Showing 102001 words to 105000 words out of 139085 words

Chapter 35 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt

shigowa, Bilal na ganin shi da gudu yaje ya rumgumr shi, Khadija ma na juyowa ta mik'e ta na dariya saboda farin cikin ganin shi ta na fad'in "...




*Addu'ar ku tamkar takobi ce a gare ni mafi kaifi a duniya, ina k'aunar ku masoya.*
25/02/2020 Γ  21:16 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘




_SAMIRA HAROUNA_




*Litattafan marubuciyar*




*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*


_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


```Fatan alkairi masoya```




_Bismillahir rahamanir rahim_




*32*




"Ango kai ne a gidan namu, lallai babban bak'o, amma dai da alama hanya ce ta d'auka ka ya sa ka biyo nan, ba dan haka ba ni dai na san ka da tsoron bayar da kud'in cefanai."


Dariya ake in da ta nufi falon Mama ta na fad'in "Bismillah Nura shigo." Bayan ta ya bi ya na rik'e da hannu Bilal, saida ya gaisa da mutanen da ke nan kafin ya k'arasa shiga ciki, zaune ya yi akan kujera ita ma ta zauna bayan ta aje ma sa ruwa da lemu, kallon ta ya yi yace "Ke haka ake sai ki tarfani a gaban manyan mutane, sai kisa su d'auka gaske ne abin da ki ka fad'a."


"Au! Ba gaske bane kenan? To ka na bayarwa ne? Yanzu fad'a min yaushe rabon da ka zo gidan nan?" Sosa kai ya yi yace "Gaskiya na kwana biyu, yanzu kuma da na samu labarin ki na nan wallahi kunya ce ta hanani zuwa."


Murmushi ta yi tace "Ba na son ku na fad'in haka wallahi, kenan idan k'addara tace za mu rabu da Usman ba da shi kad'ai zan rabu ba har da ku?"


"Ah haba dai, ai ba za mu tab'a bari ki fita a cikin dangin mu ba wallahi, ke fa alkairi ce a cikin mu, shima yasan da haka, wannan mai k'afafun angulun ce ta sauya mi shi tunanin shi."


Bilal ne ya bushe da dariya yace "Aunty amaryar ce haka?" Kallon Bilal ya yi ba alamar wasa yace "Kai k'yale shegiya mai suffar kwad'o, ai fata na ke Allah ya had'a ni da ita wata rana ta nuna min rashin kunya, wallahi ko kallon da raina bai so ba ta min sai na karya mata k'afa, yar banza hanci kamar bakin sahani (buta) amma sai iya shege a k'ugun ta."


Khadija in banda dariya ba abin da take kafin ta yi shiru tace "Kenan ni ma haka ka ke shammace ni bayan ido na?" Kallon ta ya yi yace "Ah haba dai, ke ai ko mutuwa ta na kunyar idon mahaifi, kin wuce nan wallahi."


Nan fa Nura ya kwashe duk abin da ya faru ya fad'awa Khadija tare da d'orawa da "Kin ganta fa da kod'add'iyar fuska kamar an tafasa kabewa, wai Alhaji ya na bacci, kuma lokacin tashin shi baiyi ba, sai dai ko za ka dawo wani lokaci, ke kinji bak'in cikin da ya taso min a lokacin, kamar na d'auki man da takr suyar da shi na bad'a mata a fuska ta k'arasa sulala."


Rik'e ciki Khadija ta yi tace "Dan Allah bar maganar nan kafin ciki na ya k'ulle, wallahi ba zan iya da masifar nan ta ka ba."


Gyara zaman sa ya yi ya saita nutsuwar sa yace "Kinga ba wannan ba, ni fa dama na zo ne na fad'a mi ki jibi za'a kai kaya na, kuma ke ce wacce na ke so ta shige gaba a komai, dan ni a wuri na kamar ke ce ki ka min auren nan wallahi."


