Showing 120001 words to 123000 words out of 139085 words

Chapter 41 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

dai ba wata matsala tsakanin ta da Bilal, ya na zaune gefe ta na zaune ita ma sai dai su kalli juna, dan dama ba tace ya bar shi bane saboda ta na da wani nufi akan hakan, kawai ta fahimci ta b'ata mi shi rai ne jiya saboda abin da ta fad'a, ana hakane ta shiga madafa d'ora girkin rana, ba jimawa da fara aikin Bilal ya shigo da sallama, amsawa ta yi tace "Ya dai?"


Cikin ladabi yace "Aunty dama zanje gidan aboki na *Abdallah* yanzu zan dawo."


"To shikenan sai ka dawo, amma kar ka jima kuma uban ka ya dawo ya min tijara." Ta fad'a ta na ci gaba da aikin ta, da sauri ya fita ko amsa ta biyi ba, ashe Bilal moton shi ya d'auka ya fita da shi Haseenah ba ta ma sani ba, Rabe kuma tunda bai san ba'a barin shi fita da shi ba shima bai hana shi ba sai ma bin moton da kallo da ya yi har ya daina ganin Bilal kafin yace "Kai, Allah ka bamu kud'i mu ma muji dad'in rayuwa."


Wannan addu'a fa bana bari ta wuce ba ni kai na, dan haka na amsa da *ameen*, Bilal ya je gidan su Abdallah da babu nisa sosai da nan d'in, sunyi farin cikin ganin juna dan sun jima basu had'u ba, amm bai yarda ya jima ba ya mu su sallama ya juyo ya dawo, *tsautsayi fa ance idan ya wuni baya kwana*, rabon ayi Bilal su ka had'e shi da wani mai mota a lokacin da zai shigo kwana, mutanen dake wajen ne da su ka ankara wasu kuma akayi gaban idon su ya sa suka rabka salati tare da sallalami, tuni aka rufe wajen ana jimami tare da taimakawa Bilal da tuni baisan in da kan shi yake ba, a daidai lokacin motar Usman ta shigo layin, dan gaba d'aya hankalin shi ya kasa kwanciya, yanzun ma ya taho ne da nufi ya d'auke shi ya tafi da shi duk in da ya saka k'afar shi, ganin wannan taro yasan had'ari ne dan haka ya tsaya tunda dai a unguwar su ne abun ya faru, tashin hankali da ba'a saka mi shi rana, sai ga Usman ya ga Bilal hannun mutumin da ya bige shi jina-jina kamar babu rai a tare da shi, kallon shi ya kai kan moton shi daya wargaje abinka da dama roba tafi yawa a jiki, wani irin duka ne gaban shi ya fara yi yayin da zuciyar shi kamar za ta fito, a hankali ya ke kutsowa cikin mutanen wanda ke ta hayaniya kowa da abin da yake fad'a, wasu na fad'in sun san shi za su je su fad'a a gidan su, in da wasu suka dakatar da su da cewa kar aje babu namiji a gidan mata ba lallai su rik'e kan su ba idan su ka ji irin wannan labarin, hannu Usman ya zura ya karb'o Bilal daga hannun mutumin da ke kallon shi da mamaki, yana amsar shi wayar Bilal ta fad'o daga aljihun shi ta fad'i k'asa, d'aya daga cikin mutanen wurin ne yace "Mahaifin shi ne."


Motar shi mutumin ya bud'e da nufin a saka Bilal ciki amma sai Usman ya nufi tashi motar da shi, amma daga ganin yanda ya ke takawa jikin shi sai b'ari yake haka ma hannayen shi, dan yanda ya ke kallon Bilal baya jin zaiyi rai, sosai jikin shi ke rawa har ya na neman fad'uwa da Bilal d'in, da sauri wani mutum da shi ma anan unguwar yake ya karb'e shi a hannun shi ya na fad'in "Ayi hak'uri Alhaji, ayi hak'uri, insha Allahu zai tashi."


