Showing 15001 words to 18000 words out of 139085 words
Chapter 6 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt
ai tsohon yayi ne, yanzu kuma na shigo gidan, dole za'a samu canje-canje da dama, daga yanzu in dai girki na ne gaskiya miji na zai ci abinci a nawa b'angaren ne ba na shi ba."
Juyawa ta yi har ta fara takawa Khadija ta gyara zama tace "Haseenah, nasan kinsan abinda ki ke shirin aikatawa kamar k'ok'arin rusa farin cikin gidan nan ne, dan haka kar ki ce za ki biyo min ta wannan hanyar, da ba zan d'auka ba, kin ganni nan? Wallahi ba na d'aukar raini ko rashin kunya, zaifi mi ki tun wuri ki fara taka tsantsan, abinci kuma ki d'auki kayan ki ba zan ci ba, ba kuma zan bawa yaro na ba, dan bansan me ki ka saka mana a ciki ba."
Wata dariya Haseenah ta yi tace "Ikon Allah na kwance ya fad'i, wato ke yanzu tunanin ki kenan? Nima zan yi abin da ke ki ke yi ne, hum! To ki farka, ni ba boka ba malam zan mallaki miji na, ke kuma da ki ke barbad'e a abinci sai ki yi ta yi, da sannu k'aryar ki za ta k'are a gidan nan."
Tsaye ta mik'e da mamaki a fuskar ta tace " Au! Kema tunanin ki kenan? Hhhhhhhh, lallai yarinya, in kuwa har wannan shine tunanin ki, to ki zanca tun wuri, dan wata rana zuciyar ki za ta iya raya mi ki kema ki bi boka da malam dan samun zuciyar babban mutum, kinga kuwa har abada ba za ki san sirri na ba."
Matsowa ta yi kusan ta dafa kafad'ar ta tace "Haseenah, ina kishin miji na, amma duk da haka bai sa na ji a raina cewa zan iya cutar da ke ba, ki kwantar da hankalin ki sannan ki nutsu, sannu a hankali sai kema ki ciri tuta a wajen mijin ki, ni zan taimaka mi ki kamar yer uwa ta."
Matsawa ta yi nesa da ita yace "Me? Taimako? Ki na kishiya ta za ki taimake ni dan na samu soyayyar mijin mu? Allah ya kiyaye, to me ki ka d'auke ni? Ban cika mace ba ko me? To ba na buk'ata, nasan hayoyin da zan shawo kan miji na, ba sai wani ya taimaka min ba."
Murmushi Khadija ta yi wanda har ya fito da haurun makkar ta guda biyu, Haseenah kam juyawa ta yi ta koma na ta falon ta zauna, ta na kallo Haseenah ta shigo da kwanon ta aje mata a kan teburin ta ta fice, tab'e baki ta yi tace "Ina daidai ke wallahi, sai dai duk abin da zai faru ya faru."
Ba jimawa kam sai ga Usman ya shigo, kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo da tunanin zai tarar da duka iyalin na shi anan, Khadija da ran ta ke b'ace kasa tashi ta yi ta tarbe shi kamar yanda ta saba, da gudu Bilal ya k'arasa ya rumgume shi, tare su ka k'araso wajen ta ya na fad'in "Yarima wa ya tab'a min mamanka ne haka?"
Hannu ya mik'awa Khadija alamar su yi musabaha, dan in Bilal na tare da su suna kiyayewa wajen tab'a juna tun da ba k'aramin yaro bane, hannun ta ba shi lokacin da ta ke kallon Bilal da shi ma ya ke kallon ta, murya k'asa k'asa yace "Ba komai Abba."
Zaune ya yi kusa da ita ya na kallon ta yace "Ba gaskiya ka fad'a ba yarima."
Kallon shi ta yi tace "Sannu da zuwa."
"Sannu da gida, ya kuka wuni?"