"Ba damuwa Nura, insha Allah zan kasance a duk wata hidima ta auren ka." Sun jima su na hira cikin d'aki kafin ya tashi tafiya bayan ya mata alk'awarin kawo mata amaryar shi bayan an kai kaya, haka ya tafi ya bar Khadija da Bilal da dariya duk sanda su ka tuna iskancin da ya sokawa Haseenah.


Da yamma Usman da kan shi yaje ya d'auko Aziza ya kawota gidan, suna zuwa sun tarar da Mubarak ya kawowa Haseenah maganin ta, Mariya kuma dama maganin mata ne da take anfani da shi ta bado a kawo mata, d'ayan tace ta had'a da madara tasha zai k'ara mata haiba ne da kwarjini a wajen shi, d'aya kuma tace ta binne a cikin gidan, hakan zaisa Khadija ko ta dawo ba za ta iya zama ba saita koma, dan ta k'ara rubtawa da ita kuma tace kafin ta binne ta samu takardar da alk'alami ta rubuta sunan Khadija akai,πŸ˜‚ *yaro man kaza*, Mubarak na tafiya bayan Usman ya gwangwaje shi da kud'i wai ya sa mai a moto, a lokacin anata kiran sallah magriba, Aziza ma alwala ta yi ta kabbara sallah hakan ya bawa Haseenah damar fitowa da maganin ta je wajen wata pliwa mai kyau mai bayar da sanyi wacce ke kusada panpon dake farfajiyar gida, nan ta durk'usa ta sa wuk'a ta tona rame ta binne ledar maganin, duk abinda take a idon mai gadi da yake fitowa daga ban d'aki da buta a hannu ya na kurkure baki, da sauri ya sake komawa ban d'akin ya na lek'owa dan tabbatar da abin da ya ke gani, ya na kallo har ta tashi ta koma d'aki ta yi alwala ta yi sallah, mai gadi ma alwala ya yi a gaggauce ya wuce masallaci, bayan magriba Usman ya shigo saboda zaije ganin Bilal, tun a bakin k'ofa mai gadi ya tsayar da shi ya fad'a mi shi fa da matsala a gidan nan, ya ga wani abun da bai yarda da shi ba, Usman da ya nuna kamar bai yarda ba sai ya ja shi har in da aka binne abun ya kuma sa hannun shi ya tone ya nuna mi shi, warware takardar ya yi duk da baisan me aka rubuta ba, nunawa Usman ya yi yace "Kune yan boko, ko za ka iya gane me aka rubuta anan?"


Da wani yamutsa fuska yace "khadija aka rubuta, sai me?"


Abu dai ya tumbatsa hakan ya sa Usman k'walla kiran Haseenah yace ta zo, nan ta same su tsaye gaban ta na tsananta bugawa tace "Gani."


Nuna mata takardar ya yi da ramin yace "Ke ki ka aje abin nan a ciki?" Da mamaki ta kalle shi tace "Ni kuma? Inji wa?"


Nuna mata mai gadi ya yi, nan fa Haseenah ta shiga rantsuwa ba ita bace Garba ma ya rantse yace da idon shi ya gani, k'arshe dai makirci ne ya yi aiki saboda kuwa kuka Haseenah ta saka ta na fad'in dama kowa ba k'aunarta ya ke ba, kowa bayan Khadija yake kuma ana d'ora mata laifin fitar Khadija daga gidan, dan haka ita ma barin gidan za ta yi in ya so saiya zauna shi kad'ai, hakan zai sa ba za'a zargi kowa ba, haba wa ai sai hankalin maza ya watse ya rasa nutsuwarsa amarsu tace za ta tafi, take a wajen yace mai gadi ya bar mi shi gida tunda dai shima ba k'aunar shi yake ba kuma munafiki ne, sam Garba baiji wani zafin korarshi da akayi ba, dan ya na da yak'inin akwai abin da ke damun ogan shi, dan haka ya kalli Haseenah yace "Kibi a sannu duniya ce ba matabbata ba, tabbas ni ina b'angaren Hajia uwar yarima, kuma wallahi d'an halak ne ni, dan haka zan mata hallaci a lokacin da babu wanda ya yi tsammani."


