da ita abu neda zai kallo ba, duba da babu maganar soyayya tsakaninsu, sannan ita mai kud'i ce kuma matashiyar yarinya mai ji da kyau, amma ta aure shi babu kud'i babu kyau, kuma duk da haka ta zauna da shi da kyautatawa, wannan ya sa lokuta da dama ya kan fi kiran ta da Nana Khadija baiwar Allah, lokacin kuma arzik'i ya hab'ako sosai, sai kawai ya fara da iyayen shi ta hanyar canza mu su fasalin gida, in da ya gwangwaje su da bila (villa) mai kyau yar zamani, ya d'aukarwa mahaifiyar shi wacce za ta dinga girka mu su abinci sai dai su ci kawai, lokacin da cikin Khadija ya girma ne ya samu wani babban aiki, wata kwangila da aka mallaka mi shi milyoyin kud'i, a lokacin ne ya fara mu su sabon gini su ma, ginin da a lokacin ya amsa