Showing 51001 words to 54000 words out of 139085 words
Chapter 18 - KALLON KITSE Book Complete Document by Halima k Mashi .txt
ta nufi ban d'aki ta na juya mazaunai da gayya, lumshe ido ya yi ya d'an cije lab'en k'asa ya bita da kallo, ta na shigewa ya matsa bakin k'ofar yace "Ni zan wuce sai da safe, ki kula min da kan ki dan Allah."
Shiru ta yi har ya fice daga d'akin, ta na jin ya fita ta fito dan dama ba komai ta ke yi ba, kashe wuta ta yi ta zauna bakin gadon ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin ta cire gilashin ta ta kwanta abin ta.
**************
Bilal na zaune tare da duka iyayen shi yan uwan mahaifiyar shi da kuma kakar shi, dan har yanzu ba su daina had'uwa a falon mahaifiyar su ba suna hira, hira ce ta yi hira har ta sa Bilal fad'a mu su fad'an da mahaifiyar shi ta yi da kuma auntyn shi, rashin jin dad'in abun ya sa Naseer cewa "Ni wallahi dama nasan sai anyi haka, dan tun ranar da suka samu sab'anin nan nasan yarinyar nan ba ta da kunya, in ba rainin hankali ba taya za ki bud'e baki ki ce wai ina anfanin yaro a cikin gidan uban sa? Wallahi ta yi wasa ni sai na ci uban wanda ya d'aure mata gindi ma."
Mama ce ta katse shi da cewa "Kamar ya ka ci uban ta? Matar mutane za ka daka har gidan ta? To ba na son sake ji daga yau, ku na so ace ku na taya 'yer uwar ku kishi ne?"
Naseer d'in ne dai ya d'ora da "Hajia ba ki san me ta ke mata bane, ranar fa har kuka ta saka ta da hawaye, ce mata ta yi wai makauniya, ki ji fa Hajia, ni tunda na ke ban tab'a jin wanda ya kira ta da makauniya ba."
Ashir ne yace "Makauniya fa? Khadijar ce makauniya?"
"Wallahi haka ta fad'a mata shegiyar figaggiya."
Habeeb da Bilal ke kwance kan k'afafun shi ne yace "Wallahi ni tun ran kan amarya da na ga idon yarinyar nan a tsaye da kuma k'awayen ta masu ido tsakar ka nasan dama za ayi haka, amma dai ta kiyaye b'atawa auta rai, dan ba lallai mu d'auka ba."
Bashi ne ya karb'e da "Ba maganar ba lallai bane, magana ce ta ba zamu d'auka ba ko kad'an, wallahi ba za ta shiga gidan ta ba kuma ta nemi ta raina ta, dan haka dole Usman ya sake zagewa wajen tsayawa akan gidan shi, in ba haka ba kuma to zamu ziga ta ta dinga jibgar ta mu kuma a shirye mu ke da mu tsaya mata a kowace kotun duniya."
Tsaki Mama ta yi ta mik'e ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Saida safen ku, tunda naga dukan ku babu mai hankalin da zaiyi magana ta hankali har kai da ke babba a ciki."
Nan ta bar su suka ci gaba da tattaunawa akan al'amarin gidan da kuma 'yer uwar su, bacci Bilal ya yi Habeeb ya kwantar da shi kafin suma su ka nufi wajen na su matan tare da tattara k'ananan yaran su da su ke tare da su anan.