Juyawa ya yi ya bar gidan bayan ya tattare nashi ya nashi, shi kuma ciki suka shiga saida ya k'ara rarrashin ta ya nuna mata babu fa wanda ya isa ya b'ata ran ta kuma ya yi shiru, saida ya ga murmushin ta kad'ai ya shirya ya kama hanya, anyi sallah isha'i kenan ba jimawa Usman ya zo, k'ofa ya aje mota ya sallamo farfajiyar, yara ne ke ta wasa abinsu kasancewar gobe ba makaranta kamar sallah ce a gurin su, yaran na ganinshi su ka rumtuma wajen shi su ka rufe shi suna gaishe shi, farar ledar hannun shi ya fito da ita ya bawa kowa rabon sa mai alawa da mai chocolat, bawa Bilal sauran ya yi ya shafa kan shi yace "Kawunan ka na nan?"


"Kawu Ashir da kawu Habeeb ne su ka shigo, kuma su na b'angaren su." Wata ajiyar zuciya ya sauke dan ba ya son ganin su ko kad'an, cikin rad'a yace "Hajia fa?" Nuna masa ya yi yace "Ta na falon ta."


Hannun shi ya kama yace "To muje ka rakani na gaishe ta saina koma, sauri na ke." Falon Hajia su ka nufa da sallama su ka shiga ta amsa ta mu su izinin shigowa, zaune ta ke kan kujera cikin riga da zani mai kama da siket, kallo d'aya Usman ya mata ya d'auke kan shi saboda kwarjinin da matar ke ma sa baya iya had'a ido da ita a baya ma bare yanzu da ya san shi mai laifi ne, duk da dai dattakon matar na birge shi matuk'a, dan mace ce mai kamar maza wacce kusan gaba d'aya tarbiyar yaran ita ce ta yi ta, a kunyace su ka gaisa ita kam ganin haka ya sa ta saki fuska sosai fiye da ma farko su na gaisawa, mik'ewa ya yi cike da kunya ya na fad'in "To Hajia ni zan koma, dama ina sauri ne nace dai bara na biyo."


Gyara zama ta yi tace "Maman shi ai ta na ciki, ka wuce ku gaisa sai ka wuce ko." Da wutsiyar ido ya d'an saci kallon ta ya na sosa kai, kama hannun shi Bilal ya yi sai cukuikuyeshi ya ke, kallon shi Mama ta yi ta harare shi tace "Kai dallah miye haka malam sai wani cakumar shi ka ke kamar wani wutsiyar shi, dawo nan ka zauna har ya fito."


Ta nuna mi shi kusa da ita, mak'ale kafad'a ya yi yace "Wai ke ina ruwan ki, ba Abba na bane, karfa ki ga idon Abba na ki b'ata min rai, sai na ce na fasa dawo da ke d'akin ki."


Rufe baki Mama ta yi tace "Ka ji masharranci kuma, to yaushe ka kore ni da har yanzu ba ka dawo dani ba?"


Dariya Bilal ya yi yace "Ka ji ko tsohuwar nan, wato so ki ke Abba ya bani hak'uri na dawo da ke, to na k'i d'in sai kinyi sati d'aya babu kud'in cefanai."


Usman da ke dariya shi dai cewa ya yi "Ka na manta wani abu yarima, na fad'a ma ka kafin ma Mama ta san da kai mu ta fara haihuwa, shin ka na ganin duk yawan mu za mu iya barin ta da yunwa? Abu ne da ba zai yiwu ba ai."


"Ah to fad'a mi shi dai, kuma da ka gan shi nan cika bakin ne kawai, gishiri wannan na dala biyar bai tab'a bayarwa aka siya ba, watak'ila ma ko sabon bebe da zai zo yanzu na yi miji idan na ga ya fika k'ok'arin cefanai."