Zagayawa mutumin ya yi ya kwantar da Bilal sai Usman da ya shiga ya tayar da mota, wanda ya bige shi ne ya bi bayan shi har suka isa asibitin da tafi kusa da su, amma ganin halin da Bilal ke ciki ya sa suka tura su babban gida (HΓ΄pital), nan aka karb'e shi da taimakon ubangiji aka bashi taimakon daya dace.


Usman na zaune akan wani banci amma da simitin aka yi shi ya na tunani, shin dama Haseenah na da burin kashe ma sa d'an sa ne kome? Yanzu taya zan fara fad'awa Khadija maganar nan? Sai ta ga kamar da ni aka had'a baki ma aka cutar da shi, wata zuciyar ce tace mi shi, haba dai, ba ma za ta yi tunanin haka ba, nauyayyar ajiyar zuciyar da ya sauke ce ta sa wanda ya bankr Bilal d'in kallon shi, dafa kafad'ar shi ya yi yace "Dan Allah ka yi hak'uri, abun ya faru ne a bazata, bansan..."


Kallon shi ya yi yace "Ba komai malam, tsautsayi ne da baya wuce ranar shi, nima ina da abin hawan nan, kuma hakan na faruwa sosai."


Jinjina kai ya yi yace "Allah ya tashi kafad'un shi."


Da k'yar Usman ya iya cewa "Ameen." Likita ne ya fito daga d'akin ya na cire abin da ke rufe a hanci shi, hannu ya ba Usman da ya mik'e yace "Mu gode Allah, ya na samun lafiya in Allah ya yarda, ya na bacci yanzu."


Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah, nagode sosai likita, Allah ya saka da alkairi."


"Ba komai." Cewar likitan ya na shirin shiga ofishinshi, Usman d'in ne yace "Likita za mu iya ganin shi kuwa?"


Juyowa ya yi yace "Eh, za ku iya." Da sauri Usman ya nufi d'akin, Bilal ne kad'ai a ciki kwance jiki duk bandeji, k'arasawa su ka yi kusan shi suna kallon yanda Allah ya canza hallitar shi cikin k'ank'anin lokaci, mutumin ne ya mi shi sallama tare da cewa saiya dawo, ya na tafiya ya kira malam ya fad'a mi shi, zuwa bayan sallah azahar d'akin da Bilal ke ciki ya cika da yan uwa, sai dai wajen su Khadija har yanzu ba su san me ke faruwa ba, duk suna zaune jugum har yanzu Bilal bai farka ba wayar Usman ta shiga kururuwa, cikin sanyin jiki ya fito da ita ya duba, take gaban shi ya tsinke ya fad'i saboda ganin sunan *uwar yarima*, kallon Hajia ya yi da ke fuskantar shi, har wayar ta tsinke bai d'aga ba saida tace "Ka d'auka mana, wa ya ke kira ne?"


Cike da damuwa yace "Khadija ce." Malam ne yace "Ka d'auka mana sai ka fad'a mata wani abun, inyaso sai kaje gidan ka fad'a musu a nutse."


Khadija da ke tare da k'anwar Mama da kuma Kaltume zaune kasa hak'ura ta yi ta sake aika wani kiran, dan gabanta ne taji ya tsananta fad'uwa haka kawai, ta kira Bilal kuma ba ta samu ba shi ya sa ta kira Abban shi, d'auka ya yi cike da son b'oye halin da ake ciki yace "Uwar yarima ya ake ciki? Har kinyi kewata ko?"


Hajia dake kallon shi mik'ewa ta yi ta fita saboda kunya, inda Khadija ta amsa da "Na yi kewar ka mana, kai fa?"


"Kema kinsan na yu kewar ai, yanzu fad'a min kin shirya ne na zo na d'auke ki?"


Dariya ta yi tace "Haba dai, da rana haka patsal-patsal, ai ko zan shigo saida dare."


"Kamar wata marar gaskiya, to me ya sa?"


"Saboda lokacin da za'a kaini gidan ma da daddare aka kai ni, dan haka yanzu ma sai da dare zan koma."