*****************
Washe gari ma Haseenah ce ta shirya abin karin kummalo, Usman da kan shi ya zo ya kira ta dan su ci tare amma tace wallahi ba za ta je ba, tunda dai har ta nuna abata kwanaki ita ma ta ci amarcin ta to ta bata, su biyu kad'ai su ka karya haka da rana ma da ta gama girkin aikowa ya yi aka d'aukar ma sa, tun k'arfe uku na rana Khadija ta shiga madafa ita da Uwani da wasu matasan 'yan mata biyu yaran mak'wabtan su, hakan ya sa gidan ya kaure kamar su na aikin wata hidima, kowa da abin da ya ke yi, Haseenah na iya hangen su ta k'ofa sai tsaki take da hararn su, cikin hukuncin ubangiji sai gashi zuwa k'arfe shida sun kammala komai sun gyara wurin kamar ba su yi aiki ba, a falon shi ma gyara su ka shiga yi in da Khadija ta sa suka gyara zaman komai da ke d'akin zuwa wata kusurwar ta daban, amma uwar d'akin shi da kan ta ta shiga ta yi gyaran, koda aka fara kiran sallah tuni har sun kammala musamman da ya zama akwai masu kamawa, ko da su ka yi sallah duka yaran abinci ta zuba mu su suka ci su ka k'oshi, sannan ta had'a su da kyautar turare wai su shafa tunda yan mata ne, har Uwani ma ba ta bari ba sai da ta mata, haka yaran su ka tafi bayan ta had'a su da jikka jikka, hakan ya sa duk abin da suke in dai ta tura a kira su to ko ba su yi niyyar tahowa ba iyayen za su ce su zo, saboda irin alherin da ta ke mu su, su na tafiya ta shiga uwar d'akin ta ita ma ta d'auko wasu robobi da blanda (blander) ta zauna gaban frigo (fridge).
_Kankana ta d'auko wacce ta gyara ta da kyau ta zuba a blandar ta markad'a, wata k'aramar rariya ta sa ta taceta tare da rage wata a cikin wani kofi sannan ta d'auki dabinon da ta jik'a shi da ruwan rake tare da kanunfari ta zuba, shi ma markad'awa ta yi sannan ta tace shi cikin ruwan kankanar, madara peak ta d'auka ta juye a cikin had'in sannan ta d'auki gwangwanin maltina ta juye a ciki shi ma, ta na gama had'awa ta d'auki zuma cokali d'aya ta zuba a ciki, cikin frigon ta aje robar dan ya yi sanyi kafin ta shirya._
_Wani babban kofi ta d'auka ta d'auko ayaba manya guda biyu ta fereta ta yanka a cikin kofin k'anana k'anana, saida ta gama sannan ta zuba madara peak a ciki, kafin ta d'auko wata roba mai d'auke da garin aya ta zuba a ciki cokali uku, sannan ta d'auki wata robar ta bud'e ta zuba garin dabino shi ma cokali uku, juyawa ta yi sosai ya had'e jikin shi sannan ta d'auki kofin ta kafa kai ta shanye, wannan kankanar da ta rage a kofi ta d'auka ta zuba zuma a ciki tare dafasa k'wai d'aya ta kad'a shi sosai sannan ta shanye._
Tashi ta yi ta d'auki komai ta mayar a wajen shi sannan ta dawo gaban fridge d'in ta bud'a, wani kofi ta d'auka wanda dama kullum ya na ciki da karanfani a ciki, ruwan ta shanye wanda su ka jik'a sosai da kanunfari sannan ta rufe ta shiga wanka, da k'yar ta samu ta tsarkake gaban ta saboda ruwan da su ke fitowa, ta na gamawa ta d'auro akwala, ko da ta fito sallah ta fara kabbarawa har ta ida kafin ta zauna gaban madubi, ta jima ta na shafawa ta na gogewa, kwalliya dai ba wata abu ba kam ta yi ta sosai, ta na kammalawa ta mik'e tsaye ta bud'a wata drower ta d'auko wani turare da ba kullum take aiki da shi ba sai Usman ya na gari, a