Dariya Bilal ya yi yace "To ai dai sai na sake ki sannan za ki koma gare shi, kuma idan fa aka haifo min mace ya za ki yi?"


Shiru kawai Mama ta yi sai murmushi da take ta na kallon shi, gwalo ya mata yace "Yeeeehooo, na rufe mata baki, ai ba'a aure akan aure, kuma nasan ke kishi ya mi ki yawa."


Sai lokacin Usman ya juya ya nufi d'akin Khadija, Bilal kuma zaune ya yi kusan Mama ya d'ora kan shi akan k'irjin ta, ture shi ta yi tace "Kai d'aga min nono malam, k'walelen kare da hantar kura fa, tom."


Saida ya sa hannu ya tab'a nonon yace "To me zanyi da wannan tsohon nono, abin duk ya yamutse, ga na Mummy ta nan sabo dal a leda."


Bushewa su ka yi da dariya dukansu ta janyo shi jikin shi su ka rumgume juna, tabbas kamar yanda ta ke matuk'ar k'aunar Khadija matsayin ta na mace, haka a cikin jikokin ta ma take matuk'ar k'aunar Bilal saboda wayon shi, yaro ne mai shiga rai dan shi ko irin mahaukaciyar k'uruciyar nan baiyi ba, hasalima cikin yara za ka ga shi wasan shi ta dabance, sannan bai cika son hayaniya ba kuma baida yawon surutu, idan kaji bakinshi cacaca to sun had'u ita da shi ne.


Tun kafin Usman ya shiga ya ke tunanin abin da suka fad'a na maganar bΓ©bΓ© da haihuwa, me su ke nufi? Khadija ciki gare ta kenan? Dama k'ofar a bud'e ta ke dan haka k'arasa tura ta kawai ya yi ya shiga, zaune take akan gado da littafin *hisnul muslum* ta na karantawa, ta na kallon shi ta d'auke kai ta mayar kan littafin tace "Me ya sa ba za ka nemi izini ba kafin ka shigo?"


Saida ya k'arasa shigowa har ya zo daf da gadon yace "Saboda da kai da kaya duk mallakar wuya ne."


Kallon shi ta yi fuska ba annuri tace "Kan na iya zama na ka amma banda kayan saman shi."


Murmushi kawai ya yi yace "Haka ake tarban bak'o a garin ku?"


"Duk bak'on zai iya shiga kowane lungu da sak'o na gida ba bak'o bane, musamman ma irin ka da ba sa neman izini kafin su shiga, kuma ina da tabbaci ba waje na ka zo ba, dan haka me zai sa na damu kai na?"


Kafe ta ya yo da ido ya na kallo kamar ya na karatun wani abu, jin shirun ya yi yawa ne ya sa tace "Bilal fa ya na farfajiyar gida."


"Na gan shi ai." Kallon shi ta yi tace "Hajia kuma ai ta na falo." Saida ya zura hannayen shi aljihu yace "Ita ma mun gaisa."


Mayar da hankalin ta tayi kan littafin ta tace "Da kyau." Ci gaba ta yi da karatun ta shi kuma yace "Ya beby ya ke?"


Cak ta tsaya amma ba ta kalle shi ba sai rarraba ido da ta fara yi, tambayar da take wa kan ta ita ce ya aka yi ya sani? Dan ba ta san Mama ta je ta fad'awa su Hajia ba, rasa abin fad'a ya sa Usman zaune kusan ta ya na k'are mata kallo yace "Kenan da gaske ne? To amma me ya sa ba'a fad'a min ba?"


Kallon shi ta yi cikin dagiya tace "Waya fad'a ma ka ina da ciki? Ko kuma ka na so ka b'ata min rai ne?"


"Ban gane ba? Bayan da kunnuwa na naji Mama ta na fad'a, gashi kuma na tambaye ki amma duk alamu sun nuna gaskiya ne."