Murmushi ya yi yace "To da da d'in da yanzu d'aya ne? A lokacin fa kina sabuwa ne fil a leda, yanzu kuma na bi ta ciki na fito, sannan Bilal ya fito ta nan ga kuma k'annan shi ma na shirin fitowa."


Duk da ya sassauta murya saida Hassana taji me ya fad'a, kallon shi ta yi ta kuma sunne kanta k'asa ta rufe baki cike da kunya, Khadija kam cewa ta yi "Matsala ta da kai fa kenan, yanzu dai ba wannan ba, ina yaro na yake? Ina kiran shi amma ba a samu."


Wani tsam yaji a jikin shi kafin ya daure yace "Bilal ya d'an fita tare da Murtala, mu na shago ne, watak'ila cajin wayar ne ya k'are, amma zan..." Kasa k'arasawa ya yi saboda rawar da muryar shi ke yi, da k'yar yace "Zan kira ki saina baki shi."


Ba tare da damuwa ba tace "Shikenan sai na jika, sai anjima."


Cike da zolaya yace "Au! dama muryar d'an ki kawai ki ka kira kiji? To ya yi kyau."


Dariya ta yi tace "To meye a muryar ta ka da za ta dame ni? Bayan anjima kad'an za mu kasance tare da kai."


Da haka sukayi sallama bai nuna mata komai ba, sai lokacin ne malam yace ya kamata su san halin da ake ciki, fita ya yi da niyyar zaije ya samu Ashir ya fad'a masa, hakan kuwa akayi dan ba jimawa ya isa in da Ashir ke harkokinshi, bayan sun gaisa ne ya fad'a masa abin da ke faruwa, ya jinjina al'amarin tare da tashin hankali, amma sai Usman yace "Idan dai har kai za ka d'aga hankalin ka to ya mahaifiyar shi kenan? Na zab'i na fad'a ma ka saboda ka san ta hanyr d za ka kwantar mata da hankali."


Shiru Ashir yayi kafin daga bisani yace "Hakane Usee, insha Allahu zan fad'a mata yanda za ta fahimta, kar ka damu."


Hannu ya bashi su ka yi sallama yace zai wuce gida ne, shi ma Ashir d'in gidan ya nufa daga nan dan fad'a musu, Mama ya fara fad'a ma tasan halin da ake ciki, ita kanta Mama da k'yar ta iya fad'awa Khadija, cikin tashin hankali tace Ashir ya kaita asibitin taga d'an ta, a hanya ma kuka take ta na fad'in kawai laifinta ne da ta yarda ta bashi yaron, Mama ce ta dinga tausarta da kalamai masu kwantar da hankali da k'arfafa gwiwa, suna isa asibitin aka nuna musu d'akin, da sallama su ka shiga amma Khadija na ganin Bilal kamar ba shi ba sai ta yi shiru, da k'yar ta isa ga gadon ta zauna ta na shafa fuskar shi, hawayen da suka taho mata ne ya sa malam cewa "A'a Khadija dan Allah, kar ki masa kuka mana, k'addara ce da kuma tsautsayi, ki masa addu'a Allah ya tashi kafad'un shi."


Hassana ce ta yi tsaye kanta tana shafa bayan ta tana bata hak'uri ita ma, sun jima a haka kafin ta kalli Nura tace "Har yanzu bai farka ba?"


Cikin sanyin jiki yace "Bai farka ba har yanzu, amma dai likitan yace an masa allura ne."


Cikin zubo da wasu hawayen tace "Ko dai ya mutu ne? Dan Allah ku fad'a min idan ya mutu, wallahi zan d'auki dangana."


Hajia ce tace "Haba Khadija, idan ya mutu za mu saka shi gaba ne haka, da ran shi mana gashi ma ya na numfashi."


Haka suka zauna jugum sai wasu dake tafiya wasu na zuwa, sai yamma kad'ai Bilal ya farka idon shi har sun kumbura, bud'ar bakin shi da "Mummy, Mummy." Ya fara, dama ta na kusa kam ta rik'o hannun shi tace "Gani nan Bilal, bud'a idon ka."