cibiyar ta ta fara fesawa kafin ta fesa a mara, sai bayan kunnuwan ta da wuya da kuma tsakiyar nonuwan ta, haka ma hammata sannan ta fesa a hannu ta shafa a mazaunai, rufewa ta yi ta aje kafin ta d'auko kaya ta saka, wata arniyar doguwar rigar shadda ce ta saka kai kace d'aurin auren shugaban k'asar garin su ne za ta je, wasu masifaffun takalma ta d'auka masu shegen tsini ta saka sannan ta d'auko kallabin kayan wanda dama ta sa aka d'aura mata shi musamman dan wannan ranar, wani siririn gilashi fari k'al ta sanya ta kalli kanta a madubi, murmushi ta sakarwa kan ta kafin ta dawo ta d'auki had'in ta da ta aje dan ya yi rab'a, kafa kai ta yi bata kuma aje ba sai da ta shanye duka sannan, komawa ta yi gaban madubi ta d'auki turaren ta na yau da kullum da har ya zama jikin ta, feshe kayan ta yi da shi sosai take ta sake d'aukar wani halataccen k'amshi mai kashe jiki, cikin takon isa da k'asaita ta fito daga falon, ta na shirin yin zaune a kujera ta ji mai gadi na wangale k'ofa, murmushi ta yi ta aje wayar ta ta juya ta fita, tsinin takalmanta ya sa dole take tafiyar a hankali mai d'aukar hankali, Usman da ya bud'e k'ofa zai fito ya hangota kasa fita ya yi, zuro k'afa ya yi ya na k'are mata kallo har ta tsaya gaban shi, kallon da ya ke mata ne ya tabbatar mata da wani abu ya ke rayawa a ran shi, saida ta sake narkar da ido tace "Wannan kallon fa?"
Ba tare da ya daina mata wannan kallon ba ya sauke ajiyar zuciya, ganin baice komai ba ya sa ta kamo hannun shi har ya fito ta rufe motar ta kalle shi tace "Sannu da zuwa my *Exelency*."
Murmushi kawai ya yi baice komai ba, matsowa ta yi daf da shi ta shafa fuskar shi tace "Da alama my *world* duk ka wahalar min da kan ka, yanzu muje ciki na baka agajin gaggawa."
Hannun shi ta ja su ka yi ciki shi dai kamar sakarai, sai a uwar d'akin shi suka yada zango, kayan ta fara cire mi shi ta na fad'in "My *sweet angel* ya kasa min magana saboda ya na kallo na kamar wata bak'uwa a gare shi yau, amma ba komai girmanka ne ai."
Za ta sunkuya dan cire mi shi wando ya rik'o ta, wani irin kallo ya watso mata yace "Gaba d'aya na rasa kuzari na, ban san me zan fad'a ba."
Ita mayar masa da kallon ta yi tace "Kar ka damu, zan dawo ma ka da wutar ka." Ta k'arashe da kanne ma sa ido d'aya da d'ata bakin ta har ya yi k'ara, janshi ta yi zuwa ban d'aki har ya shiga ciki, ruwa ta sakar ma sa kafin ta shafa k'irjin shi tace " *My Mine* kasan me zai faru? Yanzu ka fara wankan ina zuwa yanzun nan."
Ba ta jira me zai ce ba ta fice daga d'akin gaba d'aya, kai tsaye madafa ta nufa ta samu ruwan zafi ta saka na'ana'a a ciki tare da cinta d'anya da ganyen lipton, suna dahuwa ta tace a kofi mai kyau sannan ta zuba zuma cokali biyu, ta juyo za ta fita kenan Haseenah ta shigo ciki, kallon kallo su ka yi in da Haseenah ke mamakin irin arniyar kwalliyar da Khadija ta yi kamar za ta biki, ita kuma ta na mamakin abin da ya shigo da ita madafar yanzu, har za ta fita sai kuma ta tsaya tace "Wani abu ki ke buk'ata ne?"
Cike da gatsali tace "Eh, na zo na dafa indomie ne."
Cike da rashin nuna damuwa Khadija tace "Ayya! Ki bari ya fito daga wanka mana sai mu ci abinci, ai yanzu ya shigo bai jima ba."