Murmushi ta yi tace "Ka taya ni addu'a Allah ya bani nawa nima, amma yanzu ai amaryar ka ce ke da shi, duk da ka ce ina mata bak'in ciki."




Kafe ta ya yi da ido yace "Ki rantse da Allah ba kya da ciki." Cikin mamaki tace "Rantsuwa kuma? To miye na rantsuwar? Abin da na ke nema ido bud'e zan samu kuma na kasa fad'a ma ka."


"Ba ki ke nema ba dai, mu ke nema, kar ki manta da haka, har yanzu ina son sake ganin abin da zai fito daga tsatsonki." Kallon shi kawai ta yi shi kuma ya mik'e yace "Kin dai tabbatar ba ki da komai?"


"Eh." Ta fad'a, sake jajjadawa ya yi "Kin tabbatar babu?" Cikin k'osawa tace "To! Na ce babu, babu, idan ba ka yarda ba ka je ka tambayi su Maman ka ji, su a zatonsu ne ciki gare ni saboda rashin lafiyar da na yi, ni kuma wahala ce ta sani wannan rashin lafiyar na dukan da ka min."


Murmushin gefen labb'a kawai ya yi ya sunkuyo da kan shi kusan fuskar ta yace "Kin tabbatar dai ba kya tare da ciki na ko?"


K'asa ta sauke idon ta hakan ya sa yace "Sai kin kalli ido na." Kallon shi kam ta yi tace "Eh, babu komai." Tsaye ya mik'e yace "Shikenan, amma ki tabbatar duk ranar da na ji labari yasha bambam wallahi sai kin gane kurenki."


Saida ta sake kallon idon shi tace "Na yarda." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan, saida safe."


Juyawa ya yi ya fice daga d'akin ta bishi da kallo, saida ta tabbatar ya bar gidan ta fito ta samu Mama ta tambaye ta, ba ta b'oye mata komai ba hakan ya sa tace dan Allah kar su sake ya san ta na da ciki, dalili Mama ta tambaya saita nuna mata kawai ba ta so ya sani yanzu, dan ta na tsoron rashin imanin yarinyar nan matar shi.




*Bayan kwana biyu* an kai kayan Nura, kuma kamar yanda ya fad'a Khadija ma saida ta halarci kai kayan, kuma da yake a dangi ma ba kowa bane yasan abin da ya faru, Haseenah dama ba ta je ba dan haka ma ba su had'u ba, anje lafiya kuma ayi duk abin da ya dace, lokaci kawai za'a jira *wata uku* mai zuwa lokacin hutun farko na yan makaranta, duk lokacin da biki ya taso irin haka akwai wanda Khadija ce ta ke mu su d'inkin anko, yanzun ma ba ta gaza ba ba ta kuma duba abin da ya faru ba, haka ta d'inka kaya kala takwas ta aikawa kowa na shi daga ciki har da Hajia da kuma k'annan ta guda uku, k'annan Baban Usman biyu sai wasu tsofaffi biyu suma, kamar yanda Nura ya yi alk'awari ya kawo Choukra ta wuni gidan su Khadija, sai dare ya zo ya d'auke ta su ka koma bayan tasha goma ta arzik'i.


*Haka* abubuwan suka ci gaba da tafiya da dad'i ba dad'i, Khadija na kula da cikin ta cikin kulawa sosai, Bilal na karatun shi hankali kwance ba tare da matsala ba, ranar da babu karatu kuma Khadija na kiran Nura ya zo ya d'auke shi ya kai shi wajen su Hajia, amma basu tab'a katarin had'uwa da mahaifin shi saboda yanzu gida sai su yi sati kwana shida ko biyar basu gan shi da idon su ba, wayar ma sai da k'yar ake iya samun shi wani lokacin, kuma har yanzu bai san Khadija na da ciki ba, dan malam yace ba ya so ya sani sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login