Bud'a ido ya yi ya kalle ta sosai, hawaye ne suka taho mi shi yace "Mummy ina Abba na?"


Saida ta mayar da na ta hawayen tace "Ya tafi gida yanzu zai dawo."


Da k'yar yace "Mummy, ciwo na, ki bani ruwa na sha." Ruwa ta d'auka ta bashi, komawa ya yi ya kwanta yanda ya ke har bacci ya sake d'aukar shi.


*B'angaren* Usman kuma tun a hanya yake tunani dama Haseenah ta shirya raba shi da yaron shi, in ba haka ba me ya sa ta hana shi ya fita da shi? Kawai makirci ne ta shirya mi shi dan ta raba shi da Bilal d'in shi, tunda ai tasan baya bari Bilal ya fita da moton shi, ko a k'afa bai cika son ana aikan shi ba wajen ti-ti, da wannan tunanin ya k'araso gida dan d'aukar mataki akan amarsu.


_Ita dama rayuwa haka take tafiya, ka shuka alkairi saika girbi alkairi, a baya mutane suna ganin laifin Khadija saboda makircin Haseenah, wanda ita Khadija a kan gaskiyarta take, yau kuma gashi Haseenah ita ma bata da niyyar cutar da Bilal, amma sakkayar Allah dama haka take, gashi ita ma yanzu za'a hukunta ta akan laifin da bata san hawa ba bata san sauka ba, Allah ka mana agaji da kan ka._


Haseenah da ke madafa a lokacin da waya a kunne ta kira Mariya ta na tambayar ko za ta zo? Cewar Mariya "Haseenah ba zan samu damar zuwa ba wallahi, saboda kwana biyun nan munyi hidimar biki, ko na tambayi Abban Fadila ma ba zai bar ni ba, amma ke ki zo ki kawo kud'in, idan na samu dama sai naje wajen malam d'in."


Cikin damuwa tace "Haba aunty Mariya, na fad'a mi ki fa halin da nake ciki, wallahi Usman ko magana ba ya son yi min, ina ga fa Khadija wani asiri ta masa ya juya min baya, kuma yace za ta dawo gidan, jiya ma kar ko so kiji maganar da ya fad'a min akan Bilal, to ina ga ta dawo gidan? Ai sai dai ya sake ni."


Mariya ce tace "To ya za ayi? Ni dai yanzu na fad'a mi ki uziri na ai, kinga kuwa dan na gyara aurenki ai bana b'algace nawa ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "To shikenan, bara ya shigo saina tambaye shi naji idan zai bar ni, ko zuwa gobe sai naje na kai mi ki kud'in, amma fa aunty Mariya wannan karan so na ke gaba d'aya a zautar da shi ya zama ba komai a gabansa sai ni, sannan ba shi kad'ai ba har iyayen shi da yan uwan shi ina so a rufe bakin su, su zama babu ruwansu da harkar shi bare har wani ya yi tunanin taimaka masa da ko da addu'a ce."


Da matuk'ar mamaki Mariya tace "Ke Haseenah, a ina ki ka koyi mugunta haka? Yaushe zuciyar ki ta zama marar imani haka? To kinga gaskiya no ba zan iya wannan aikin ba, dan in na biye mi ki mu ka yi haka to kashin mu zai bushe wallahi."


Cikin rashin nuna damuwa tace "Me ki ke nufi? Kamar ya banda imani?"


Muryar Usman ce ta bata amsa da "To ki na da shine imanin?"


Bata san lokacin da ta saki wayar ba ta juyo da k'arfi, hannu tasa ta rufe bakinta matuk'ar tsoro a fuskarta, tabb', lallai yanda ta ga alamunshi ta san yau babu tsumi ba dabara, amma duk da haka bara ta jaraba lallab'a shi ko Allah zaisa a dace, a cewar ta fa, durk'ushewa ta yi ta had'e hannayenta ta kalle shi tana hawaye tace "Dan Allah dan girman Allah Abban Bilal ka yi hak'uri, wallahi tallahi sharrin shaid'an ne da zugar aunty Mariya, ka yi hak'uri ka yafe min dan Allah ko dan cikin nan dake jiki na, wallahi na ma ka alk'awarin haka ba za ta sake faruwa ba."