"A'a nagode." Ta fad'a kai tsaye ta k'arasa shiga madafar, tab'e baki ta yi ta fita ta bar ta, ta na zuwa ta samu ya na ciki bai fito ba, cire takalmin ta yi da d'aurin d'an kwalin ta ta shiga ciki, ba tare da sanin ta shigo ba ta karb'i sabulun hannun shi ta fara goga mi shi a baya, juyowa ya yi ya na ganin ta ya fizgo ta ta fad'a jikin shi, dariya ta yi ta rufe ido saboda ruwan da suka zuba jikin ta, had'e ta ya yi sosai da jikin shi ya cire gilashin ta ya aje gefe, haka ma doguwar rigar cire ta ya yi ya jefar, a tak'aice dai tare su ka yi wankan su ka fito, da gaggawa ta d'auki kofin shayin da ta had'o mi shi ta ba shi ya shanye, cikin sauri su ka shirya su ka fito, ita tebur ta nufa shi kuma ya wuce d'akin Haseenah dan ya kira ta, ya na zuwa ya same ta ta kasa cin indomien da ta dafa saboda rashin dad'i, nan ya lallab'o ta suka fito falon a tare, cike da mamaki ta k'araso ta zauna ta na kallon Khadija ta gefen ido saboda ganin ta canza kayan jikin ta babu kwalliya a fuskar ta, a ran ta kam cewa ta yi "Hum! A nunawa shege shegentaka, wato ki nuna min wani abu ya faru har kinyi wanka, to mu zuba zuwa ni da ke."
Baki Haseenah ta saki ganin abinci har kala kusan hud'u saboda kawai aci yanzu, tunda su ka fara ci take kallon Usman yanda a ke cin abincin, kenan ita ce ya raina ko? Ta tambayi kan ta, Khadija kam daga k'asa take wasa da k'afafun ta ta na shafar Usman da su har su ka kammala, saida ya ma Haseenah saida safe kafin ya dawo d'akin shi, a lokacin Khadija na d'akin ta ta na kama ruwa da ruwan kanunfarin da ta tafasa, saida ta k'ara shfa turare ta yi sassauk'an kwalliya ta saka rigar bacci, doguwar abaya ta d'ora sama sannan ta nufi d'akin.
Kwance ya ke akan gado babu riga a jikin shi ya rufe ido kamar mai bacci, har ta shigo ta rufe k'ofar ta kashe hasken d'akin ta maye gurbin shi da siririn haske bai bud'a ido ba, cire rigar ta yi ta baccin ta bayyana, kallon shi ta yi har yanzu ido rufe tace " *Mon ange*, ka bud'e idon ka mana."
Bud'ewa ya yi tare da sakin murmushi, ganin yar rigar dake jikin ta ya sa shi waro ido yace "Wayyo Allah, zo Khadija, zo gare ni dan Allah."
Cikin salo da k'warewa ta haura kan gadon ta fad'a jikin shi, rumgume shi ta yi amma saiya k'ara matse ta sosai yace "Ki rik'e ni sosai Khadija."
*To kowa dai ya san me zai faru, dan haka babu kyau shiga rayuwar ma'aurata.*
Haseenah da kishi ya hanata bacci ta kasa samun sukuni, gagara bacci ta yi in da shed'an ke zugata ya na hura mata wutar k'iyayya, a k'arshe ji tayi kawai bara ta lek'a ta ji me ke faru a d'akin, cikin sand'a ta fito ta tsaya k'ofar d'akin ta na saurare, sambatu da surutan da take ji ne su ka sake d'ugunzuma mata tunani, irin yanda taji muryar Usman ya tabbatar mata da kuka ya ke tsabar dad'in abin da ya ke ji, musamman da ya ke fad'in kar ta kashe shi ta yi hak'uri ya bata komai da ya mallaka, ba ta yi bacci ba a daren ko kad'an in da masoyan kam suka kwana k'wak'ume da juna cikin farin ciki, tabbas Usman ya sake yarda aure kawai muk'addari ne daga Allah, amma ba dan haka ba babu abin da zai sa shi k'ara aure ya na da kamar Khadija, da haka asuba ta yi su ka tashi sallah.