"Lafiya k'alau." Ta fad'a a tak'aice, dariya ya yi ya kalli Bilal yace "Ka gani ko? Na fad'a ma ka akwai wani abu, ba haka Khadija ta ke amsa min ba."
Murmushin yak'e ta yi tace "Kai ma kasan in dai ka na lafiya to mu ma mu kan kasance cikin k'oshin lafiya."
D'an juyawa ya yi yace "Ina amaryar ki ne ban ganta ba?"
D'an canza fuska ta yi tace "Ta na b'angaren ta mana."
Mik'ewa ya yi tare da kamo hannun ta da na Bilal yace "Muje to mu ci abinci ko, dan yunwa na ke ji sosai."
Fizge hannun ta ta yi tace "Kaje kawai ka ci, mu har munci abincin mu ai."
Da tsantsar mamaki ya ke kallon ta, amma sam ta k'i had'a ido da shi, hannun ta ya sake kamawa su ka nufi d'akin ta ya maida k'ofar ya rufe ya juya ya na kallon ta yace " Ina jinki, fad'a min me ya faru?"
Zaune ta yi akan gado tace "Ba komai."
Had'e fuska ya yi yace "Khadija kar ki min k'arya, gaskiyar abin da ya faru na ke so na ji."
"Nace ba komai ko, ba komai, kaje kawai ka ci abincin ka, ni da d'ana har munci."
Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kusa da ita yace "Khadija, wannan ba d'abi'ar ki ba ce, dan Allah kar auren da na yi ya sa ki canza daga yanda na sanki, kinji ko."
Shiru ta yi har sai da ya janyo ta ya na shirin kai bakin shi a nata ta yi saurin rufe bakin ta da hannun ta, wani tuhumammen kallo ya mata yace "Meye haka? Ba kya so ne?"
"Eh." Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, fizgo ta ya yi ta koma kan gadon da k'arfi, kafe ta ya yi da ido yace "Me ya sa?"
Juya mi shi baya ta yi, sake juyo da ita ya yi yace "Nace me ya sa ba kya so? Sai kin fad'a min dalili na rabu da ke."
Zuciya a wuya sai kawai Khadija ta fashe da kuka ta fad'a kan k'irjin shi, cikin kukan tausayi tace "Ba na so kawai, Abban Bilal ba na so ka na kusanto ni, haushin ka na ke ji Abban Bilal, na k'arar da rayuwa ta wajen killace ma ka kai na da mutunci na, amma kai a dare d'aya tak ka kusanci wata mace, zuciya ta bugawa take, ji na ke kamar zan mutu dan bak'in ciki wallahi."
Usman kam jikin shi ne ya yi sanyi sosai, tunawa da yanda auren su ma ya kasance, duk da kusan had'a su ne akayi amma ko sau d'aya duk da matsayin Khadija na mace, ba ta tab'a nuna ma sa k'iyayya ba ko a idon ta, amma yau gashi ta na fad'in ba ta son yana zuwa kusa da ita, a hankali ya d'ago ta ya share mata hayawen fuskar ta ya na girgiza mata kai, hannayen ta ya had'e ya rufe idon shi ba tare da ya had'a ido da ita ba yace "Ki yi hak'uri Khadija, ki gafarce ni idan hakan da na yi ya b'ata mi ki rai, har zuciya ta banyi haka dan muzguna mi ki ba, ba kuma na yi bane saboda wani kaso daga cikin kason da ki ke da shi a zuciya ta ya ragu ba, babban k'arfin gwiwa ta akan auren nan shine, Nana Khadija mai halin girma da hak'uri za ta taya ni kare hakk'in da ke kai na, sannan a lokacin da aka d'ora min nauyin Haseenah a kai na wallahi zuciya ta ta fad'a min cewa Khadija na tare da kai, da izinin ubangiji za ta taimaka maka wajen ganin ba ka k'untatawa yarinyar mutane ba, amma kash! Shed'an na ta k'ok'ari sai ya kutso cikin gida na ya tarwatsa min kan su, babban abun bak'in cikin shine, ya na so ne ya shigo ta hanyar mata ta Khadija abar so da k'auna ta kuma abar alfahari na."