Takowa ya yi har kusanta ya sa hannu ya kashe wutar gas d'in, tsayawa ya yi ya na k'are mata kallo, wai yarinyar da ya aura saboda nutsuwarta da hankalinta, ita ce ta yi sanadiyar faruwar abubuwa marasa dad'i irin haka a rayuwar shi, ita kam kallon da yake mata ne ya sa ta sake cewa "Dan Allah babban mutum ka yi hak'uri, wallahi ba laifi na bane, wall..."


Marin da ya zuba mata ne ya sa ta kwamtsa wata k'ara ta fad'i kwance, duk'awa ya yi ya d'ago ta cikin zafin rai ido jawur yace "Haseenah me nai mi ki a rayuwa? Me ya sa ki ka cutar dani? Me ya sa Haseenah?"


Cikin duburburcewa tace "Wallahi ba ni bace, ka yi hak'uri dan Allah, ba zan.." Shak'e mata wuyan da ya yi ne yasa komai nata tsayawa idon ta fitowa waje, cikin fitar hayyaci Usman ke fad'in "Haseenah ke annoba ce, jaraba ce kuma masifa ce ke da bala'i, barin irin ki a doron duniya wallahi japa'i ne, wallahi da zan kashe ki amma ba zan iya ba saboda cikin da ke jikin ki, Haseenah banga anfanin zama da ke ba a rayuwa ta, kin raba ni da hankali na da ubangiji na, kin raba ni da iyaye na da 'yan uwa na, kin raba ni da matar da nafi so a rayuwa ta, sannan kin raba ni da d'ana da ya fito daga ciki na, Haseenah ni kam ya zanyi dake? Wane irin hukuncin ma zan mi ki ne da zai sa na huce abin da ki ka min."


Haseenah dake ta fafutukar neman rayuwa ya na sakin ta ta samu ta sauke wasu numfarfashi, mik'ewa ya yi tsaye ya juya baya ya cire hular kan shi yana shafa sumar shi kamar zai cire kan, sake juyowa ya yi ya nuna ta da hannu yace "A dalilin ki yanzu haka Bilal na kwance asibiti, bansan ko zai rayu ba saboda yanda jikin shi yake, dan haka Haseenah ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kije gidanku kawai na sake ki saki biyu."


Wata k'ara Haseenah ta yi ta d'ora hannu akai tace "Ahhhhhhh, na shiga uku na lalace, dan Allah Usman ka rufa min asiri ka yi hak'uri ka yafe min, wallahi ba zan sake ba na rantse ma ka, ka taimaka min mana ka dubi cikin nan dake jikina, kar ka mayar dani bazawara tun yanzu Usman ko haihuwar fari banyi ba."


Girgiza kai yayi ya tab'e baki yace "Hum, ai ko meya faru ke kika jawa kan ki, dan haka ki tattara naki ya naki ki bar min gida na, idan ki ka bari na dawo gidan nan na same ki wallahi saina lahira ya fiki jin dad'i."


Yana fad'a ya fice daga madafar ya shiga b'angaren shi, rage kayan jikinshi ya yi ya shiga ya watsa ruwa saboda yaji sanyi, yana fitowa maganin ciwon kai yasha kafin ya canza kaya ya bar gidan ko kallon b'angaren Haseenah baiyi ba, a tunanin shi ma tana barin gidan zai ruguza wannan b'angaren dan ya zauna lafiya, dan ba zaisake bari zuciyarshi ta raya mi shi sake k'ara wani aure nan gaba, lokacin har an fara kiran sallah la'asar sai kawai ya tsaya ya yi sallah kafin ya isa asibiti.




*Ana tare*🀝
11/03/2020 Γ  19:36 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login