*A gurguje*
Haka rayuwar gidan Usman ke tafiya da dad'i wasu lokutan kuma sai a sannu, sai dai yanzu Haseenah ta d'an shiga taitayin ta ba ta cika shiga harkar Khadija ba bare har ta fad'a mata magana, Khadija kuma dama rayuwar ta take yi babu ruwanta da ita, Bilal ma na wajen kakanin shi hankali kwance ya na zuwa islamiyyar shi, ranar talata da yamma Khadija ta saki aiki Haseenah ta kama, sosai Usman ya yarda Khadija ita ce ta san shi farin sani, bayan kwana biyu ita ma ta saki aiki a ranar alhamis ta saki aiki Khadija ta kama, a ranar kuma ta kama ranar sunan matar Issoufou, tunda rana Usman yace su tafi tare tunda Khadija na da mota, sannan ta san gidan sab'anin Haseenah da zuwan ta d'aya kuma cikin dare.
Tun Khadija na jiran ta kammala aiki su tafi dan ta samu ita ma ta dawo ta kama na ta aikin har ta gaji da jira, ganin ba kowa a gidan da zata aika ya sa ta sallama da kan ta har falon ta, Haseenah da ke uwar d'aka kwance ta amsa sallamar tare da fitowa, ta na ganin Khadija ta ja birki k'ofar d'akin ta na k'are mata kallo, da mamaki Khadija ta kalle ta ganin ko wanka ma ba ta yi ba, cikin dakiya tace "Wai Haseenah ba ki shirya bane?"
A kasalance ta amsa da "Ban shirya ba."
Jin ba ta sake cewa komai ba ya sa tace "To dan Allah ki gaggauta ki shirya mu wuce, wallahi ba dan ke ba ma ni ban tab'a kai wannan lokacin ba ban fita ba, musamman da nasan zanyi aiki."
"To." Haseenah ta fad'a ta juya kawai ta koma ciki, Khadija na ganin haka ta fito ta na mita, a k'alla ta sake b'ata minti talatin ba Haseenah ba labarin ta, ran ta ne ya kai matuk'a wajen b'aci kawai ta d'auki jakar ta ta fita, Haseenah na jin fitar Khadija ta fito ta rufe d'aki dan dama ta shirya tunda ta mata magana, kawai ba ta yi ra'ayin fitowa da wuri bane, har farfajiyar gidan ta fito ta samu mai gadi tace "Wai har ta tafi ne?"
Cikin girmamawa yace "Yanzun nan kam ta fita, dan ga motar can ko titi ba ta hau ba."
Wayar ta ta ciro cikin jaka ta dannawa Usman kira, ya na d'auka ta fad'a mi shi ya zo ya d'auke ta Khadija ta tafiyar ta, da mamaki yace "Wai dama har yanzu ba ki fita daga gidan ba?"
Cikin turo baki tace "Na shirya fa na ke ta jira aunty Khadija ta min magana, tunda ai ba zuwa zanyi ba na tisa ta a gaba har sai ta gama shirin ta, ina falo kawai sai fitar ta na ji."
Ba dan ya yarda da abin da ta fad'a ba yace ta jira shi ya zo ya d'auke ta, dan in dai Khadija za ta fita to bata kaiwa warhaka bata fita ba saboda taje ta dawo da wuri ta kama aikin gaban ta, hanya ya d'auko dan ya zo ya d'aukar ta ya kira Khadija a waya, bayan ta d'auka ne yace "K'anwar ki ta kira ni tace wai kin tafi kin barta, shine na ce ya akayi haka ta faru?"
Khadija da ke tuk'i ne tace "Ba ta fad'a ma ka na kai mak'ura bane wajen jiran ta? Ko kuma kawai ta fad'a ma ka abin da