Tafin hannun ta tasa ta goge hawayen, murmushi ta masa mai d'aukar hankali, matuk'a tasan mijin ta na son ta, kalaman shi kullum suna k'arfafa mata gwiwa da kuma sace mata gwiwa, ganin wannan murmushi ya sa ya kama kumatunta yana murmushi yace "Dariya a fuskar ki shine abin da Usman ke son gani a kullum, murmushin ki kuma shi ne silar nawa murmushin, ki ci gaba da murmushi irin haka har lokacin da zamu koma ga ubangijin mu."
K'asa ta yi da kan ta tace "Kalaman ka su na sani jin kunya."
Tallabo fuskar ta ya yi yace "Ke ce sarauniya, na baki zuciya, ke ce guda d'aya duniya ta masoya."
Yanda ya rera mata baitin ya sa ta sake fad'awa kan kirjin shi ta na murmushi, d'agota ya yi yace "To a bani sumbata kafin na fara zanga-zanga a gidan nan."
"Me ya yi zafi? Ba sai an kai ga haka ba, bani bakin ka nan."
Sai da su ka gama lobayyar su kad'ai su ka fito, Haseenah da ta ji shigowar shi ta gaji da jiran shigowar ta shi kasa jura ta yi, falon Khadija ta shigo sai Bilal kad'ai ta samu ya na karatun shi, tun ta na zaune har ta fara kai da kawowa tsakiyar falon kamar za ta had'e zuciya ta mutu, ta na jin bud'a k'ofar ta juya da k'arfi, taushe b'acin ran ta tayi ta tafi a guje dama ba nauyi ba kamar niπ, ai kuwa sai ta d'ane a jikin shi ta na fad'in "Rabin rai na, na yi kewar ka sosai, har zan fara kuka."
Bilal da Khadija kallon su suke da ido, a hankali ya d'ago ta daga jikin shi da nufin mata magana, sai kawai Haseenah ta fashe da kukan shagwab'a ta na fad'in "Wallahi da k'yar na iya riskar wannan daren saboda kewar ka, a gaskiya ba za ka sake bari na gidan nan ni kad'ai ba."
Sake fad'awa ta yi jikin shi, Khadija da ta ji wasu hawayen na neman taho mata ne ta juya ta kamo hannun Bilal su ka bar falon, lallab'a ta ya yi su ka koma na su falon, duk k'ok'ari Haseenah ta yi shi ta saka shi kalar nata farin ciki, wanka ta mi shi ta saka mi shi kaya marar nauyi, har uwar d'akin ta kai mi shi abinci a bakin gado ta aza akan k'aramar kujera, sam bai iya tuna su Khadija ba haka Haseenah ta dinga yanka masa loma ta na aika masa a baki ya na wucewa da ita ta mak'ogoro, ita kam dad'i ne ke kashe ta saboda ya na sake cin abincin da ta zuba garin maganin da malam ya bata, sai da ya k'oshi kad'ai ta bar shi ta ci nata a zuwan ta k'osar da wanda yafi mahimmanci a gare ta, falo ya koma ya na kallo ita kuma ta na d'aki ta d'auko garin maganin matan ta wanda sai za'a kwanta ake sha, duk da madara ta sha su kafin ta shiga ban d'aki ta sake zaunawa a cikin tafasashen ruwan bagaruwa, sai da su ka huce ta fito ta d'auki wani arnan magani na matsi emergency, k'anana ne fari kamar k'wayar magani, matsawa ta yi haka ma miski sannan ta fito ta saka kayan bacci ta shek'a kwalliya, minti sha biyar ta koma ta kama ruwa da ruwan zafi k'a'idar maganin kenan, fitowa ta yi cikin sand'a ta rufe mi shi ido ta baya, murmushi ya yi yace "K'amshin nan da na ke ji ya sa babu abin da na ke son gani sai ke."
Bud'e mi shi idon ta yi cikin karairaya ta dawo gaban shi, k'are mata kallo ya yi yace "Iyeh! Wow, wane irin kyau ne wannan? Tabarakalla ahsanul-kalik'ine, Allah abun godiya."
Janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi, k'amshin humrar ta ne ya tafi da imanin shi, tuni ya fara aika mata da wasu sak'onni wanda take ta ke karb'ar su, dan magungunan da tasha masu k'arfi ne sosai, da k'yar dai su ka iya kai kan su uwar d'aki su ka kashe wuta, surukina gyara kimtsi mana, ina fa taya 'yata kishi.π
Abunka ga ba saban ba, sosai Haseenah ta yabawa aya zak'inta, amma dai tun da taji Usman na gurnani ya na sambatu da surutai har ya na neman shid'ewa, hakan ya sa ta ji kwalliya ta biya kud'in sabulu, dama kuma *ado gwanja* yace "Rai ba'a bakin komai ya ke ba wajen biyan buk'ata."π
Haka dukansu su ka yi baccin gajiya rumgume da junan su, washe gari kam bai bari Haseenah ta shiga madafa ba, kuma ba ya so yace Khadija tayi, fita ya yi ya samo mu su soyayyen k'wai da dankalin turawa, ya na zuwa kuma ya samu Khadija har ta had'a abin karin da ta san d'an ta ya fi so, falon ta ya same ta suna karyawa da yaron ta, gaisawa su ka yi kafin yace "Yarima har ka shirya ne?"
"Eh Abba."
"To idan ka kammala sai ka fito mu wuce."
Kallon shi Bilal ya yi yace "Abba yau ina so na je da d'an moto na, kaga ba sai na jira ka je d'auka ta ba."
D'an b'ata rai ya yi yace "Kai Bilal, mahaukaci ne ni da zan barka ka tafi a hanyar ababen hawan nan kai kad'ai akan moton ka, bana so, kuma na fad'a maka hawan moton ka kar ya wuce cikin unguwar nan, duk da cazashi ne ake amma ba na so, kar kuma ka kuskura na gan ka ko a bakin titi ne, dan ran ka zai b'ace."
Mik'ewa Bilal ya yi ya matsa kusan shi yace "Ka yi hak'uri Abba, ba zan sake ba."
Kan shi kawai ya shafa bai ce komai ba, jakar shi ya d'auka mai d'auke da littafanshi yace "Na gama."
Kallon shi ya yi yace "Ka tabbata ka k'oshi?"
Kai kawai ya d'agaalamar Eh, hannun shi ya kama yace "To muje."
Juyowa ya yi ya d'agawa mahaifiyar shi hannu yace "Sai na dawo sarauniya."
Murmushi ta masa tace "Allah ya tsare, a kula sosai ka ji ko?"
Usman ma kallon ta ya yi yace "Ni ma na tafi ba zan dawo ba."
Ba alamar wasa a tare da ita tace "Sai na bika duk in da ka ke ai."
Dariya ya yi yace "Kar ki damu sarauniya zan dawo ai, ke ce fa."
"Ah to, sai na ma riske ka duk in da kaje." Ta fad'a ta na tashi dan had'a kayan da su ka karya.
*Kafin mu ci gaba, za mu waiwaiya baya mu ji yanda wannan soyayyar ta fara ta Khadija da Usman.*
_Sai mun had'u a shafi na gaba._β
10/01/2020 Γ 12:20 - πππ: ππππππππππ
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
ππππππππππ
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*9*
*Alhaji Ahmad*, dattijo mai dattako, mutum ne da Allah ya wadace shi da komai, dukiya, ilimi da 'ya'ya, matar shi d'aya *Hajia Sadiya*, suna zaune lafiya cikin farin ciki, mutum ne shi da bai da ra'ayin tara mata, hakan ya sa suke zaune daga Sadiya sai yayan ta, Allah ya azurta su da yaya maza guda biyar, *Ashir* shine babba, sai *Bashir* sai kuma *Habib* da *Mansur* da *Naseer*, Naseer na da shekara biyar aka samu cikin da ya wahalar da Sadiya, tun a lokacin su ke ji a jikin su cewa Allah zai musu sauyi ne, cikin ikon Allah kam bayan laulayin da ta sha sai gashi ta haifo kyakyawar yarinya mai kama da ita, *Nana Khadija*, yarinya ce da ta zama tamkar wata zinariya a cikin mutane, kowa soyayya ya ke nuna mata, lele kawai da gata take gani, su kan su yan uwanta suna matuk'ar k'aunar ta, dan har fad'a suke akan wanda ya fi sonta ko wanda zai d'auke ta, haka Khadija ta taso cikin gata da kulawar iyaye da yan uwa, sai dai tun da ta fara tafiya suka lura kamar tana da matsalar ido, basu b'ata lokaci ba wajen ziyartar likitoci, nan aka sanar da su tana da matsalar gani, bata iya gani da kyau sai dishi-dishi, sosai mahaifinta ya damu kuma yake yawon nema mata magani, amma sam ba'a dace ba har k'asar waje an fita da ita, haka dai suka hak'ura aka d'ora ta akan saka gilashi mai k'ara gani, wannan laurar sai tasa iyayenta da yan uwanta sake tausaya mata da k'ara k'aunar ta, sam larurarta bata tab'a damunta ba bare tasa damuwa, tana jin dad'in kasancewarta a yanda take, duba da wasu sam idon ne ma basa da su, tana da shekara *goma sha biyu* a duniya ranar wata alhamis da dare, suna zaune a farfajiyar gida su na ta hira Khadija na kan k'afafun mahaifin ta, da sauri ta juya ta kalli baban ta tace "Baba, ka ga wani ya shiga d'akin ka."
Da mamaki ya juya ya kalli k'ofar d'akin na shi ya gan shi rufe, murmushi ya yi ya kalle ta yace "Auta ni banga kowa ba, gashi ki na gani ma d'akin a rufe ya ke."
Naseer ne yace "Wallahi nima Baba sai na ga kamar giftawar mutum."
Sake juyawa ya yi ya kalli k'ofar yace "To wa zai shigo cikin gidan bayan ga k'ofar nan a gaban mu kuma ace ba mu ga shigowar shi ba."
Almajirinsu da ke zaune nesa da su ne ya na cin abinci ne yace "Baban Khadija wallahi nima na gan shi, wani dogo da fararen kaya, amma banga fuskar shi ba, kuma na so inyi magana saina kasa na ji tsoro."
_Wallahi wannan wani abun al'ajabi ne da ya faru da wata baiwar Allah da na sani, za mu iya cewa mala'ikan mutuwa ne_
Sadiya ce tace "Kai Ashir tashi ka duba mana."
Kallonta ya yi yace "Mama, ni kad'ai? Kawai ki bar shi idan ya ga ji zai fito ai mu gan shi."
Dariya aka saka sai Baba ne yace "Ki bar shi kawai, watak'ila fa gizo idon su ke musu, na ga ai ga k'ofar shigowa nan, babu wanda mu ka ga ya shigo."
Haka aka share wannan magana aka ci gaba da hira, Khadija ce bacci ya dauke ta a k'afafun shi, a hankali ya d'auke ta ya kai ta makwancin ta ya shafeta da addu'a, fitowa ya yi su Ashir ma har sun tashi, dawo da su ya yi suka zauna, ya jima ya na musu nasiha da su rik'e Khadija da kyau su zama gatanta ita kad'ai ce k'anwar su mace, har sha biyu na dare ta wuce kad'ai suka tashi, d'akin